 Tafiyar karar kwana
Labarai daga ALIYU ABDULLAHI GORA II da IRO MAMMAN a Kaduna; ASHAFA MURNAI BARKIYA da SANI MOH'D MAIKATANGA, a Kano
BA iyalan gidan su Amina, 'yar wasan fim da aka sani da sunan Balaraba Mohammed, da mutanen Unguwar Kaji da ke Kaduna ko kuma duniyar shirin fim na Hausa kawai ba, za a iya cewa arewacin Nijeriya baki daya an girgiza, an kuma dimauce, yayin da labarin rasuwar Balaraba Mohammed da 'yan'uwanta uku ya fara bazuwa a yammacin ranar Asabar, 16 ga Maris, 2002. Da yawa ba su gaskata labarin ba. Wannan ya sa tun a ranar da abin ya faru, mutane daga bangarori daban- daban suka rika yin tsinke zuwa gidan mutuwar, wasu kuma suna bugo waya a ofishin mujallar Fim ko ofisoshin shirya fim a garuruwan Kaduna da Kano, don su tabbatar da gaskiyar labarin.
Mutane sun gigita ne domin jiya-jiyan nan ne aka daura wa fitaccciyar 'yar wasan fim din aure da wanda take tsananin so, wato fitaccen dan wasa Shu'aibu Lawan (Kumurci). Su Balaraba sun yi mummunan hadarin ne a wani kauye da ake kira Dumbin Dutse kan hanyar Kaduna zuwa Zariya tare da 'yan'uwanta da suka raka ta zuwa Kano don halartar bikin 'Gala'da abokan ango suka shirya a gidan sinima na 'Lale'da ke can. Sun yi hadarin a cikin karamar mota. Ficen da Balaraba da Kumurci suka yi a fagen shirin fim, da kuma yadda aka yayata labarin auren, musamman a mujallar Fim (wadda ta buga hotonsu a bangonta na watan Maris) sun sa abin ya kara kidima jama'a.
DA misalin karfe 3:30 na yammacin Asabar, 16 ga Maris, 2002, su Balaraba suka bar gida zuwa Kano a motoci biyu. Daya karamar mota ce kirar Nissan Primera, wadda su Balaraba ke ciki, dayar kuma bas ce samfurin C20, mai lamba XB 894 FGE wadda ta kwashi 'yan rakiyar amarya, ciki har da fitattun 'yan wasa su Hajiya Usaina Gombe (Tsigai) da Baffa Ahmed (Cinnaka).
Motar su Balaraba tana dauke da mutum bakwai: ita Balarabar da 'yan'uwanta mutum hudu da kananan yara guda biyu. Akwai babban wansu, Abdullahi (wanda aka fi sani da sunan Riskuwa), da mai bi masa, Jummai, da 'yarta Nana Khadija 'yar wata uku da haihuwa, da Hafsat, kanwar mahaifiyar Balaraba da danta Isyaku (wanda ake kira Datti), wanda kuma dan shekara uku ne, da direban motar, Muhammadu Sani, wanda kane ne ga mijin ita Jummai kuma dalibi a Jami'ar Abuja.
Bayan sun fita bayan garin Kaduna, a wani matsakaicin gari mai suna Rigachikun, a wani gidan mai da ke kusa da makarantar sakandaren da Balaraba da Jummai suka kare karatu, sai motocin suka tsaya suka sha mai. Bas din ta fara sha, ta tsaya jiran sauran. Sai Abdullahi, wanda soja ne a Kaduna, ya ce wa mai bas din ya ci gaba da tafiya, za su same su. A garin Jaji, sai fasinjojin bas din suka ga Nissan din ta wuce. Da misalin karfe 4:30 na yamma, su Balaraba suka isa kauyen Dumbin Dutse, wanda yake da nisan kilomita 50 daga Kaduna. Kauyen yana gaban Mararrabar Zangon Aya, kafin a kai wata shahararriyar kwana wadda daga ita sai wurin wasu masu saida dankalin Turawa. A daidai wannan wurin akwai wasu ramuka a tsakiyar titin, wadanda duk mai bin hanyar ya san da su. An sha yin hadurra a wurin har rayuka na salwanta. Mafi yawancin lokuta yaran kauyen sukan tsaya suna ciko da kasa, suna kuma nuna wa motoci masu zuwa cewa akwai rami, don su kauce.
To abinka da karar kwana, Muhammad Sani, wato direban su Balaraba, bai san hanyar ba, domin shi a Abuja yake zaune, kuma haifaffen Barikin Ladi ta Jihar Filato ne. Ga kuma gudu yana yi, akalla kilomata 130 a awa daya. Saboda haka, bai ankara ba sai ya ji motar ta soma fadawa cikin ramukan. Ba tare da bata lokaci ba, sitiyarin ya kubuce masa; nan take ta yi karo da bangon tsakiyar titin, sannan ta dawo kan hanya, sai kuma ta kara komawa ta bugi bangon, ta yi ta kartarsa har ta tarar da wurin yin kwana ('u-turn'), ta shiga ciki ta fada kan daya hanyar da motoci ke biyowa daga Zariya zuwa Kaduna, bayan ta tsallake tudun da ke gefen hanyar. Daga nan sai ta birkice, tayoyinta a sama, tana kuma tafiya a kan titin. Wasu mutanen kauyen, wadanda aka yi abin a gabansu, sun shaida wa wakilinmu cewa, duk mutanen da ke cikin motar, in ban da Abdullahi, an watso su waje a wurare daban-daban ko kafin motar ta birkice. Ita Balaraba, an jefar da ita a gefen kwalta, kuma ko motsi ba ta yi, amma da ran ta a lokacin. Yayanta Abdullahi Riskuwa ya rage cikin motar saboda ya daure jikinsa da bel din kujera. Sai dai bai san lokacin da Datti da ya rike a gaba ya subuce ba ya fada waje.
Ganin abin da ya faru sai mutanen da ke kauyen da kuma sauran matafiya da suka zo wucewa suka yo caa zuwa gun motar domin ceton rai. Abdullahi ya kukuta ya fito ba tare da ya samu agaji ba, ya nufi wurin kanwarsa amarya. Ya tarar ba ta iya cewa komai.
Ba a jima ba daya motar ta iso wurin. Sai mutanen da ke cikinta suka ga an taru. Har wasu na cikin motar sun ce, "Mu wuce!" saboda suna sauri su isa Kano, to amma sai direban, wani mai suna Darda'u Saminu Zariya, ya ja burki ya tsaya a gefen titi, da yake 'yan bas sukan tsaya in sun ga an yi hadari, ko don su tabbatar idan akwai wani nasu. Suna fitowa sai suka gane motar.
A lokacin, har Jummai da Isiyaku Datti sun rasu. Motar Darda'u aka yi amfani da ita aka dauki gawarwakin aka kai su Kaduna. Ba a jima ba dogarawan hanyoyi ('Road Safety') suka zo suka dauki Balaraba da direba Muhammadu Sani, wadanda ba su rasu ba a lokacin, suka kai su asibitinsu da ke garin Birnin Yero. Daga nan ne jami'an suka dauke su suka nufi Kaduna da su, suka kai su asibitin 'A.B.U. Teaching Hospital.' Sai dai kash! kafin a shiga asibitin, Balaraba ta rasu. Shi ma Muhammadu Sani ana shiga ya rasu. Allahu Akbar! Sai aka dawo da su gidan su marigayiyar.
Da ma direban bas, Malam Darda'u Saminu Zariya, ya kawo gawarwakin Jummai da Datti gidan. Gidan ya kaure da hargowa da taraddadi. To, sai kuma ga karin gawarwaki an iso da su. Bakin cikin da ake yi a lokacin ya fi gaban misaltawa. A lokacin Magariba ta karato.
Wadanda aka bari suna jinya a asibiti mai suna 'Jinya Hospital' su ne Hafsat (uwar Datti), wadda ta karye a cinya, da kuma jaririyar da Jummai ta bari, wato Nana Khadija, wadda ta ji rauna a kada kuma a fuska.
Ba tare da bata lokaci ba, aka yi wa mamatan sutura kamar yadda Musulunci ya ce. Tun misalin karfe 6 na wannan wuni jama'a suka cika makabartar da ke bakin titi a Kawo, Kaduna. Bas din Darda'u ce ta dauki gawar Balaraba da Muhammad Sani zuwa makabarta, yayin da wata kuma bas samfurin Toyota Lite Hiace da aka fi sani da 'Dutsen Guga,' mai lamba AE 763 MGU ta dauko gawar Jummai da Datti. An fara jana'izar su da misalin karfi 6:30 na yamma. Dimbin jama'a sun taru a wannan makabarta, 'yan'uwa da abokan arziki da 'yan jarida. Bayan an rufe mamatan, an yi masu addu'o'i, sai kowa ya kama gabansa, wasu na ta sharbar kuka.
An jera kaburburan mamata uku a wuri daya: kabarin Balaraba shi ne farko daga gabas. Daga shi sai na Muhammad Sani, sai na Jummai, san'anan karamin yaron nan Datti an yi masa nasa nesa kadan daga sauran a cikin makekiyar makabartar. Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya jikansu da rahama, amin.
A daren, wakilinmu ya je asibitin da aka kwantar da Hafsat, wadda ta karye a gwiwa kuma ta rasa danta a hadarin, da diyar Jummai, wato asibitin 'Jinya' da ke kan Titin Bida a Kaduna. Ita jaririya Nana Khadija, wadda ita ma wakilinmu ya gan ta a asibitin, ta ji rauni a kanta, kuma fuskarta ba kyan gani saboda gurjewa da ta yi yayin da ta fado kan kwalta daga motar.
GIDAN su Balaraba gidan haya ne kato, mai sashe-sashe, wanda akalla akwai dakuna hamsin a cikinsa. Don girmansa ne ma ake ce masa Dogon Gida, kuma akwai kabilu daban-daban a cikinsa. Wakilinmu ya gano cewa a lokacin da Malama Binta ta samu labarin abin da ya faru ga 'ya'yanta, nan take ta yanke jiki ta fadi sumamma. Mutanen gidan kuwa, saboda rudewa, suka kasa yin komai in ban da kururuwa, suna fadawa kanta.
Ganin haka, mahaifin Balaraba, Malam Muhammadu Kaura, ya ga za a kashe masa mata, ga kuma 'ya'ya sun rasu, ya yi niyyar dauko bindiga cikin rudewa, amma ya fasa, ya dauki wani ice, ya yi barazanar kai bugu. Nan take aka watse, matar ta samu shan iska. Da al'amarin dai ya gagara, dole aka dauke ta zuwa asibiti inda aka kwantar da ita a dakin da aka kwantar da kanwarta Hafsat. Ko lokacin da ake jana'iza, su suna asibiti. Da wakilinmu ya je asibitin, daga cikinsu ba wadda ke iya amsa gaisuwa.
Malam Muhammadu Kaura ya yi iyakar kokarinsa don ganin bai fita hayyacinsa ba, amma ina! hakan ba ta samu ba, domin kuwa cikin dare ya kasa, shi ma aka kai shi asibiti, aka kwantar. Wannan zama da suka yi a asibiti, ya shafe kwanaki; akwai lokacin da aka dawo da su gida, amma aka maida su. Abin ya yi masu yawa, musamman dayake babu da nasu da ya taba mutuwa, sai ga shi sun rasa da yawa a lokaci daya. Allah kenan, Sarkin Iko!
Kusan a wannan dare, har safe mutane ba su tsinke ba a gidan su Balaraba, wasu na kuka, wasu kuma ba su iya ko magana saboda juyayi. Washegari kuma kai ka ce koro mutane ake yi zuwa gidan, domin ciki da kewayen gidan dan mutum ne ba masaka tsinke. Ba abin da kake ji illa "Inna Lillahi, Wa Inna Ilaihir Raji'un!" Da misalin karfe 2 na rana, sai ga shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, ya iso don yin ta'aziyya. Jim kadan kuma shugaban Kungiyar Furodusohi na Jihar Kaduna, Malam Adamu Bello Ability, ya iso da tawagarsa, har wakilinmu ya gan shi yana kuka da hawayensa.
'Yan fim da dama sun samu halartar ta'aziyyar. Daga cikin furodusoshin da wakilinmu ya samu gani akwai Malam Adamu Bello Ability, Alh. Magaji Suleiman, Alh. Tukur Aliyu, da kuma furodusan fim din Asali, Malam Aminu Mirror, dukkansu daga Zariya. Daga Kano kuma, da ma akwai 'yan fim wadanda ba su koma gida ba bayan daurin aure har abin ya faru. Sun hada da tsohon shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alh. Auwalu Isma'il Marshal, Mu'azzam Boss, Muktar M.D., da Abdulmunafi Sani, da sauransu. Sa'annan labarin da ya kai Kano ya sa wasu dimbin 'yan fim din suka garzayo zuwa Kaduna domin yin gaisuwa. Sun hada da Iyan-Tama, da shugaban kamfanin 'HRB Production,' Alh. Rabi'u Harabs. A Kaduna kuma, Ibrahim Sheme, Aliyu Abdullahi, Shafi'u Magaji Usman, Nasiru Dan Bisalla, Ashiru Sani Bazanga, Salisu Umar Salinga, Saminu Mohammed Mahmud, da sauran 'yan fim, sun halarci gaisuwar.
Wan Balaraba, Abdullahi, tare da shi ake karbar gaisuwar, domin kwanansa daya a asibiti saboda bai samu mummunan rauni a hadarin ba. Tare da shi akwai 'yan'uwansa, surukai, da makwabta. Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin, a kullum gidan cike yake da jama'a da suke ta zuwa gaisuwa. Kowa ka gani idonsa ya yi nasha-nasha kamar hawaye za su zubo masa.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|