Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 33   Satumba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Maryam Umar Aliyu ta ce
BA NI DA AURE!

A ganinta abokan gaba ne suke son su ga bayanta ·

Labarin soyayyarta da Shu'aibu Kumurci

Maryam
Maryam sabuwar budurwar Shu'aibu 'Kumurci'

Daga IRO MAMMAN, MUHAMMED NASIR a Kano da BASHIR YAHUZA a Katsina

ABIN mamaki ba ya karewa, musamman a fagen shirin fim na Hausa. Kyakkyawar yarinyar nan Maryam Umar Aliyu, wadda muka ba da labarin yadda mahaifinta ya yi ikirarin cewa har yanzu tana da aure, ta karyata maganar, ta ce ita dai a iya saninta tuni mijinta ya sake ta.

Amma Maryam, wadda kusan a ce babu 'yar wasan da ta kai ta kankantar shekaru a yau, ba ta ce babanta karya yake ba, a'a, cewa ta yi tana shakkar sahihancin labarin, domin a cewarta shi babanta ya san mijinta ya sake ta "har sau biyu," don haka ya zai ce wai har yanzu tana da aure?

Ranar da mujallar Fim ta fito dauke da labarin, mutane da dama sun tarbe ta sun ce mata, "Maryam ashe kina da aure?" tun ma kafin ta ga mujallar. Ba ta karanta ta ba sai a ofishinmu na Kano inda ta je da sauri don jin yadda al'amarin yake. Da ta ji bayani daga bakin editanmu sai ta ce to insha Allahu za ta dawo bayan kwana biyu ta fadi nata bangaren labarin, domin gaba daya ba ta yarda da abin da baban nata ya fada ba.

Bayan kwana biyu, wakilanmu sun gamu da ita a filin da ke ofishin hada hotunan bidiyo na 'Kwality Audio-Visual', inda matattarar 'yan fim na Kano ce. A wurin ne 'yar wasan, wadda shekarunta 16 yanzu, ta zanta da wakilanmu.

Maryam ta fadi abin da ta fara yi bayan ta karanta labarin kalamin mahaifinta. Ta ce, "Ni dai da aka zo min da wannan labari wanda kuka buga kuma na gani, to na tambayi babana da waliyyaina da mahaifiyata, 'Ko aurena ya mutu ko bai mutu ba?' suka ce min ai ya mutu."

'Yar wasan ta bayyana cewa ba ita ce ta tafi Katsina ta yi wa babanta magana kan abin da ya ce ba, a'a, wai kanwar mahaifiyarta ta sa ta je ta tambaye shi. "Saboda haka ni dai na san aurena ya mutu, amma ban san yadda aka yi ba har kuka buga min wani auren daban sabo," inji ta. Ta kara da cewa, "Ai (mahaifina) ba zai tozarta ni ba."

Sai dai kwana biyu bayan wannan tattaunawar da ta yi da wakilinmu, Maryam ta zo ofis dinmu da ke Gyadi-Gyadi domin yin karin bayani. Da farko ta kara nanata cewa ba ta yarda mahaifinta ya yi maganar ba, to amma da ta ji bayanin yadda aka yi maganar da shi a shagon 'Salamah Video Centre' da ke Sabon Layi, Katsina, sai ta tsaya ta yi tunani, sa'annan ta ce, "E to, gaskiya na yarda zai iya yin wannan maganar a lokacin. To amma yanzu mun shirya. Ya kyale ni."

Yarinyar, wadda 'yar asalin kabilar Abzinawa da ke Jamhuriyar Nijar ce, ta taba auren wani mutum wanda ke zaune a unguwar Gwammaja, bayan Sakatariya, a cikin shekarar 2000. "Duka duka kwanana biyu a gidan sai na gudu, domin ba na son shi," inji ta. Ta kara da cewa ita ce ta hudu a cikin matan alhajin.

Maryam ta kalli labarin da ya fito a Fim ta watan jiya kawai a matsayin wani yunkurin wasu makiyanta na ganin bayanta. A ganinta, akwai 'yan wasa mata wadanda ba su kaunarta ita da Maryam Aliyu, jarumar shirin Mushaqqa (budurwar Ahmed S. Nuhu) domin kyaunsu da sauransu. Suna ganin cewa zamanta ita da Maryam wata barazana ce a gare su, domin dai furodusoshi da daraktoci suna son saka kyawawan mata a finafinansu. "Kai, bari in fada maka," inji ta, "wannan ba wani abu ba ne sai kulle-kulle don a bata min suna. To ni dai na riga na yi gaba, na zama ciwon ido - sai hakuri! Masu son ganin bayana sai dai su mutu!"

"Ba wai ni kadai ba, har da 'yar'uwata Maryam Aliyu ake son ganin bayanmu, ana wani menene menene. To, kowa ya sani, na gaba ya riga ya yi gaba. Ba yadda saura za su yi da mu. Kuma mu haka muke, ba bori ba malam. Ni a cikin Industiri kaf babu wata wadda ta isa in daga fuska in kalle ta." Ta tafa hannaye kuma ta bugi cinya.

To, bayanan Maryam sun dami wakilanmu, don haka mun tafi har Katsina don ganawa da uban Maryam da kuma wakilinmu na can Bashir Yahuza. Mun tarar cewa lallai mahaifin nata ba ya Nijeriya, ya tafi Nijar tun kwanan baya, don haka ba gaskiya ba ne wai ya yi magana da wani a kan batun 'yar tasa bayan labarinmu ya fito. Bashir kuma ya tabbatar mana da cewa ya yi hira da Alh. Umar Aliyu a shagon 'Salamah Video', har uban yarinyar ya ce masa, "Ina so idan na dawo daga Nijar za ka taimake ni mu tafi Kano tare da kai ka taya ni in gano inda Maryam take." Shi a tunaninsa har yanzu wasu 'yan fim sun boye ta a birnin na Dabo.

Ga alama, furodusoshi da daraktoci sun daina jin irin tsoron nan na saka Maryam a finafinansu. A yanzu Maryam ta yi finafinai da dama a karkashin darakta Tijjani Ibraheem da wasu furodusoshin. Sun hada da fim din Hakarkari, Tafiya 2, Hawayen Jini, Ufula, da wadansu da ta ce an ki fadin sunayensu sai za su fito saboda tsoron satar sunan fim da wasu ke yi. Wani dan wasa ya ce, "In dai Maryam ta samu iyayenta suka sakar mata mara, to gaskiya za ta yi tashe. Ni ina ma ganin sai ta fi Maryam Aliyu yin fice. Sai ta doke kowace yarinya a harkar fim."

A yanzu Maryam da Maryam sukan yi wasa tare a fim a mtsayin ya da kanwa.

A cikin zancen da ta yi da wakilanmu a ofishinmu a ran 14 ga Agusta, Maryam ta lissafa sunanyen 'yan wasa mata guda uku wadanda ta ce su ne suke ta kulle-kulle don su ga bayanta, ta ce har daya daga cikinsu ma ta sa mata ciwon tarin fuka (asthma). Sa'annan kuma ta ce akwai wadda ta ji an ce ta ce wai ita Maryam karuwanci take yi. Bayan ta karyata maganar sai ta ci gaba da cewa ai in maganar karuwanci ce, to ita waccan 'yar wasan ita ce karuwa, domin ko a gidansu sun yi gadon karuwanci.

Tun da fari sai da ta umurci wakilinmu da ya isar da wani sako nata ga 'yan fim mata baki daya: "Ka shaida wa duk masu ganin mun tsare masu gaba cewa ni da Maryam mun kusa bar masu Industiri, amma su dau hakuri tukuna."

Shu'aibu Kumurci
Shu'aibu a wani shirin fim

A nan, tana magana ne kan batun aurensu da ta ce ya kusa. Ita dai Maryam Aliyu, za ta auri Ahmed S. Nuhu nan da wata biyu, inji wata majiya, ita kuma Maryam Umar Aliyu yanzu ta fara zurfafa a cikin kogin soyayya da fitaccen dan wasa Shu'aibu Lawan (Kumurci), wanda bai dade da fitowa daga cikin matsanancin hali ba na rasuwar amaryarsa Balaraba.

Da muka tambaye ta kan irin zurfin soyayyarta da Shu'aibu, wadda ake ta labarinta a Kano, sai yarinyar ta kada baki ta ce ai maganar aurensu ma ta yi nisa. "Sai ma abin da ya yi gaba," inji ta.

Ta kara da cewa tun lokacin da ta fara soyayya da Shu'aibu, makiya da dama sun yi masa caa, suna zuga shi kan cewa gaskiya bai kamata ya neme ta ba, ana ambaton muggan kalamai game da ita. Ta ce shi kansa labarin da Fim ta buga inda ta ruwaito mahaifin Maryam yana magana, ya kara ruruta wutar zugar da aka yi wa Shu'aibu. Amma dai ta ce babu wadda ta isa ta raba ta da dan wasan, domin shi kansa yana son ta kamar me.

Maganar da wani wakilinmu ya yi mata a karshe addu'a ce kan batun soyayyarta da Shu'aibu, yana mai cewa, "Maryam, Allah ya tabbatar da alheri." ·

Ita kuma ta amsa, "Amin."

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin