|
Yadda Rabilu Musa Danlasan, Ibro ya kwace kasuwar finafinan Hausa
Ibro a walimar taya zakarun 'yan fim na Arewa murnar cin gasa a otal din 'Central' na Kano. A dama, Furodusa Yusuf Khalid ne
|
A YAU, yayin finafinan Ibro ake yi. Je ka kira shi abin da za ka kira shi, amma Ibro ya amshe kasuwar, ya bar manyan furodusoshi suna shan sudi ko kuma zuciya ta kashe su suna ta kyata.
Rabilu musa Danlasan bai damu ba. Lokacinsa ne. Duniyarsa ce; dole ya ci abarsa da tsinke. Wata rana sai labari.
Shin yaya aka yi haka? Mutumin da a da ake kallonsa a rainE, wai shi camama kurum yake yi, wato irin finafinan nan masu nuna rayuwar kauye, wadanda ake yi da arha. Amma yanzu fa dube shi. Daga Sarkin Barkwanci ya koma Sarkin Farin Jini ga 'yan kallo, yanzu kuma Sarkin Cin Riba. Ya ka yi kasuwar Ibro ta bude? Me ya sa ake rububinsa? Meye sirrin nasararsa?
A da, ana ganin finafinansa a matsayinmarasa ma'ana. Can baya, duk da cewa akwai masu sha'awar kallonsa, Ibro yana da dimbin makiya masu lura da cewa mafi yawan wasanninsa na kauye ne kuma duk soki-burutsu ne a ciki. Inda ma aka sako Ibro a cikin fim din birni, misali Maula, za ka ji suna kyata suna cewa,"Ibro ya bata fim!" Sa'annan idan sun ji shi ya yi magana sai su ce, "Kai ku rabu da Ibro, mahaukaci ne."
Irin wannan sa-ido ne ya haifar da sanya wa finafinan da Ibro ya fito a matsayin jarumi wannan sunan na raini, wai camama. To, duniya juyi-juyi, sai ga shi wannan duk ba su hana goga Ibro tashe ba kuma sukar da ake yi wa finafinansa bata hana mutane sayensu ba. A halin yanzu sakamakon wani mummunan jidali da furodusoshi suka samu kansu a ciki, da yawa daga cikinsu sun karkata jarinsu daga shirya "manyan" finafinai irin Sai A Lahira ko Mujadala, wadanda na fadakarwa ne, masu bukatar manyan 'yan wasan da za a kashe wa kudi masu dimbin yawa irin su Ali Nuhu ko Hauwa Ali Dodo.
Akwai dalilai da suka sa ake yayin Ibro. Da farko dai, mutane sun gaji da kallon labaran soyayya (dauke da wakokin da ake ganin irin na Indiya ne) wadanda yawancin "manyan" finafinai suke dauke da su. Labaran Ibro ba na soyayya ba ne; akan gina su ne a kan matsalolin yau da kullum, wadanda mutane suka fi sani, musamman masu kallon finafinan Hausa, wadanda yawanci ba hamshakan attajirai ba ne.
Wasu masu kallon kuma suna son a nishadantar da su da barkwanci; to duk dariyar da suke nema za su same ta a fim din Ibro. Sa'annan Ibro ya yi dabarar gina al'adar shirin fim a kan sunansa, wato ka ji an ce Ibro kaza Ibro kaza. Koda yake ya ce ba shi ne ke ba da sunayen ba, yin haka ya sa komai ya ta'allaka ne a kansa. Duk da yake akwai wasu sarakan barkwancin (misali Kulu, Moda, Gidigo da Baban Mulika), Ibro dai aka fi sani. Har ma akwai "Ibron Zariya."
WAta dabarar da Ibro ya yi ita ce da ya hadiye wasu manyan sarakan barkwanci, ya maishe su kasansa. Sun hada da Bashir Bala (Ciroki) da Shu'aibu Sama'ila (Kulu). A da, duk fim ba ya cika fim har sai Ciroki ya fito a cikinsa. Yanzu ko an daina yayinsa, ya koma Wudil yana aiki a karkashin Ibro, inda yakan fito a finafinai irin su Maraba Da Shari'a.
To amma a binciken da muka yi, mun gano cewa babban dalilin da ya taimaka wa bunkasar Ibro a daidai lokacin da muke ciki ba zai wuce matsanancin karancin cinikin "manyan" finafinai da ake fuskanta a kasuwa ba. Hakan kuwa ya faru ne sakamakon yawan finafinai da ake yi barkatai wanda abin har ya kai mai sayen kaset sai ya binciki kamfanin da ya shirya fim kafin ya saya. Akwai manyan kamfanonin da suka yi tashe amma ya zuwa wannan wata da muke ciki sun dauki lokaci mai tsawo ba su shirya fim ba saboda babu riba. Akwai kuma wanda ya yi tashe amma yanzu gurguwar kasuwa ta maida kamfanin na-baya-ga-dangi. Dadin dadawa kuma, akwai masu karbo kwangilolin shirya fim amma a karshe sai ka ga an kare da zargin juna saboda rashin ciniki. Furodusoshi da yawa sun daina shirya fim, sai bin dillalan kaset suke yi kullum, wai a ba su na miya. Manyan 'yan wasa da daraktoci sai zaman-kashe-wando suke yi. Wata sa'a sai babban jarumi ya kwana bakwai bai ji lokeshin din da ake nemansa ba.
Abin takaicin da ke damun wasu shi ne ta yaya furodusa zai zuba N400,000 ko fiye ya shirya fim amma idan bai yi sa'a ba fim din Ibro da aka kashe N100,000 zuwa N200,000 sai ya fi shi ciniki? Da yake abin ba don lada ake yi ba, ko don "habaka" al'adu da addini, wannan ya kawo karkatawar furodusoshi ya zuwa wurin Ibro domin shirya masu camama.
Akwai finafinai da dama da aka shirya da sunan Ibro tun can baya. Amma wanda ya fi daukar hankalin mutane shi ne Ibro Awilo wanda ya fito ba da dadewa ba. Wakar fim din, "Mu Daina Shan Ganye," ta game ko'ina kusan fiye da wakokin "Sangaya" da "Wasila". Shi kansa fim din na Awilo ya karbu a gidajen sinima da na bidiyo fiye da wasu manyan finafinai da aka kashe wa makudan kudade.
Kafin Ibro Awilo, an yi wasu wadanda suka dauki hankalin masu kallo. Sun hada da irin su Ibro Usama, Ibro Dandaudu, Ibro A Makka, Ibro Kaftin, Ibro Tela, da sauransu.Wani abin mamaki shi ne yadda kowane fim ba shi da wani suna sai na Ibro. Ibro kaza, Ibro kaza sun yawaita. Ga su nan irin su Ibro Sana'a Goma, Ibro Ganduroba, Ibro Dankama, Ibro Fafalolo, Ibro Kansila, Ibro Dan 419, Ibro Lecturer da kuma Ibro Farfesa. Akwai kuma irin su Ibro Dan Baiwa, Ibro Bodari, Ibro Niga, Ibro D.P.O., Ibro Babanbola, Ibro Dattijon Biri, Mijin Hajiya, Kuku, Alhaji Malam Ibro da kuma Game Gari.
Babban abin da ya fi daukar hankali yanzu shi ne yadda ake sa ko a yi amfani da Ibro ya kwaikwaayi wani malami ko mawaki. Wannan ya kara janyo masa farin jinin da a kullum sai furodusoshi sun yi masa sallama a Wudil don ya yi masu wani fim ko wasu finafinai masu tafiya da sunansa. Wani sabon labari da wannan mujallar ta binciko ya nuna cewa furodusoshi sun dukufa wajen neman labarai masu suna Ibro; tuni har an rikice wajen karkata labaran finafinai ta yadda za su yi daidai da irin dabi'un barkwancin da aka san Ibro, Shu'aibu Kulu, Yautai da kuma Malam Dare ke da su.
Mujallar Fim ta gano wasu sababbin finafinai da ke kan hanya nan gaba musamman irin su Ibro Craig David, Ibro Horo (Horror), Ibro Micheal Jackson, Ibro Tupac, Ibro Soja da kuma Ibro Indiya. Shi Ibro Indiya kuwa, bincike ya nuna cewa ana ma neman kai ruwa rana a kansa. Dalili kuwa shi ne mutane hudu ko biyar ne suka dukufa domin yinsa. Akwai wanda ya riga ya buga fosta ya lillika a wurare daban-daban. A jikin fostar, wadda marubuci Dan'azumi Baba Cediyar 'Yangurasa mai kamfanin 'R.K. Studio' ya yi, akwai hoton Usaina Gombe (Tsigai) da kayan Indiya (sari) da kuma dogon gashi irin na Indiya. Shi kuma Ibro yana daure da katon rawani irin wanda aka san Musulman kasar Indiya suna daurawa.
Baya ga Dan'azumi akwai wasu furodusoshi biyu wadanda sun tsara labarinsu a rubuce kowanensu da sunan Ibro Indiya. Inda takaddamar take kuwa shi ne ita ma Tsigai ta tubure ta ce za ta sa kudinta ta yi Ibro Indiya. Dukkan furodusoshin babu wanda bai saka Tsigai a labarin fim din ba. Tambayar da ake yi ita ce shin idan Tsigai ta ce za ta yi anya Ibro zai yi wa wani ba Tsigai dinsa ba?
Masu karatu daga yau duk wata katuwar mota komai kyawonta idan dai ta wani furodusa ce to muddin kuka ga ta wuce Tashar Mariri ba ta tsaya ba ku tabbata Wudil za ta gidan Ibro. Ibro yana daya daga cikin masu nasibin samun kudi a harkar fim. Shigar da yake a fim ke sanyawa wasu na yi masa kallon tsoho. Ba tsoho ba ne, yaro ne, amma kammalallen magidanci mai mata hudu da arzikin motocin hawa.
Yawan finafinan da ke gabansa zai kara tabbatar da cewa Ibro tamkar yanzu ne ya daura damarar karbar kudi daga hannun furodusoshi. Wasu daga cikin furodusoshin da ke kan layi a wurin wannan dan wasa sarkin barkwanci sun hada da Salisu Yomen wanda Ibro zai yi wa Ibro Sisqoo, Alma Jos mai Ibro Bob Marley, sai Hajiya Zayya Dantata wadda nan ba da dadewa ba za a yi mata Ibro Tupac.
Wani dillalin kaset kuma furodusa ya tabbatar wa Fim cewa, "Duk karfin kamfani yanzu idan ya yi fim ba zai ci kasuwa sosai ba. Amma da ya shirya fim na Ibro sai ka ga ya kwashi kudi kawai". Ba mamaki wannan dillalin kaset ya ce, "A duk cikin shekarar 2002 babu kaset din da ya samu kasuwa irin Ibro Awilo." Shi dai Ibro Awilo, wani matashin dan kasuwa mai suna Abdulhadi ne ya shirya shi. A da can ya yi fim mai suna Kauna, fim din da ya ci gasar Arewa ta bara.
Wasu karin sunayen finafinan da ke kan teburin Ibro sun hada da Ibro Shata, Ibro Agent, Ibro Hogan, Ibro Maikilago, da Ibro Mai Unguwa wadanda duk na Alhaji Idris Danzariya ne wanda ke da katon shagon sayar da kaset mai suna El-Duniya. Akwai kuma Ibro Danshayi shi ma a tafe. Ganin cewa furodusoshi sun raja'a wajen yin finafinan Ibro wanda ake kwaikwayon mawaka sai shi Ibro ya shigo da wata sabuwar hikima inda ya shigo da tsarin nan na 'booking', wato rubuta sunan furodusan da aka fara yin yarjejeniyar yin wani fim da shi. Ma'ana a nan, babu wanda za a yi wa Ibro Tupac sai Zayya Dantata, wadda ta taba shirya manyan finafinai (sentimental), ciki har da na karshen da ta yi mai suna Gwi-Da-Yara, kuma Ibro Shata tilas sai Danzariya.
Kafin a haukace bukatar Ibro a da can idan ya yi maka fim sai abin da ka ga dama ka ba shi, ba zai raina ba. Duk da haka yakan yi yarjejeniya da wasu. Amma an ce kowa ya samu rana zai yi shanya, domin yanzu Ibro ya nada amininsa Auwalu Idris (Malam Dare) a matsayin manajansa. Duk mai son ganin Ibro to ya je wurin Malam Dare, shi zai yanka wa furodusa kudin da za a biya Ibro idan zai yi fim. Kwanan nan wani wakilinmu ya binciko wani kokari da wasu ke yi na yin wani fim mai suna Ibro Craig David, wanda shi ma mawaki ne Ba'amurke. Shirye-shirye sun yi nisa har an buga wakoki a kamfanin 'Sulpha'. Wani furodusa ya shaida wa Fim cewa, "Ai da mu ake zagi don muna yin finafinan Ibro, yanzu kuma kowa ya dawo kansa; masu zagin Ibro kuwa hassada ce kawai."
Daya daga cikin furodusoshin da a da suka guji Ibro amma suka dawo masa shi ne Mohammed Munzali Mohammed (Ahlan Yoko). Kamar yadda Ibro ya labarta wa wakilinmu a Kaduna, lokacin da aka ja ra'ayin Ahlan da cewa ya daina yin camama ya koma "babban" fim, ya daina din. Ya tafi ya shirya fim mai suna Hijirah. Amma tilas da ya ga "boni" ya koma wa Ibro, yana ta hada shi da Allah. Da kyar Ibro ya yarda suka yi Ibro Dandaudu.
Ba ni tsoron uban kowa!
Rabilu Musa Danlasan ya kare kansa daga zargin jama'a da malamai, kuma shi ma ya yi tasa tsinuwar, sa'annan ya bayyana yadda kasuwar finafinansa ke ci, da yadda dangantaka take tsakaninsa da Shu'aibu Kulu.
Daga ALIYU GORA II a Kaduna
FIM: Ibro, bari mu fara da tsokaci a kan yadda taken finafinanka ya canza alkibla, wanda yanzu duk finafinanka daga Ibro wannan sai Ibro wancan, misali Ibro Tela, Ibro Awilo, Ibro Dan Daudu, da dai sauransu. Me ya kawo faruwar haka?
IBRO:A'uzu billahi minash-shaidanir-rajim. Bismillahir Rahmanir-Rahim. A, duk yawancin sunayen, Ibro kaza Ibro kaza, ni ba ni ba ne ke sa su. Ka san Hausawa sun ce iya ruwa fidda kai. Duk abin da mutum ya yi, sunan fim ma yana sa mutum ya fidda kudinsa. Kamar misali, ana cewa camama da sentinental; kamar mu mu aka dauka mu 'yan kauye ne kuma mu komai namu kauyanci ne, kuma kudi kalilan ake kashewa, shi ya sa ake ce mana camama. To camaman nan, ita tana nan a camamarta. Tunda na farko ba za mu sa mutum ya saida kayan matarsa ba don za mu yi masa fim. Ba za mu sa mutum ya je ya ranto kudi a banki ba don za mu yi masa fim. Kuma mutum ba zai zo mu yi masa fim ya ce da mu Allah-wadai ba, babu wanda zai zo ya ce Allah-wadai da abin da muka yi masa, ko kuma abin da muka karba daga wajensa. Muba ma jan kyauro, kuma mu din mu ake cin riba da mu. Kuma wannan abin alfahari ne a wajenmu, kuma muna gode wa Ubangijinmu. Amma ba mu ke kirkiro sunayen fim ba, furodusa shi yake tsayawa ya hango me ya kamata ya yi ya ci riba, sai ya ga ai sai ya sa 'Ibro kaza'.
FIM: Yanzu ban da Ibro Awilo da ke cin kasuwa, akwai wasu irinsa da kuke shirin yi ?
IBRO: E, akwai Ibro Michael, Ibro Bob Marly da Ibro Tupac, akwai duk... Ai yanzu Ibro-Ibron ya yi yawa. Don ba zan ma iya lissafa wadanda za a yi nan gaba ba.
FIM: Ya kake yi da maganganun masu cewa finafinanku suna saba wa addinin Musulunci?
IBRO: Mu a matsayinmu na Musulmi ba mu taba saba wa addinin Musulunci ba, sai dai mu nuna abin da za a yi a gyara Musulunci. Kuma na ji dadi a lokacin da nayi Ibro Usama, na sha addu'a da zage-zage a masallatai. To amma abin mamaki, wadanda suka yi addu'ar nan (suna cewa) Allah ya la'anci Ibro, ya yi menene, da Usaman ya fito suka ga ba yadda suke hange ba ne, Ibro ba Kirista ba ne, Ibro ba arne ba ne, Ibro Musulmi ne, saboda haka ai ba zai yi abin da zai cuci Musulunci ba. Amma rashin tunani da rashin sanin ya kamata na malaman haure, ba ma namu na Nijeriya ba, ya sa ake zagina. Don malamanmu na Nijeriya sun san abin da suke yi, kamar su Isa Waziri, su Ustaz Yusuf Ali, malamai ne wadanda za mu yi alfahari da su, da wadanda ban rike sunayensu ba. Akwai malamanmu wadanda aka haifa a Kano. Iyayensu a Kano suke, kakanninsu a Kano suke. Ba haurowa suka yi ba. Kuma Allah ya taimake mu gwamnatinmu mai sanin ya-kamata ce. Saboda haka ba ta amfani da abin da wasu malamai suke yi, saboda ta riga ta gane cewa yanzu ko Hadisi ma wani malamin in ya tashi jawowa, daga karshe sai ka ji na maula ne.
An binne Ibro za a jefe shi saboda aikata laifin zina a cikin Maraba da shari'a
|
FIM: Me ya hana Kulu fitowa cikin fim din Ibro Awilo?
IBRO: Lokacin ba ya nan ne. Amma a saurari na biyu, yana cikin na biyu.
FIM: Ka taba samun wani sako na gyara ko kuma yabo daga fim din Ibro Awilo?
IBRO: E, ba laifi, jama'a suna zuwa, kuma ana alfahari da wannan fim. Ni dai na tabbatar da duk abin da zan yi, ba zan yi wanda zai saba wa ka'ida ba. Kuma ina dada tunatar da 'yan haure, malamanmu na waje, wadanda malamanmu na gida da suka je karatu suka gan su suka biyo su nan gida Nijeriya, musamman Kano. Kano kasa ce mai albarka; Allah ya albarkaci Kano, amma kuma Allah ya kawo mana 'ya'yan banza cikin Kano.
FIM: Daga cikin finafinanka akwai wanda ka taba yin da-na-sani bayan ka yi shi?
IBRO: Ni ban taba yin abin da na yi da-na-sani ba. Kuma ban taba yin abin da na yi dar-dar ba, kuma ban taba yin abin da na yi shayi ba. Kamar misali lokacin da muka yi Ibro Usama, har dadi nake ji in ji ana cewa "Allah ya tsine wa Ibro" a masallaci da meye, saboda na san ba ni ake tsine mawa ba. Masu yin addu'ar nan, na fada a baya kuma ina fada, kuma ina nan a kan fada, ba ni suke yi wa addu'a ba, iyayensu suke yi mawa. Idan uwar mutum tana da rai to zai ga ta lalace. In kuma uwar mutum ta mutu duk wanda ya yi wannan addu'ar ya je ya haka kabarinta zai ga tana cin wuta. Ba ni ya yi wa addu'a ba. Kuma ba na shayi. Saboda kullum kafin in yi abu sai na je na samu iyayena na tsugunna su shafa mani kaina su ce ka je Allah ya kiyaye. Saboda haka ba na tsoron wani 'Inyamuri'. Ai yawanci duk wanda za ka ji yana sukar wani, in ka bi, komai rawaninsa ba malami ba ne, arne ne!
FIM: Ka taba samun matsala da iyalinka dangane da irin yadda kake gudanar da wasan kwaikwayonka ?
IBRO: (dariya) To ni kam ya za a yi in samu matsala ta iyali, bayan ta haka na same su? Ai da iyayena da iyalina da 'ya'yana da 'yan'uwana gaba daya... kai, duk dan garinmu, da masu kaunata, murna suke yi suna kuma yi mani addu'a ak an wannan abin da nake yi. Domin duk abin da na samo, ba a gidana ba ma, har a gidan iyayena duk abin da aka ci ni ne. Saboda haka suna alfahari da abin da nake yi kuma suna yi mani addua'a ko da yaushe.
FIM: Daga cikin 'ya'yanka kana da sha'awar wani ya zama tauraro kamarka a fagen shirin fim?
IBRO: E, amma kuma ina nan na raba kafa kamar yadda malamai suke zaginmu ina nan ni ma dana na sanya shi a makarantar Islamiyyar nan ta koyon Larabci, shi ma ya je wajen nan ya yo karatu ya dawo. Kuma in ya dawo in rokon Sarkin Kano a ba shi limanci a Kano.
FIM: Ibro, shin akwai wani lokaci da ka kebe wa kanka cewa in ya zo za ka bar wasan kwaikwoyo?
Ibro a hawan sallah da ta gabata a Kano
|
IBRO: Sai tatassara. Sai dai in na mutu.
FIM: Me za ka ce dangane da masu kiran irin finafinanka camama?
IBRO: A, camama, ... masu zagin camama sun yi ridda. Su yi istigifari (tunda) sun san abin da suke yi ba daidai ba ne. Yanzu gaba daya sun ajiye sentimental. Ai sentimental sunanshi 'lashe-money'. Don ba na mantawa, akwai wanda nake tare da shi kuma aminina ne, Ahlan Yoko, ba na mantawa tare muke, kuma ina yi masa finafinan na inna naha. Da shi kuma ake haduwa a zage mu. Kuma zai zo jikina in yi masa. Duk ban san wannan ba. Daga karshe da na gane shi ake zaginmu, har ya zagaye ya je ya yi wani fim, shi wannan sentimental din, wato lashe-moni, ya je ya yi shi, ya kashe kudadenshi bukata ba ta biya ba. Aka saki fim din ma ba mai nema. Daga baya ya yi roko, ya yi ta roko, ya dawo aka yi mashi Ibro Dandaudu, sannan ya farfado . Amma lokacin da 'lashe-moni' ta tasa shi a gaba, shagonsa ma in ka je sai ka tausaya masa. Ni dai har kuka na yi masa. Dalilin da ya sa na yi mashi Ibro Dandaudu kenan don ya farfado.
FIM: Shin gaskiya ne da ake cewa Hukumar Tace Finafinai ta Kasa ba ta san da yawancin finafinanka ba?
IBRO:Ldariya) A'a, a'a, ai ban taba yin fim din da ba a kai shi Hukumar Tace Finafinai ta Kasa ba. Ai mu duk abin da za mu yi muna bin doka, muna bin ka'ida. Ai mu da mu da gwamnati, gwamnati ta fara rungumarmu hannu biyu-iyu saboda ta san mun san abin da muke yi. Kuma su kansu ta bangaren kudin shiga babu inda suka fi samu illa bangaren irin finafinanmu saboda duk sun mara mana baya, kuma suna ba mu goyon baya.
FIM: Kana nufin ba ka taba samun matsala da Hukumar Tace Finafinai ta Kasa a wani fim daga cikin finafinanka ba?
IBRO: E, kamar yadda dai na gaya maka a baya, babu wani fim da muka taba samun matsala a Hukumar Tace Finafinai irin Ibro Usama; Ibro Usama ne akai ta kai suka ana ta meye. Kuma alhalin 'yan Nigerian film sun yi Usama Bin La, sun ci mutuncin addinin Musulunci. Ba a zagi wadannan ba sai Ibro. Saboda Ibro dan kauye ne, kuma mai saukin kai ne. To Ibro ba mai saukin kai ba ne billahillazi la'ila ha'illahuwa! Wallahi ni ba na shayi kuma ba ni tsoron uban kowa. Ni dai ga ni. Allah kuma ya halicce ni sai kuma ranar da Allah ya dauke ni. Mutum bai isa ya min wani abin da Allah bai yi mani ba. Abin da na ajiye kenan. A yau idan ciwon ciki ya same ni ba wani ba ne ya dora mani, Allah ne. Amma wallahi in mutum yana neman wani abu da ni, kar ya fara.
FIM: Me za ka ce dangane da kwatanta basirarka da kuma ta Kulu a fagen shirin fim da wasu ke yi?
IBRO: Kulu ai ni na ba shi dama. Ai ko wanene yanzun in ina son shi zan iya janyo shi jikina ya yi. Daukaka ce ta Allah, ba ni nake bayarwa ba, Allah ke bayarwa. Amma na tabbatar da duk wanda ya zo ya zauna da ni abin da yake so zai samu. Abin da Kulu ya yi kenan. Shi Kulu yana tare da ni ne ba don komai ba sai don shi ma yana son ya yi suna, kuma Allah ya ba shi.
FIM: To Malam Ibro mun gode.
IBRO: Ni ma haka.
NI ba zan taba rabuwa da Ibro ba
Inji Kulu
Daga ALIYU A. GORA II a Kaduna
WAKILAN wannan mujallar sun dade suna farautar dan wasan nan Shu'aibu Sama'ila, wanda ake kira da lakabin Kulu, wanda aka sani a matsayin babban dan wasan kungiyar Ibro. Rannan sai muka ji ya bulla a Kaduna tare da maigidansa Ibro, sun zo yin wani wasan dabe a gidan hira na 'Marhaba' da ke kasuwar Barci a Tudun Wada. Nan da nan wakilinmu ya garzaya gidan, inda nan ne masaukin da tawagar ta 'Asheik Malam Ibro,' kuma suka tattauna da Kulu.
Shu'aibu Sama'ila (Kulu) a ciki kayan Sarki a fim din Rimi-Rimi
|
Kun tuna da wani baiti na wakar Ibro Awilo inda Ibro ke cewa, "Kulu, Kulu, Kulu ya daina!"? To wannan Kulun ne, koda yake ba a nuno shi a fim din ba. Kulu ya yi fice ne da ban dariya a wasanninsa. Saboda iya-shegensa har akwai 'yan kallo da ke jayayya kan cewa ya fi Ibro iya wasa. Kulu ya yi bayani a kan irin wannan jayayyar a cikin hirar da wakilinmu ya yi da shi.
FIM: Kulu, bari mu fara da jin cikakken sunanka da kuma takaitaccen tarihinka.
KULU: Sunana Shu'aibu Sama'ila, kuma ni mutumin Malali ne da ke Unguwar Bawa a Saminaka a cikin Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna. Amma ni dai ban yi boko ba, amma na zauna karatun Islamiyya. Na yi makaranta a Maiduguri na tsawon shekara goma sha uku. Na zo Zariya na kuma karanci nahawu na tsawon shekaru uku. Ya zama shekaru goma sha shida kenan ina karatun Islama. Na fara diramata a 'Dahiru Bauchi Nurul- Islam' da ke Kofar Wunti a Bauchi; da Larabci muke dirama. Daga baya kuma sai na shigo gari ina yin ta. Na tafi Katsina na zauna a (gidan hira na) Damaga kamar shekara hudu. Daga nan na tafi Legas, na zauna na tsawon shekaru uku.
FIM: Yaushe ne ka fara haduwa Ibro, kuma ta yaya kuka hadu, har ka fara wasan kwaikwayo tare da shi?
KULU: Mun fara haduwa da Ibro wani zuwa da ya yi Legas. Lokacin na tafi wasa Fatakwal. Da ya zo ya yi wasa, sai wani mutum mai suna Alhaji Ali A-Kashe Dan Mamman ... to a lokacin su Ibro sun yi wasa a Agege sai aka ga wasansa ya kusa iri daya da nawa, aka ce, "A, wannan ga shi kamar dan'uwan Ibro! Kuma wannan ya yi kama da Kulu! Saboda haka lokacin da suka zo suka same ni, farkon zuwansu ina Legas. To bayan da muka yi wasa da Ibro kuma a lokacin nan Ibro yana sona. Har na nemi adireshinshi ya ba ni, adireshinsa a Wudil. To a Wudil din da na taso na samu kamar shekara daya ban zo ba. To bayan samun shekara daya sia na taho, na zo na same shi a Wudil, a lokacin nan ma yana aikin gandiroba. To wannan lokacin sai na zauna a gidan Ishaq Sidi Ishaq, wanda ake kira "yaro dan kwalisa". To, ina zaune a wajensa har muka yi wasu wasanni guda biyu: Ganin Kyashi da kuma Halin Mutum Jarinsa; a lokacin nan ina tare da Ishaq. To daga baya kuma wannan dai adireshin da Ibro ya ba ni har kuma Allah ya hada mu tare. A lokacin muka ci gaba da finafinai tare da Ibro. Kuma tsakanina da Ibro ba mu taba fada ba sannan kuma da ni da Ibro wani in ya gan mu zai tsammanin dan wa ne da dan kane. Kuma ni din nan mutum ne wanda yake girmama Ibro. Akwai wasu finafinai da za a rika ganin ba ni ciki, ana zaton mun yi fada ne da Ibro ko wani abu. To in Alah ya yarda, .... ni dai ba muyi fada da shi ba, kuma na dauki aldawarin daga nan har karshen abincinmu a dirama, ina nan da shi. Kuma ban taba tsammanin ko a mafarki zan yi wani rikici da Ibro da.
FIM: Wane fim ne na farko da ka yi tare da Ibro?
KULU: Fim din da na fara yi tare da Ibro shi ne Halin Mutum Jarinsa. Bayan mun yi shi sai kuma wani mai suna Ganin Kyashi.
FIM: Za ka iya lissafa yawan finafinan da kuka yi tare da Ibro?
KULU: A gaskiya ba zan iya sanin yawansu ba. Domin finafinan gaskiya sun yi yawa. Kuma ba zan iya tunaninsu in ce ga yawansu ba.
FIM: Mutane suna ganin kamar akwai sabani tsakaninka da Ibro, shi ya sa ba ka fito cikin fim din Ibro Awilo. Ba menene gaskiyar lamarin?
KULU: Alal hakika an yi fim din Ibro Awilo ba ni a ciki kuma ana kiran sunana kwarai da gaske. To ba wani sabani muka yi da Ibro ba. Wannan fim ya faru ne lokacin da ni na kwashi yarana. Da ma ni ina da yara a garin da aka haife ni. Don ina jin akwai yara wadanda za su tasam ma mutum sittin daga wasu jihohi da yake ni ina da kungiyar koroso. To a lokacin da aka yi fim din Ibro Awilo ni ina hanya. Don ni ban ma fara jin kaset din Ibro Awilo ba na rediyo sai a Numun na ji shi; na zo kuma Yelwan Shendam na kuma ji shi. To daga baya, na je Yelwan Shendam din. A nan na ce masu... sai suke gaya mani cewa ai akwai fim da aka yi mai suna Ibro Awilo, amma ba su gan ni a ciki ba. To sai suka sa mani fim din na gani. A nan ne na fara ganin fim din.
To kafin a yi fim din an neme ni ba a gan ni ba, domin na yi tafiya, har lokaci ya kure ban dawo ba. Saboda haka ina ba masoyana hakuri amma zan fito a na biyu in Allah ya so. Ban da shi ma akwai wasu wadanda suka fi shi za mu yi kwanan nan .
FIM: Ka taba samun labarin jayayyar da masoyanku ke yi cewa ka fi Ibro wasa, wasu kuma suna cewa ya fi ka?
KULU: E, gaskiya wannan kalami yana zuwa kunnena. To, amma ni abin da na dauka kauna ce kawai wadda kowa yana kaunar dan'uwansa, kuma kowa yana da gwaninsa. Sai dai wannan abu, abin da zan ce kawai, am, shi wasa haka yake. Lokacin da kake sha'awar mutum sai ka ga ba wanda ya fi shi a wajenka, tunda shi kake kauna. To, amma duka dai wannan abin duk lokacin da aka zo to sai in dan ji kuma abin... ka san duk mutumin da kake tare da shi, a ce shi yana oganka ne kuma ana irin wannan magana, to nakan ji, ban jin (dariya) kowa da irin halinsa, wani ya ji dadi wani kuma ba zai ji ba.
Ibro yakan yi finafinai wadanda ke tuna wa masu kallo irin rayuwa da suka fi sani. A nan yana wasa ne a cikin shirin Ibro Dan shayi
|
FIM: To kai ya za ka kwatanta basirarka da ta Ibro?
KULU: Wato, kwatanta basirar wasa, kowanne da irin tasa. Ni Allah ya hore mani kirkira. Don akwai basira da yawa. Don dalilin da ya sa na san dirama, wato na karanci littattafai sosai na Larabawa. Saboda a duk halittun da Allah ya yi a duniya, ina ganin babu mai labarin Balarabe. Kuma na taba karanta wani littafi na wani mutun wanda shi ne ya fara yin dirama a duniya. Wani Balarabe ne mai suna Nasahir Bann. To bayan na karanta littafin ne, to a nan wurin ne, saboda ni nakan iya abin ne saboda karanta Nahawu da na yi, sai nake dan... Allah ke kara mani basira a kan wannan sashe.
FIM: Kana da burin rabuwa da Ibro ka kafa taka kungiyar kai ma ka rika cin gashin kanka?
KULU: Am, ba ni da wannan buri, domin me? Lokacin da muka fara haduwa da Ibro, na yi masa bayani kan cewa ni kaina ina da kungiya, kuma a cikin kungiyar ne na fara yin fim mai suna Dan Jagora na 1 da na 2. Amma ba ni da sa zuciyar cewa za mu rabu da Ibro har in muna nan tare. Sai dai, shi ma kanshi ya sani cewa akwai lokacin da zan tashi in je in yi fim. To amma duk fim din da zan yi sai na yi kokari in ga cewa mun yi tare da shi ko da nawa ne na kungiyata saboda kada mutane su rika zaton cewa mun raba da shi.
FIM: Wanne fim ya fi kwanta maka a rai, daga cikin finafinan da ka yi tare da Ibro?
KULU: E, to, akwai su da dama. Ka ga kamar Ibro Dan Cana, da kuma wani wanda muka fito kauraye amma bai fito ba.
FIM: Akwai wani fim da ka taba yin da-na-sani bayan kun yi shi?
KULU: E, akwai shi, wato kamar misali Dan Kwara wanda na fito karamin yaro a cikinshi, Ibro ya fito a matsayin mahaifina. Na yi da-na-sani a kan wannan wasa. Domin misali akwai mutanen da suka yi fim din Goyon Kaka, ya nakasu, dangane da irin matsayin da suka fito, babban mutum ya fito karamin yaro. To ni sai Allah ya sa mutane ba su ankara ba, balle a ce su yi fushi da ni. To amma ina addu'a in Allah ya yarda daga wannan fim, ba zan sake yin irinshi ba. Shi ne kawai fim din da na yi da-na-sani.
FIM: Kai ma kana tsayawa a gida kalli finafinanka?
KULU: E, ina kallo, amma ba sosai ba saboda rashin lokacin zama gida. Yau muna wannan gari gobe muna wancan.
FIM: Kamar yadda mutane ke kallon finafinanka su yi dariya, kai ma kana yi wa kan ka dariya in ka kalli fim din da ka yi?
KULU: Kwarai kuwa, nakan yi dariya. Ballantana ma in gan ni tare da Ibro, to nikan ji dadi in kuma yi wa kanmu dariya.
FIM: Maganar iyali fa, kana da aure ko babu?
KULU: A, hakika ina da aure, matata ta farko sunanta Talatu, amma daga baya muka samu dan sabani muka rabu. Ta haifar mani 'ya'ya biyu duk mata, da Samira da Lubabatu. Sannan sai na sake auren wata mai suna Zainab. Ita ma ta haifi 'ya daya tare da ni.
FIM: Yanzu shekarunka nawa da haihuwa?
KULU: Yanzu zan kai shekaru ashirin da biyar da haihuwa.
FIM: Akwai wani lokaci da ka dibar wa kanka cewa idan ya yi za ka daina shirin fim?
KULU: Ni abin da na dauka kawai, wannan sana'a na dauke ta gaskiya ce, kuma na dauke ta sana'a ce. Sai dai duk ranar da Allah ya canza mani sana'a ba dirama ba, to ita zan yi. Amma a yanzu ina ganin ita Allah ya ba ni. Saboda haka tunda ba ni sani ga Allah ban isa in ce ga lokacin da zan ajiye ba. Sai dai na ajiye abu biyu: na farko mutuwa, ko kuma zamani. In zamani ya ce ba da ni zai yi ba, to duk dai abin na Allah ne.
FIM: Kana da ra'ayin daga cikin 'ya'yanka a samu dan dirama kamarka?
KULU: A yanzu dai zan ce a'a. Tunda duk 'ya'yana mata ne. Kawai abin da nike so da matan nan, in sanya su makaranta, bayan sun yi makaaranta sun dan yi sakandare, ba sai sun ja shi da yawa ba ma, in yi masu aure. Kuma fatan da nike yi, Allah ya sa kafin yaran su isa aure a ce na samu abin da zan yi sadaka da su ba tare da na karbi kudin wani ba.
FIM: Me ya sa ba ka son 'ya'yanka su shiga wasan kwaikwayo?
KULU: Saboda mata ne. Kuma na biyu idan Allah ma ya ba ni namijin har in ya ce zai koyi wasan in Allah ya sa sana'arsa ce, don zan yi tunani da cewa in na ga ya dauki wannan matsayi nasa kila ita ce sana'ar da Allah ya ba shi. In kuma bai dauka ba to ta yadda ya dauko sana'ar haka zan bi shi, in ba sana'ar banza ba ce.
FIM: Ka taba samun matsala da iyalinka ko iyaye a kan wannan sana'a ta fim?
KULU: A'a, ban taba samun matsala da ko daya ba. Saboda da auren iyalin nawa da abincin da za su ci, to ai ina ganin duk a kanshi ne. Saboda haka ka ga a nan, in tana sona ka ga ba za ta ki sana'ata ba, tunda ba sabo nake yi ba.
FIM: Idan da za a sa kazar-karfi tsakaninka da Ibro, kana ganin za ta ciwu gare ka?
KULU: E, a nan wurin, gaskiya sai dai in ce sanin gaibi sai Allah. Sai dai, shi irin wannan dama, kai ba za ka iya fadi ba sai dai magoya bayanka su fadi. Saboda haka tsakanina da Ibro, ni ban ma fatan ranar da za a sa mana kazar-karfi. Kawai dauka da ni da shi, ni, shi ogana ne ni kuma yaronshi ne, muna nan tare, ba ni son ko da ga 'yan kallo a ce an sa mana kazar-karfi. Kuma ko an sa, ni ba za ni ba saboda ogana ne.
Jahilai ne ke ganin muna yin kuskure
Malam Dare ya ce ba ya shisshigi
Muhammad AUwal Idris (Malam Dare) fitaccen dan wasa ne da aka fi sani musamman a cikin finafinan Ibro. Kamar yadda muka taba gaya maku a wata hira da muka yi da shi a watannin baya, Malam Auwalu bai cika fitowa a wani matsayi ba sai malami, kuma yana yawaita jawo ayoyi da hadisai a cikin finafinai. Da yawa daga cikin 'yan kallo suna son shi, yana burge su saboda yawaita amfani da hujjoji na addini da yake yi. To amma kuma wadansu sun tsane shi, saboda a ganinsu, kuskure yake tafkawa, kuma wai bai kamata yana jawo aya ko hadisi a fim ba, domin suna ganin kamar yana wasa da Alkur'ani da Hadisi ne. A yau, ga Malam Dare mun kawo maku yana kare kansa, tare da kawo hujjojinsa daga inda ya saba, wato Alkur'ani da kuma Hadisai, a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu ALIYU ABDULLAHI GORA II a Kaduna kwanan baya:
Auwalu Idris (Malam Dare)
|
Fim: Da yawa da ga cikin finafinanka, ka fi yawan fitowa a matsayin malami. Shin wannan zabinka ne, ko kuwa furodusoshi suka ga shi kadai ne matsayin da ya dace ka rika fitowa da shi a fim?
DARE: 'Yan kallo ne suke ganin kamar haka, suna ganin kamar role daya nake dauka a fim. Akwai wani abu da ake cewa, wato "sabo turken wawa." Wani lokaci zance ne ke shigo da zance, ko darakta bai sa ni a role din malami ba, saboda ba lallai malami ne kawai ya kamata ya kula da addini ba, duk Musulmi ya kamata ya kula da batun addinin shi, saboda haka ko an sa ni ana zance, zance ya shigo da zance zan ja aya in kuma fadi hadisin Ma'aiki sallallahu alaihi wa sallama. Bari in ba ka misali da abu daya, a cikin fim din Soyayya Gamon Jini a saurayi na fito, kuma akwai kananan kaya a jikina, amma wannan bai hana ni fadar ayar ko hadisin Manzon Allah (s.a.w.) ba,
Wannan shi ne kawai tsarin tunda nake yin fim ma in babu wani darakta, ko furodusa wanda ya taba ce mani in ja aya kaza, ko hadisi. Ni ma ina zuwa location (wurin daukar shirin fim) ban san abin da zan fada ba, ana kunna kyamara wallahi ban san abin da zan fada ba.
FIM: Me za ka ce game da mutanen da ke ganin kamar kuskure ne yawan ayoyin da kake jawowa a fim? Wasu suna ganin kamar izgilanci kake yi.
DARE: To menene abin kuskure? A siyasa akwai addini... Bari in gaya maka wani abu, na dade wannan sakon da muke fada ko, sako ne wanda yanzu ya game Nijeriya kwata, har ya shiga makwabtan Nijeriya, za mu iya cewa ma kusan duniya. Amma tun daga sakandare nake yin harkar wa'azi wanda ban shigo cikin fim ba tukuna. Tun a wannan lokacin za a taru a bakin shagona a yi abubuwa, har abubuwan suka yi nisa, ka gane? Amma sakon bai bazu ba sosai kamar yadda yake yanzu a fim, saboda da, in na fadi hadisi guda daya, bai fi mutum goma ko ashirin kawai za su amfana da shi ba. Amma yanzu idan na fadi hadisi daya ko ayar Alkur'ani daya duk dan kallon da yake a Nijeriya sai ya gan ta. Kuma Ma'aikin Allah (s.a.w.) yana cewa: "Duk wanda ya ji sakona ya kiyaye shi, sannan ya isar wa da mutane wannan sakon, sakamakonsa gidan Aljanna."
FIM: Da yawa 'yan kallo suna korafi cewa kun yi wa Musulunci shisshigi a fim din Jahilci Ya Fi Hauka. Ya ka gani?
DARE: Ina ji, na sha ji, har yanzu ma ina ji. Amma kuskure ne abin da mutane suke fada. Na sha fada wa mutane a kan batun jihilcin nan. An taba masu kudi a kan harkar fim, an taba talaka , an taba jahili, an taba masu mulki, kowa an nuna halinsa mai kyau da marar kyau. To menene abin ki kuma don an ce bari a zo a ga halin malamai su ma? Akwai mugayen malamai, akwai kuma malaman kirki, saboda haka kullum idan ka nuna wa mutane cuta, sai ka nuna masu maganinta. Kuma duk abin da Ibro ya yi a fim din Jahilci Ya Fi Hauka akwai wasu malamai masu irin wannan halin.
FIM: Me ya sa ka fin son yin wasa a finafinan Ibro?
DARE: E, akwai dalili. Na farko, rabin rayuwata tare da Ibro take, tun kafin mu fara tunanin wani abu wai shi fim nake tare da Ibro.
FIM: Za ka iya tuna yawan shekarun da ka yi tare da shi?
DARE: Zan iya tunawa. Mafi karanci, yanzu na kai shekara goma sha bakwai tare da Ibro.
FIM: Ka taba yi wa Ibro gyara a kan wani abu da ya yi ko yake yi, wanda ya saba wa Musulunci a fim?
DARE: Akwai. Kuma wannan ba abin mamaki ba ne. Annabi (s.a.w.) ya ce duk dan'adam mai kuskure ne, amma fiyayyen mai yin kuskure shi ne wanda in ya yi kuskure yake tuba. Kullum abin da muke lura in za mu yi fim, ina zuba ido in ga menene in an sa shi a fim zai saba wa Musulunci, sai in ba Ibro shawara cewa a cire shi. Mu mun san muna yi wa Musulunci aiki a fim, shi ya sa duk addu'ar da wasu malamai ke yi a kan Ibro ba za ta yi tasiri ba. Bata ma kansu lokaci kawai suke yi.
FIM: Yanzu kamar yadda ka saba da Ibro, ya za ka yi idan Ibro ya daina wasan kwaikwayo?
DARE: Ni ma na daina, don ma kar ka bata ma kanka lokaci!
FIM: To, Malam Dare, mun gode.
Tsinuwa kan Ibro Usama: 'Ba ta yi mana komai ba!'
Mutumin da ya kirikiro Ibro Usama ya fada wa Ashafa Murnai Barkiya dalilin shirya fim din.
IDAN al'amari ya jibinci addini, to tilas sai an yi taka-tsantsan. Babu ma kamar a harkar shirya fim din Hausa, inda wasu mutane sun kafa wa masu harkar kahon zuka suna son su ga bayansu. A baya, an yi finafinai da ake ganin sun tabo addini, har aka yi suka a kansu. Misali shi ne fim din Ibro mai suna Jahilci Ya Fi Hauka inda rawar 'Salawaitu' ta jawo ka-ce-na-ce. Kuma wasan da Ibrahim Mandawari da Ali Nuhu suka yi cikin wani fim na 'yan legas mai suna Shari'a: Holy Law, shi ma ya jawo surutai.
A kwana-kwanan nan kuma sai wani fim din na Ibro ya jawo hayaniya. Fim din, mai suna Ibro Usama, an yi shi ne ganin yadda al'amarin Balaraben nan dan kasar Saudiyya, Sheikh Usama bin Laden, ya tayar da muhawara bayan harin da aka kai wa Amerika a ran 11 ga Satumba, 2001, inda har yaki ya barke tsakanin Amerika da Afghanistan. Tun kafin fim din ya fito aka shiga cacar baki a kansa, wasu na cewa ya dace, wasu na cewa bai dace ba. Wasu suna tsoron ko Ibro, wanda ya yi kaurin suna wajen rashin tsoro tare da cabo magana a fim, ya ci zarafin addini a cikinsa. A Kano, sai da ta kai rundunar tsare dokar Musulunci, wato Hisba, a karkashin jagorancin shugabanta Sheikh Aminuddeen Abubakar, ta rubuta takarda ga Hukumar Tace Finafinai ta jihar, tana neman a hana fim din fitowa. Wata majiya ta fada wa wakilanmu cewa ita kuma hukumar, ta riga ta ga fim din kuma ta gamsu da shi. Har ta rubuta wa 'yan Hisba takarda tana gayyatarsu su zo su kalli fim din kafin ya fito. Hisba ba su je ba. Saboda haka aka ba masu fim din izinin su fito da abinsu kasuwa. Duk da haka, an ci gaba da sukar fim din tun kafin ya fito. A wasu masallatai ma har tsinuwa aka rika yi a kan fim din da shi kansa Ibro.
Shi ko Rabilu Musa Danlasan (Ibro), wanda ya fito a matsayin Usama a fim din, ya bayyana cewa Ibro Usama yana daga cikin finafinansa da yake alfahari da su, yana cewa fim ne wanda "jahilai suke kwarwa a kansa." A wata hira da ya yi da wata mujalla, an ruwaito Ibro yana cewa, "Wasu jahilai ne suke ta kwarwa a kan Ibro Usama, suna kokarin su hana shi fita. To wallahi duk wani malamin da ya ce zai bakin ciki ina gayyatar malamai su je su ga wannan fim, idan suka ga cewa babu wani batanci ko kuma wani abin da bai kamata ba, to Allah ya tsine masu albarka. Kuma ina gaya maku, ku makiya, cewa ba addu'a za ku yi mani ba, ko menene ba zai kama ni ba!"
Da fim din ya fito a ran 10 ga Mayu, 2002, ya samu karbuwa, musamman a makonnin farko na fitowarsa.
Wani dan wasa mai suna Malam Mato Na Mato ne ya kirkiri labarin Ibro Usama. Kuma shi ne manajan shirya fim din, sa'annan a fim din ya fito a matsayin Firayim Ministan kasar Ingila Tony Blair. Kwanan nan ya tattauna da mujallar Fim kan tsinuwar da suka sha, da dalilin shirya fim din, da kuma kafar ungulu da aka nemi yi masu don ganin an hana su fitar da fim din. Shin me ya yi zafi har malamai suka yi saurin yin tsinuwa kan fim din duk kuwa da cewa Inyamurai sun yi Osama Ben La na 1 da na 2 wanda kuma batanci ne ga Musulunci amma malamai ba su yi wani abu ba?
Ga Mato Na Mato:
FIM: Mu fara da sanin sunanka.
MATO: Sunana Mato, amma a shirin Ibro Usama na fito da suna na Tony Blair, shugaban kasar Ingila.
FIM: Da ma can kai dan wasan kwaikwayo ne?
MATO: Hakika na dade ina yin wasan kwaikwayo. Zan kai kamar shekara sha daya ina wasan kwaikwayo amma sai wannan lokaci ne Allah ya nufa na fara fitowa a bidiyo jama'a suka fara kallona a cikin Ibro Usama.
FIM: Ashe kai dan kungiya ne kenan?
MATO: To, ni dan kungiya ne.
FIM: A ina?
MATO: Ni ina wasan kwaikwaiyo ne a Karamar Hukumar Potiskum da ke Jihar Yobe.
FIM: Ya sunan kungiyarku?
MATO: Sunan kungiyarmu 'Nasiha Video and Film Production'.
FIM: Ina dalilin yin Ibro Usama? Kuma kai ne furodusan fim din?
Mato: Ni ba ni ne farodusan ba amma ni ne Production Manager (Manajan Shirin) kuma ni ne na kawo labarin har kamfanin 'Nasiha Film Production' ya dauki nauyin kawo shi.
FIM: Mato, can baya na tambaye ka dalilin shirya Ibro Usama.
MATO: Dalilin da ya sa na yi tunanin kirkiro Ibro Usama (shi ne) saboda shi dai Usama mutum ne wanda ke son addinin Islama. Kuma mutum ne wanda yake nuna wa sauran kasashen duniya abin da ya kamata. Shi ne na ga ya kamata mu yi fim da sunansa domin mu nuna wa duniya duk wani Musulmi ya koyi irin abin da Usama yake yi domin samun ci gaban Musulunci baki daya.
FIM: Me ya sa kuka dauko Ibro kuka hada da sunansa?
MATO: Ai duk 'yan wasan Hausa da suke Nijeriya kaf, idan ka duba ba za ka kira wani dan wasa ka ce … yanzu a misali za ka ce Tahir Osama? Ko Ciroki Osama? Yaushe fim din zai yi suna? Amma da ka ce Ibro Usama, kowa ya san Ibro mutum ne mai ban dariya kuma duk wasanninsa sun shafi ba da dariya.
FIM: Kafin fim din ya fito mun ji cewa kungiyar 'yan sa kai da sa ido ta Hisba ta yi kokarin hana fitowarsa. Shin sasantawa kuka yi da su?
MATO: Wato su 'yan Hisba na Kano ai ba su da laifi; wasu furodusoshi ne a Kano suka je suka same su suka ce a cikin fim din Ibro yana wulakanta addini kuma yana wulakanta mutane. Su kuma 'yan Hisba suka je wurin Gwamnan Kano domin a ga lallai an hana fim din nan fitowa.
Kulu tare da ogansa Ibro a shirin Ibro Uwar Dawa
|
Sa'annan kuma a masallacin (Jami'ar) Bayero an yi salla an tsine mana ak an Ibro Usama, a Wudil an yi salla an tsine mana a kan Ibro Usama, sa'annan a Kaduna an tsine mana a kan Ibro Usama, a Maiduguri an tsine mana a kan Ibro Usama. Amma daga baya, ranar da fim din ya fito, akwai malaman da suka tsine mana sun kuma sayi fim din suka je suka ga fim din ba yadda suke zato yake ba, suka dawo suka yi da-na-sani.
FIM: Wato malaman sun yi riga-malam-masallaci ne suka tsine maku kafin fim din ya fito su gani?
MATO: Hakika, saboda kawai sun ji an ce 'Ibro Usama,' ba su kalli fim din ba, amma da ma wadannan malamai makiya Ibro ne. Ba suna fada da fim ba ne, suna yi ne Ibro.
FIM: Ya kuka yi da Hukumar Tace Finafinai?
MATO: Na ji dadin wannan tambaya. Akwai wani darakta da furodusa daga nan Kano, suka je Abuja suka ce kada a ba Ibro Usama lasi, idan aka sake shi zai iya haddasa yaki. Su kuma da muka je, aka sa Ibro Usama suka gani suka ga ba a zagi addinin Musulunci ba, su ma Kiristan ba a ci masu mutunci ba, sai A.A. Kurawa (daraktan Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano) ya ce zai ba mu lasi amma sai mun cire wakokin da ke cikin Ibro Usama. Shi ya sa ba a ga waka a cikin fim din ba.
FIM: Yanzu me ke gabanku?
MATO: Nan da sati biyu za mu yi Ibro Usama na 2 tare da wani fim dinmu mai suna Sharifiya.
FIM: Su wa suka taimaka maku wajen fito da Ibro Usama, domin kai bako ne?
MATO: Na farko Alhaji Hassan Adamu, sai Auwalu Marshal, sai Sule Yahaya Bosho wanda ya fito a matsayin Bush a fim din.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|