Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
RAHOTO


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection


An ba Zik kashi a kan hakkinsa!

Dukan jarumi Zik a kasuwa sabon salo ne a tsamar furodusoshi da dillalai

Daga MUHAMMED NASIR da SANI MAIKATANGA a Kano

GOGAN naku, Malam Zurke, ya yi wani hasashe a Fim ta watan jiya, inda ya ce: "...Bayan dukan Ibro da aka yi na kanga kunne a industiri in ji kuma wa za su buga. Tunda dai har Ibro ya bugu ba a yi komai ba, to na san babu wanda zai fi karfin bugu a cikin 'yan fim. Na sa kunne in ji idan za a gamu da Mandawari ko Ali Nuhu ko ..., a fizo shi daga cikin mota a bakin randabawul, a "hora" shi. Ko kuma a gamu da Biba a kan mashin, ko Saima ko Mutu-Ka-Raba, a zane ta a kan laifin rawa da waka da ta yi a fim din... Ka san idan an doki wadannan manyan, to don su wance 'yan ku-ci-ku-ba-mu kuwa ai idan aka doke su ko labarin ma ba za ka gani a mujalla ba..."

Shin ko Zurke ya san kwafsawar da za a yi ne a ranar 22 ga Fabrairu, 2003 har ya fadi haka? A'a, bai sani ba, arashi ne kawai. A wannan ranar dai an sami sabanin da ya kai ga yin kazamin fada tsakamin mataimakin shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano kuma fitaccen dan wasa Zulkifilu Muhammad (Zik) da kuma mataimakin shugaba na daya na kungiyar masu sayar da kaset na bidiyo da rikoda ta Jihar Kano, Alhaji Isma'ila T.M. A cewar majiyar mujallar Fim, fadan ya samo asali ne lokacin da Zik ya ga fosta ta fim dinsa a mai suna Na'am a kantin Isma'ila inda ya yi zargin Ism'aila da laifin buga fostar ba tare da masaniyarsa ba. Wasu wadanda aka yi abin kan idonsu sun bayyana wa Fim cewa fadan ya kazance ne yayin da Zik ya rutsa Isma'ila ya rika zunduma masa zagi. Jama'a da yawa a cikin Kasuwar Kofar Wambai sun taru domin su bai wa Zik hakuri amma abin ya ci tura. Wani mai suna Ibrahim Yayo, wanda kuma yana cikin masu rabon fada. Ibrahim ya ce, "Ban san yadda abin ya faru ba, amma na ga Zik yana kai ma Isma'ila duka, daga nan sai muka shiga tsakani". Amma ya tabbatar da cewa shi da ya je rabo, sai da aka yi wa rigarsa fata-fata. Dalili shi ne, Zik ya zarge shi da goya wa Isma'il baya. Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa wasu samari ne suka yi wa Zik dukan da har sai da ya kai kasa. "Zik ya tsaya a kofar kantin Isma'ila yana zage-zage, aka rasa mai matsawa kusa da shi, sai wani matashi ya je ya tsaya a gabansa, ya gantsara masa zagi kuma ya kai masa naushi a fuska. Daga nan sai aka rufe shi da duka", cewar wani wanda aka yi abin a kan idons.

Ya zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari, jami'an tsaro sun damke wasu mutane biyu da ake tuhuma da laifin dukan Zik. Duk kokarin da aka yi na ganin abokan fadan biyu ya ci tura. Wakilinmu ya je kantin Isma'ila inda aka yi arangamar amma ya sami kantin a kulle. Ta sami bayanin cewa babu wanda ya san inda Isma'ila yake. Yaran da ke tsaron kantin kuwa sun kulle sun gudu ne don sun ga su Zik sun shigo kasuwa (kwana daya da yin fadan) tare da 'yan sanda da wani soja don a kara kama mutane.

Wannan mujallar ta tuntubi shugaban kungiyar furodusoshin, Alhaji Ibrahim Mandawari, wanda ya tabbatar da aukuwar abin. Shugaban bai yi wani Karin bayani ba domin, kamar yadda ya ce, maganar na neman komawa kotu. Ya tabbatar da cewa kungiyarsu za ta yi taron gaggawa kan wannan abu da ya sami mataimakin shugabanta.

Da ma can baya sau da yawa an sha zargin Isma'ila T.M. da laifin buga fostar finafinai a boye ba tare da sanin furodusa ba yana sayarwa ga masu sayar da kaset na wakokin finafinan Hausa. Ko shekarar da ta gabata, idan ba a manta ba, aikin da sabuwar kungiyar furodusoshin jihar ta fara yi jim kadan da rantsar da ita, shi ne na mika Isma'ila ga hukuma kan zarginsa da suka yi na buga fostar finafinai ba bisa ka'ida ba.

Kamar yadda aka sani can baya, mafi yawan kantunan sayar da kaset na rikoda a Kasuwar Kofar Wambai suna sayar da kaset na mawaka daban-daban na Hausa, Indiya da ma wasu wakokin, yanzu duk wakokin finafinan Hausa suka fi sayarwa. Kantin Alhaji Isma'ila TM kuwa, duk cike yake dan da fosta iri daban-daban kama daga ta Shata, Dankwairo da duk wani mawakin Hausa, ta malamai, Indiya, finafinan Hausa, mawakan Sudan... kai, da duk fostar kaset na wani mawakin da wakarsa ta sami gindin zama a cikin kunnen Bahaushe.

Isma'ila ne ya ce su kashe ni Inji Zik

Daga WAKILINMU a Kano

Fim: Zik, da farko za mu so mu ji yadda wannan rigima taku ta faru.

ZIK: (bayan ya yi bismillah) Wato a ranar Jumma'a, 21 ga Fabrairu, na je wurin Alhaji Nasiru Charanchi don in amshi kudade na finaifinaina da nake binsa bashi. Ina zuwa bayan na amshi abin da zan amsa, sai na ce don Allah ya ba ni fostar fim dina Na'am kwaya biyar saboda zan yi kyauta da su. Sai ya ce a'a, ai idan na ga wani abu, ba zan ji dadi ba. Sai na ce a ba ni, me zai faru? Ya ce, "A'a, a dai bar maganar a haka". To ina shiga shagonsa kawai sai na ga dauri guda na Na'am. Na ce, "Ina ake samowa? Da ma can kwanan baya ya fada min cewa an fara buga min fostana, ya kamata in san abin da zan yi. Sai na ce bari in je kantin (Isma'ila) in gani. Ina zuwa shagon (na Isma'ila) na ce, "Akwai Na'am?" Suka ce, "Ba Na'am." Da ma tare da Aminu Kwai-A-Baka muka tafi. Sai na ce a kira shi Isma'ila. Aka kira shi, ya zo. Na ce, "Sama'ila, me ya sa kake buga min fosta dina?"

Ya ce, "Yo rashin kunya ka zo ka yi min?"

Na ce, "Ya a kan hakkina za ka ce zan yi maka rashin kunya?"

Sai ya ce in fita in ba shi wuri. Ban ankara ba sai ga yaransa sun fara taruwa. Sai na ga an turo ni waje. Wadansu suka fara dukana. Wannan ya kawo duka in kare ta nan wancan ya kawo duka. To gaskiya har sai ta kai ma ban san wa ke rabon fada ba, wa kuma ke kai min duka ba.

Fim: Cewa aka yi kai ka fara kai wa Sama'ila duka. Shin da gaske ne?

ZIK: Maganar ni na fara kai duka ma ba ta taso ba; su ne suka zo suka hankado ni ta baya, saboda a lokacin an cika gaban shagon.

Fim: An ce har da makami a wurin fadan naku. Gaskiya ne?

ZIK: Nan ma maganar makami ai ba ta taso ba, saboda a lokacin 'yar-shara ce a jikina. Kuma lokacin da na je ban yi tsammanin hakan zai faru ba, don watakila da na yi shiri.

Fim: To an ji maka ciwo a jikinka?

ZIK: E. Yanzu idan ka kalli wuyana za ka ga alamun yanka ga shi nan. Sa'annan ga hannuna za ka ga tabo (rauni). A lebena ma ga tsagewa nan. Ga kuma idona ya kumbura har ya fara yin ja. Ga kuma kirjina har sai da muka je asibiti aka yi min X-ray.

Fim: Da wane irin makami suka ji maka ciwo?

ZIK: Ba wani makami; kawai tarar min suka yi. Kuma ta ko'ina duka suke kawowa.

Fim: Wane asibiti ka je?

ZIK: Asibitin Murtala, tare da polis, aka rubuta magunguna, wadanda har yanzu ga su nan a aljihuna.

Fim: Su yaran da ka ce sun dake ka, shin ubangidansu ne ya umurce su ko kuwa fushi ne suka yi da fushin wani?

ZIK: Ai shi (Isma'ila) ne ma ya zo ya shake ni ta baya. Sa'annan ina ta kici-kicin kwacewa, har na je kasa. Suna kawo min duka, yana cewa, "Ku kashe shi!"

Fim: To Zik akwai wani uzuri da akan danganta da abokin fadan naka a duk lokacin da aka yi rikici da shi. Shin kai ma ka yarda da uzurin?

ZIK: E, to gaskiya ni abin da na dauke shi mutum ne mai hankali saboda yana neman kudi kuma da ba shi da hankali da ba zai buya ya gudu ba. Ka ga yana da hankali kenan. Ai da ko don saboda gadara sai ya zauna. Amma sai ya rufe shagunansa suka gudu. Sai yaransa guda biyu kacal aka samu, su ma suna hannun 'yansanda. Duk sauran sun gudu.

Fim: Za ka je kotu?

ZIK: Gaskiya abin yana hannun 'yansanda. Idan ta kama a je kotu, sai a je kotu. Saboda wannan abu ya faru a kaina, nan gaba ba a san wanda za a yi wa irin wannan ba. Zik kenan aka yi wa a matsayina na Mataimakin Shugaban Kungiyar Furodusoshi Jihar Kano, furodusa, kuma darakta. Ina a ce wani karami ne fa? Ni ma fa kenan - mai karfin karewa; duk da irin dukan da suke yi min ana rabawa na mike.

To ina ga wanda bai kai karfin haka ba?

'Za mu dauki matakai'

An dade ana tsama tsakanin furodusoshi da dillalan kaset na bidiyo da na rikoda. Rikicin ya ta'allaka ne a kan cutar da furodusoshi ke ganin 'yan kasuwa na yi masu, ya-Allah wajen kin biyansu kudin jaket da wuri ko biya gutsin-gutsin, ko kin buga fim lokacin da ake bukatarsa (ga 'yan bidiyo kenan) ko kuma satar basira ta fuskar buga jaket din kaset din rikoda na wakokin finafnai ba bisa ka'ida ba ko kin biyan hakdin furodusoshi da sauransu (ga 'yan audio kenan). Yayin da duk wannan ke gudana, kungiyar furodusoshi ta zura ido kawai ana yi wa 'ya'yanta hawan kawara. Sau da yawa duk wani yunkuri da ta yi na kawo karshin abin yakan ci tura. A baya, ta taba kwafsawa da Isma'ila T.M., amma abin ya wuce. To yanzu ga sabuwar rigima ta taso.

Alhaji Baba Shariff ne Sakataren Kungiyar Furodusoshin Jihar Kano ('Kano State Filmmakers Association'). A wannan hirar da ya yi da wakilinmu ya fadi matsayin kungiyarsa a kan wannan al'amarin, tare da shan alwashin cewa daga yanzu za a ga canji a mu'amalar furodusoshi da 'yan kasuwar kaset, musamman na rikoda. Ga bayanansa kamar haka:

Wannan rigima ba da Zik da Sama'ila ake yin ta kadai ba. Ana yin ta ne da Sama'ila da sauran duk wani mai shirya fim a Kano. Abin mamaki shi ne, babu wani dan kasuwa da yake goyon bayan Sama'ila lokacin wannan rigima. Kowa cewa yake yi, "Bai kyauta ba, Sama'ila ne ke karya harkar kasuwancinmu". Saboda haka babu wata matsala tsakaninmu da masu sayar da kaset. Masu sayar da na bidiyo ai ba su yi mana irin wannan.

Masu sayar da na wakar rikoda ne ke yi mana, su ma wasu tsiraru ne ke yi. Su kansu sauran ba su goyi bayansa ba. Kuma duk wanda ya ce maka Isma'ila ba shi da hankali, wallahi karya yake yi. Mahaukaci ya san ya sa sutura mai kyau? Mahaukaci ya san ya hau abin hawa mai kyau? Mahaukaci ya san ya yi salla kan lokaci? Mahaukaci ya san ya bude shaguna barkatai har ana yi masa bizines kala-kala? Har ya san ya karbi kudadensa? Babu wani abu da zai nuna cewa shi mahaukaci ne. Kuma wancan lokacin da muka yi kes da shi a State CID, ai ba a nuna wata shaidar rashin lafiya kansa ba.

Za mu yi taro kan wannan, kuma doka ba kan Sama'ila kadai za ta tsaya ba, har da kanana cima-zaune wadanda ke zaluntarmu, misali, masu yin selection na audio (masu hada dadaddun wakoki daga finafinai daban-daban suna sayarwa). Ko a cikin kasuwa suke, ko masu turawa a kan kekuna ne suna sayarwa a cikin gari da kuma masu buga takardu da masu satar fasaharmu ta CD. Mu yanzu kan-mai-uwa-da-wabi kawai, mun fito duk yadda za mu yi mu kwaci 'yancinmu sai mun yi. Mun fito, duk wanda ya ce mana kulle, mun ce cas!

Wai Kabir Nadakila ya kuturce?

Daga BASHIR YAHUZA, a Katsina

A SAKAMAKON jita-jitar da ta yi ta bazuwa a Katsina kamar wutardaji da bazara cewa wai fitaccen dan wasan nan na barkwanci, Kabir Abba, wanda aka fi sani da sunan Nadakila, ya zama kuturu na gaskiya, shi ya sanya wakilinmu ya tuntube shi domin gano gaskiyar haka.

Shi dai Nadakila, fitaccen dan wasa ne a birnin Katsina, musamman ma ga masu nacin kallon tashar talbijin ta KTRTV, sun fi saninsa da wannan suna Nadakila a shirin barkwancin da tashar ke watsawa mai suna "Nayalli". Dan wasan yana fitowa ne a matsayin kuturu, duk kuwa da cewa yatsunsa garas suke. A zahiri kuma shi jami'in kula da lafiyar hakora ne, inda yake aiki a Babban Asibitin Katsina. Ya shaida wa wakilinmu cewa ya fara shirin Nadakila ne tun a 1992 a gidan talbijin na Katsina. Kuma ya fito a finafinai da dama, wadanda yawancinsu ba su shiga kasuwa ba. Amma ga wadanda suka kalli fim din Amana wanda 'Damaga Motion Pictures,' Katsina, suka fitar a 2002 sun ga kuturu Kabir Nadakila cikinsa. Haka kuma a fim din da zai fito na kungiyar 'yan wasan kwaikwayo ta Jihar Katsina, mai suna In Rana Ta fito…, nan ma dai a kuturun ya fito da sunan Nadakila.

To me ya kawo ka-ce-na-ce game da dumin da ke bazuwa cewa wai Nadakila ya kuturce? Wasu ma tuni suke rika cewa wai kutaren Katsina ne suka yi masa sammu don yana kwaikwayonsu, shi ya sanya shi ma a yanzu wai ya zama kuturu. Wasu kuwa har gidansa suke zuwa don ganin kwaf, wadanda suka san yana aiki a Asibiti kuma har can suke zuwa domin su karas. Dalili kenan wakilinmu ya gana da shi, inda suka tattauna a shagon sayar da kaset din bidiyo na Salamah da ke Sabon Layi Katsina. Wakilinmu dai ya gan shi da nadin bandeji a babban yatsansa na hannun hagu. Da ya tambaye shi me ya yi zafi haka? Shin da gasken ya kuturce? Shi kuwa ya labarta duk mafarin wannan jita-jita.

Ya ce ba zai manta da wannan rana ba, ranar 1 ga Janairu, 2003 ne ya hau babur dinsa zuwa wani shagon sayar da kayan gyaran babura da ke Tsohuwar Kasuwa a birnin na Dikko, da nufin ya sawo kebur na burki. Da ya sano kebur din sai ya nada shi a hannunsa na hagu, ya tuko babur din zuwa wajen mai gyara. Ya ci gaba da cewa inda tsautsayin ya rutsa da shi shi ne daidai wata makarantar firamare, inda bai ankara ba, ashe wayar kebur din nan ta dan warware har ta shiga cikin sufuroket na babur din. Nan take kebur din ya zarge masa babban dan yatsa na hayu, kuma ya tsinke gaba daya ta yatsan. Jini ya kwarara, aka kai shi asibiti, aka yi masa magani. Wato kenan hadari ne ya samu, ba cutar kuturta ba ce ta same shi. Ya ce yatsunsa duk garas suke, sai wannan daya ne kawai ya guntule da gaba daya, kuma ya kusa warkewa.

Wakilinmu ya tambaye shi, me zai ce game da yadda yake kwaikwayon kutare da wasanninsa, ko yanzu zai daina yin haka? Nadakila ya ce ai wasan kwaikwayo kamar ma yanzu ya fara. Don haka ba zai daina ba, har sai abin da Allah ya yi gaba.

A cewarsa, a sanadiyyar wasan kwaikwayo ya samu daukaka, ya samu farin jinin jama'a. Domin an fi saninsa a dan wasan kwaikwayo fiye da yadda aka san shi a matsayin malamin asibiti.

Da aka tambaye shi shin ko ya taba samun sabani da kutare a sanadiyyar kwaikwayonsu da yake yi, sai Nadakila ya ce: "Sam sam, ni ban taba sabani da su ba, hasali ma na samu kusanci na mutunci da su. Domin a sanadiyyar wasannina, sai da Sarkin Musakai na Katsina ya gano ni, duk ranar Jumma'a yana kawo mani ziyarar bara, kuma ina ba shi sadaka daidai gwargwado."

To me zai ce game da wadanda suke yada jita-jitar cewa wai ya kuturce? Nadakila ya ce: "Ni babu abin da zan ce a kansu. Ni dai na amince da ikon Allah. Wannan hatsari da na samu, na danganta shi ga nufin Allah. Amma bai da wani dangantaka da wasan da nake yi. Yo direba da ke sana'ar tuki yake rasa ransa kwata-kwata, ni don na rasa gaba daya ta yatsa na sai me? Ai na gode ma Allah ma da ya takaita raunin haka. Kuma ba ni da kaico! Su kuma masu yada jita-jitar cewa na kuturce, to ban kuturce ba, na dai rasa gaba daya ta yatsana na hannun hagu a sanadiyyar hadari, ba cutar kuturta ba, Allah ya sauwake!"

Kabir Abba Nadakila dai na da burin kaiwa kololuwar wasan kwaikwayo. Kuma ya yi amfani da wannan dama wajen gode wa dukkan masoyansa da suka je gaishe shi don jajanta masa kan wannan hatsari da ya samu. Ya ce zai ci gaba da nishadantar da su kamar yadda ya saba.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin