Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Ahamed Sadiq Nuhu: Yaro Mai Tashi

Ahmed
'Ango' Ahmed da A'isha B. Umar a fim din Daren farko

AKWAI wani al'amari da ya faru ga Ahmed S. Nuhu, a rayuwarsa ta dan wasan fim. Kwanan nan ne wani furodusa da kanensa darakta suka je gidan su Ahmed a Kano, suka samu 'yar'uwarsa Hajiya Amina (yayar shahararren jarumi Ali Nuhu). Da suka zo, sai suka yi ta kewaye-kewaye a kan ainihin abin da ke tafe da su. Sai can ne daya ya ce mata, "Bayan haka muna so mu sanar da ke cewa daga yanzu mu mun daina sa Ahmed a finafinanmu."

"Saboda me?" ta tambaye su.

"Saboda ya fito a wani fim da mujallar Fim ta shirya. Mu kuma kin san ba mu da abokan gaba da suka wuce mujallar Fim. Shi ya sa muke ganin tunda muna tare da Ahmed ba mu yarda ya je ya yi wa mujallar Fim fim ba."

Abin ya ba Amina mamaki matuka. A lokacin Ali da Ahmed ba su gida, sai da suka dawo ne suka ji labari. Hankalinsu ya tashi, har shi Ahmed ya harzuka, yana cewa, "Arziki fa na Allah ne. Idan sun daina sa ni a fim sai me kuma? Don suna gaba da 'yan mujallar Fim shikenan kuma ni ba zan yi hulda da 'yan mujallar ba?"

Irin wannan ra'ayin na Ahmed ya taimaka gaya wajen samun bunkasar wannan hazikin matashi, wanda tun tashin farko ya biyo sawun kawunsa Ali Nuhu wurin samun daukaka a wannan harka. Ahmed mutum ne mai hankali wanda duk abin da zai yi sai ya tsaya tsaf, ya yi tunani, kafin ya aiwatar. Idan kuwa ya aiwatar, to fa ba zai taba yin nadama ba. "Ban damu ba," inji shi lokacin da yake ba wani darakta labarin wadancan maziyartan. "Su je sui ta yi."

Kwanan nan Ahmed ya gama aikinsa na daukar shirin Daren Farko, fim na biyu da mujallar Fim ta shirya, bayan Gagarabadau, wanda zai fito a ran 20 ga wannan watan. Kuma ya nuna hazakar da aka san shi da ita, wadda ake ganin ta sa ake ganin lallai Ahmed yana daga cikin zaratan zakaru da ba su wuce biyar ba da ake jin dayansu zai ci gasar finafinai ta Arewa a ajin Jarumin Jarumai (Best Actor). A bana, ya yi manyan finafinai wadanda suka sa, bayan mujallar Fim ta nada Ali Nuhu Yaro Mai Tashe (a cikin 1999), yanzu kuma ta nada Ahmed Yaro Mai Tashi. Tashin da yake yi kuwa tashi ne irin na gwauron zabo. Allah kadai ya san inda zai tsaya.

Mun dade da yin wannan hirar da Ahmed, domin mun yi ta tun kafin Allah ya yi wa Balaraba rasuwa. Mun yi ta daga buga ta ne saboda al'amuran da suka dinga faruwa a fagen shirin fim, kama daga aure da rasuwar Balaraba, da zuwan Fati Mohammed kasar Ingila. Sai dai mun sake waiwayarsa har sau uku don mu kara tabbatar da wasu abubuwan daga gare shi, musamman wadanda suka biyo bayan hirarmu ta farko da shi, ciki har da labarin furodusoshin da suka kai wa Amina ziyara, suna yi mata barazana a kansa, sai ka ce su suka kawo shi Birnin Kano ko kuma za su iya sa ya bar birnin.

Yanzu dai ga ku ga Ahmed. Bismilla:

FIM: Ahmed, kai ba dan Kano ba ne, amma dalilin fim ka zo Kano har ka yi fice. Shin za mu iya jin yadda kake jin dadin zama cikin garin a matsayin garin da ba naka ba?

AHMED: Farkon zuwana garin ba ya yi min dadi saboda bakunta. Amma yanzu kam ina jin dadin Kano sosai, don ka ga na samu abubuwa masu muhimmanci da ba zan iya mantawa da su ba.

Kamar me?

AHMED: Na samu daukaka, na yi suna, kuma na samu rufin asiri duk a harkar fim din nan. Ba abin da zan ce wa Kano din nan sai kawai Allah ya kara mata daukaka.

Bayan Mujadala da Kudiri da ka fito ciki kuma ka yi fice, akwai wasu finafinai da ka fito da wata sifa daban kamar a Huznee inda ka fito bebe kuma mai tabin hankali?

AHMED: A lokacin da na yi Huznee ni kaina abin ya ba ni mamaki, saboda ban zata zan iya yin role din ba. Lokacin da darakta ya ba ni, ni ban je gidan mahaukata ba. Amma sai daga baya da ina kallon fim din sai nake mamakin kaina da kaina - wai ni ne na yi wannan fim din, sai ka ce wani mai iskokai! Saboda, ba zan taba mantawa ba, lokacin da shi darakta ke karanta min role dina a fim din sai na ji tsoro. Na ga kamar idan na yi fim din mutanen gari za su zage ni. Saboda na yi negative role (shirin da kan nuna halin banza).

Kuma gaskiya dalilin Huznee na samu kyautuka da dama da ake aiko min, kamar turare ko shadda. Wasu har wasiku sukan aiko a kan su ba su taba ganin dan wasan da ya yi kamar wannan ba. Sai ni na fitar da wata sifa daban wadda ba tawa ba ce. Ni dai ba irin haka nake ba. Amma ko a jiya wasu sun yi fada a Brigade, wasu sun dauka ni mahaukacin gaske ne. Daya daga cikinsu ya ce ai shi ya ma gan ni shekaranjiya, daya kuma ya ce ai wallahi tallahi na tabu, ina gidan mahaukata zaune. Shi ne suka kwaso jiki suka zo suka same ni suka gan ni, na ce masu ai shirin fim ne. Ni kam Huznee sai dai in yi wa Hafizu Bello godiya don na samu daukaka dalilinsa. Wasu daga Malesiya ma, wani Bature ya aiko min da wasika ta godiya a kan wasan da na yi a cikin fim din.

An ba ka kyautar mai bin jarumin jarumai na shekarar 2002. To me za ka ce game da wannan?

AHMED: Gaskiya na ji dadi, amma kuma na yi mamakin yadda masu ilimi suka shirya wannan gasa har aka samu failure (kasawa). Ai ta farko da aka shirya a Kano ta yi sosai. Su kansu wadanda suka shirya wadannan abubuwa ni ba su burge ni ba.

To ko don sojoji ba su shaida ka a wurin ba har suka dake ka da gindin bindiga yayin da ka je shiga?

AHMED: Gaskiya, daga farko ka ga babu tsaro. Ba a shirya abin daidai ba. Na je zan shiga shi kuma soja yana daga bindiga zai daki wasu don su matsa in wuce, sai ya dake ni a kirji har aka kai ni asibiti. Mutane da dama wasu har kuka suka yi a wajen, suna ganin kamar ma na mutu. A daren da aka kai ni asibiti na yi kokari na dawo wajen wannan gasa.

Da, na ki in je in karbo wannan kyauta da aka ba ni saboda in ka lura a Mujadala ni ba 'supporting actor' ba ne. Don in aka ce in zaba daga cikin Mujadala to ba zan zabi kaina ba sai dai Abida ko Fati. Amma abin mamaki sai suka zabe ni inda muke shan lemo. Ai kamar ma talla ne muke yi masu. Kawai na ga yarinya ne, nake nuna ta, daya yake ba ni shawara yake cewa mu je. Ban ga wani acting da na yi a nan ba.

Ai kafin nan mutane na cewa kai ne 'actor' a Mujadala. Shin ba 'supoporting actor' ba ne kai?

AHMED: Exactly, ni bai dace kwata-kwata ba a ce an ba ni (kyautar) supporting actor ba. Ni Best Actor na nema a Mujadala da Huznee inda na yi mahaukaci kuma bebe, sai Kauna inda Abida ta fito a kurma, da kuma Kudiri inda Fati ta fito a mahaukaciya. To wadannan ukun in za a yi alkalanci dole ne a san abin da za a ba ka.

Ahmed ga shekara ta 2002 ta shigo. Yaya kake ganin yiwuwar cin Best Actor a gasa mai zuwa?

AHMED: Wallahi ni ba na so.

Ko don kana ganin akwai zaratan 'yan fim matasa?

AHMED: A'a, ni tunanina akwai na gaba da ni, su ya kamata su samu. Kai ni tun da na sami wannan problem (na dukan da aka yi masa a Kaduna) ni wajen ma ba na son zuwa. Zan zama kamar Amir Khan na Indiya. Ka ga shi ma ba zuwa yake wurin bikin ba da award ba. Haka ya fi min sauki, kuma hankalina zai fi kwanciya.

A gasar wannan shekara mutane na ganin har da kai za a kara fafatawa. Shin ya kake ji idan aka sa finafinanka da na wasu kamar su Ali, Momo, Sani Danja ko Zulkifilu cikin wadanda za su kai matakin karshe (nomination)?

AHMED: A takaice, ka san shi abin, Ubangiji Allah ne ke bayarwa. Na san a shekarar da ta wuce an yi son kai da yawa. Amma wannan karon ko za su sake ko ba za su sake ba, ban sani ba.

Son kan da kake fada, to kai aka yi wa ko wani naka?

AHMED: In ka lura bai dace a ce na ci Best Supporting Actor ba.

Mu koma kan finafinanka da za su iya shiga takara. Daga watan Nuwamba zuwa yanzu wadanne finafinai ne kake takama da su?

AHMED: Na farko ina da fim din Sharadi da Juyayi da Zubaida da kuma wasu biyu, ciki har da fim din da mujallar Fim ta shirya (Daren Farko); shi ma ina takama da shi; ina matukar son ganin ya shiga cikin gasar Arewa; sai kuma wani sabon fim na Lere mai suna Soyayya.

Cikin finafinanka na wannan shekara ko akwai wani wanda ka fito da wata irin siffa da ba a san ka da ita ba kamar yadda ka fito a cikin Huznee a shekarar da ta gabata?

AHMED: E, Daren Farko da kuma Juyayi. Ina ganin insha Allahu za su karbu a hannun mutane.

Can baya ka yi maganar yadda Allah ya hore maka jama'a masu aiko maka da wasiku da kuma kyaututtuka. Mun taba ganin wata wasika da wani babban mutum ya aiko cewa a shirye yake ya dauki nauyin karatunka a jami'a. Shin ka mayar masa da amsa?

AHMED: Wannan bawan Allah babu abin da zan ce sai dai in gode masa saboda alherin da yake aiko min da shi daban-daban. Kuma wannan mutumin sai daga baya na bincika ma na samu tabbatarwa dan'uwa ne ma; ya hada dangantaka da babana. Shi kansa bai sani ba, sai da ya gan ni a Abuja ya san ni. Shi ne a yanzu haka ya rike ni tamkar dansa na cikinsa.

To yanzu me kuke ciki? Maganar makarantar tana nan ko kuwa sai dai wani taimako kawai na musamman?

AHMED: Tana nan, amma sai na yi aure zan ci gaba da karatuna. Saboda ya daure min gindi cewa ko wace makaranta nake so a duniya zan iya zuwa ya nema min hanya in tafi.

Kana ganin za ka iya hada gudu da susar kafafu - ga fim, ga makaranta ga amarya?

AHMED: Kwarai. Yanzu idan ka lura, akasarin dalibai wasu sai sun yi aure ma suke karatu. Yanzu ka dubi irin su (Ibrahim) Mandawari da Shehu Hassan Kano, ai duk sun koma makaranta, ba don komai ba sai kara ilimi. Amma ni makarantar da zan koma, University of Abuja, Asabar daLahadi ne kawai zan je in ji lacca in dawo in ci gaba da harkokina, shikenan. Kana ba zai hana ni sana'ata ba, kuma aure ba zai hana ni karatu ba.

Wasu idan sun gan ka sukan yi maka kallon Dandugaji; shi ma wasu na yi masa kallon Ahmed S. Nuhu. Ko ka taba shiga cikin rintsin mutane aka rika ce maka "Ga Dandugaji! Ga Dandugaji!"?

AHMED: Ba zan taba mantawa ba, ko da can kafin in yi suna ana ce min 'Dandugajin Jos'. Lokacin da na fara yin fim dina na farko, Dijangala, da muka je wani gari, fim din kasa yiwuwa ya yi saboda yara na ce min Dandugaji. A da so nake yi, amma yanzu (dariya) ba na so. Shi comedian (mai wasan barkwanci) ne, ni kuma actor ne. Amma yanzu an fara ganewa ni ba Dandugaji ba ne.

Ana yabonka wajen sakin fuska ga jama'a. Shin wannan halinka ne ko kuwa ka taba daga wa wani kai shi kuma ya dankwafar maka da kan kasa, shi ya sa ka yi hankali?

AHMED: Gaskiya ni halina na gada ne daga wajen mahaifina. Tun kafin ya rasu yake fada mana cewa duk inda muka ga mutum kada mu wulakanta shi. In Allah ya ba ka daukaka ko arziki kana wulakanta mutum, shi kuma ba ka san abin da Allah zai yi masa ba. Ya ce min idan na wulakanta mutum, to kamar shi na wulakanta, kuma bai yafe mani ba. Kamar fim dina Zubaida, ai idan ka lura Hausa ce na yi ciki kan masu wulakanci. Mu ('yan fim) fa ba kudi gare mu ba, amma za ka ga masu kudi ko 'ya'yan masu kudi sun zo wurinmu saboda daukakar da Allah ya ba mu. To menene amfanin wulakanci? Babu. Wallahi ko kuturu ne ya zo wurina ni ba zan wulakanta shi ba. Saboda ni ma ba komai ba ne, suna ne kawai na yi. Daga Nijar, Kamaru, Chadi da Ghana duk ana tahowa a zo ganinmu ba don komai ba sai don kauna.

Can baya ka ce ba za ka zarce makaranta ba sai ka yi aure. To da ma Hausawa na cewa idan ka ga kare na sunsunar takalmi, to dauka zai yi. Shin kai wane takalmi ne ka gani da maiko har kake kokarin dauka ka kai gida?

AHMED: Yana nan a boye saboda ba yanzu ba ne zai iya fitowa fili.

Amma me za ka boye? Ai magana ta game 'yan fim da cikin gari cewa kana neman Maryam Mushaqqa da aure. To ka fada wa mutane gaskiyar abin da ake ciki.

AHMED: Wato ka san su mutane idan suna ganinka kana fim da mace, sai su rika yi maku zargin kamar kuna soyayya ne, alhali rikon amana ne da kuma kusantaka. Amma ni ba zan iya fadar wai ko muna soyayya da Maryam ko wani abu ba, sai dai lokacin da Allah ya yi su ga matata.

Amma ai kai da Maryam kun je wani shirin fim kwanan baya, Mu Shakata na 4. Shi wannan fim an gayyaci wadanda ake da tabbacin aurensu, kamar Rabi Mustapha da A'isha Ibrahim, da kuma Balaraba. To idan babu zancen aure tsakaninka da Maryam, me ya kai ku wurin har mai gabatarwa Halima Adamu Yahaya ta yi maku tambayoyi?

AHMED: Ni Mandawari bai kira ni da sunan in je za a yi min tambayoyi a kan maganar aure ba Ya dai kira ni ne zai yi Mu Shakata 4 na zo, na ga an gayyaci Maryam a wurin; shi ma kansa sai da ya gane; kusan mu 'yan fim ba mu da sirri.

Ya gane me?

AHMED: A lokacin shi Mandawari ya gane babu wani zancen aure tsakanina da Maryam (dariya). Aka tambaye ta, ta ce abin sirri ne, ni ma aka tambaye ni na ce abin sirri ne!

Me ya hana ka ce babu aure tsakaninku in har babu? Su mutane na ganin kai Ahmed da Maryam kun boye wani abu, to kuna gudun kada 'yan zuga su je su bata lamarin ne?

AHMED: Wato idan ka lura, duk wanda aka ce maka yana wasan fim ko dan kwallo, duk wallahi ba mu da sirri. Duk abin da ka yi a rayuwarka za a bi ka a je a ga menene kake yi. Yau ko rashin lafiya ne ya same ka sai duniya ta ji. Saboda haka shi aure fa aka ce sirri ne daga Ubangiji kuma sunna ne daga Manzon Allah (SAW). Ka ga yadda na yi suna bai zama lallai ba ne in gaya wa duniya zan yi aure. Ka ga kamar Momo, ga ranar auren tashi nan ta kusa amma ba wanda ya sani.

Shi ya sa kake boye naka kenan?

AHMED: Zahiri shi ya sa nake boye nawa, har lokacin ya zo in yi aure amma na san ina da mata a Kano kuma tana nan ta san kanta ita matar tawa.

Abin ya kusa kenan?

AHMED: E, abin ya kusa in Allah ya yarda, don gara mutum ya yi aure ya huta.

Ko gakiya ne wasu daga cikin danginka sun yi kokarin hana ka yin auren?

AHMED: Wallahi duk ba haka ba ne. Saboda ni ma abin da nake son yi, yanzu kanena har matarsa ta haihu, haka daya kanen nawa kwanan nan ya yi aure. Ni kadai ne ban yi ba.

Farkon shigowar Maryam fim sai muka ji ana cewa kai da Maje El-Hajeej kun dan yi kasayya…

AHMED: Gaskiya surutan mutane ne. Ni da Maryam har tsokanarsa muke yi. Da mun ga Maje ya zo wuri sai mu rika cewa "Maryam ga angonki". Daga baya shi kuma Maje sai ya dauka da gaske ne.

Ba mamaki ko don ka ga ka kasa shi don haka kake tsokanarsa?

AHMED: (Dariya) Wallahi ba haka ba ne, tsokana ce kawai don mun ga Maje ya yi masifar fadawa cikin son Maryam, saboda haka ni da su Dauda da Malam Ibrahim (ma'aikatan 'Fasaha Films') muke tsokanar shi, "Ga angon ya zo, ga matar ta zo!" Kawai sai ya hau ya rikice. Ban sani ba sai daga baya ya kira ta ya nuna yana son ta, sai ta fada masa ita a zuciyarta wanda take so daban.

Mu koma zancen fim. Yaya ka ji lokacin da ka kake wakar 'Lailailai Lakanin Kauna' wadda kuka yi da Fati da Abida a cikin Mujadala na 2?

AHMED: Gaskiya ina bakin cikin wannan waka da na yi. Ya za a yi kamata a ce mata sun kasa ni? Ranar da aka buga wakar sai da na yi wa Ali kuka cewa ni ba son wakar nake ba. Wallahi ranar da aka yi wakar ne Abida da Fati suka haddace ta don kawai suna so su huce haushi kaina, su ci min mutunci. Kana na yi tunanin wakar kamar an soka min wuka a zuciya. Amma kuma wakar sai mata suke son ta saboda an ci wa namiji mutunci a ciki.

Yanzu kai ba ka son wakar?

AHMED: Wallahi ba na son wakar duk da tashen da ta yi.

Amma kuma idan ana wani taro ka sha yin wakar tare da wasu 'yan mata a gaban jama'a.

AHMED: Kawai don wakar kamfaninmu ce. Ai in na kalli wasu 'yanmatan sai in rika tuna abin da Abida da Fati suka yi min. Na rasa abin da ya sa na tsani wakar. Ka san a Mujadala 1 na ci wa mata mutunci, a Mujadala 2 kuma sai suka rama a wannan waka, ka ga ai sun kada ni.

Me za ka ce game da fim dinka Zubaida?

AHMED: Alhamdu Lillahi. Ka san ni ba a haife ni a Kano ba, amma kakannina a Kofa aka haife su. Ga shi na zo Kano, na zama dan Kano kuma na fitar da 'yan Industry kan zargin da ake mana cewa wai mu ba mu da aikin yi, ko 'yan iska ne. Sai na zauna ni da Ali muka rubuta labarin muka saki har aka gani. Amma ni fim dina na gaba ba a Kano zan yi shi ba, a Legas zan yi shi.

Wane fim ne wannan?

AHMED: Nawa ne, sunansa Kusufi.

Me ya sa za ka je Legas ka yi fim?

AHMED: Ka san ya kamata a rika samun canji da kuma ci-gaba, ana tafiya wuraren da ba a ma taba zuwa aka yi shirin fim ba.

Ka samu wanda zai ba ka location kyauta ko kuwa kudi za ka ware ka kama otel ko hayar gida?

AHMED: Ina da yaya a Legas, kuma babban jami'in harkar shigi-da-fice ne (Immigration), shi ya ba ni shawarar idan zan je zai min duk abin da nake so. Kuma akwai wasu abokanmu wadanda muka gama makaranta daya da su, iyayensu manyan ma'aikata ne a can, duk za su yi min hanyar samun gidaje da ma jirgin sama.

Ali yana yin Nigerian Films, to kai ma idan ka je Legas suka gan ka suka yi maka audition (gwaji) ko za ka fara idan suka dauke ka?

AHMED: E, amma idan abin da zan yi bai saba wa Musulunci ba. Don ka san yanzu suna sa Kiristanci a ciki. Idan bai saba wa Musulunci ba kuwa, kuma na ga zan iya, to zan yi.

Me za ka ce game da surutan da mutane ke yi cewa kai ba dan'uwan Ali ba ne na jini?

AHMED: Abin da zan ce wa mutane shi ne, Ali dai dan'uwana ne, shi kanen mahaifiyata ne. Kusan kenan dan'uwana ne. Ina zaune a hannunsa, dole ne ya rika control dina.

Shi Ali, wasu na cewa yana da zafin rai. Tunda ka fi kowa kusantuwa da shi me za ka ce game da halinsa?

AHMED: E, gaskiya ko a gida Ali yana da zafi. To da wasu suka gane haka sai suka rika zuwa kawai don su tsokane shi, wasu kuma zugo su ake yi don su kular da shi, idan ya yi magana a ce ya faye zafin rai ko wulakanci. Ka ga idan wasu suka zo za su yi sallama su ce "Mu masoyanka ne," a yi ta hira, har ya raka su su hau mota. Amma idan wasu suka zo suka same shi yana hira da wasu, to su ba za su iya jira ba sai su ce an yi masu wulakanci. Za ka ji suna cewa, "Kai ana yi maka magana, banza!"To irin wannan shi ba zai hakura ba. Dole sai ya mayar masu domin wurinsa suka zo suka same shi. Wallahi yawanci wasu matan idan sun zo za ka ji suna ce mana, "'Yan diramar nan 'yan iska ne." Ka ga haka bai dace ba. Wasu kuma kana cikin mota za su sha gabanka, (su ce) "Kai mun zo wurinka kana yi mana yanga kana yi mana wulakanci..." Abu ne dole sai hakuri,amma mutane su gane, shi ba wulakanci yake yi ba.

Kwanan nan kan wasu finafinai mun ga har ka fara daukar bindiga. Shin kai ma rikidewa za ka yi ka zama dan dadi-daukar-rai?

AHMED: Ba haka ba ne. Gaskiya akwai finafinan da na yi kwanan nan wadandanake so. Ka ga kamar Juyayi, ina sonsa kwarai.

Saboda ka yaudari Maryam a ciki?

AHMED: E, saboda na yaudare ta a ciki. Ka ga ni ban taba acting irin wannan ba. Na fito a matsayin mutum biyu ne - daya dan kauye, daya kuma dan birni, mugu kuma mai kudi.

Saboda son da ake yi wa 'yan wasa har fada ake yi a kan ku. Wane kira za ka yi wa matasa masu dukan juna saboda ku, ko kuwa kyale su za ka yi su rika bai wa hammata iska?

AHMED: Lokacin da nake kallon Indiya, wallahi ni ma har dambe ake yi da ni ina cewa ni sai Saif Ali Khan, wasu na cewa sai Shah Rukh Khan, da sauransu. Sai ga shi abin mamaki yanzu a finafinan Hausa wasu har yankan jikinsu suke yi saboda mu. Ina so don Allah su daina irin wadannan abubuwa, su san cewa mu 'yan fim idan mun gama shiri, to kanmu a hade yake. Su gane wasa ne muke yi. Fadan da ake yi a fim ba fada ba ne, shiri ne.

Kana daukar wani tsawon lokaci a wani ko wasu lokutan ba ka je fim ba?

AHMED: Wallahi tun da na fara harkar fim a Kano ban taba yin wata daya zunzurutu ba a ce ban fita fim ba. Wata rana har sulalewa nake yi in je in ga mahaifiyata in dawo. Wasu kuma abokan da nake da su da ina ta nema in ganar da su cewa ba na zama shi ya sa ba na zuwa wurinsu, muna hira. Don Allah su yi hakuri.

A cikin wane fim ne ka taba shan wuya wadda ba za ka manta ba?

AHMED: A cikin sabon fim din Ali, Sharadi. Har in mutu ba zan manta da shi ba. Na sa takalmin taya na fadi na yi targade. A daren ranar da na yi targaden kuma za mu yi waka. Na daure ina yi, cikin masu waka wani ya kama hannuna. Wallahi yadda ka san ana zare min rai saboda zafi, amma tilas na daure muka ci gaba da wakar don fim din dan'uwana ne. Idan na ce zan tsaya sai na samu sauki fim din zai kara cin kudi don da babbar kyamara aka dauki shirin. Fim din da na sha wahala kenan.

Wanda kake jin dadi fa?

AHMED: Wanda na je na ji dadi hankalina a kwance babu kamar Nazari.

Fim din da Abida ta yi maka danyen wulakanci a gaban jama'a ta ce ba ta sonka abokinka take so?

AHMED: E. Duk da haka, wannan wulakancin bai kai wanda suka yi min a Mujadala 2 ba.

Mu koma makaranta Ahmed. Shin idan ka gama karatu ka sami wani aikin, ka bar fim?

AHMED: E, zan iya barin fim, amma fa na riga na saba da shi, na kuma dandana na ji dadinsa. Kuma idan Allah ya ara maka lokaci, sai ka yi amfani da lokacin. Sai dai idan na samu aiki a babban wuri ai ci-gaba ne, fim kuma sai ya zama tarihi.

Akwai wanda ya taba rubuto maka bakaken kalamai dalilin wani fim da ka yi?

AHMED: Ba zan manta ba, an taba yin wata hira da ni a mujallar Fim inda na ce ina sha'awar wulakanta 'yanmata. To sai wata yarinya ta aiko da wasika aka buga a mujallar Fim wai Ali ya ja min kunne game da wulakanta 'yanmata. Ina so yarinyar ta fahimci cewa ni a cikin fim nake magana, ba wai a zahiri ba.

Menene cikakkiyar ma'anar FKD?

AHMED: FKD kamfani ne daga sunan mahaifiyar Ali, kuma suna ne na Barebari. Yana nufin Fatima Kaderan Degima.

Wasu na cewa finafinan FKD na Indiya ne ake dauka a canza masu siga yadda za su dace da Hausawa.

AHMED: Mutane suna fada ne kawai. Ka san yanzu mutane sun saba kallon Indiya. To duk abin da ka yi sai a rika ganin ya yi kama da Indiya. Mu yawanci labaranmu ba na Indiya bane. Mu ke kirkira labarinmu mu maida su fim. Amma an sha aika mana da wasiku wannan ya ce wannan fim din ne, waccan ta ce wancan fim din ne.

A matsayinka na kusa da Maryam Aliyu, me za ka ce kan kaurace wa harkar fim da ta yi har kusan wata daya? Wasu na cewa rashin lafiyar ta wai jifa ce aka yi mata?

AHMED: Ka san harkar fim idan abu ya faru kowa yadda zai ta fassara shi daban. Ni ina ganin rashin tawakkali ne kansa wasu yin haka. Abin da na sani shi ne Maryam rashin lafiya ne ta yi, Allah ne ya dora mata, kuma ya ba ta sauki.

Batun da ake yi fa na cewa mahaifiyarta ta hana ta shirin fim, kuma ga shi ta dawo?

AHMED: Ni gaskiya ban san wannan maganar ba. Babu ita, don kuwa ko darakta (Tijjani Ibraheem) ban ma taba jin ya fadi haka ba. Da akwai maganar da gaske, kowa ai da ya sani.

To kwanan nan mun sani labarin cewa ka sami sabani da wasu iyayen gidanka. Ya gaskiyar al'amarin yake?

AHMED: Gaskiya abin ya samo asali ne daga fim din da na yi wa mujallar Fim (Daren Farko). Ni dai wadannan iyayen gida nawa ba su fito fili gaba da gaba suka yi mani maganr ba. Amma su sun bata ransu ne wai don me ni ina yi masu fim kuma zan je in yi wa mujallar Fim? Ni abin da na lura shi ne, idan iyayen gidana biyu suna gaba, to ni ba zan dauki wani bangare ba, kowa nawa ne. Ni dan wasa ne. Fim din mujallar Fim contract kamfanin ya dauke ni na yi masa wasa ya biya ni kamar yadda su ma suke dauka ta su biya ni. Mujallar Fim daban, fim din mujallar Fim daban. Kuma ka lura, ai akwai iyayen gidana biyu duk an yi fim din da su - ga Alhaji Hamisu Iyan-Tama ga kuma Hafizu Bello wanda shi ne ma darakta. To ni sai in ce ba zan yi ba don kawai wasu masu saka ni a fim suna gaba da mujallar Fim?

To nan gaba idan mujallar Fim ta kara gayyatarka za ka je yi mata fim?

AHMED: Zan je mana! Ai na fada maka, ni babu ruwana idan iyayen gidana biyu na gaba. Dukkansu manyan kamfanoni ne.

Ahmed, mun gode.

AHMED: Na gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin