Har dai wata rana wakilinmu ya kasa hakura ya tambayi wani mutum a kofar gidan dalilin yawan fitar shahararren dan wasan da wuri. Mutumin ya ce ka sa yawu idan kaga ya fita da sassafe, zuwa yake yana gaishe ka.
Daga bisani an rutsa Malam Kabiru a dandalin taron kungiyar wasan kwaikwayon da yake yi wa shugabanci mai suna 'Dabo Film Dramatic Association'. Tunanni wakilinmu shi ne tunda Nakwango gwani ne wajen iya magana, ya yi masa shiri sosai kafin su fara tattaunawa. Sai dai kuma ana kanga masa rikodar nadar labarai a baki sai Nakwango ya koma tamkar mai amsa tambayoyi a gaban alkali.
Ashe alkalin na cikin fim fim akasi lamfalewa wakilinmu ya yi. Ai can da hira ta yi nisa sai ga Nakwango yana daga yatsa sama, sai dangwalar kasa, sai bugun kirji, kai abin har da jijjiga rigar da yake sanye, da harara, murmushi da kuma cizon baki.
Ga yadda hirarsu ta kasance inda Nakwango ya bayyana irin wautar da ya yi sa'adda bai mallaki hankalin kansa ba. Yadda ya samu kudi ta hanyar saye da sayar da hatsi, inda ya koyo da inda yake koyarwa, siyasarsa, alakarsa da karuwai da kuma dalilan da suka sa ake zagin 'yan fim, da sauran bayanai. Bismilla:
FIM: Malam Kabiru, kana daya daga cikin wadanda a wannan shekara masu kallo da masu karatu suke neman jin tarihinsu.
NAKWANGO: Assalamu alaikum. Ni an haife ni a ranar 2 ga Fabrairu, 1958, a unugwar Karofin Kangiwa cikin Karamar Hukumar Dala ta birnin Kano.
FIM: Sai batun karatu.
NAKWANGO: Na taso na gan ni a Dala Islamiyya wadda mahaifina da abokansa ne suka kafa makarantar. Ban san lokacin da aka sanya ni ba, gaskiya na taso na gan ni a cikinta. Da na kare ta sai na samu jarabawa kusan kashi uku. Na samu sakamako da ke kirana zuwa Makarantar Horon Malamai ta Gwale (GATC), na samu wannan ya kira ni zuwa makarantar hiron malamai ta harshe Larabci, wato 'School for Arabic Studies,' kuma na samu Aliya. Amma a karshe sai na tafi S.A.S. Ina a S.A.S. shekara ta 1974, ban kare ba saura shekara daya na samu matsala a zuciyata, wato na ji ba ni sha'awar Larabci; abokaina da nake tare da su duk boko suke yi. Wannan ya sa na bari, na dawo kuma na shiga makarantar firamare a Dala a cikin 1975 zuwa 1980. Sai na wuce 'Government Secondary Commercial College' - makarantar sakandaren koyon sana'o'i ta kan Titin Filin Jirgin Sama. Mu ne dalibai na farko da aka fara diba a makarantar.
A shekarar da nake kokarin kammalawa, kuma a wannan shekarar babana ya ce sai na je na yi jarabawa ta 'S.A.S. High Islamic', ya ce zai je ya nemi alfarma wurin malaman S.A.S. cewa zan dawo in cika shekarata daya kuma in zauna jarabawa. Na ce ai ni boko nake yi, shi na fi maida wa hankalina. Sai ya ce shi dai yana so in je in zauna waccan jarabawa. Ya dinka min kayan makaranta.
A karshe dai na je inda yake so din kuma na ci jarabawa sakamako mai kyau. Amma da na dawo na zauna wanda na fi so, watau na boko, sai sakamakon da na samu bai kai karfin na Arabiyya din ba. Daga nan kuma sai na dawo kan abin da gidanmu ke yi - kasuwanci, noma da karatu.
FIM: Wace irin sana'a ka fada?
NAKWANGO: Sai na fada sayar da hatsi kuma.
FIM: A wace kasuwa kake sayar da shi a lokacin?
NAKWANGO: Bafatake ne ni, duk inda ake zuwa sayen hatsi a Arewacin Nijeriya ba inda ban je ba. Na yi suna, na shahara, na samu kudi masu yawan gaske, har sai da ta kai ana misali da ni a cikin harkar. Ina nan ina yi, to daga baya sai na koma kan abin da na gada gun mahaifina, wato koyarwa. Kuma a wannan halin ina koyarwa a makarantar Islamiyya. Akwai kuma wata makaranta ta Islamiyya da muka kafa a unguwarmu. Akwai wata ma a nan Gwammaja tun a lokacin har yanzu ni ne ke shugabantar makarantar. Rayuwata gaba daya ta kare ne a kan koyarwa da kuma koyo, musamma na Alkur'ani.
FIM: Kana aikin gwamnati?
NAKWANGO: To ina aiki da wancan sakamako na S.A.S; da shi na nemi aiki, na samu.
FIM: Can baya ka ce ka yi kudi a harkar kasuwancin hatsi. To jarinka ne ya kare ko 'yan daukar bashi ne suka gurgunta ka?
NAKWANGO: A wancan lokacin da tafiya ta yi tafiya sai rikice-rikicen siyasa da wasu al'amurra suka taru suka lalata min kasuwancina. Daga baya sai wani aminina wanda yana daya daga cikin abokaina wanda a rayuwata nake alfahari da shi ya ce min tunda a da kyauta nake koyarwa, in dauko sakamakona in koma gwamnati ta ci gaba da biyana. Yanzu haka malamin makaranta ne ni, a 'Dala Special Primary School.'
FIM: Zuwa yau shekararka nawa kana koyarwa?
NAKWANGO: Kusan na fara koyarwa tun 1972-73.
FIM: Kai sunanka Kabiru. Shin wanene Nakwango? Mahaifinaka ne ko kuwa lakabinka ne, sunan banza ne ya bi ka tun kana yaro?
NAKWANGO: Cikakken sunana Kabiru Abubakar Aliyu. Mahaifina ba shi da alaka da 'Nakwango'. Wato akwai matasa da dattawa da sukan taru ana hira, a yankin Makwalla ne. A wannan taruwar da suke wajen gidan Malam Aminu Kano, to ni na taso da wauta, don duk abin da ka zo da shi idan kana tsoronsa ni zan iya yi maka shi kai tsaye. Kai, sai da ta kai ana gindaya kara kan kwata a ce min, "Ga gada nan, hau!" Ba ruwana, saboda wauta sai in hau.
Sai wasu suka ce min, "Wannan yaron, wauta kamar Baba na Gwammaja!" Yana nan inda yake ya koma wani wuri a Layin Famfo yana saida goro da taba. To shi wannan tsoho ana ce masa Baba Nakwango. Sai wasu kuma ke ce min, "Wauta kamar Baba Nakwango!" Asalin wannan suna kenan.
Inda sunan Nakwango ya yi karfi daga 1978 zuwa yau. 1977 zuwa ta 1978 ne na shahara a fannin kwallon kafa, kuma a lokacin nake kan ganiyata ta karatun Alkur'ani; lokacin ne nake kan ganiyata ta harkokin kungiyoyi; sai da ta kai har a jikin babur na rubuta 'Nakwango.'
FIM: Da ka ce ka yi wauta. Toban da wautar kana yaro matashi ka yi hatsabibanci kamar cin zalin din yara wurin wankan kududdufi inda ake jefa su cikin ruwa ana tsamo su bayan sun galabaita?
NAKWANGO: Ni ba hatsabibanci ba ne. Amma dai na yi wankan kududdufi.
FIM: Daga wane lokaci ka fara wasan fim? Kuma kungiyar Dabo kai ne ka kafa ta ko zuwa ka yi ka same ta?
NAKWANGO: Ba zan iya kiyaye shekarar da na fara wasan kwaikwayo ba, amma dai na san na fara yin wasan Hausa na rediyo. Wasan Kasimu Yero na fara gani na fara sha'awa, tun zamanin RTK. Sai wasu yayyena, Hashimu Sa'id da Yusuf Mohammed, a lokacin farkon shigowar rikoda, suka shirya wasan kwaikwayo a kaset na rikoda. Shikenan sai na shiga ciki ni ma. Amma dai na san lokacin kungiyar Jankare ce; kungiyar kankare ta rushe cikin 1973.
FIM: To shigarka Dabo fa?
NAKWANGO: Kafin in shigo Dabo na yi kungiyoyi da yawan gaske kuma na rike shugabanci sosai; sai da ta kai a nan Kano an kafa Majalisar Kungiyoyin Wasannin Kwaikwayo wadda cibiyarta ke karkashin Hukumar Adana Tarihi da Al'adu ta Jihar Kano, ni ne babban sakatarenta; Sawun Kura shugaba, Hajiya Tururuwa Allah ya jikanta tana shugabar mata.
Daga nan akwai wata kungiya mai suna 'Sardauna Youth Dramatic Society'. Ina cikinta sai wani rikici ya sa na ga ba zan iya daurewa ba, sai abokaina suka ce min sun iya harkar wasannin motsa jiki, me zai hana mu kafa wata kungiya? Da na zo nan sai na ce zan kafa kungiya. Da na kafa aka sa mata suna wai ita kisimasi. Na ce ban yarda ba. Daga baya na ce me zai hana a sa mata suna Dabo? Saboda duk dan da yake Kano yana alfahari da Gidan Dabo. Ita kanta Kanon ma, ai 'Kanon Dabo' ake ce mata. Sai muka sa sunan 'Dabo Films.'
FIM: A wace shekara kenan?
NAKWANGO: 1994.
FIM: Wace shekara ka fara fim din Hausa masu tafiya cikin bidiyo a yanzu?
NAKWANGO: Wanda bai je kasuwa ba ina da kamar 14, tuni na yi su. Amma wanda ya je kasuwa kuma na fara fita a cikinsa shi ne So Ne Ko Kauna? Shi ne kuma fim din Hausa na farko da aka fara nunawa a allon sinima na Wapa. E, kuma shi ne farkon fim din action (na gumurzu) a Kano.
FIM: A cikin finafinan Hausa yanzu kusan a ce kaina ke jan ragamar masu fitowa a matsayin iyaye maza. Ya kake ganin wannan?
NAKWANGO: A takaice takaitawa duk lokacin da na fito a matsayin uba, to ina kokarin in kwantata yadda iyaye suke yi da 'ya'yansu, walau iyayen masu kirki ne ko kuma wadanda ba su fahimci abin da ya kamata su yi wa 'ya'yansu ba. Nakan yi kokari in kwatanta irin yadda wadannan mutane ke yi a yanayin rayuwarsu. Duk irin role din da ka zo da shi a wasan kwaikwayo, matsawar ba zai taba addini na ko mutuncina ba, to ina yinsa.
FIM: Akwai masu tunanin ko ka taba yin wani karatu na fanninwasan kwaikwayo ganin idan kana wasa sai su ga tamkar da gaske ne abin da suke kallo.
NAKWANGO: Gaskiya ni ban yi karatun wasan kwaikwayo ba. Na fadi yadda na gudanar da rajyuwata. Yanzu ne ma na ke karatu a 'College of Education,' FCE. Karatun Alkura'ani kuma na yi shi a gaban Malam Habu Zanzan - Allah ya jikansa da gafara - sai kuma mahaifina; daga baya kuma akwai wasu.
FIM: Su ma mata, musamman iyayen yara, suna yaba yadda kake fitowa a matsayin uba, koda yake dai akwai wadansu wuraren da akan yi tsokaci kanka.
NAKWANGO: Dangane da wannan, wato na yi la'akari da zamani. Ni dai babu abin da nake so a rayuwata illa mutum ya zama mai da'a da kuma biyan hakkin mutane da tsare mutunci. Ni koyar da wasa nake yi. Amma abin tunani shi ne duniya ta canza, sai malami ya yi wa'azi da yawa ba a damu da shi ba. Amma sai Bature ya cuce mu ya cusa mana kallo, muka dogara da shi don debe mana kewa. To sai na ga ta wannan hanya da zan isar da sako ne ya wadatar. Da, ba na fitowa sai dai in koyar, daga nan sai na yanke shawarar shiga don isar da sako: ko dai in hana wani yin wani abu mara kyau don in na yi mara kyawun ya gani - ka gane? - ko kuma in yi mai kyau ya ga nasarar da na samu. Alal misali, a Linzami Da Wuta abin da na fito ka ga ai duk abubuwan da mutanenmu ke yi ne kamar kwasar bashi da ruwa, cutar mutane. To sai na ji dadin wannan fitowa da na yi, sai mutane suke ganin akibar abu kuma ya zama darasi.
Sa'annan ana cewa mutanen da ke wasan kwaikwayo ga-su-ga-su yadda suke. Ai ba ka yashe masai ka ce ba ka taba kashi ba. Idan har ka zo ka aibata masu wasan kwaikwayo, to tasu ce ta fito fili don sun ware sunansu - "'yan wasan kwaikwayo". Amma wa ya san abin da wasu ke yi? Ba a bincike. Ni ina tabbatar maka akwai da yawa wadanda idan ka kusance su da masha'a sai ku bata - maza da matanmu. Amma saboda abin ainihin wasan Hausa a nan kasar Hausa ba mu ne ke yinsa ba, ba wai maza ne da matan kirki ke yin a ba, asalin abin da karuwai aka fara, to sai wancan bin ya biyo mu. Sa'adda a da can nake kungiya har karuwan za ka gani; za ka ga don dai su zauna lafiya har karuwai za ka suna za mu kama masu gidan haya suna zaune. Amma nasarar da na samu ina alfahari da ita. Kabiru Nakwango na daura wa uku aure: karuwai ne amma cikin iko Allah muka shiryar da su. Akwai ma wadda a yanzu tana da 'ya'ya biyar ko shida. A Dabo din nan ma 'ya'ya biyu mata muka aurar, kuma a shigata wasan kwaikwayo na san mutum takwas sun musulunta. Biyu sun mutu sauran kuma mata cikinsu sun yi aure, don ko kwanan nan ma wata wadda tai aure a Sakkwato ta zo gidana.
FIM: Cikin fim din So..., diyarka ta sha guba ta mutu. A cikin Akasi kuma ka yanke wa dan abokinka hukuncin kisa. To kamar cikin wadanne finafinai ne aka taba kashe ka?: wato a dirka maka dalma ko a daba maka wuka ko kuma ka taba yin mutuwar tulun-dangaruwa inda ka mutu da igiya a wuyanka?
NAKWANGO: Kwarai kuwa, ai ko a Dan Halak harbe ni aka yi. Ina nuna wa mutane ne yadda illolin rayuwa suke. A kwanan nan ma an tare ni a kan hanya an kashe; fim din bai fito ba. Amma kamar fim din Akasi da So wadansu finafinai ne masu wata manufa ta musamman.
FIM: Tunda ka fadi haka da bakinka bari mu shiga cikin fim din So... Yayin da matasa ke cewa Ali ya burge su don ya i rinjaye kan akidarka, su kuma wasu cewa suka yi bai dace a rinjaye ka ba. Me za ka ce?
NAKWANGO: Abin da ake nunawa, idan zamani ya riske ka, sai ka hakura. An dai same ni da kafewa kan ra'ayina. Lokacin da kake kan bakin aikinka, kada ka yarda ka yi sake da aikinka, ka gane? Ina tsare mutuncina da na al'ummana. Ai labarin ya nuna wa maza da mata ake ha de amma fitina sai ta fara faruwa. 'Yata dai ce? To na cire ta daga makaranta. Shi kuma wancan tunda ya fara koyo mummunar dabi'a in na bar shi zai iya lalata wani. Saboda haka na kore shi. To abin da ake so shi ne ya yi karatu. Bai hakura ba, sai ya je ya yi ta karatu, ya samu matsayi da ya dawo yake koyarwa. Amma shi ma akwai wata manufa kyakkyawa da yake son aiwatarwa.
FIM: Idan fim da Kabiru Nakwango a ciki za a kagara ya fito wai don an san za ku zuba tsabar Hausa a ciki. Wasu ma cewa suke yi furodusa da darakta kan ba ku damar yin free dialogue, wato ku daina bin labarin a rubuce kuna yin abin da ake cewa saki-ba-ka'ida. Haka ne?
NAKWANGO: Farko na fada maka abin nan ba yau na fara ba kuma duk abin da kake yi, kana da tunani a kansa, yana da muhimmanci, sa'annan kuma duk mutumin da ya motsa a rayuwa ya girmama Hausa, to ni ina girmama shi. Sa'annan kuma duk mutumin da zai motsa, saboda haka idan har Bahaushe ba zai ci gaba ba, a kan abin da nake yi, to ni ba na yinsa. Wadannan kalmomi da nake nunawa a fim, ina nuna wa Hausawan yanzu ne ga fa wata Hausa wadda tun kafin a haife ka tana nan tana yawo. Yanzu a nan Dabo akwai ranar da nake warewa in dauko masu manya-manyan kalmomi; wani ma zuwa zan yi in tambayi wani tsoho ya fada min. in dauko kalmomi in ce me ake nufi da kaza- irin su alkaki irnsu kashin giwa, duk ko in zuba wasu karin maganar da sai Bahaushen gaske ne zai gane wannan.
Maganar free dialogue da kake magana, ya danganta. Idan mutum mai fim ya zo ya ce yana so mu yi abu da zai yi kyau kuma ya burge, to idan na ga abin da zan yi zai fi wanda shi ya zo da shi kyau, sai in yi shi. Amma idan kuma na ga wanda ya zo da shi ya fi wanda zan yi kyau, sai in yi nasa.
FIM: Na dauka ka taba zama cikin wani kungurkumin kauye shi ya sa ka iya wadannan maganganu.
NAKWANGO: Ba zan yi maka musu ba. A gidanmuna taso na ga mutumin kauye daga daya zuwa sama da ashirin, babana ke rike da su. Kuma da mutumin kauye da na birni daya suke. Ni kaina na rike mutanen kauye sun kai takwas ko tara, kuma har yanzu suna nan suna alfahari da ni. Wasu ma sun girme min. Na yi zama da mutanen kauye. Na sha zuwa harkar fatauci a wani gari in zauna in yi kwana biyu. Na yi gogayya a siyasa, kusan a kasar nan ba inda ban danna ba a dalilin siyasa.
FIM: Wace jam'iyya ka yi?
NAKWANGO: Jam'iyya dai na yi PRP, daga baya ta rikice ta zama 'Santsi' da 'Tabo,' na bi 'Santsi'. Aka zo aka yi NRC da SDP, na bi NRC. Suka rushe na bi DPN. Aka rushe aka yo na yanzu sai na hakura.
FIM: Ya ka hakura da siyasa kuma?
NAKWANGO: Saboda koyarwar da nake wa dalibai da koyarwar da nake ta wasan kwaikwayo duk za su samu tagwaye sai na hakura da siyasa.
FIM: Daga lokaci da ka yi har yanzu da ka daina siyasa, shin da romon siyasa da kuma wahalarta wane ka fi sha?
NAKWANGO: Gaskiya wahala ta siyasa tana da yawa fiye da kima. Ina jin a lokacin duk abin da ke aljihuna nakan cire in batar kan siyasa.
FIM: Lokacin 'Santsi' da 'Tabo' an yi rikici da makamai inda gariyo da barandami suka yawaita a saboda 'yan adawa. To ko an taba sararka, kuma kai ma ka taba sarar wani?
NAKWANGO: Idan ka ga mutum ya sara ko an sare shi, to yana daga cikin layin masu sara sai fa wanda tsautsayi ya aukawa. Tunda nake ban taba shiga amma dai ita wannan sunanta farauta kawai. Amma ban taba sara ko a sare ni ba, Allah bai taba dora min ko na dora wa wani ba.
FIM: Daga lokacin da kake fitowa a matsayin uba, ko kana ganin a finafinanka kun fara cin wasu nasarorin hikimar da kuke so iyaye su dauka ko kuwa har yanzu wahala kuke yi wai saje babu gemu?
FIM: NAKWANGO: Alhamdu lillahi, farko akwai wani scene fitowa daya tak da na yi a cikin Marainiya na Mandawari: ya zo ya ce min nasiha yake so in yi wa Alasan Kwalle, sai Allah ya saka min abin da zan ce kuma ya yarda abin da zan fada din ya fito yadda ya kamata mutane su ji su fahimta, sai na fadi Wani malami sai ya ji... ni ba ni da ilimin Arabiyya, Allah ya san haka. Amma da malamin ya ji, sai ya kira Mandawari ya yaba wa fim din. Ya ce sama da shekara 20 yana wa'azi kan abin da na yi a Marainiya 2, amma da Marainiya 2 ya fito, sai abin ya fito karara. Da fim din ya fito da yawa an gane, da yawa an daidaita.
FIM: A matsayinka na wanda ke fitowa a uba, wuce nasiha za ka yi kan 'yan fim musamman mata masu fada da junansu, ko ba komai don kada jama'a su rika yi maku kallon Bilamu dan Baura wanda ya yi karatu bai yi aiki da shi ba?
NAKWANGO: Farko dai mace duk inda take fitina ce. Jan hankalin da zan yi bai tsaya ga mata kadai ba, har mu maza. Kai, a Dabo akwai sama da mace 30, amma babu matar da za ta yi fada da 'yar'uwarta mu ci gaba da zama da ita. Ba wadda za ta zo da mummunar kama ta zauna nan. Kuma kullum na zo sai na ware minti biyar ko goma ina jan hankalinsu kan aure da muhimmancin iyayensu.
Kullum kai furodusa idan mace ta zo wurinka, to a fuska kada ta ga wasa. Idan ba ta ga wasa ba, ba za ta yi maka wasa ba. Ranar da duk ka yi wa mace wasa, to sai ta zo da wasan da ya fi naka. Amma idan ka tsare fuskarka, to za ta zama mai kame kai. Namiji duk inda yake idan har zai sakar wa mace fuska ko ya yi wasa da ita, to za ta zo masa da fitina. Laifin ya fi karkata ga mazanmu.
FIM: Wadanne finafinai kungiyanka ta Dabo ta yi?
NAKWANGO: Kungiyar Dabo ta yi finafinai da dama. Wasu da sunanta, wasu ba da sunanta ba. Fim din So Ne Ko Kauna wanda na fara fitowa a ciki, ita ta shirya shi. Akwai Al'ajabi, ya fita da sunna 'Danbazau Entertainment,' sai Dan Halak, Hadarim Soyayya, da sauransu.
FIM: Ka taba cin karo da wata kyauta sakamakon yin fim da kake aka ga ka burge a ba ka?
NAKWANGO: Ban taba cin karo da wata kyautar kudi ba. Amma dai in je wuri a girmama ni, na sha karo da wannan, haka kuma duk gidan da ke garin nan idan ana bin layi to ni ba na bin layi idan na je da dan babur dina ko motata. Ko na bi akan ce don Allah fito. Wannan kyauta ce babba. Sa'annan kuma duk inda nake akan kalle ni da kyakkyawan kallo. Wannan duk kyauta ce da ba zan iya manta irinta ba. Akwai kauna tsakanina da wani mutum daban wanda ina alfahari da shi a duniyar nan; shi ne Alhaji Habibu Sani Kofar Soro. Ba wani abu ba, haka kawai ya tako daga Katsina ya ce ya zo ne ya gan ni ya gaishe ni. Yanzu zumunci har ya wuce mu ya kai ga matanmu da iyayenmu.
FIM: Matanka nawa? 'Ya'yanka nawa?
NAKWANGO: Matata daya 'ya'yana biyar kuma duk masu rai. Ni kuma mahaifana suna nan da ransu.
FIM: A karshe wane sako zaka yi wa magidanta maza da mata?
NAKWANGO: To don Allah idan an gan ni a matsayin mai shakiyanci ko rashin tausayi ko rashin kirki, ba Nakwango ne ya zo da wannan hali ba, a'a, ina koya wa mai irin wannan halin ne ya gyara. Idan an gan ni da hali na kirki, so nake mutane su kula su dauki halin kirki. Wannan shi ne sakamako idan an ga kuskure, a yi mana afuwa; idan an ga ba daidai ba, a zo a same mu a ba mu shawara. A karshe in a rokon addu'a: abin nan da muke yi, Allah ya sa sila ce ta ci gaban addini. Don mu mun san irin amfanin da muke yi wa mutane. Kuma idan muka bar harkar, ba mu san irin lalacewar da za ta yi ba. Don a yanzu harkar fim na cikin barazana saboda yara masa kuruciya da kuma fitina na zamani da iya-shege na kasar nan. Yanzu misali abin da ya fi ci mini tuwo a kwarya, duk fim din Inyamurai za a yi tallar tsiraici da Kiristanci da iskanci, amma ba a taka masu burki a Abuja, sai mu idan mun kai mai dauke da addini sai a ce ya yi addini da yawa. Na yi fim da kaina na kai Abuja amma suka ce sai na cire sin tara. Wannan ya ba ni haushi na kona fim din gaba daya!
Mu nan Arewa da ba masu taimaka mana ba yadda za mu yi . An yi Tafarki an ce sai sun cire wadansu wurare da yawa. Su kuwa ('yan Kudu) har fim suka yi da suka ci wa 'yan Arewa mutunci irin su Jarman Kano. Akwai fim din da na yi na shari'a da yadda mace take a Musulunci da yadda da yake bai wa ubansa gudunmuwa da komai. Amma da muka je sai suka ce wai muna lalata Kiristanci. Ina kira ga malamanmu da masu kudinmu, su shigo a gyara. Idan kun kiya kuwa ga satalayit nan da finafinan Indiya.
FIM: Malam Kabiru, mun gode.
NAKWANGO: Ni ma na gode.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin