 Lilisco da Zulai
Auren Ban Mamaki
"Tun da na tashi a unguwar nan, ban taba ganin daurin auren da ya yi armashin wannan ba!" WANI dattijo ne aka ji ya ambaci haka a cikin taron daurin auren fitaccen dan wasan fim kuma gwanin koyar da rawa, wato Idris Shu'aibu (Lilisco) da fitacciyar jarumar finafinai, Zulai Dalhat. An dai daura auren ne a gidan iyayen amaryar wanda ke kan titin Bida a cikin garin Kaduna, a ranar Asabar, 13 ga Disamba, 2003 da misalin karfe 2:30 na rana. Daurin aure ne wanda ya burge mahalartansa, ya ba da mamaki, har ya sa wasu matasa (maza da mata) suka rika cewa, "Da ma a ce mu ne!"
Cikakken labari
Tsigai: Ina Ta Fito, Ina Za Ta?
A DAWO LAFIYA: Tsigai a cikin motarta
|
HAJIYA HUSSAINA GOMBE (TSIGAI) tana daga cikin manyan 'yan wasan fim na Hausa wadanda da jibin goshinsu aka kwaba bulullukan da aka gina harkar da su. Kamar yadda muka sha gaya muku a hirarrakinmu da ita a baya, ta fi yin fice ne a finafinan Ibro, koda yake ta yi wasa a wasu finafinan kamar "Dan'adam Butulu" da "Darasi." To, an dan jima ba a ji duriyarta a wannan mujallar ba, ga shi kuwa al'amura da dama sun wakana daga lokacin da kuka karanta hirarta da ta gabata zuwa yau din nan. Harka dai ta yi kasa, kuma akwai abubuwan da su kansu jama'a suke son su sani game da ita Tsigai. Misali, me ya sa har yanzu guguwar aure da ke ta kadawa ba ta wuce da ita ba? Mecece babbar nasararta a sana'ar fim? Da gaske ne cewa yaron nan mai suna Salisu dan'uwanta ne kamar yadda wasu ke cewa ko kuwa danta ne ko kuma dai kawai dauko shi riko ta yi? Me za ta ce kan irin kallon da wasu mutane ke yi wa 'yan fim? Wadannan tambayoyin, da ma wasu, su ne wakilinmu na Jihar Kano, SANI MOHAMMED MAIKATANGA, ya yi wa Hussaina kwanan baya lokacin da suka tattauna a Kano. Hirar ta bayyana mana inda Tsigai ta fito a wannan harka, da kuma inda ta dosa. A sha karatu lafiya.
Cikakkiyar hirar
Mudassir Ya Yi Amarya
Mudassir da Amaryarsa Zainab
|
FITACCEN dan wasa kuma furodusan nan Mudassiru Haladu yayi aure a ranar Lahadi, 7 ga Disamba, 2003. An daura aurensa da masoyiyarsa Zainab Sani Darma. Tun da farko mahalarta daurin auren sun hallara a gidan Sharif Musa a unguwar Hanga kusa da makarantar Malam Mamman, daga nan suka nufi wurin da aka daura auren, wato gidan Alhaji Ibrahm Maigoro Agadasawa.
Ga cikakken labarin
Ali Nuhu ya janyo sabuwar muhawara? Duk yarinyar da ta rasa miji, to ta zo industiri mu tallata ta ta samu, inji shi
Ali Nuhu da A'isha B. Umar suna cashewa a wurin piknik
| HAKIKA, kowa ya san irin cece-ku-cen da ake yi a kan 'yan fim, musamman mata. Kusan gani ake yi duk yarinyar da ta shiga harkar fim, to sallamammiya ce daga gidansu. Da yawa 'yan fim suna ganin tsangwamar da ake yi musu kusan nema ake a dake su, tamkar su suka kirkiro duk wani iskanci da ake yi. To sai dai wani abin mamaki shi ne, duk da irin kyamar da ake yi musu, wadda har ta hada da ko aure kake nema, sai a ce ba za a ba ka ba, wai don kawai kana fim. Amma da wuya ka ga an yi bikin da yake yin armashi kamar na 'yan fim din.
Cikakken labarin
Burina in yi kida ba a Kano kawai ba - ADAM USER
Adam User a bakin aiki
|
ADAM User yana daga cikin manyan makadan wakokin finafinan Hausa a wannan zamanin. Yana aikinsa ne a fitaccen situdiyon nan mai suna 'Sulpha Musical Studio' da ke Zoo Road, Kano. Hasali ma dai wasu na kiransa 'A kori-Aleebaba', ba don komai ba sai don nuna amincewea da kwarewarsa.
Ga cikakken labarin
SAI NA KASHE IBRAHIM SHEME, inji Sulaiman Sa'eed
GASKIYAR maganar da Hausawa kan yi da suka ce "baki shi ke yanka wuya" ta fito fili kwanan nan a Kano. A Litinin, 1 ga Disamba, 2003, mawallafin mujallun Fim da Bidiyo, Ibrahim Sheme, ya je ofishin fitaccen dan wasa kuma daraktan nan Aminu A. Shariff (momo) da ke rukunin shagunan SHY Shopping Complex, Gadon Kaya, don yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa. A wannan lokaci, mawallafin yana tare da wakilin mujallar Fim na Kano, wato Sani Mohammed Maitanga.
Ga cikakken labarin
|