Shirin fim: Sai mai ilimi?
Daga Ashafa Murnai Barkiya
A ranar Juma'a ne 14 ga Yuni, 2002 aka shirya wani gangami na masu shirya finafinan Hausa don tattauna wata matsala da ta taso. A taron, an hada daukacin masu harkar finafinai na arewacin kasar nan don tattaunawa kan matsalar da ke neman kunno kai cikin harkar shirya finafinai a Nijeriya. Taron, wanda aka yi shi a a gidan sinima na Marhaba, an yi shi ne bisa gayyatar Kungiyar Masu Shirya Fim ta Nijeriya, reshen Arewa ('Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN).
Jigajigan masa harkar fim na Hausa sun taru a wurin sun kuma labarta wa sauran membobinsu matsalolin da ke Neman kunno kai. A jawabin da shugaban MOPPAN a Arewa, Malam Abdulkarim Mohammed ya yi a taron, ya nuna cewa manyan 'yan fim na kudancin kasar nan ne, a karkashin kungiyar, suka zauna suka kafa wasu ka'idoji wadanda tuni an gabatar da su a gaban majalisa a Abuja, abin da kawai ake jira shi ne su amince su sa masu hannu su fara aiki.
Wasu daga cikin dokokin sun hada da:
i. Babu wani furodusa, darakta, dan wasa, mai daukar hoto ko wani abu da za a yi wa rijistar dan kungiya har sai idan yana da horo na shekara daya;
ii. Kuma ko da kana da horo, to sai kana da ilimin shaidar digiri;
iii. Su kansu wadannan sharuddan ba za su isa mutum ya zama cikakken dan kungiya ba sai bayan shekara biyu. Kafin nan kawai mutum zai zama dan kungiya na wucin-gadi ne, wato associate member.
Bayan Abdulkarim ya wasa daga cikin sharuddan, sai ya furta cewa, "Idan muka bari aka yi haka, tilas sai mutum ya je Legas cikin wadannan mutane ('yan Kudu) ya yi kwas". Wanda kuma ya ki bin doka, ya je ya yi gaban kansa, to doka za ta hau kansa. Daga nan sai shugaban na MOPPAN a Arewa ya kara da cewa, "Muna so mu fito da namu. Mun taru ne a nan don fada wa kowa ya san abin da ake ciki, kuma na san kowa a nan ya san muna da dokokinmu wadanda ba irin nasu ba ne".
An ba kwararren tsohon ma'aikacin talbijin din nan Mista Matt Dazie fili don ya ce wani abu. Dazie, wanda ya yi fice ne a matsayin dan wasan wani shirin NTA mai suna Cockcrow at Dawn, yana daya daga cikin w'yan kwamitin zartaswa na wadanda suka yi zaman tsara ka'idojin na MOPPAN. Shin ba da son ran aka yi wasu dokokin ba kensan?
A cikin jawabin da ya tashi tsaye ya yi, Mr. Dadzie ya ce, "A gabanmu akwai babbar matsala. Shi ya sa muka zo nan don mu hada kanmu". Kan batun sai mai ilimi zai yi harkar fim kuwa, sai ya ce, "Don mutum bai je makaranta ba, ba zai yiwu ba a ce ba shi da basira, ni ba zan yarda ba".
An bai wa wasu mahalarta taron damar ba da shawararsu domin a san mafita. Tashin farko sai Jarumin Jarumai na 2001, Aminu A. Shariff (Momo), ya yi tsam ya mike tsaye ya kwartsa kabbarori guda uku: "Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!" Haba, ai sai wuri ya yi tsit kuma duklokacin da ya yi kabbara daya sai yawancin 'yan fim din sun amsa masa da kabbara. Momo ya rika jefa kalamai kamar, "Ba za mu bi kafirci ba! Musulunci ba zai taba bin kafirci ba!! Bahaushe ba zai bi Inyamiri ko Bayarabe ba! Mai yawo cikin sutura ba zai bi mai yawo timbir ba!"
Bayan ya kara nuna cewa al'adar Yarabawa da ta Inyamirai ba daya take da ta Hausawa ba, sai dan wasan ya ce don haka bai yiwuwa a yi mana dokoki iri daya a ce su za mu bi don tafiyar da al'adarmu. Angon ya yi amfani da damar da ya samu ya nuna cewa, "Duk wannan abin da ake son yi mana sakaci ne na manyanmu".
Daga nan kuma sai ya yi kira ga gwamnati da ta fahimci cewa sana'ar fim "mun shigo ne domin riba, yada addini da kuma al'adar Bahaushe." Kuma ya kara yin kabbarori uku, daga nan ya zauna.
Bayan ya zauna ne sai shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama ya mike tsaye ya ce wa Momo, "Ba matsalolin kungiyoyi muka zo tattaunawa a nan ba. Mun zo ne don neman shawarar yadda za a bullo wa wutar da ta taso yanzu." A nan shi ma sai ya yi wata tambaya inda ya ce shi bai san dalilin da ya sa ake neman rubutaccen jerin sunayen 'yan fim ba. "Ai an taba aiko da fim through (ta hannun) MOPPAN, an cike an rubuta sunaye. Shin shi ba zai ya amfani ba kenan?"
Abdulkarim Mohammed ya amsa wannan tambaya da cewa, "Wancan rekod ne na Hukumar Finafinai ta Kasa. Ita ce ta nema, aka ba ta, ta kuma ajiye abinta".
Shi ma sabon ango Ahlan Shariff, jarumin cikin Laila, cewa ya yi, "Kamata ya yi MOPPAN ta kira jami'an kungiyoyin fim su tattauna da su." Haka dai jama'a da dama suka rika mikewa tsaye suna fadin albarkacin bakinsu. Wasu na kiran sakacin shugabanni wasu kuma fadar cewa ba zai yiwu a ce an yi ka'idoji da dokoki iri daya ba ga al'adu uku na kasa - wato Hausawa, Inyamurai da kuma Yarabawa.
Wannan kalli-kalalla za a iya cewa ta samo tushe ne daga wani rikici da masu shirya finafinan Kudu suka yi da 'yan wasan da suke kira 'yan Nigerian film. Cakudewar kasuwar da masu shirya finafinan Inyamurai wadanda yawancinsu dillalan kaset ne ke daukar nauyin shirya su, ya sa har suka yi shelar dakatar da shirya finafinai har tsawon wata biyu. Daga cikin abubuwan da suke ganin zai iya kawo gyara ga kasuwar finafinansu ne suka gabatar da ka'idoji bai daya da ake son majalisa ta sa wa hannu don aiki da su a kasa baki daya. Shin wadannan ka'idoji za su yi wa masu shirya finafinan Hausa dadi?
Mujallar Fim ta tuntubi Alhaji Hamisu Iyan-Tama kan al'amarin, sai ya ce, "Ba zai yiwu Bayarabe da Inyamuri su shirya wa Bahaushe ka'dojin da zai bi ya yada al'adarsa ba". Haka nan batun cewa an kai ka'idojin gaban majalisa, Iyan-Tama cewa ya yi, "Ya kamata a san cewa dokar kasa ta ba da dama ga kowace jiha ta gudanar da wasu dokokin da suka shafi jiharta. To a harkar fim ma dole sai an ba mu damarmu mun ba da tsarinmu wanda yake daidai da al'adar al'ummarmu."
Sai dai kuma shugaban kungiyar na Arewa ya ce wannan wani yunkuri ne ake yi don yin gyara daga yadda ake shiga harkar ba cikin tsari ba. Duk da haka sai ya ce ba za a ce gyara ya saba wa al'adar wata kabila ba. "Mu ba mu yarda a saba al'adarmu ba," inji shi.
Kan batun sai mai wata takardar shaida kuwa, a nan cewa ya yi, "Ai babban daraktan duniya bai yi wani ilimi mai zurfi ba. Wanda bai da ilimi idan ya taba shirya fim mai ma'ana, sai a kalla; kuma ai akan sami wanda ba shi da ilimi ya fi mai shaidar katin ilimi yin abin da za a karu ko kuma kwarewa wajen iya wani abu".
'Yan fim din sun watse bayan an yi addu'a ba tare da sun cimma wata yarjejeniya kwakkawara guda daya ba. Da ma wasu manyan furodusohi fita suka rika yi daga dakin taro da dai dai. Da ma wasu ba su ko zo taron ba, cikinsu har da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mandawari, wanda muka ji daga wata majiya cewa tun farko bai goyi bayan taron ba. Manyan furodusoshi wadanda suka halarci taron sun hada da manajan kamfanin Mu'azzat, da Hamisu Iyan-tama, Sani Mu'azu, Abdulkarim Mohammed, Matt Dadzie, Balaraba Ramat Yakubu, Ahmed Mohammed Amge, da Adamu Mohammed (Kwabon Masoyi).
An dai tashi ana Allah-wadai da wani furodusa wanda ya yi furucin da ke nuna cewa 'yan fim ba daya suke ba, akwai 'yan Kano da wadanda ba 'yan Kano ba, wanda hakan yana iya ruruta wutar rashin hadin kai a tsakanin 'yan fim.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin