DAUKAKA daga Allah take zuwa. A fagen shirin fim za ka ga mai shirya fim ko dan wasa ya shafe shekaru da dama yana ta hakilo ba a san shi ba, ba a kula da shi ba, kuma ba a damu da shi ba. Wani sai ya shirya finafinai masu tarin yawa, komai kyansu ko ma'anarsu ko kudin da aka kashe a kansu don su burge, amma sai ka ga bai yi fice ba. Ya dinga hakilo don ya zarce sauran, amma a banza. Wani kuwa da ya yi fim daya ko biyu sai duk duniya ta san shi, ya-Allah fim din ya yi kyau ko bai yi ba. Zai yi wuya a fadi dalilin hakan illa a ce Allah ne mai yin komai. Shi ya sa Hausawa kan ce sa'a ta fi manyan kaya.
Irin wannan al'amari ya faru - ko mu ce yana faruwa a yanzu - ga wasu mutum biyu a Kano. Daya sunansa Rabi'u Ibrahim Harabs mai kamfanin 'HRB Production'. Dayar kuma mace ce mai suna Fatima Baffa Sa'adu, wadda aka fi sani da sunan Fati Baffa Fagge.
Shi Rabi'u da shi aka fara harkar fim na kaset. Da kafar dama ya shigo, domin dukkan finafinan da ya shirya sun ciri tuta a gun 'yan kallo kuma sun yi kasuwa. Su ne: Tawakkali, Abin Sirri Ne, Furuci, Mashi, da Rawani. Ba su da yawa, amma abu dan kadan mai amfani, inji Hausawa.
A baya, duk da wannan nasara da ya samu, 'HRB Production' bai yi tashen wasu kamfanonin ba. To amma yanzu yana neman ya taushe su baki daya, domin a gaskiya yanzu a Kano shi ne kamfanin da ya fi kowane tashe.
A daidai lokacin da kamfanoni da yawa suke cikin garari, HRB sai bunkasa yake yi, musamman tun fitowar shirin Mashi. Lakabin kamfanin da shi kansa Rabi'u shi ne "Babban Kamfani".
Fati Baffa Fagge ce jammar shirin Mashi. Ita din ma ta sha wuya a baya kafin Allah ya tarfa wa garinta nono har ta yi fice. Ga shi dai ba ta dade a fagen shirin fim ba, domin duka-duka shekararta daya. Ta zauna cikin kungiyar dirama ta Janzaki. Saboda rashin farin jininta a baya, bayan ta yi wani fim wai shi Takama, sai da ta kai furodusan shirin ya ce an cuce shi an sa masa jarumar da ba a sani ba.
Yanzu ko Fati ta shiga sahun gaba na 'yan wasa mata, wadanda tauraruwarsu ke haske. Kai, a yanzu ma dai ita ce lambawan a cikin jerin jarumai mata. Kuma fim biyu kawai suka janyo mata shaharar, wato Mashi da Rawani na 'HRB Production'. Lakabinta shi ne "Bararoji" saboda wakar "Baram Baram Bararoji" da ta bi a Mashi 1, wakar da fasihin nan Yakubu Muahmmad ya rubuta ya rera, kuma Apolos A. Dengu ya yi wa kida a kamfanin 'Sulpha Audio-Visual' da ke titin gidan Zoo.
A yanzu dai "Babban kamfani' da "Bararoji" sun kulla auren zobe, ko mu ce huldar zobe. Sun kara yin wani fim din mai suna Sunduki, kuma nan gaba kadan za su shirya wasu biyu masu suna Tubali da Kasko. Shi Kasko, na Hajiya Hadiza ne, wadda ta taba daukar nauyin shirya Mushaqqa. Shi Rabi'u, tuni ya zama darakta, ya fara da Rawani, kuma shi ne zai ba da umurni a dukkan finafinansa da ke tafe. Mun kuma fahimci cewa kamar yadda ya saba a duk finafinansa na baya, Ali Nuhu ne jarumin finafinan da Rabi'u zai yi. Mun ji an ce Rabi'u ya ce in dai da rai da lafiya, to babu fim din da zai yi wanda ba Ali ba ne jaruminsa domin kwarewar Alin da kuma dadaddiyar abokantakarsu. Wato dai za mu rika ganin tsari kamar haka:
Kamfani: HRB Production
Darakta: Rabi'u Ibrahim
Jammi: Ali Nuhu
Jaruma: Fati Baffa Fagge.
Shin wai ma wacece Fati Baffa Fagge? Ita 'yar ina ce? A ina ta yi makaranta? Yaushe ta shigo harkar fim? Me ya sa? Menene ra'ayin iyayenta? Ya aka yi ta zo "Babban kamfani"? Menene burinta a nan gaba? Ta taba yin aure kuwa?
Mun aje lokaci da Fati a 'HRB Production' - wato karfe 7 na dare a ran 19 ga Satumba. Na riga zuwa ofishin, muka shiga labari da Rabi'u, Yakubu Muhammad, da Baballe Hayatu. Rabi'u ya aika mata da sako ta wayar GSM, ya ce mata, "Kin manta da batun karfe bakwai ne?"
Ba a jima ba sai ga Fati B. ta zo. Yarinya ce fara, mai fasali, mai yawan fara'a. Mun sha haduwa a da, ko a ofishinmu na mujallar Fim ko a wani wuri, don haka ni ba bako ba ne a wurinta.
Bayan mun ci gaba da zantuttuka, sai Rabi'u da Yakubu, wadanda sun rukume suna ta labarin yadda za a tsara shirin Kasko, musamman bangaren wakokin fim din, suka fita daga ofis din suka ba mu wuri domin mu ji dadin yin hirarmu ni da Fati B.
Shikenan, na dasa rikoda muka fara hirar da ta dauke mu awa daya da rabi. Bismilla:
FIM: Mu fara da takaitaccen tarihinki.
FATI (murmushi): Assalamu alaikum. Ni dai sunana Fatima Baffa Fagge. Ni haifaffiyar Fagge ce (a Kano) amma mahaifana haifaffun Karamar Hukumar Taura ne cikin Jihar Jigawa. Na yi firamare a 'Festival Primary School', na gama a 1988. Na yi JSS 1-3 a Jahun, na yi JSS 4-6 a 'Garki Secondary School,' na gama a 1995.
Yanzu kin kai shekara nawa da haihuwa?
FATI: Shekarata ashirin da biyu.
Bayan kin gama makaranta a Garki, me kika yi kuma?
FATI: Sai na tafi na yi difiloma a 'Federal College of Education' (FCE) , Kano, na karanta 'Accounting and Audit'; daga difloma na wuce na yi 'advanced diploma', duk dai a kan 'accounting and audit.' Shikenan da na gama kuma ban kara ba.
A wace shekara kika gama?
FATI: A bana na gama.
Kin taba yin aure?
FATI: Na taba, bayan na gama sakandare. Auren dai bai fi (tsawon) wata shida ba.
Ba 'ya'ya kenan?
FATI (ta girgiza kai): Babu.
A wace shekara kika shiga harkar fim?
FATI: A gaskiya ba zan iya tuna shekarar ba, amma (bayan) an yi auren Fati ne, domin har na je bikin Fati. A lokacin ban yi fim ko daya ba, kuma ina so in fara fim a lokacin. Bayan an gama bikin ne na shiga kungiyar (wasan kwaikwayo ta ) Janzaki.
Ya aka yi kika shiga kungiyar Janzaki?
FATI: Akwai wani (mutum) a nan layinmu a Fagge (mai suna) Ibrahim Ibrahim. Shi na samu na tambaya ya ake ake shiga fim.
Wanene shi wannan Ibrahim Ibrahim din?
FATI: Wani ne wanda yake a ofishin "Mandawari Enterprises.' To da na tambaye shi yadda ake shiga harkar fim sai ya ce ina so in shiga ne? Na ce e. Shi ne ya ce to in zo zai shigar da ni ta hanyar kungiya. Shi ne ran Asabar ya dauke ni ya kai ni kungiyar Janzaki. Ya gabatar da ni a gunsu, suka amshe ni, suka ba ni fom na cike, duk irin tambayoyin da suka yi min duk na ba su amsa. Shikenan suka dauke ni.
Daga na kun rika yin wasanni irin na dabe ne ko kuwa?
FATI: Gaskiya ni dai ban fiye yin wasannin dabe ba.
A kungiyar ba ki taba yin wasan dabe ba?
FATI: A'a, mun taba.
To yaushe ne kika fara shiga ainihin wasan fim na kaset?
FATI: Wata rana ne ina nana cikin kungiyar sai Rufa'i Kudi, wanda ya yi fim din Dace, ya same ni ya ce yana son in yi mai fim. Amma karashe ne, don an kusa yin shekara da (soma) yin fim din. Ya ce sauran waka, saboda haka za a ba ni waka in zo in yi wannan wakar. Aka ba ni waka na je muka yi rihazal mukai komai, na zo na yi wakar. Shi ne dai fim din da aka fara dora min kyamara, a fim din Dace.
Daga nan wadanne finafinai ne kika yi kuma?
FATI: Finafinan da ni ce na ja fim din? Na fito a Takama, Jayayya, da Hudubar Shedan.
Za a iya cewa fim din Mashi ne ya fito da ke fiye da sauran. To yaya aka yi kika shiga fim din na Mashi?
FATI: Ka san komai daga Allah ne, kuma Allah ne ke hada mutum da mutum. Ni dai na san ranar da Allah ya hada ni da Rabi'u a 'Dukku Production,' su Lilisco suna editin wani fim (mai suna) Dana. Muna zazzaune ana hira sai Rabi'u ya zo. Muka gaggaishe shi. A gaskiya lokacin ban san shi ba. Sai ya tambaye ni ina yin fim? Sai Lilisco ya ba shi amsa. Ya kira ni ya tambaye ni iyayena sun yarda in yi fim? Na ce e iyayena sun yarda. Ya ce to ya za a yi ya tabbatar? Na ce in yana so mu je gun iyayena ya zo mu je. Muka sa rana, muka dauki kafa muka je gun mahaifiyata, ya tabbatar daga bakinta, sannan ya zo ya sanya ni a Mashi.
Da ma ita mahaifiyarki ba ta nuna rashin gamsuwa ba tun da farko da kika shiga harkar fim?
FATI: Gaskiya mahaifiyata ba ta nuna damuwarta ba. Daga mahaifiyata har mahaifina sun dauki harkar fim din sana'a ce. A lokacin da na je na nuna masu cewa ina so in yi fim, abin da mahaifina ya fara ce min shi ne Allah ya ba da sa'a, Allah ya taimaka min - amma in kare mutuncina. Haka na koma gun mahaifiyata na durkusa na ce ina son in yi fim. Ita ma ta ce Allah ya ba da sa'a amma in kare mutuncina. Su sun yarda da harkar fim ba harka ce ta iskanci ko ta bariki ba, don haka suka ba ni goyon baya a kan in je in yi sana'ar fim.
Ban da Mashi da Rawani, akwai wani fim da kika yi wanda kike ganin yana da karfi shi ma?
FATI: E, akwai su. Gaskiya wasu ban san sunansu ba, amma akwai Hannun Dama da Mandawari ya yi kwanan nan.
Ke ce yariyar fim din?
FATI: A'a, ni ba ma wani matsayi sosai aka ba ni ba; sin daya kadai na yi a fim din. Amma na san komai na Allah ne kuma Allah ne mai yin abin da ya so.
Shin kikan je can garinku Taura?
FATI: Ina zuwa sosai ma kuwa.
Ta yaya mutanen garin suke kallonki a matsayin 'yar garinsu da ta zama fitacciyar jaruma?
FATI: Sau da yawa in muka je, yaran gari sukan taru a kofar gidan mahaifina. Shi mahaifina… duk wanda ya je Taura ya ce Alhaji Baffa Sa'adu za a kai shi wurinsa tun daga bakin tasha. In muka sauka tun daga tasha da zaran yara sun gan ni za a fara cincirindo har zuwa kofar gidanmu. Sai su je su yi ta wakokina, wasu su yi wakar Rawani wasu su yi ta "Bararoji", wasu su yi ta Sunduki, har lokacin da za mu gama abin da za mu yi mu bar garin. Duk da dai da ma tun kafin in fara fim ina zuwa garin amma sanadin fim din sai na zame masu kamar bakuwa. Hatta matan aure in na je garin suna zuwa a gaisa da ni.
Yaya kike ji idan mutane sun taru suna kallonki a gidan biki ko a kasuwa ko a kan layi? Kina jin haushi, ki ji kamar ana damunki?
FATI: (dariya): Haba, wane irin jin haushi? Daukaka ce daga Allah. Kuma daman dukkanmu nan da muke fitowa muna yin harkar nan abin da muke neman kenan, kuma mu roka Allah ya ba mu. Saboda haka ni a duk lokacin da na ga irin wannan ba ni komai illa farin ciki da annashuwa da kuma sake gode ma Ubangijinmu da ya kai ni wannan matsayin.
To ga shi sunanki Fati, kuma an taba yin wata Fati da Allah ya daukaka. To ya kike ganin tashenki zai kasance idan an kwatanta shi da na waccan Fati din? Kina jin za ki yi fice kamar nata?
FATI: To, wannan abin daga Allah ne, kuma Allah shi yake ikon shi. Saboda haka ni ba zan iya tabbatar da gaibu ba. Sai yadda Allah ya yi kawai.
Yanzu ana kallonki a matsayin yarinyar kamfanin HRB. Wadanne finafinai ne za ku yi a wannan kamfanin a nan gaba kadan?
FATI: E, akwai su. Akwai Tubali, akwai Kasko.
Kuma ke ce yarinyar finafinan?
FATI: E, to, ba zan iya tabbatarwa ba, sai an gani.
Kikan je wasu garuruwan domin yin fim ko kuwa sai a Kano kawai kike yin fim?
FATI: a'a . Na je Kaduna, Zariya, Abuja, Birnin Kudu, da Jos.
Kuma duk a matsayin yarinyar fim din?
FATI: Ban da dai na Abuja da na je, gaba daya wadannan ni na ja fim din.
Menene burinki a nan gaba cikin wannan harka?
FATI: Hakika ba ni da niyyar dadewa a harkar industiri. Burina shi ne idan Allah ya fitar min da miji nagari, mai kaunata, ni ma kuma ina kaunarsa, shikenan mu yi aure.
Kina nufin har yanzu ba a samu wanda ya ce yana so ba?
FATI: (dariya): Abin sirri ne!
Me za ki ce kan mugun kallon da wasu ke yi maku musamman ku 'yan wasa mata?
FATI: Hakika ba abin da zan iya cewa illa masu yi mana kallon 'yan iska ko mu karuwai ne ya kamata su tsaya su lura da (cewa) duk wata yarinya da take yin fim, ko namiji da ke fim, shin yaya yake wasansa kuma ya yake? Saboda duk mutumin da yake dan iska ne shi ba zai dauki sana'a ya sa a gabansa ba, sai dai ya sa rayuwar nan da ya sa a gabansa. Mu kuma ina ganin duk wadda ta sa ranta a harkar nan, to in an duba an tace za a ga ba 'yar iska ba ce. Don kowace da za ka ga ta fito, da mutuncinta da darajarta. Ina kira ga duk 'yan'uwana Musulmi, masoya finafinan Hausa, masuyi mana irin wannan kallon, don Allah don Annabi su daina. Su dauke mu da mu da su tamkar daya muke.
Shin Fati da gaske ne wai kin fara yin karatu a Jami'ar Bayero kika daina?
FATI: (girgiza kai): Gaskiya ban taba ba.
Wane sako za ki so ki isar gaa 'yan kallo masu kaunarki?
FATI: Ba abin da zan ce wa masoyana masu kallon finafinaina illa godiya da kuma Allah Ubangiji ya kara mana zumunci tsakanina da su. Da wanda na sani a zahiri da wanda ban sani ba da wanda sai dai in ji sako cewa daga gu kaza ina da masoya wadanda ban taba ganinsu ba, da kuma masu aiko min da kyaututtuka, sai dai in sake cewa Ubangiji Allah ya kara mana dankon zumunci da arziki da soyayya.
Wane kira za ki yi ga 'yan'uwanki 'yan wasa?
FATI: Ina kira ga duk wata 'ya mace, daga manyanmu zuwa yaranmu matasa, don Allah mu hade kanmu mu zama daya, kuma ya zamana cewa bakinmu ya zama daya, kuma mu zamana muna kishin 'yan'uwanmu wanda abin da ya samu dayanmu ko da daya ba ta sani ba idan ta ji labari… mu hade kanmu, mu taimaka ma junanmu. Kuma duk wani abu da zai zamanto mana bacin rai ga rayuwarmu, mu kiyaye shi. Mu kuma kare mutuncinmu daga duka wani abu mara kyau wanda zai zamanto na waje ya gani ya zage mu.
Haka su ma 'yan'wanmu maza, su ma su daure su hade kansu daga manyansu har yaran, su ma su zamanto komai nasu ya zama daya. Wani surutu a waje game da matanmu, don Allah su kiyaye shi. Kuma in sun san za su yi wani abu da zai bata mana, mu mata, don Allah su kiyaye shi saboda gaba dayanmu mu zama daya, mu zama tsintsiya madaurinmu daya.
Fati, na gode kwarai da gaske.
FATI (dariya): Ni ma ina godiya.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin