 Yadda muka rabu da Balarabata
Hirar musamman da Shu'aibu Kumurci
ABIN bakin cikin da ya samu Shu'aibu Lawan (Kumurci) zai iya samun kowa. To amma ba kowa ba ne zai iya karbar kaddara irin yadda shi Shu'aibu ya karba a kan rasuwar amaryarsa Balaraba Mohammed.
Shu'aibu ya maida komai ga Mahaliccinmu. Ya nuna tsananin imani, domin ya amince cewa Allah ne mai bayarwa kuma mai amshewa. Yin wannan imani ya ba shi kwanciyar hankali, ta yadda ba tare da dadewa ba har ya koma cikin hayyacinsa. Duk wanda ya gan shii ya san lallai ya jigata, to amma kuma ya soma maida jiki da kuma annurinsa.
A cikin wannan hirar da suka yi da mujallar Fim mako uku bayan hadarin, Shu'aibu ya fadi yadda rabuwarsu ta kashe da Balaraba ta kasance a ranar da ta rasu, da yadda labarin ya zo masa, da kuma ra'ayinsa kan batun cewa wasu ne suka "jefe" ta, sa'annan da wani mafarki da ya yi game da Balaraba wanda a cewarsa zai iya kasance alkhairi gare shi da kuma iyayenta.
Allah ya jikan Balaraba, Jummai, Isiya Datti, da Muhammadu Sani, kuma ya ba danginsu jimirin jure wannan babban rashin, amin.
Bismilla:
FIM: Shu'aibu, mujallar Fim da dukkan ma'aikatanta suna yi maka ta'aziyyar rashi na su Balaraba.
SHU'AIBU: To madalla, ina amsawa.
FIM: Mu fara tun lokacin lafiya daurin aure. Dalili shi ne wasu sun fahimci cewa kamar ba ka cikin kuzari a ranar. Shin akwai dalili?
SHU'AIBU: E to, gaskiya wancan lokaci da Allah ya kawo mu, na wayi gari (na ga) cewa yau za a daura mana aure, sai nake jin wasu abubuwa daban a jikina wanda kamar ba ni ba. Kuma irin kusan wasu buruka da na ci a lokacin amma da safe da na tashi sai na ji ni ba na jin dadin komai. Ga shi dai a ranar za a daura min aure, to amma sai na ji na zama wani daban. Ni kaina sai nake ganin kaina da wasu kamannu biyu-biyu haka.
FIM: To bayan an daura aure ka baro Balaraba a Kaduna ranar Asabar. A kofar gidansu kun tsaya a bakin motar Sani Mai Iska kun yi bankwana. Ko za mu iya jin maganarku ta karshe kai da ita?
Shu'aibu: A lokacin da aka daura mana aure wato sai da ni da ita muka shiga wani hali haka irin... ni dai na farko na kasance jama'a sun yi min yawa. Akwai yayanta Abdullahi wanda ya zo ya dauke ni zuwa wani daki ya ajiye ni a can. Allah da ikonsa ina nan sai ga ta ta zo. Tana zuwa sai muka tsaya muna kallon juna. Sai take ce min, "An daura auren!"
Na ce, "E, an daura!"
Mun zauna a dakin wasu 'yan lokuta masu tsayi, ba ta yi min magana ba haka zalika ni ma ban mata ba. Daga nan kuma shi ne 'yan jarida suka shigo suka fara daukarmu hoto. A wannan lokaci ban sani damar tattaunawa da ita ba. Saboda haka sai na ce ta koma ciki. Lokacin mutane suna ta zuwa, kowa yana so ya gan mu. Allah da ikonsa da dare bayan na dawo sai muka hadu a dakin mahaifiyarta. Sai mahaifiyarta ta ba mu fili muka zauna. Lokacin Balaraba tana kan gado. Da na shigo sai ta tashi. Na ce a'a ta zauna. Sai take cewa, "A'a, ai yanzu kai Shu'aibu ka hau wani matsayi na daban; kai za ka zauna a kai!" Sai na zauna a inda ta tashi, ita kuma ta zauna a kasa.
To sai na ga ta dafa cinyata. Nan take sai ta fara zubar da hawaye. Ban san dalili ba ... ko don murna ce? Na ji ba ta ce min komai ba. Sai ta kama yatsana karami na dama, sai ta sa nata yatsan na dama karami ta hada da nawa muka kulla. Kawai tana yin haka sai ta fara tambayata wasu abubuwa.
Ta ce, "Don Allah don Annabi, Shu'aibu ina so ka cika min alkawari kamar yadda na cika maka."
Ta ce, "Ka san dai ni na cika 'ya, ko?"
Na ce, "E."
Ta ce, "Na kuma cika maka alkawari."
Na ce, "E."
To sai ta ce, "Don Allah, don Allah kada ka sake ni!"
Sai na yi shiru. Can da aka jima sai na tambaye ta: "Wai menene dalilin da ya sa kike fada min wannan magana?"
Sai ta kara cewa, "Ni dai don Allah kada ka sake ni, ko wahala ko dadi ni dai muna tare."
Na ce, "Na yarda, Balaraba."
Ta ce, "Ni dai mutuwa kawai za ta raba mu."
Har a lokacin nake ce mata, "Balaraba, wane irin ruguntsumi ne ba mu shiga ba, kuma ni da ke ba wanda ya bar juna sai yanzu don na ga ragamarki tana hannuna? Idan na yi maki haka ai na yi maki wulakanci!"
A can sai ta ce ta yarda da ni.
Har dai muka ci gaba da maganganu tana so ta fada min wata magana wadda tun kafin mu yi aure take so ta fada min Allah bai yi ba. Na ce, "Ya za ki fada min wata magana fa?"
Tana cikin fara fada min sai babanta ya fito. Sai na tsaya muna gaggaisawa.
Da zan tafi wurin kwana har ta rako ni a wurin mota, take ce wa direban, "Don Allah ka tuka shi a hankali!"
Da na je wurin kwana ni sai na kasa yin barci saboda ina ta tunanin wasu abubuwa.
Da Allah ya kai mu gari ya waye sai na same ta. Muna zaune muna cin abinci, sai na ga tana hawaye. Na tambaye ta, ta ce min, "Ba komai." Sai ni ma na ji hawaye na zubo min. Mun zauna amma dai ba mu yi wata cikakkar magana ba sai dai kawai wani irin kallo da muke wanda kamar ba mu ba, daga ni har ita.
Can sai ga mahaifinta ya shigo da yayanta Abdullahi. Aka fara shirya tafiya. Mahaifinta ya ce ni da abokaina mu yo gaba, su Balaraba za su taho. Ba don komai ya yi haka ba sai don ya tausaya min saboda ya ga kudina sun kare a lokacin. Kuma ya ga mutane da dama da suka je daurin auren sun kwana amma ba su da kudin mota na komawa. A can Kaduna na yi buga-buga na samo kudin mota aka ba su suka taho. Ganin haka sai mahaifin Balaraba ya tausaya min, ya ce akwai wata mota ta 'yan'uwansu da za a kawo Balarabar a ciki.
Shi ne nan ta rako ni wurin mota. Muka zo har wurin mota. Na dauki kudi na ba ta, sai ta ce min ba za ta karba ba; ta san ba ni da kudi, saboda haka kada in damu. Na takura mata na ce, "Ai saboda halin tahowa." Shi ne ta karba. Muka je karshen layi muna yi wa juna bye-bye. Shikenan, rabuwana da ita kenan.
FIM: To lokacin da ka iso Kano...
SHU'AIBU: Lokacin da na iso Kano, muna filin Gala sai na fara ji a jikina. Da na duba agogo sai na ga lokacin nan ya ci a ce sun iso in dai har sun taho. Mutanen da muke tare da su da dama daga cikinsu sun fahimci ba na son magana kuma na kebe waje daya. Mutane suna tambayata, "Lafiya?" Ina cewa, "Lafiya."
Ina nan, sai na ga wani kamar a mafarki ya gitta yana kuka. Kafin na je wurinsa har an fita da shi. Ashe a lokacin abin ya faru amma ba a son in sani. Sai nake tambayar Sani (Mai Iska) abin da ya faru, sai suke ta rufe min. Duk wanda na kalla sai in ga ba ya son hada ido da ni. To daga nan jikina ya fara ba ni. Har muna nan dai aka fito da ni zuwa ofis din Sani Mai Iska.
Lokacin da muka je duk na tarar da mutane jugu-jugum. Ina ta tambaya amma ba wanda ya ba ni amsa. Sai jikina ya kara ba ni. Sai na fara yi masu wasu kalamai ina cewa, "Ni din nan Musulmi ne kuma na yi imani da Allah. Na san dai duk abin da zai faru ba zai wuce a ce Balaraba ta rasu ba ko kuma hadari..."
Amma fa ba sani na yi ba. Illa dai iya tunanina shi ne iya abin da zai iya faruwa wanda zai sa hankalina ya tashi a yanzu.
To sai suka dan boye min, suka ce an aiko sun yi accident sun koma gida an aiko min an ce mu je can Kaduna. A wannan lokacin mun fito waje ni da kanin Balaraba, kuma ba na son ya fahimci wani abu kada hankalinsa ya tashi. Sai na dauki kudin mota na ba shi na ce ya tafi unguwar Tarauni zan zo in same shi. Muna cikin haka sai wata yarinya ta zo ta fada masu abin da ya faru. Da yawa daga cikinsu sai suka fara ihu. Nan ne aka yi tunanin a taho da ni gida. A cikin motar sai kowa ya yi shiru. Ni kuma nake ce masu, "Wallahi na sani, Balaraba ce ta rasu! Allah ya jikanta!" Sai na fara salati. Sai kowa daga cikinsu ya fara kuka.
FIM: Daga nan ya aka yi ka sami kanka a asibiti?
SHU'AIBU: Lokacin muna tahowa sai na fara kuka ina salati. Muna zuwa gida sai na tarar duk an cika, mutane sun zo ana ta'aziyya. Ganin haka sai na ji hankalina ba ya jikina.
Abin da zan iya tunawa kawai shi ne, an shigo da ni daki, na ga hotunan da muka yi na saka a daki. Ina shiga sai na ga duk an ciccire su. Akwai wani babba da ke saman daki. Sai na daga kaina don in ga ko yana nan? Lokacin da na yunkura kaina don in gani, kawai sai farkawa na yi a asibiti da mutane a kaina. Na yunkura zan tashi sai na ji ina daure da ledar ruwan drip.
FIM: Wane asibiti ne?
SHU'AIBU: A nan gaban Court Road yake, sunansa Premier.
FIM: Kwananka nawa a asibitin?
SHU'AIBU: Kwanana daya.
FIM: Shu'aibu, me ka sani game da abin da daya daga cikin 'yan'uwan Balaraba ya fada cewa ta ce idan aka daura mata aure ba za ta wuce kwana uku ba za ta mutu?
SHU'AIBU: E, maganganu daban-daban lokacin da muke tare da Balaraba na ji da yawa. Akwai mutane da suke mata irin wadannan miyagun fata, amma ban san ko su wanene ba. Idan ta zo ta fada min sai in nuna mata Allah. Akwai mutane daban-daban, musamman masu kudi a nan Kano, wadanda akwai wasunsu nakan hadu da su haka kuma sanadiyyar tana so na sukan gaigaya mata maganganu, ita ma tana gaigaya masu. Irin wannan da dama, na sha haduwa da su. Akwai wadanda ke nuna mata cewar gara ma ta rabu da ni tunda ni ba abin da zan ba ta sai ma in wahalar da ita. Ita kuma take nuna masu cewar in har suna ganin wani abu ne suke da shi wanda za su ba ta, to ita hankalinta ba ya kan abin da za su ba ta. Idan suna takamar arziki ne, to Allah shi ya ba su, ni ma shi zai ba ni.
FIM: Ina maganar wancan kalami da yayanta ya fada a cikin mujallar Fim da ta gabata?
SHU'AIBU: Ni ba ta fada min a ranar ba, amma dai na san da irin wadannan maganganun. Na san su ba nema ne na Allah, na gaskiya ba. Duk mai imani, in dai ya san akwai wanda zai auri yarinya, to ba zai taba furta wata magana a kai ko kuma ya nuna yana son ta tunda ya san akwai batun aure tsakaninta da wani. Idan mutum nagari ne sai dai yai addu'a (ta alheri a kan auren). Amma su masu fadar maganganun sun kasance miyagu za su yi iyar kokarinsu su ga sun sami kanta, karshe idan ba su yi nasara ba, sai su jefo mata irin wadannan maganganu, da dai sauransu.
FIM: Tsakanin kai ko iyayenka akwai wani mataki da kuka dauko ko za ku dauka a kan wannan abu?
SHU'AIBU: Wannan abu ai shi kansa wanda furta hakan ya tuna wannan magana da ya furta kada ya ga cewa wani abu ya je ya yi ta mutu. Karya yake yi! Mu mun yi imani da Allah ba abin da zai same mu face sai abin da Allah ya kaddara. Wannan abu ya fada ne, in ma wani abu ne ya yi, to abin ya zo daidai da lokacinta. Dan'adam in an deba masa kwanaki, daidai da minti daya ba zai kara ba. Sanin haka shi ya sa za a yi watsi da wadannan maganganu, kuma ba wani mataki da za a dauka. In ma na ce zan dauki mataki, a kan me? Balaraba dai babu wanda zai dawo da ita. Ko ma me za a yi, ai kenan kamar mun nuna mu ba masu imani ba ne.
FIM: Akwai wani darasi da za ka iya cewa ka dauka dangane da al'amarin bani adam kan wannan abu?
SHU'AIBU: E, darasin da na dauka shi ne na kara yarda da cewa komai na Allah ne. Mutum yana tasa Allah yana tasa. Wanda kai abin da kake ganin za ka yi ko za ka iya Allah kuma bai saka maka ikon iyawar a cikin rayuwarka ba. Illa kawai abin da aka kaddara ma ka ga suna ta faruwa iri-iri. Shi dai mutum ya kasance mai imani, ya mika wuya ga Allah cewa duk abin da ya tsara masa haka yake.
FIM: Me za ka fada kan masu taya ka jaje da kuma masu cewa ai ka zautu?
SHU'AIBU: Abin da zan fada ga wadanda suke daga ne sa har ma da na kusa wadanda wannan labari ya same su, to duk abin da ya faru a kaina Allah ne ya kaddara shi haka. Kamar yadda na ga wannan masoyiya tawa ta kwanta ta mutu na san dai zan mutu ita ma za ta mutu. To amma mutuwar ta zo min a wani yanayi wanda na duba na ce ashe abin haka yake? To haka na yi imani cewa ko ma menene ya faru gare ni to daga Allah ne.
Idan na tuna zamana da ita shi ne rashin nata ke yi min kunci saboda irin shirye-shiryen da muka yi da kuma irin zaman da muka yi amma yau ga shi ba ta nan sai ni kadai. Wannan yakan sa zuciyata tana sosuwa. Amma idan na tuna Allah da abin da ya kaddara, hakan yana kwantar min da hankali. Kuma ina fata in Allah ya yarda za mu tare a Aljanna. A duniya dai an daura mana aure amma Allah bai bari mun tare ba. Za ta yiwu Allah ya shirya mana haka ne saboda soyayyarmu babu zalunci kuma babu cuta.
FIM: Su fa masu tunanin cewa ka haukace?
SHU'AIBU: Wannan kuma to! Ai ko shi kansa mahaukaci da ka tambaye shi zai ce shi ba mahaukaci ba ne, zai ce shi mai hankali ne. Kawai dai mutane sun gan ni a ranar da wasu kamanni daban. Ni dai abin da na rike a zuciya shi ne Allah. Wanda kuma ina iyakar kokarina in ga na gode masa. Idan na yi tunani a zuciyata na kawo Allah sai in ga ban ji haushi ba. Kuma ban fadi wani abu da ya fidda ni daga cikin addinina ba. Mutane da nake tare da su sun shaida na tambayi wadanda suka yi dawainiya da ni zuwa asibiti, na tambaye su: "Shin ko na furta wani abu wanda yake na sabo?"
Suka ce, "Wallahi duk haka ba ta faru ba."
A nan na ce, "To na gode wa Allah."
Ka san su mutane kowa na fadar irin abin da zai ji dadi a bakinsa. Abu ne wanda ya faru mutane ba su saba ganin irinsa ba. Ko da ma sun taba gani, to ba su taba ganin kamar wannan ba. Amma ni alhamdu lillahi lafiyata kalau.
FIM: Ga shi yau kwanaki 12 da yin rasuwar amma ba ka je Kaduna ba. Me ya sa?
SHU'AIBU: Abin da ya sa shi ne mun shigo wani yanayi ni da mahaifanta. Mahaifinta yana kaunata kwarai da gaske. Ni kaina a yanzu idan na doshi Kaduna yayin da na yi arba da shi ban san irin halin da zan shiga ba. Kin zuwa da na yi wani ragi ne nake masu wanda idan suka gan ni za su rika ganina da kamannin Balaraba. To ka ji dalilin da ya sa na jinkirta zuwa Kaduna gidan su Balaraba. Kuma har yanzu jikina ban gama jin karfinsa ba. So nake in sami kaina cikin lafiya sosai wanda ko da na je kamar shi mahaifinta akwai wasu bayanai da nake so na yi masa wanda za mu kara fahimtar juna.
FIM: Kumurci, muna so a nan ka yi wa iyayen Balaraba ta'aziyya yadda masoyanka da na Balaraba za su ji daga bakinka.
SHU'AIBU: Ni gaba daya iyayenta da danginta ina yi masu ta'aziyya. Kuma don Allah wannan abu duka su mika shi ga Allah. Da ma sun riga sun mika shi ga Allah. Kaddara ta riga fata. Kuma Allah ya nuna masu rana tun a nan duniya tsakaninsu da ita kowa ya biya wa kowa hakkinsa wanda gaba dayansu sun amince sun gafarta mata. A wannan lokaci Allah ya dauki ranta. Ina mai nuna masu cewa wallahi Balaraba diya ce. Akwai dan da za ka haifa wanda darajarsa za ta iya samun mahaifansa. Aurar da Balaraba da suka yi kamar jihadi ne suka yi a kai. Sanadiyyar haka Allah ba zai bar su a haka ba. Akwai wani abu da nake roko na musamman: Allah ya ba iyayenta wanda hankalinsu zai kwanta. Kullu nafsin za'ikatil mauti: Idan lokaci na mutum ya yi to Allah ba ya barin wani don wani. Balaraba Allah ya jikanta.
FIM: To yanzu sanadiyyar wannan abu ko alkiblar rayuwarka za ta canza?
SHU'AIBU: Wani abu ne da ban sani ba. Ni dai a imani da na yi da Allah ba ni da zabi a rayuwa. Kuma na kasance ko me na tunkara nakan sa addu'a a gabana.
FIM: Ga shi kun rabu har yanzu duk muna cikin jimami. Shin yanzu me kake ji game da Balaraba?
SHU'AIBU: Wannan abu da ya faru... To bari ka ji. Shekaranjiya (26/3/02) da zan kwanta sai na yi salloli na roka mata gafara wurin Ubangiji. Bayan na gama na kwanta ina barci sai na yi wani mafarki wanda wannan mafarki, insha Allahu, alhairi ne ga ita da ni da sauran danginta baki daya. Abin da na gani a cikin mafarkin shi ne lokacin da ina wannan barci sai na fara kuka. Ina ta kuka ina ta kuka ni kadai. Allah da ikonsa sai na ga Balaraba ta shigo ta zo ta zauna kusa da ni. Ina kwance. Sai ta ce, "Shu'aibu, menene?"
Sai na daga kai na kalle ta ban fada mata dalili ba. Amma na ci gaba da kuka. Sai ta saka hannunta a jikina tana rarrashina tana ce min in daina kuka. Tana cikin yi min haka sai na dauki hannu ni ma na taba ta. Sai ta ce min, "Shu'aibu, menene a hannunka?"
Na ce mata, "Wallahi ban sani ba."
Nan ta kama hannuna tana bambare wani abu a jikinsa. A cikin mafarkin da na bude ido sai na ga kamar kanta ko saba a jikina take dayewa. Ana cikin haka, sai na farka. Nan na kara yin godiya ga Allah saboda na san insha Allahu wannan mafarki akwai alkhairi a cikinsa.
To Allah da ikonsa wannan mafarki da na yi shi ne ya zame mani kamar wani magani a jikina. Ni da ba wata cuta gare ni ba sai dai kawai ina ji na haka ba dadi. To daga wannan mafarki da na yi sai ya zame mani kamar wani magani. A ranar sai na tashi na ji hankalina a kwance. Na kuma gane alama ce wadda zan iya samun komai ta dalilinta. Kuma alama ce ta ni da iyayenta wani abu na alkhairi zai same mu.
Kuma wannan mafarki a zuciyata abin da ake min nuni da shi shi ne ina tare da Balaraba ko da yaushe. Ina sa ran idan na koma ga Allah zan tashi tare da ita. In Allah ya yarda za mu dauwama a gidan Aljanna.
Fim: Allah ya tabbatar tare da mu.
SHU'AIBU: Amin amin.
KARIN BAYANI:Kwana 4 bayan mun yi wannan hirar, Shu'aibu tare da mahaifinsa da mahaifiyarsa da yayyensa sun je Kaduna gidan su Balaraba suka yi masu ta'aziyya. Haka kuma sun ziyarci kabarin Balaraba suka yi mata addu'a.
- Edita
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|