Mintoci kadan bayan an daura mata aure, BALARABA MOHAMMED ta zanta a takaice da mujallar Fim inda ta bayyana farin ciki kan aurenta, amma kuma ta ce tana jin duk "wani iri, ba dadi." A lokacin sauran kimanin awa 24 Allah ya yi mata cikawa. Ga hirar:
FIM: Balaraba, yaya za ki iya kwatanta farin cikinki a wannan rana ta daurin aurenki da Shu'aibu Lawan?
BALARABA: Ba abin da zan ce (illa) ni dai ina farin ciki.
Wannan aure ya yi jama'a. Ko kina da godiyar da za ki yi wa abokan arziki?
BALARABA: Gaskiya ina yi yi masu godiya, kuma Allah ya kai kowa gida lafiya. Kamar yadda suka zo nawa, Allah ya ba ni ikon zuwa nasu.
Ya za ki kwatanta irin yadda kika ji a zuciyarki kafin a daura maki aure da kuma yanzu da aka daura auren?
BALARABA: Dadi kawai kake ji, ba wani abu ba!
A rayuwarki kin taba jin dadin da ya wuce wanda kike ji a yau?
BALARABA: A'a.
Wace shawara gare ki ga angonki Shu'aibu Lawan Kumurci?
BALARABA: (dariya) Ina jin ba wata shawara da zan ba da, illa dai in ce Allah ya ba mu zaman lafiya kawai.
Kin shaku da iyayenki da kannenki da yayyenki. Yaya kike ji a ran ki tunda ga shi an daura maki aure, za ki tafi ki bar su?
Ta wani fannin ina jin dadi, ta wani fannin ina jin wani iri ... ba dadi.
Kina da wata shawara da za ki ba kawayenki wadanda ba su sami damar yin aure ba?
BALARABA: To, sai dai in ce masu su ma Allah ya ba su miji nagari.
Alhamdu lillahi. Mun gode Balaraba.