Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 42   Agusta 2003
RAHOTO


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection


An nada Ashiru Bazanga Danmasanin Nasarawa Kaduna

Daga ALIYU A. GORA II a Kaduna

MARGAYE! Gyara kimtsi da kyau! Takawarka lafiya dan toron giwa!

Wannan shi ne kirarin da maroka suka yi ta antayowa a fadar mai girma Sarkin Nasarawar Kaduna yayin da ake nada shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, Alh. Ashiru Sani Bazanga, a matsayin Danmasanin Nasarawa. An fara gudanar da bikin nadin sarautar da misalin karfe 10 na safiyar Asabar, 19 ga Yuli, 2003.

Alh. Ashiru yana daya daga cikin mutane 16 da Sarkin na Nasarawa ya yi wa nadin sarautu daban-daban a karkashin masarautarsa.

Da yake zantawa da wakilinmu jim kadan bayan nadin nasa, sabon Danmasanin godiya ya fara yi wa Allah Madaukakin Sarki da ya zabe shi daya daga cikin mutanen da ake hangen suna da mutunci da har za a dora masu irin wannan babban nauyi na mulkin jama'a. Ya kara da jawo hankalin jama'a da su ba masarautun gargaji hadin kai, tare da ba su shawarwari na kwarai don su samu sukunin sauke nauyin da aka dora masu tare da kare hakkokin talakawansu ba tare da nuna kabilancin yare ko bambancin addini ba.

Daga karshe ya yi godiya ta musamman ga shugaban Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina, Alhaji Bishir Lawal Danja, wanda ya samu halartar bikin tare da tawagarsa. Ya kuma yi godiya da ban-gajiya ga 'yan'uwa da abokan arziki da suka goya masa baya suka halarci bikin.

Wadanda suka samu halartar bikin daga cikin 'yan fim sun hada da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alh. Ibrahim Mandawari, Shehu Hassan Kano, Dan'azimi Usman (Dafe-Dafe), Saminu M. Mahmud, Yahuza A. Ilu, Rabi'u Rikadawa, A.S. Mohammed, Abdullahi Tasiri, Aliyu Abdullahi Kabala, Nuhu Garba Isah, Awwalu Marshal, da kuma Nasiru Dan Maliki. An dai tashi taron lafiya da misalin karfe 1:15 na rana. Shi kuwa Danmasani, sai mu ce Allah ya taya shi riko.

Ban saki Rabi Mustapha ba, cewar mijinta

Daga ALIYU A. GORA II, a Kaduna

ALHAJI Yahaya Abubakar ya karyata ji-ta-ji-tar da ake ta yadawa cewa wai aurensa da zabiyar zabiyoyin finafinan Hausa Rabi Mustapha ya mutu.

Ita dai Rabi, wadda ta yi aure da Alh. Yahaya har ta haihu a Abuja, ta janyo surutai a industiri din Kano yayin da 'yan fim suka dade suna ganinta a cikinsu cikin 'yan kwanakin nan. Wasu sun ce sun gan ta a situdiyo tana waka kamar da, wasu kuma suka ce sun gan ta a wuraren bikin auren 'yan fim. Wannan ya sa wasu suka rika baza ji-ta-ji-tar cewa an sako ta ne, shi ya sa ta dawo fagen shirin fim.

Da yake yi wa wakilinmu bayani kan al'amarin ta wayar tarho, Alhaji Yahaya, wanda ma'aikacin gwamnati ne, ya bayyana cewa mutane daga wurare daban-daban sun sha bugo masa waya suna neman karin bayani daga gare shi game da zargi da suka ji ana yadawa a gari cewa wai ya saki Rabi. Ya ce kuma mata da dama daga garuruwa kamar Gusau, Kebbi, Filato, Kaduna da dai sauransu sun je har gidansa a babban birnin tarayyar don su gane wa idonsu idan ta fita din.

A cikin bayanin nasa, ya ce ya san duk irin bayanin da ya sha yi wa masu zuwa da kansu, da yawa daga cikinsu ba za su gamsu ba, ba don komai ba kuma sai don a lokacin ita Rabi ba ta gidan, tana Kano wajen iyayenta. Haka kuma ya kara da cewa abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne irin yadda da yawa daga cikin 'yan fim suke bugo masa waya cewa wai sun samu labarin cewa ya saki amaryar tasa, har ma wasu daga cikin 'yan fim din sun yi tattaki har zuwa inda yake don su tabbatar da gaskiyar lamarin. Alhaji Yahya ya ce gaskiya abin da ke faruwa shi ne, tun da ya auri Rabi ba ta taba zuwa ganin gida ba har ta haihu. Bayan ta haihu ne kuma sai ga sako an aiko cewa mahaifiyarta ta haihu. Saboda haka, a cewarsa, ya tura Rabi zuwa Kano don ta halarci bikin sunan, sa'annan kuma ya ba ta damar ta hada da hutun ganin gida, wanda ya ce ta kwashe fiye da wata daya a Kano tana hutawa tare da iyayenta.

A cewarsa, babu mamaki, wannan zaman ne wasu suka yi amfani da shi suke yada irin wannan mummunan zargi. A karshe ya jawo hankalin masu yada irin wannan ji-ta-ji-tar da su ji tsoron Allah su daina yada maganar da ba su da masaniya a kanta. Ya kara nanata cewa, "Aurena da Rabi Mustapha yana nan daram."

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin