Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002
Babban Labari


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 



Tafiya mabudin ilimi

Rabo na minallahi, tauraruwar taurari Fati Mohammed tana daga dakin mijinta ta samu gayyata zuwa London. Babban dan rakiyarta shi ne mijinta Sani Mai Iska. Me suka je yi? Me suka gano? Me suka koyo? ASHAFA MURNAI BARKIYA ya fahimci cewa ba wanda ya fi SANI MAI ISKA sanin yadda tafiyar ta kasance daga bangaren Fati. Don haka sun tattauna.

Fati da Sani
Fati da Sani, tare da abokan tafiyarsu, sun dauki wannan hoton a birnin London
SHI rabo tamkar makami mai linzami ne wanda ake harbo jirgin sama da shi. Idan aka culla shi ga jirgi, ai duk irin kaucewa ko waskiyar da direban zai yi sai an kabo shi. To haka rabo yake; idan Allah ya tsaga mutum na da rabo kan wani abu, duk inda yake sai ya kurda ya same shi.

Irin haka ya faru ga shahararriyar 'yar wasan nan da ta yi aure, Fati Mohammed, kwanan nan inda wani kamfani ya bi ta har gida ya dauke ta tare da mijinta Sani Musa (Mai Iska) ya sheka da su birnin London.

Don jin sunan kamfanin da kuma abin da Fati ta yi a Turai har tsawon mako daya, wakilinmu ya je yi masu barka da dawowa kuma ya sami jin ta bakin Sani. Cikin wannan hira da aka yi da mijin wanda shi ma fitaccen dan wasa ne, za ku ji bayanai dalla-dalla kan yadda suka isa London da wainar da suka toya a can da abubuwan da suka burge su, da kuma yadda suka karke da shahararren dan wasan fim na kasar Indiya, mai suna Govinda, wanda Fati a tsinta a kan titi. Sani ya kuma fayyace wani nau'i na rayuwar aurensa da jarumar da ta fi kowace jaruma sa'ar yin sana'ar fim, musamman ma dai matsalolin da suke fuskanta daga wasu mata masu kai wa Fatin ziyara. Ku karanta ku ji.

FIM: Sani, muna yi maka maraba da dawowa daga Ingila da kai da matarka Fati.

SANI: Ni ma ina amsa maku da wannan barka da zuwa da kuka yi mana.

FIM: Masu sha'awar kallon finafinai za su so su ji abin da ya kai ku Ingila.

SANI: Wannan tafiya mun yi ta ne a bisa sakamakon wata gayyata da wata kungiya ta yi wa matata. Amma bisa sharadi na addini ba zai yiwu matar aure ta yi tafiya ba tare da mijinta ba, shi ya sa muka yi wannan tafiyar tare.

FIM: Za mu so mu ji abin da kuka je yi.

SANI: To abin da muka je yi ko kuma in ce abin da na raka ta ta je yi shi ne, akwai wata kungiya wacce take yaki da cutar kanjamau (AIDS), wannan kungiya ce ta ga ya cancanta ko kuma ta ga yiwuwar cewa za su yi amfani da wasu mutane wadanda fuskoki musamman na matasa suke da kauna tare da wannan mutane. Sai ya zama cewa matata ita ta samu wannan gayyata daga Arewa, aka ga cewa ita ta fi samari da 'yanmata; kusan kashi 70 daga cikin 100 suke da shauki ga ita wannan baiwar Allah da nake aure. Suka ga ita ce ta fi cancanta da wannan abu da suke son a yi.

FIM: An samu nasarar yin shi wannan abin?

SANI: E, alhamdu lillahi, mun je an yi shi kuma Allah ya sa mun dawo lafiya.

FIM: Mun ji an ce a da a nan Nijeriya aka yi niyyar aiwatar da abin, amma saboda babu kayan aikin ne a nan aka ce lallai sai an je can da ita.

SANI: E, to wannan ban san gaskiyar takamaiman abin da ya faru ba. Amma dai tun lokacin da suka zo muka fara maganar sun ce suna ganin saboda wasu mutane da za su yi amfani da su a wannan abu, ba a nan za a yi shi ba sai dai in ya zama dolen dole domin zabinta shi ne zabinsu.

FIM: Ka ce nan a Arewa ita kadai aka dauka. To ko akwai 'yan wata kasa ko wasu 'yan nan Nijeriya wadanda aka dauka kuka je can kuka hadu da su?

SANI: To a lokacin da muka zo kan tattauna maganar sun fada min cewa za su yi amfani da mutum hudu ne a Arewa: da ita da Tijanni Babangida, a Kudu kuma Kanu Nwanko da 'Miss World' (Agbani Darego). Kuma lokacin da muka je Legas wurin karbar biza sai suka kira ni suka ce sun canza wannan abu musamman da wadannan 'yan kwallo (Babangida da Kanu), sakamakon akwai wani abu ko da ya faru sakamakon wani kwallo da za a yi, saboda haka suka canza wadannan mutanen suka ce illa iyaka tana nan ita a Arewa a matsayin wadda aka dauka.

FIM: Lokacin da kuka shirya kuka tafi ya ka rika ji lokacin da kuka hau jirgi za ku je London, kuma ya ka ji lokacin kuka dira a filin jirgi?

SANI: Ban gane me na ji ba, misali.

FIM: Kamar ka ji wani irin canji ganin cewa lokacin ne ka fara dira a nahiyar Turai?

SANI: Ni wannan tafiya zan iya cewa kusan an yi ta ne ina barci domin kawai da ma mun bar Legas misalin karfe 12 na dare saura, kuma ba na mantawa mun dan yi 'yar zirga-zirga kuma da ma a ranar Asabar ce.

FIM: Da kuka isa birnin London ya kuka ji?

SANI: Da ma muna sauka birnin London bayan an gama screening na iyar binciken da suke yi na mutum idan ya je, duk da cewa alhamdu lillahi mu mun ci wasu arzuka ba a yi mana wannan bincike-bincike ba illa iyaka akwai wadansu mutane da yake abu ne ba na kai kadai ba da muka hau jirgi da su. Mu kam da ma da mun je akan bar mu mu wuce musamman idan sun duba faso din mu sun ga a matsayin ni mijinta ne ita, kuma matata ce. Muna gama wannan muna fitowa waje, already akwai wasu motoci da ke jiranmu, suka dauke mu suka aje mu a masauki.

FIM: Ita ainihin tallar wadda ta yi, a jaridu ko mujallu ko a fasta za a rika likawa haka?

SANI: Wadannan talla sun gaya min cewa da yake gaskiya su abubuwansu gaskiya akwai tsari, ba irin kara-zube ba ne, za ka ga cewa kowane abu za a nuna maka shi dalla-dalla. Wannan talla za su yi amfani da shi kamar fastoci haka da kuma stickers (daye-manna) kanana, sa'annan kuma za su yi amfani da gundarin maganr da ta yi (dialogue) a lokacin da ake yin kwallo, ko in an tafi interval (hutun rabin lokaci) ne za su nuna maganganun da ta yi.

FIM: Turawa ne ko kuwa bakaken fata suka shirya abin?

SANI: Na san wadanda suka zo suka gayyayce mu nan farko Hausawanmu ne na nan Arewa. Kuma da suka fada min wadanda suka ba da sunan ita Fati suka ce a yi bincike a tsakani suka ce sun ba da sunayen wasu mutane. Abin dai daga cikin mutanen har da wata Ministar Lafiya; akwai kuma wani mutum, sunanshi ya kwanta min.

FIM: Abin ya shafi sanin hukuma kenan.

SANI: E. to ya shafi da hukuma mana hakika.

FIM: Ko ka rike sunan ita kungiyar da ta gayyace ku?

SANI: The Society for Family Health shi ne ainihin sunan kungiyar.

FIM: Ta duniya kenan ko?

SANI: Zan iya cewa haka kenan, sanina dai sunanta kenan, ban sani ba ta duniya ce ko ba ta duniya ba ce, allahu a'alamu.

FIM: Kai da matarka kun je wata kasa wadda a tunaninku a lokacin ba ka zaci Allah zai kai ku can ba, sai ga shi dalilin harkar fim haka ta faru. To me za ka ce da wannan sana'a?

SANI: Ai maganar ma me zan ce da wasan kwaikwayo, wani abu ne wanda ni a kan kaina ba zan iya fadin menene ba sai dai in ce Allah Ubangiji na gode masa. Kuma daga cikin abubuwan da na gani na ban mamaki, wato dan wasa abu ne mai daraja musamman idan ka fita waje. Ba na mantawa, lokacin da za a yi mana passport an tambaye ni menene sana'ata? Sai na ce a sa min kanikanci. To akwai wani mutum, ana ce mai Dokta Sani Isa, wani malami da yake a Kaduna, da man da shi muka yi tafiya don ya duba abin ta fuskar addini, shi ya ce kada a sa min kanikanci, a sa artist (dan wasa). Da na tambaye shi sai ya ce ai matsayin artist a Turai, kamar nan ne a ce dokta wane ko furofesa wane ko sheikh wane.

Don haka wasan kwaikwayo sai dai in ce Allah ya kara masa daukaka, musamman mu na nan Arewacin Nijeriya. Duk wanda ya je wurin duk da cewa kwata-kwata kwananmu bakwai, amma na ga abubuwa na ban mamaki; sai na ce mu a gaskiya kamar yadda aka ce wasan kwaikwayon, to mu wasa muke yi makar yadda na ga su nutanen suke tafi da ayyukansu.

FIM: Wane irin bambancin kayan aiki ne ka gani har ya nuna maka cewa mu nan da wasa muka dauki abin?

SANI: Ba wai ina nufin wasa haka ba. Irin yadda na ga tsarinsu da kuma yadda na ga irin daurin gindin da suka samu. Mu kanmu nan muna son yin sama da wannan amma ba mu da wadanda suka tokara mana in ba Allah ba, da kuma wasu tsiraran mutane wadanda ba a rasawa. Gaskiya duk mutumin da ya ga yadda mutanen nan ke aiki kuma ya auna da namu zai ga akwai bambanci ba ma daya ba.

FIM: Malamin da ka ce kun tafi da shi, ku kuka dauke shi ko hukuma ce ta dauke shi don ya je ya ga yadda al'amarin yake tafiya?

SANI: Wwato da ma abin da ya faru, ka san akwai kungiyoyi na addini kuma musamman na Arewa din nan wadanda suke da hedikwatarsu a Kaduna. Lokacin da suka fitar da abubuwan, da sunan Fati ya fito sun tuntubi malamai a kan menene illar abin? Kuma yaya za su bullo wa abin? Da suka hada abubuwan da malamai a ciki, sai aka yi gyare-gyare. Kuma sai malaman suka ce in suna so a kara nasara a kai, to dole a tafi da wani mutum wanda yake da wayewa da zamaninshi kuma masanin addini ne, sa'annan abin ba zai saba al'ada ko addini ba. Saboda haka wannan malami su suka dauki nauyinsa muka tafi da shi.

FIM: Wadanne abubuwa ne suka burge ka? Kuma ko kun sami sukunin yin wadansu 'yan ziyarce-ziyarce?

SANI: To gaskiya ka san duk mutumin da ya yi tafiya irin wannan, musamman wani wuri wanda ba ka taba zuwansa ba, zai zama duk abin da ka gani a wannan wurin bako ne a wurinka. Don haka zan ce kusan duk abin da na gani gwargwaon hali ya burge ni, sai dai kuma dan'adam ba ka raba shi da wani abu wanda zai gani ya bata masa ko ya kuskure masa. Amma dai na ga abubuwan da suka burge ni, musamman yadda mutanen ke haba-haba da bako.

FIM: Lokacin da ka labarta wa Fati maganar tafiya, me ta nuna? Kuma da kuka je ta kara nuna cewa ita zakara ce a harkar fim?

SANI: Fati wata aba ce wadda Allah shi ya san sirrin da ya sanya mata game da al'amarin rayuwarta. Ni kaina na yi tunanin wannan abu, musammana yadda suke girmama ta ga su kuma sun ci gaba, Turawa ne. Amma irin yadda suke nuna kololuwarta a kan abu, na yi tsammani za ta samu wani girman kai, musamman idan ta duba ta ga cewa kusan duk gayyar mu bakwai an yi tafiyar ne saboda ita, idan ka fidda Turawa guda biyu masu jagorantar abin. Amma sai ya zama wannan bai sa ta canza min daga rayuwarmu da muke da ita ba, sai ma abin da zai kara kwantar min da hankali da ita. Sannan a lokacin da labarin ya zo min, domin mutanen sun zo nan sun kwana uku ba mu hadu ba, sai wani mutum mai suna Kwaki ya kawo su ya ce daga Legas suka zo suna son ganina. Suka gaya min gashi ga shi abin da suke so, suna so za su yi amfani da matata a matsayin wani abu da suke so su tallata wani abu domin wayar da kan jama'a kan wani abu.

Lokacin na nuna masu cewa ba zai yiwu ba domin gaskiya aure take yi, sai dai na ce ba zan ce ba zai yiwu ba, sai na yi shawara da wadanda suka san hukuncin Allah a ciki. Na ce su ba ni kwana biyu ko uku zan yi bincike a kan wannan. To a nan sai suka nuna min cewa in dai wannan ne sun gama already. Sai suka fada min sunayen malaman da suka tuntuba a kan wannan abu. Kuma suka ce idan ina da bukata ban gamsu da abin da suka fada min ba, to in je mu je domin in ji daga bakin wadannan malamai. A karshe na bincika na gano haka ne.

FIM: Wane kira za ka yi wa 'yan fim da sauran masoyan Fati? Kuma rana daya aka gama aikin ko kuwa?

SANI: Gaba daya da ma shirin na sakan 45 ne, to amma ka san abin da aka ce za a yi tafiyayya, sun bukaci za ayi rehearsal (atisaye) da wasu abubuwa. Don har lokacin da muka je Ingila shi wannan script na gundarin maganganun bai zo hannunmu ba, illa iyaka dai mun san me za a yi. Bayan mun je da kwana biyu, suka zo muka zauna mitin da su. Suka ce ga script amma abin da suke so ta zauna ta yi rehearsal na kwana biyu ranar ta zauna ta yi rehearsal na kwana biyu, ranar na uku sai a yi shooting.

A nan ta nuna ba sai ta yi rehearsal ba, in don wadannan maganganu ne tana ganin za ta iya su. Har ma akwai (wani mutum) daya da muka tafi da shi, ya takura ya ce yaya ba za ta yi rehearsal ba kuma ga shi daya wanda suka yi abin shi fitacce ne a duniya amma sai da ya yi rehearsal? Sai shi daraktan abin ya ce a kyale ta tunda ta ce ba sai ta yi rehearsal ba za ta iya. Haka kuwa aka yi, sai ranar da za a yi abin muka je da karfe 9 na safe. Wajen karfe 2 na rana aka fara zuwa 4 na yamma an gama, muka koma.

FIM: Shin yanzu a shirye kake in an sake kiranta ko da wata kasa ce za ka bari kenan idan abin dai saba wa addini ko al'ada ba?

SANI: Ai wannan wani abin a yi alfahari da shi ne, domin kyauta ce daga Allah. Kuma kamar yadda ka fadi, ka ce idan bai saba addini ko al'adarmu ba, ai kai ma ka yake hukunci, in dai saba wa addini ba ai bai zama haramun ba. Kuma sannan wannan da ta yi wani abu ne kamar kara maimaita wata aya da Allah yake cewa, "Wa amiru bil ma'arufi wa yan hauna alal munkari," cewa "ku yi umarni da aikata abu mai kyau sannan ku yi hani da mummunan aiki." To ita abin da ta je kenan ta yi. Ka ga zan iya cewa ta yi wa'azi ne amma tana dakin mijinta kuma sannan ta samu wani amfani na duniya har ni ma nan ga shi na ci albarkacinta na samu bakin gwargwado.

FIM: Mu dan saki tafiyarku London, mu koma kan ita Fati. Lokacin da aka dauka maku aure ta tare Allah ya albarkace ta da dimbin masoya. Daga cikin masu zuwa ganinta a gidanka akwai masu korafin cewa 'yan gidan da kuma ita Fati suna canza mata fuska. Shin menene gaskiyar abin da ake yadawa?

Sani, mijin Fati
Sani Mai Iska
SANI: Gaskiya ana nuna mana kauna har ya zuwa lokacin da nake maganar nan. To amma da yawa wasu ba'arin mata irin abubuwan da suke zuwa suna aikata mana gaskiya duk mutumin da yake da hankali ba zai so a gidansa haka ta faru ba. Domin mutane za su zo a kullum gidanmu sai ka dauka gidan biki ne ko wani asibiti haka, wannan ya zo wannan ya tafi. Kuma ka san jiki da jini. Za ka tarar da mata akalla kusan guda 40,30,50 sun zo gidanmu, wasu a waje, wasu a soro wasu a daki, wasu kuma a tsakar gida.

To idan mutum ya zo a matsayinsa na ziyara, ya kamata idan kun gaisa to ya fito ya tafi. Amma sai ya zama akasari sai kuma abin da zai biyo baya, "A fim kaza ya akai kika yi kaza?" To da zarar ta ce, "Ni yanzu aure nake ba na bukatar wannan zancen tare da ni yanzu," (sai a ce:) "Da ma ke mai wulakanci ce don kin zama wani abu? Ke ba Annabi ba ce!" da suaransu. Sai ka ga har da doke-doke.

Kuma ka auna ka ga rayuwa irin ta mata, gidanmu family house ne (gidan yawa), akalla akwai mata wadanda ke aure kamar guda hudu. Sannan akwai yara 'yan gidan wadanda sun kai takwas ban da 'yanmata wadanda suke kannenmu ne. To ya wata mata mace ta zo a matsayinta na bakuwa, don kin zo kawai ganina don na ce ba ni da bukatar yin wata magana da kika zo min da ita shikenan sai zagi ya biyo baya? Ta yaya wadannan mata ko yara za su kyale? Ka ga zai yiwu ba.

FIM: Wane kira za ka yi wa masu zuwa wurinta da kuma wadanda akan kai wa wasu labarai game da ita?

SANI: Kauna alhamdu lillahi musamman mata sun nuna kauna; ba ma mata ba kawai mutane da yawa sun nuna kauna da yawa a kan al'amarin Fati da kuma ni. Gaskiya, kiran da zan yi mata shi ne don Allah don Annabi duk wadda ta je gidanmu idan ta ga gidan a rufe, ba a so a shiga. Ai mutum yana da dama a gidansa ya ce kada a shigarmasa. Musulunci ma ya hana ka zo gidan mutum kai-tsaye ba tare da ya san da zuwanka ba. Idan kuma ka zo ba tare da ya sani ba, to za ka yi sallama guda uku ne; idan an ce ka shigo, to sai ka shiga; idan an ce kada ka shigo shikenan ka yi tafiyarka, tunda ba wani abu ka zo nema wurinsa ba. Ka zo ne domin yi masa addu'a, kana rokar masa Allah.

Saboda haka don Allah mata su yi hakuri, saboda irin abubuwan da suke faruwa idan sun je gidan suka ga an hana su shiga, to su yi hakuri. Abin ne ya zama babu yadda za mu yi. Domin daga aurenmu zuwa wannan lokacin ina tabatar ma a kan rigingimu na mata, wata ma kawai za ta zo ne yaron unguwarmu ne zai ce an hana shiga za ta ce, "Ina ruwanka?" Shikenan idan sun yi fada sai ta kai kara 'police station' ai ta zo gidan Fati an ci mata mutunci har an dake ta ko ta ce ta jefar da sarkarta ko waye, da sauransu.

Saboda haka wallahi na je 'police station' ban san adadinshi ba, ban da wanda ba na nan babana zai je ko wana zai je. To ka ga duk wannan ina amfani? Ina ganin ita wannan yarinya (Fati) ta yi aure ne domin ta huta da wasu masifu da gallazawa irin na rayuwar waje. To ka ga ta yi auren nan ba ta huta ba, menene amfani kenan? A nan mutane sun zaman mata masifa maimakon su zamo mata rahama.

Kuma wani abu karin dadin dadawa, za ka sha mamaki, ya kamata duk ziyara ta Allah da Annabi a kawo ta daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma. Amma sai ka ga har karfe 12 na dare an zo gidanmu - wallahi Allah kuwa! Ka ga wannan ai ya wuce kima!

FIM: Wane kira za ka yi wa 'yan fim na su kara rike sana'arsu da daraja domin kai ka fita kasar Ingila inda ka gano martabarta?

SANI: 'Yan fim wannan ba wai kira ba ne, gargadi ne, domin ni ina ganin kamar ina so in isar masu da wani sako ne. A gaskiya, wannan sana'a idan mutum ya yi mata riko goma ne, to ya ninninka ya yi mata riko dubu. Domin sana'a ce wadda take ba karama ba. Za ta iya kai ka maytsayin da a mafarki ba ka taba tunanin wannan ba.

FIM: Me za ka iya cewa kun gano wanda ba za ku taba mantawa da shi ba?

SANI: Gaskiya na ga abubuwa daban-daban, sai dai kawai in fadi wadanda suka zo min a kaina. Wanda na fi ji shi ne guda biyu: da muka hadu da wani shahararren jarumi da ake ce da shi Govinda har muka yi hoto da shi. Kuma akwai Ministan Karafa na nan (Nijeriya) da muka hadu da shi. Shi ne ma ya zo ranar Jumma'a ya kai mu har masallaci mukai salla. Wadannan abubuwa na daga cikin abubuwan da ba zan manta da su ba cikin wannan tafiya da muka yi.

FIM: Shi Govinda, abin da kuka je yi ne ya je ko kuwa haka kawai Allah ya hada ku da shi?

SANI: Mun tafi cin abinci ne, muna cikin tafiya, daga cikin mazan ba wanda ma ya gane shi, sai Fati ta ce, "Wancan kuwa Govinda ne!"

Har ma aka dan yi jayayya, wasu na cewa ba shi ba ne. Akwai wani Abdullahi Maiwada, yana kwala masa kira, ya ce, "Govinda!"

Sai (Govinda) ya katse wayar (da yake yi). Muka je muka gaisa. Da ya tambaye mu daga ina muke, sai muka ce Nijeriya. To cikin dan barkwancin da muka yi da shi, ko da Maiwada ya ce masa "Wannan (Fati) tana acting din dirama ne a Nijeriya, a Arewa, shi ne to da wasa yake cewa ai suna da labarin abin da ke faruwa; ba mu ne muka kashe kasuwar finafinan Indiya ba?

Shi ne Maiwada ke ce masa ai har yanzu ana kaunarsu, don da ba a kaunarsu ai da (Fati) ba ta kira sunansa ba ko ta gane shi. Daga nan muka kara yin wasa, ya wuce muka wuce.

FIM: To akwai ...

SANI (ya katse hanzari): Ina son in kara yin magana kan mata masu son kawo ziyara. Ba ina nufin na hana mata kawo ziyara ba ne. Ka gane? Duk mutum na jama'a zai so mutum ya zo wurinshi. To amma akwai sharudda. Wadanda suka biyo ta wajena nakan ba su shawara. Duk mata ina ba su shawara tunda Allah ya sa ni na dan bude matsuguni (ofis) a matsayin mijinta. To a biyo ta ofis dinmu, sai in hada mutum da yaro ya je a gaisa, don na sha yi wa baki haka. Idan kuma gida aka je, to a dan rika rubuta dan bayani a aika cewa "mu ne baki daga wuri kaza," ba wai a ce sai an shiga da karfi ba. Idan wannan ta faskara, to akwai lambar waya. Idan suna da sha'awar zuwa sai su bugo wannan lamba kafin su zo: 080-23419849.

FIM: A karshe, shin gaskiya ne abin da ake fadi cewa Fati tana da juna biyu dan wata bakwai?

SANI: Fati ta samu rabo amma Allah bai bar shi ba.

FIM: Ta yi raggon kaya kenan?

SANI: Ban gane 'raggon kaya' ba. Ban san wannan Hausar ba.

FIM: To ta yi bari kenan?

SANI: Yauwa, haka ne!

FIM: Allah ba ta rayayye.

SANI: Amin.

Fati ba ta yi fim daga gidana ba - Mai Iska

FITACCEN dan wasa Sani Musa (Mai Iska) wanda ya auri Fati Mohammed ya karyata rade-radin da wasu ke yi wai Fati ta fito a cikin wasu finafinai ko wani fim bayan ta tare a gidansa. Sani ya karyata zargin ne kwanan baya kafin tafiyarsu Ingila, lokacin da yake amsa wasu 'yan tambayoyi daga mujallar Fim.

Ya ce duk abin da ake fada ba gaskiya ba ne domin irin wannan yarfe da suka ba sabon abu ba ne a wurinsu. Ya yi nuni da cewa Fati ba wadda za a iya yin wani fim a boye da ita ba ce. "Idan kuwa da an yi ai da kowa ma ya ji," inji shi.

Mijin fitacciyar jarumar ya ce abin da ke faruwa shi ne Fati ta yi finafinai da yawa kafin ta yi aure, wasu har yanzu ba su fito ba. "To wasu idan suka ga fim din kwanan nan sai su yi tsammani ko a gidana aka je aka dauko ta ta yi fim din," inji Sani.

Kuma ya furta cewa a halin yanzu akwai wani fim mai suna Rikicin Bankwana wanda ita Fati Mohammed din ce furodusar fim din. Da aka tambaye shi yadda fim din yake sai ya ce an yi fim din ne tun kafin ta yi aure. Mafi yawan abin da fim din ya kunsa, inji Sani, shi ne hannunka-mai-sanda kuma abubuwa ne da suka zama kulle-kullen da wasu suka yi kan auren nasu da kuma "makirce-makircen da wasu suka yi don kawai su ga cewa aurenmu bai tabbata ba."

Fim din Rikicin Bankwana zai nuna matsaloli da nasarorin da muka fuskanta. Zai nuna sharrin makiya da na munafukai," cewar Mai Iska.

Fim ta kuma tambayi Sani Mai Iska ko Fati za ta ci gaba da daukar nauyin shirya fim, wato ta zama furodusa tana daga dakinta? Sai ya amsa, "Ya danganta da sha'awarta da yin haka."

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin