Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Balaraba a cikin farin cikin angwanci tana hira da Fim
Ba zan hana 'ya'yana yin finafinai ba

Cewar Uwar su Balaraba

TA yi asarar 'ya'ya biyu a hadarin motar: Balaraba da yarta Jummai. Kuma kanwarta Hafsat ta ji rauni a cinya bayan danta Isiya ya rasu shi ma a hadarin. Jummai kuma ta bar mata renon jaririyarta Khadija. Bayan haka, kanen surukinta ma ya rasu duk a hadarin. Babu mamaki MALAMA BINTA MOHAMMED ta jigata tun da aka yi wadannan asarorin. Duk da haka, ta karbi kaddara, hankalinta ya kwanta domin ta mayar da komai ga Sarkin Sarauta.

A nan kasa ga irin tunanin da ke ran ta dangane da abin da ya faru gare ta:

Fim: Mama, me za ki ce game da faruwar wannan al'amari?

MALAMA BINTA: Abin da zan ce shi ne, na gode ma Allah, na gode ma Annabi. Kuma na gode ma jama'a a kan yadda suke ta zuwa yi mana ta'aziyya daga birni da kauye. Allah ya saka masu da alheri.

Fim: Yanzu a wane matsayi Shu'aibu zai kasance a wajenki ganin cewa Balaraba ta hada ku kuma ga shi ta rasu?

BINTA: Na dauke shi tamkar ni na haife shi tunda ma ni yanzu ai na haifa da cikina. Saboda ya wanke mani zuciyata, ya kuma share mani hawayena rannan da ya zo ya gaya mani cewa in kwantar da hankalina, tunda Balaraba yanzu ba ta, amma shi yanzu shi ne Balaraba.

Fim: Kina da ra'ayin ku ba shi auren wata mata daga cikin zuriyar ku?

BINTA: E, ba na ce a'a ba, don saboda wannan al'amari na Allah ne. Cikin 'ya'ya da jikoki duk wadda ya gani ya ce yana so ai ba na ce ba a ba shi ba. In suka shirya kansu ta ce tana son shi ai shikenan. Ka gani, in ya nuna kanshi ita ma ta nuna kanta ai shikenan.

Fim: Me za ki ce dangane da rade-radin da ake yi cewa wai mutuwar su Balaraba akwai sa hannun makiya?

BINTA: E, to, ina da shawara, don ni ma nan kaina an zo nan an gaya mani, aka ce ba mutuwar Allah da Annabi suka yi ba, an yi masu ne, aikin yasin ne. Na ce masu a'a, ni da aikin Yasin, da ba aikin Yasin, ni na dauka Allah ne ya aiko da wannan al'amari. Mutum ba ya wuce lokacinsa. Saboda haka in ma mutun ya yi, shi ma ya jira lokacinsa. Kawai ni abin da na ce, su daina ma bata masu gawarwakinsu. In ma mutane ne suka yi, in ma ba mutane ba ne suka yi, ni na dauka Allah shi ya karbi abinsa; shi ya ba ni shi ya karba, saboda haka su daina bata masu suna kawai.

Fim: Daga cikin 'ya'yanki akwai wanda ya taba rasuwa kafin su Balaraba?

BINTA: E, akwai. Haihuwar farko, ba rashin kunya ba. Don ya karbi suna kenan ya koma. Ban san daddin shi ba, bai san nawa ba.

Fim: Za ki iya barin wani ko wata daga cikin 'ya'yanki ta kara shiga harkar shirin fim?

BINTA: E, to, ita ma Balaraba ban zata za ta yi fim ba; ban taba yin tunanin cewa za ta yi fim ba. Allah ne ya kaddara da cewa za ta ci abinci a wajen har mu ma mu ci a jikinta. Saboda haka idan daga cikin 'ya'yana wani ya ce zai yi sai in ba shi goyon baya ya yi. Ni ban ga illar fim ba. In dai yaro zai rike kanshi. Kuma in yi rike kanshi, zai samu alheri. Saboda haka cikin 'yan'uwan Balaraba duk wanda ya ce yana ra'ayin fim, ni ma sai in ba shi dama, Ubangiji Allah ya ba shi sa'a.

Fim: To yanzu wannan jikanya taki da kike jinya wadda hadarin ya ritsa da ita, za ki maida ta wajen mahaifinta ne bayan ta warke, ko kuwa ke za ki ci gaba da rikonta?

BINTA: Yanzu ba zan ce za ta zauna wurina ba, saboda sai shawarar da uban ya yanke. Ni in zai bar mani ai ina so, amma in ya ce mani in an yaye ta a ba shi kayanshi, sai a ba shi, ba a jayayya a kan 'ya. Amma ni a son ra'ayina, in ya yarda, to ya bar mani in rika ganinta a gabana.

Amarya ta gudo gidan su Balaraba ba tare da sanin ta rasu ba

Larai Bala Tela

Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN, a Kaduna

ABIN mamaki ba ya karewa. Kwanaki 25 bayan rasuwar Balaraba, wata yarinya mai kimanin shekaru 17 da haihuwa mai suna Larai Baba Tela ta gudo daga dakin mijinta a Wuse, Abuja, kwatsam sai ga ta a gidan su Balaraba, ba tare da sanin cewa ita jarumar ta rasu ba. Labarin da kawai take da shi shi ne Balaraba ta yi aure.

Larai dai ta dira gidan a ranar Laraba, 10 ga Afrilu, 2002.

A daidai lokacin da take gabatar da kanta ga iyayen Balaraba bayan wani dan acaba ya kawo ta daga tashar mota, wakilanmu guda biyu suna tare da mahaifan na Balaraba suna tattaunawa.

Bayan da Larai ta bukaci Malam Muhammadu Kaura (uban Balaraba) da ya yi mata masauki, sai kai tsaye ya nuna mata cewa ba zai iya ba, kasan ne kuma ga halin da yake ciki na juyayin rasuwar 'ya'yansa. Da ya tuhumce ta kan dalilin zuwa gidansa maimakon wani wurin, sai ta ce tsananin soyayyarta ga Balaraba shi ne dalili da kuma tunanin su iyayen na Balaraba za su iya magance mata matsalar da take damunta na auren tilas da ta ce an yi mata ta ki zama fiye da shekara guda da ta wuce.

Bayan da wakilan namu suka ji takaitaccen bayanin Larai, da kuma matsayin mahaifin Balaraba kan matsalarta, sai daya daga cikinsu ya kebe ta don jin karin bayani daga gare ta.

Ya fara da gano cewa ainihin sunanta Karimatu, ya kara tuhumarta kan gaskiyar labarinta, inda ta bayyana masa cewa ita aurar da ita aka yi ga wani dattijo a matsayin matarsa ta uku amma ba ta kaunarsa. Ta ce dattijon ya taba neman yarta ta ki shi, amma ita saboda mahaifiyarta ba su tare da mahaifinta sai aka tilasta mata aurensa.

Larai ta ce a tsawon zaman da suka yi da auren, sau daya rak ta taba yin wata daya a gidan mijin (tana guje-guge) amma an ki a raba auren. Ta ce an yi ta azabtar da ita domin tilasta mata ta zauna, ta ki. Har ta kai maganar kotu, mahaifinta mai suna Isyaku (Baba Tela) ya je ya sa aka yi watsi da maganar, aka tilasta mata komawa gidan mijin.

Matashiyar matar ta kara da bayyana cewa sau biyu ana kulle wani tsohon saurayinta a kan matsalar har na tsawon kwanaki. Kakarta ma (mahaifiyar uwarta) an taba tsare ta saboda zargin tana goyon bayanta. A karshe dai ta yanke hukuncin sake tserewa daga gidan mijin zuwa Kaduna wajen iyayen Balaraba don su taimake ta t a zauna da su saboda labarinsu da ta ji cewa su mutanen kirki ne, ba sa kaunar tilasta 'ya auren wanda ba ta so.

Ko da wakilinmu ya ji wadannan bayanai na Larai, sai ya tausaya mata, ya dauke ta zuwa gidan Rediyon Tarayya na Kaduna inda aka yi hira da ita a shirin "Jakar Magori," aka watsa a ranar Jumma'a, 12 ga Afrilu, 2002. A yayin da yake kokarin gano mijin Larai ko iyayenta, wakilin namu ya yi wata dawainiyar da ita, kamar sama mata masauki a hannun sarakunan unguwar da yake zaune (Kabala Costain), ya kuma hada ta da Kungiyar Mata Lauyoyi (FIDA) da kuma Hukumar Jin Dadin Jama'a ta Jihar domin su ba ta taimakon da ya kamata kan matsalarta.

A yanzu haka dai Larai tana gidan Sardaunan Matasan Nijeriya, Alhaji Ibrahim Musa Gashash, domin daukar matakan da suka dace a kan makomar rayuwarta.

Saboda haka iyayenta da mijinta za su iya tuntubarsa ko wannan mujallar domin su sami saduwa da ita don a warware mishkilar da ke tattare da ita.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin