Fim: Mun ji labari cewa ka sami sabani da Rukayya Dawayya, har ya kai ka ga fasa aurenta. Ya gaskiyar abin take?
MISBAHU: E, to alhamdu lillahi. Magana dai ce da kowa ke fadar albarkacin bakinsa; kowa na fadin irin nasa zancen. Wasu lokuta da suka wuce akwai maganar aure da muka yi da Rukayya, amma daga bisani sai muka sami matsala. Da ma akwai su (matsaloli) guntaye-guntaye, har suka taru har zuwa lokacin da na janye maganar ta aure wacce da mutane ke tunanin akwai ta.
FIM: Batun auren naku ya je ga iyaye?
MISBAHU: Maganar ta je wurin iyayenmu tabbas. Amma iyayena ba su je wurin iyayenta ba.
FIM: Su iyayenta sun san cewa za ka aure ta?
MISBAHU: Sun sani. Amma ni ban taba ganin mahaifiyarta ba; (domin) ba ta kasar nan. Amma mahaifinta ban taba ganinsa ba.
FIM: Ita Rukayya ta san iyayenka kuwa?
MISBAHU: Rukayya ta san iyayena; na kai ta har cikin gida, kai, har cikin dakin mahaifiyata. Babana ne dai ba ta taba gani ba.
FIM: Ya aka yi har sabanin ya kai makura yadda ba za ku daidaita ba?
MISBAHU: Magana ni dai a kan Rukayya-ka gane ko?-ita ce ni dai ba na so in yi, a kan dai wani abu da ya shafe ni da ita. Saboda ni gani nake yi kamar na ci baya. Shi ya sa ban tsaya na ce kaza ta ce kaza ba. Na farko dai, ita mace ce, ni kuma namiji ne; idan wani abu take takama da shi, ni na ninka ta. Rukayya in suna ta yi, a dai cikin jinina ta yi suna. Sa'annan na girmi Rukayya. To matukar zan yi magana kanta, to ni na ci baya. Don haka ina so ka rufe shafina ni da Rukayya. Amma zan koma in yi wani tsokaci kan mutumin da ya zama shi ne wanda ya kawo matsala ta karshe tsakanina da ita; shi ne Suleiman Sa'eed.
FIM: Wannan fa ka san magane ce mai karfi; mutane za su so su ji hujjojinka cewa shi ne ya yi wa aurenka da Rukayya kafar-ungulu.
MISBAHU: Ni dai sau daya na taba ganin Suleiman; ya san ni, bai san ni ba, ni ban sani ba. To kawai ban ankara ba, mun sami matsala saboda Rukayya ina hana ta kula samari haka, tunda akwai magana ta aure tsakanina da ita, bai kamata kowa ya rika zuwa wurinta ba. To na je na same ta awannan hali. Aka ba ni hakuri, muka sasanta. Na kara zuwa washegari. Sai ma na ga abin ya zama kamar kasuwa-kasuwa. Akwai wata kawarta, Rashida, wata 'yar Agulla ce - ta dawo daga Saudiyya-to ita ke hure mata kunne wai ba na son zuwa wurinta. Ni a lokacin ma ba ni da lafiya. Suna da samari masu harkar motoci tuwaris, daya na son Rukayya, daya kuma ita Rashida-to su ke hure masu kunne suna yi masu karya...
FIM: Rabu da Rashida ka koma kan Suleiman.
MISBAHU: Tsaya ka ji! Sai muka zauna da Rukayya na kafa mata sharadi cewa ban yarda in kara ganinta da wani ba. Na ce, "Kin yarda?" Ta ce ta yarda.
FIM: Ku biyu ne a lokacin ko kuwa akwai na cikon ukunku?
MISBAHU: A gaban Ishaq Sidi muka yi; shi ne ma ya sasanta mu. Da na zo gida sai na yi tunani: don me zan tsaya kishin yarinyar nan? Kullum ina so ki kintsu, saboda maganar aure ba fa wasa ba ce. Ita kuma tana tunanin kullum holewa take sawa a gaba. Duk da haka na daure. To shi ne sai na ce bari in yi maganinta kawai. Sai na yi fushi na rubuta 'message' (wasika ta wayar tarhon GSM) na ce mata, "Tunda haka ne, ni ba zan iya ba. Da na san haka ne, da ba zan ce za ni aure ki ba. Maganar aure na hakura." Ka ga (in) da ta dauke ni da muhimmanci, da za ta fada wa wani dan'uwana ko abokina abin da Misbahu ya yi sai a zo a yi kirana. Ko kuma ita ta tambaye ni me ya sa na yi haka? Rukayya da ta tashi sai Suleiman ya hure mata kunne da ita da wannan Rashida, saboda abokin Suleiman saurayin Rashida ne. Ashe shi kuma Suleiman ta bayan fage yana son Rukayya ni ban sani ba! Washegari ba ta ma damu da hukuncin da na yi ba, sai ta tafi Jos. Ba ta dawo garin nan ba (Kano) sai da aka yi kwana 13 ko 14; ban sani ba, amma dai ta haura kwana 10. Dawowar da ta yi sai na ji 'message'. Ban ba ta amsa ba, na yi mata shiru. Bayan kwana uku na saki fim dina Kansakali a kasuwa, sai ta rubuto 'message' cewa "Allah ya bada kasuwa."
FIM: Cikin 'yan fim a nan Kano ana ta cewa Suleiman ne ya kai ta Jos, kuma a can an gan su tare. Shin ka bi ba'asin maganar?
MISBAHU: Ita ce ai maganar da ta ba ni mamaki. Saboda me? Da da ta dawo ta zo na ji ta da kyakkyawan lafazi, shikenan. Duk da cewa na hana ta tafiya, ta yarda. Ashe Suleiman Sa'eed shi ya rude ta suka tafi. Suleiman bai ga mutuncina ba, bai ga wani komai nawa ba; ya rufe idonsa saboda shi gurinsa ya kama yarinyar nan ya lalata ta. Don haka sai ya ajiye Rukayya sai da suka yi tsawon kwana hudu suna kwana a daki daya shi da Rukayya a otal.
FIM: Ya aka yi ka san haka?
MISBAHU: Yauwa! Ali Nuhu ya zo, akwai wani yaro mai sai da gilas (tabarau) wanda ya yi fim din Ibro Awilo, wato Abdulhadi. Muna hira yake ce min Ali ya ce zai saka ta a fim dinsa sabo (Turba) sai (shi Abdulhadi) ya ce, "Ni ba za a sa min Rukayya ba." Ya ce, "Saboda me?" Sai ya ce saboda ba ta son aure." Sai Ali ya ce, "Gaskiyarka. Ko ka san tafiyarmu Jos sai da ta kwana hudu a dakin Suleiman Sa'eed?" Sai abin ya ba ni mamaki. Menene matsayinta? Wane matsayi ta tafi ta bar ni tana kwana a dakin wani kato ba dan'uwanta ba? Kai ko da dan'uwanta ne uwarsu daya ubansu daya, shari'a ta ce su shiga daki su biyu su rika kwana? Kuma a kan idon mutane! To don haka sai abin ya fara ba ni mamaki. A can ya hure mata kunne har ma sai ta rika saita wayarta tana kara. Sai ta dauka, (ta ce) "Hello!" Sai kuma ta kalli wayar ta yi tsaki, ta ce, "Ba zan dauka ba." Idan an ce, "Waye?", sai ta ce, "Wannan banzan Misbahun ne". Sa'annan a nan (Kano) kuma da ta dawo ta ji ana zaginta, ana yi mata habaici, idan tana cikin 'yanmata kawayenta su Ummi Nuhu da Hadiza Kabara, a lokacin ana shutin, sai ta rika saita wayarta, idan ta yi kara, sai ta ce, "Hello Misbahu, ina gajiya? Kana nan lafiya?" Wai a zuwan ni ne na buga mata waya. Wai ita don a ce muna tare, ba mu bata ba.
FIM: Can a Jos da aka ba ka labarin tana kwana tare da Suleiman, a lokacin babu 'yan fim na Kano? Kuma ba su gan ta ba?
MISBAHU: Ai 'yan fim da yawa irin su Ali Nuhu da Ahmed S. Nuhu duk suna garin. Duk tare ake kuma su suka gani ra'ayil aini. Ali ya maimata min haka a gaban Suleiman Sa'eed, Sulaiman bai yi musu ba.
FIM: Ya aka yi aka hadu da kai da Ali kuma da shi Suleiman har Ali ya fadi wannan magana a gabansa?
MISBAHU: Da Suleiman Sa'eed ya ji maganar ta zo har nan a kunnena. Saboda Rukayya ta fada masa don a nan garin ma tana zuwa har dakinsa, ka gane ko? Da ta je dakin Suleiman ta gaya masa, sai kuma ta yi wa Ali waya ta gaigaya masa magana tana cewa shi ya gaya min wai ta je tana kwana da Sulaiman Sa'eed. Don haka sai ya ce mata to ta zo a je wajen Suleiman din. Ashe a lokacin ita tana gidan Suleiman din za ta je. Da ta je kuma...
FIM: Shi Ali da nufin me zai kwashi Rukayya ya kai ta gidan Suleiman?
MISBAHU: Shi Ali cewa ya yi Rukayya ta zo su je gidan Suleiman a zauna a yi magana, cewa yana shaida, ya tabbatar haka ne ta kwana a dakinsa (shi Suleiman). Don haka, da ta je gidan Suleiman din, sai Suleiman ya karbi lambar Ali ya buga masa waya ya tuttura wa Ali zagi. Da Ali ya ji haka sai ya ce min yana so ya dauki Rukayya su je wajen Suleiman. Sai na ce, "Ka rabu da ita, mace ce. Allah zai fito da gaskiya". Can kuma sai ya kara bugo min waya ya ce ga Suleiman Saeed na ta zaginsa ta waya: "Don haka Misbahu ka taimaka min ka zo ina jiranka a ofis dina."
Ban ma san me za mu yi ba. Sai kawai na yi addua'a: "Allah ka tabbatar min da gaskiya in san inda rayuwata ta sa gaba tsakanina da yarinyar nan, da wani makirce- makirce." Har ma abokina, da yake shi ya yi azumi a ranar, na ce ya taimnaka min da addu'a.
FIM: Wanene wannan abokin naka?
MISBAHU: Mahmud Uba Lida.
FIM: Da shi kuka tafi?
MISBAHU: Da shi muka yi goyon biyu a kan babur, muka tafi ofis din Ali, muka hau motar Ali, daga nan sai gidan Suleiman.
FIM: Wace rana kenan?
MISBAHU: Shekaranjiya (3 ga watan biyu, 2003). Don haka muna zuwa sai na yi tunanin kada a yi wannan abin ba Rukayya. Na ce bari na yi wa Rukayya waya, in ce ta zo nan gidan Suleiman; in ta sani, in ma ta nuna min ba ta sani ba, sai in hau motar Ali in dauko ta, don dai a warware gaskiya. Sai na tsaya daga baya, sai Ali ya shiga. Mamuda ma ya bi shi. Ni kuma ina cikin soro. Sai Ali ya kwankwasa kofar daki. Ni kuma sai na kira Rukayya ta waya a gidansu. Sai wannan Rashida 'yar Agullar ta dau waya. Tana dauka, abin da ta ce min, "Wanene?"
Na ce, "Misbahu ne. Ba ni Rukayya."
Sai ta ce, "Ba ta nan." Sai na ji ga maganarta a wayar, kuma ina jin maganar tata a cikin gidan nasu (Suleiman); ashe tana dakin Suleiman, ita ma Rukayya tana cikin dakin Suleiman!
Ka ga kenan red handed mun kama su.
Sai na ce a wayata, "Ina take?"
Sai (Rashida) ta ce, "Ba ta nan."
Sai na ce, "Ga ni nan a gidan da kuke yanzu!" Sai na kashe waya. Ali Nuhu da ma already, ya bi shi.
Ko da muka shiga, (sai muka ga) Rukayya daga ita sai riga da zane, babu dan kwali, ba komai - yadda ka san mace a dakin mijinta, haka Rukayya take; gara ma ita Rashida da dankwali da mayafinta a kirjinta. Kayan wannan hoton na bayan littafin nan naku (A Clean Break), to shi ne a jikinta. Tana bayan katifa a tsaye. Saboda su Ali da suka riga ni shiga sun ce min sun same ta a kwance kan katifa ta dora kafarta a jikin bango. Amma da ta ji har da ni, kafin na soka kai cikin dakin ta yi zumbur ta mike a tsaye.
Shikenan na shigo. In na kalli Rukayya na sunkuyar da kai na haka. Sai suka fara cacar baki da Ali da shi Suleiman; Suleiman na cewa shi (Ali) munafuki ne. Sai muka ga mu ba wannan maganar ce ta kai mu ba. Abin da muke so mu fahimta shi ne: shin Suleiman na neman Rukayya? Kuma lallai suna kwana da Rukayya a Jos? Kawai abin da ya kai mu kenan. Duk wani abu ban da wannan mai sauki ne. Mace a ce ga shi kana nemata da aure amma a ce wani na nemanta, yana saninta 'ya mace - yana kwana da ita, kai kuma kuna tare tana yi ma maganar aure! Ka ga wannan ba karamin tashin hankali ba ne. Don haka wannan mu shi ya dame mu, in muka tabbatar da wannan, duk wani abu shirme ne.
Don haka sai na tsai da Alin da Suleiman din da Mahmud din na yi masu magiya. Saboda bakin ciki hawaye har suna zuba a idona. Na ce, "Allah don zatin Allah..." Na yi magiya wadda duk Musulmi in ka yi mashi ita sai jikinsa ya mutu. Na ce, "...Don Allah a matsayinka na Musulmi, zan maka tambaya guda uku, ka ba ni amsa."
Ya ce, "To."
Na ce, "Don Rasulullahi, ka san cewa ina neman Rukayya da aure?"
Wallahi kafin ya yi min magana, saboda tsabar rashin gaskiya, kafin ya yi min magana yana tsaye, sai da ya tsuguna, ya dafa tebur, ya ce, "Misbahu, na ji maganarku (ta aure) da Rukayya amma daga baya na karanta a wata mujalla (Tauraruwa) cewa an fasa auren."
Na ce, "Ni ka ji na fada ko ita?"
Ya ce, "Ita."
Na ce, "To a surutun da take yi ne wannan."
Sai ya ce, "Ka ga ina da hujja".
Na ce, "Hujjarka ta me?"
Ya ce, "Hujjar da zan iya neman Rukayya". Sai kuma ya ce min, "To amma fa abin da nake so ka gane, tambayoyin da za ka yi min ba lallai ba ne in iya amsa maka su a nan." Tambaya ce mai nauyi. Duk rashin kunyar mutum ga jama'a ga yarinyar ba za a tambaye shi "Wane ka kwanta da ita" ba, ya ce "E!"
FIM: Mun ji tambaya daya. To ina sauran tambayoyin biyu?
MISBABU: Bai bari na yi ba, sai ya ce kada na yi masa wadannan tambayoyin. Sai ya ce min amma yanzu maganar da ake yi, zai auri Rukayya bayan Sallah. Na ce, "To falillahil hamdu, shikenan? Shikenan, an sallame ni?" Har na tashi zan wai tafi sai suka ce akwai kuma magana; wai ina so ya san tun suna can Ali ke yi min "message" (sako ta wayar selula). Na ce, "Wallahi Ali bai taba yi min message kuna can ba, sai bayan an dawo kawo."
Ya ce, "To da gaske ne na yi wa Rukayya message cewa Ali ya gaigaya min ga abin da suka yi a can?
"Na ce, ni message din da na yi mata, ba da miyauna ta tafi Jos ba. Amma tunda kin riga kin tuncin ki, saboda kannenki da kike riko duk abin da kike yi shi suke kallo, kuma shi za su dauka.' Na ce 'ki huta lafiya'. Shawara ce ta addinin Musulunci. A lokacin ma already na ce na fasa aurenta."
Na ce masu, "Ni abin da ya sa na biyo Ali shi ne don in kure ramin karya; saboda abin da na dauka, Ali karya yake fada min. Amma yanzu ga shi gaskiya ta yi halinta." Na ce don haka ni babu ruwana. Sai wannan yarinyar, ita 'yar Agullar ta ke cewa...
FIM: Ba a zo kan wadda kake cewa 'yar Agulla ba tukuna. Tambaya a nan ita ce lokacin da kake ta wannan cacar baki ita Rukayya tana ina, kuma yaya ta yi?
MISBAHU: Tana tsaye a wajen. Gaba daya ita da wannan yarinya sun kasa samun sukuni. Saboda ka san tun farko ita yarinya ta dau waya ta ce min ba su nan, ta nuna min a gidansu suke. Ga shi kuma Ali ya kara fada ya ce, "Har ga Allah ni na fada. Kuma na fada wa Misbahu cewa tare kake kwana da Rukayya a Jos," kuma Suleiman bai musu ba. Ita ma Rukayya ba ta yi musu ba. Tare suke kwana!
Sai ya ce min ai shi abin da ya sa take kwana a dakinsa, saboda ya san munafincin su Ali shi ya so ta rika shigowa cikin 'yan industiri, ka za da ka za. Na ce, To wannan ba hujja ba ce, amma magana ta kare. "Ita kuma kuwar Rukayya abin da ta ke daiming a kai, wai ta ji an ce na yi wata waka. Akwai wata waka da ma uo simam wakar "Tahuta". Na yi ta, saboda lokacin Rukayya tana Jos. Na yi ta bayan ta dawo. Sai na yi wakar na dan buga ta a studiyo. Ina sawa ina dan ji haka.
FIM: Wakar ta mecece?
MISBAHU: Menene gugar zana? Ni ba wata ba'a da na yi mata. Kawai dai... ai za a karanta wakar, gata nan a rubuce. Kawai dai na fadi matsayina da kuma irin rikon da ta yi min. amma bana son yin magan kan Rukayya. Wannan ina fada ne don ya shafi mutane har ana ta hayagaga a kai. Amma da daga ni sai Rukayya ne, to da ba wanda zai ji mu har mu ji mu rabu. Wannan don ya shafi su Suleiman ne. Na ce wa Suleiman, "Ga ya nan".
Na tashi zan tafi suka ce min in tsaya saboda an ce wai na yi wata waka, sai na ce, "Ai ba ka da damar da za ka yi min bincike a kan wata waka. Ka bari sai waka ta fito idan ka ji akwai sunanka." Sai ita Rashida ta ce wai ta ji an ce ita ce 'yar Agulla, ita ta hada. Na ce, "To kin ji sunanki? Ta ce ai ita "ba dan (kaza-kazan) da ya isa ya sa a harkar fim tunda ba harkar fim take ba!" Ka ji, amma kuma duk inda ake tsegumin harkar fim sai ka ji an ce da Rashida!
Kuma ni tsakanina da Rashida... kuma ni tsakani na da Rukayya, Rashida tana daya daga cikin wadanda suka kara zuga abin. Domin Rashida ta zama kamar kawaliya, ita ke kai wa Rukayya samari su je gidan. Tare kuma suke yawo, su yi nan, su yi nan, su yi nan, ka gane ko? Sai take amsa kira a kotu.
To ni kuma yanzu na lashi takobi zan yi waka, hadaddiyar waka, zan yi da abin ya faru a kaina kuma duk dan'adam din da ya tsoma baki a kaina, in dai ina da shaida, ina da garanti, akwai shi a cikin lalacewar harkar nan…. Saboda ni na ji haushi. Haushin da na ji, na bata lokacina. Sa'annan abin na ga kawai yaudara ce. Rukayya ta yaudare ni! Rukayya ta yaudare ni!! Ta bata min lokaci. Amma ba zan ce ba, ta cuci kanta.
FIM: Mu koma cikin gidan Suleiman. Lokacin da ka shiga cik in dakin wane irin mamaki ya kama ka?
MISBAHU: Mamakin da nake yi? Shi ne shin wai ni ne tare da wannnan yarinya a ckin gidan nan-Rukayya? Wadda na yi wa maganar aure? Wadda na kai ta cikin 'yan'uwanna, na wanke ta, suke ganinta da haske, na rike ta, nake yi mata addu'a a idon a duniya kowa ke kallonta da daraja? A kan Rukayya in gaya ma akwai abokaina da suka daina yi min magana, ba su hulda da ni, saboda na ce zan aure ta.
FIM: Wane irin wanki ka yi mata?
MISBAHU: Yauwa! Na farko dai duk inda ka kawo min sukar Rukayya, sai in kalle ka in ce, "Ikon Allah nake jira. Ka bari in Allah ya sa zan aure ta ka gani; idan kuma ba matata ba ce ka gani". Kai, sa'annan wallahi duk abin da zan yi na rayuwa wanda ya shafi da zan yi, wallahi ina yi wa Rukayya addu'a.
FIM: Ana yawan kawo ma sukarta ne cewa kada ka aure ta?
MISBAHU: A'a ai dole ne wannan. Ka cire ma cewa tana 'yar fim; Rukayya tana daya daga cikin 'yan matan da suka fi kowa bakin-jini a cikin industiri.
FIM: Lokacin da ka baro gidan Suleiman ka dawo gida, ko ka iya barci kuwa?
MISBAHU: Ai sai da na kai karfe 4 na asuba ban yi barci ba. Kanina (Aminu) tare nake da shi muke kwana a nan, wallahi sai dai in dare ya yi dare in ba shi runke mai sanyi daga cikin firij in ce ya yi min karatu. Shi ne yake yin karatu da wasu addu'o'i ya tofa. Sannan na samu na yi barci. Barcin da na yi bai fi minti 30 ba, na farka kamar an firgita ni. Kai a karshe saboda bacin rai sai da aka zaunar da ni aka yi min karatun Alkur'ani a kaina da kwawana sa'annan na samu na dawo cikin hayyacina. Saboda me? Saboda lokacin ina dakin Suleiman Sa'eed in na kalli Rukayya sai hawaye su rinka zubo min saboda bakin ciki.
FIM: Wane darasi ka dauka?
MISBAHU: In dai yarinya 'yar fim ce, gaskiya ni ba zan iya yarda da ita ba. Na daina yarda da su! Na hakura. Iyakaci dai a yi ta yi masu addu'a Allah ko waye ya ba miji Allah ya shirye ta. Ni a kan kaina, na dau darasi. Kai ni totally mace ta duniya ma tsoronta nake yi! Saboda Rukayya sai da aka yi shekara biyu cur tana sona kafin in saurare ta, tun da muka yi Dawayya. Dalilin cewa zan auri Rukayya, shi ne lokacin da aka yi auren Abida muna wurin. Na ga ga Fati ga mijinta, ga Maijidda ga mijinta, ga kuma Abida ta yi aure. Lokacin tsararta sai Habiba saboda Balaraba Allah ya yi mata rasuwa. Tunda na ce ina sonta, da aka yi bayan wata daya, shikenan ba a yi sati biyu sai aka yi wamman abu. Ina dannewa, ina dannewa. Ba wanda ya sa min cajin kwakwalwa na ga ba zan iya dannewa ba, sai wannan. Amma ba abin da zata yi min na rayuwa, a matsayin son da nake yi mata ban hakura ba. Wannan shi ne na ji ba ni iyawa. E, ba ni iyawa!
FIM: Tsaya mu dawo kan kai kanka. Ka san yadda al'amuran rayuwa suke; 'yan magana na cewa, "Kama tadinu, tadanu". Anya ba abin da ka yi ne kai ma aka yi maka ba? Ba ka taba yaudarar wata yarinya ba wadda ko za ka yi tunanin cewa soyayyarta ce haka ya faru gare ka?
MISBAHU: To ai ni ban taba samun mace in ce har ina sonta mu rika yi mata maganar aure ba, sai wannan. Ai ni ban ma dade da fara soyayya ba. Dalili na na hada aure har shidda da bakinan nawa. Amma ban taba ce wa wata mace zan aure ta ba.
FIM: Amma kuma an ce akwai lokacin da Rukayya ta zo wurinka ta duba selularka sai ta ga wata wasikar "message" wata yarinya ta yi maka kuma an ce daga lokacin ta fara daga maka. To ka gani fa?
MISBAHU: Ah! Yo in dai wannan za ta gani, ita a gabanmu nan ga mutane idan ta zo nan samari suna yi mata waya. Waya ma, ba "message" ba! Kuma a kwanan nan in gaya maka daya wayar ta hannunta tawa ce, da ma na ba ta aro da tata ta bata, da na karbo ta, wallahi wayar sai da ta yi kwana biyar a hannuna amma mace hudu kadai ta yi mata waya a ciki. Amma maza sama da 28, ina rubutawa. Gaba daya cikinsu mutum biyu kadai ne 'yan fim: Musa Jalingo wanda dan'uwanta ne, sai SK. Amma duk sauran maza ne, ban san daga inda suke ba.
FIM: To kai ita waccan yarinyar da ta yo maka "message" a selula budurwarka ce ko 'yar fim ce ko mai sha'awar fim ko wakarka (fan)?
MISBAHU: Ba budurwata ba ce, 'fan' dina ce. Kuma ni ina da 'fans' da yawa fiye da yadda kake zato.
FIM: A karshe shin magana ta je wurin iyayenka cewa ka fasa aurenta?
MISBAHU: Kwarai, maganar ta je. Ba ma wai na fasa ba, da nake gaya masu, sai suka ce in rabu da ita kawai.
FIM: To da kai da ita Allah ya hada kowa da ranonsa na alheri.
MISBAHU: Amin amin.
Ban damu ba don mun rabu da Misbahu
Inji Rukayya
RUKAYYA UMAR SANTA ta zauna tare da editan Fim, ASHAFA MURNAI BARKIYA, a dakin sabon saurayinta Suleiman Sa'eed sun tattauna a kan zargin da Misbahu ya yi mata. A wurin akwai shi kansa Suleiman da kuma Rashida, kawar Rukayya wadda Misbahu ya zarga da laifin yi wa soyayyarsu kafar-ungulu.
FIM: Bari a mu fara da kiranki "Rukayya Suleiman" ko?-tunda yanzu "Dawayya" ta kau!
RUKAYYA: Kai ni sunana Rukayya Umar Santa, ba Rukayya kowa ba! Har yanzu babana ne ke rike da ni.
FIM: Ya aka yi rabuwa ta shiga tsakaninki da Misbahu bayan duk kun yi sanarwar aurenku?
RUKAYYA: Jama'a, assalamu alaikum! Shi aure nufin Allah ne, kuma matar mutum kabarinsa. Aure zuwa yake yi. Da ma an ce zo mu zauna, zo mu saba. Shikenan. Mun zauna tare da Misbahu mun yi soyayya da shi. Sai yanzu Allah ya kawo rabuwarmu. Mun rabu. Duk dai samari da 'yanmata wadanda suke karanta mujallar Fim sun san ana soyayya, ana fada, ana rabuwa. To mu don mun zama taurari ne a duniya shi ya sa har abin da muke yi ake fito da shi fili. Amma ana yin wanda ma ya fi namu. To soyayya ana tare ce, kuma ana rabuwa. Ni addu'a nake Allah ya zaba mana mafi alheri.
FIM: Da yake bayyana wasu daga cikin dalilin rabuwarku, Misbahu ya ce akwai yawan tara samari da kike yi a gida rututu. Kin taba zaunawa ya gindaya maki sharudda, daga baya kuma sai ya ga ba ki daina ba.
RUKAYYA: Gaskiya ne ya ce ba ya son samari su zo wurina. Na ce na amince. Ya kuma zo gidanmu ya ga samari. To ni 'yar wasa ce. Kuma ni yarinya ce budurwa. Ina alfahari da wannan. Kuma ni ba zan yi wa mutum wulakanci don ya zo wurina a matsayina na 'yar wasa ba. Ya zo ya ga samari, bai tsaya ya yi bincike ba shin samarina ne?, sai kawai ya yi fushi ya tafi. Ya kamata ya tsaya ya tambayi me ya kawo su wurina? Su wanene? Daga ina suke? Har gobe, har jibi. Shi kansa Suleiman din da nake tare da shi, yana zuwa ya ga samari a kofar gidanmu, kuma ya tsaya ya gaisa da su, in gabatar da su cewa wadannan daga gari kaza suka zo ganina. Suleiman da Misbahu kowa tunaninsa daban ne; shi Mishabu idan ya ga abu, ba zai tsaya ya yi tambaya a kai ba.
FIM: To babban dalilin rikicin shi ne batun zuwanku Jos har aka ce kin kwana hudu a daki daya da Suleiman.
RUKAYYA: Misbahu ba abin da ba zai iya fada a kaina ba saboda yana bala'in sona. Saboda haka idan ma yana zargina shi da Allah. Amma ni na tabbata ban kwana daki daya da Suleiman Sa'eed ba. Kuma ina cikin mahassada. Kuma ni 'yar wasa ce, Suleiman dan wasa ne. Muna cikin bainar jama'a. Suleiman shi ma na cikin mahassada a otal din; komai za su iya fada a kaina. Kuma karin karfin abin da ya sa aka fadi maganar shi ne, ni dai fim din Suleiman Sa'eed na je yi. Shi ya ce min ba ya so in shiga sauran tawayar 'yan wasan. Haka kuwa aka yi. Tun da muka je, idan ka gan ni a kasa, to shutin za mu tafi, sai in gaisa da su. Ban je na kwana dakin Suleiman ba.
FIM: Dakinki daban nasa ma daban kenan?
RUKAYYA: Dakina daban, nasa daban. Kai, ni karewa ma tare da kawata na tafi, muna daki daya.
FIM: Wacece wannan kawar taki?
RUKAYYA: Rashida wadda Misbahu ke zargi.
FIM: To ya aka yi wannan magana har ta zo Kano kunnen Misbahu?
RUKAYYA: An san muna tare da Misbahu amma ba a san mun rabu da Misbahu ba. Saboda haka komai za a iya zuwa a fada masa.
FIM: Kina nufin kafin tafiyarki Jos kin rabu da shi?
RUKAYYA: E, na rabu da shi tun kafin in tafi Jos, tunda ya zo kofar gidanmu ya ga samari, sai kawai ya tafi, ya yi fushi ya ce shi ya daina kula ni, mun rabu. Na ce masa, "To shikenan Allah ya zaba wa kowa abin da ya fi alheri."
FIM: Wannan wace irin rabuwa ce haka?
RUKAYYA: Da ma rayuwar duniya haka take-zo mu zauna, zo mu saba. Idan har ana soyayya tsakanin saurayi da buduwa ko da ba a industiri suke ba, to sai budurwa ta toshe kunnenta, saurayi ma ya toshe. Ballantana ma a industiri muke kuma mun bayyana wa jama'a halin da muke ciki. Kowa ya sa mana ido. Duk wanda ba ya kaunata zai iya zuwa ya bata ni a wurin Misbahu don kawai a ga mun rabu. In Misbahu na da tunani, bai kamata ya zauna ya dauki maganganun mutane ba. Sai ya same ni ya tambaye ni. Ai ni kaina ana zuwa a gaigaya min maganganu a kan Misbahu, to amma ni da yake na zauna da kwakwalwar kaina na yi tunani, ba na saurare. Ka san duk mutumin da ya kama hanyar wani siradi na alheri kokarin mutane da shaidanu shi ne su ga sun kautar da mutane daga kan wannan hanya. Ka gane ko? Kuma shi lamarin duniya komai ana sukarsa. To abin da ya kawo rabuwa, shi Misbahu ana kai masa sukata yana dauka. Ni kuma ana kawo min sukar Misbahu ba na dauka. Saboda haka in dai da ma mutum zai fi fita fita, in dai mutum bai da ra'ayin kansa, to kullum fa… in ma yau ya tashi ya ce zai yi salla, in wani ya ce kada ka yi, to ba zai yi ba. To kawai shi Misbahu ba shi da ra'ayin kansa kawai.
FIM: Ranar da Misbahu ya zo nan ya same ki a dakin Suleiman ya ce ya kara tabbatar da cewa Sulaiman yan a nemanki.
RUKAYYA: Ni ina da tabbacin Misbahu zai zo gidan nan a ranar. Ni na yi wa Ali Nuhu waya saboda na ji maganganun da ya yi don in nuna masa ban ji dadi ba. Ina zuwa na ce, "Suleiman, ka ji abin da ke faruwa. Ka ji abin da Ali Nuhu ke fada." Direct aka buga wa Ali Nuhu waya. Ali ya ce to ga shi nan shi kuwa zai zo nan gidan. To na tabbatar Ali ba zai zo ba sai tare da Misbahu. Don ko ya zo shi kadai duk maganar da za a yi cewa zai yi shi ya sa ya taso Misbahu a gaba. Rashida ita ma na ce ta zauna ta wanke kanta "don ya daina zargin da yake maki. Har waka ya je buga kan ki". Shi ya sa na zo na zauna a gidan nan jiran Misbahu. Kai ni fa Misbahu ko me aka ce ya fada a kaina ba zan mamaki ba.
FIM: Shi ya yi rashi ba ke ba kenan?
RUKAYYA: Wallahi FADI SONKAhi ni dai ban damu ba (ta kada kai ta wurga idanu kuma ta doki cinyarta biyu da hannayenta). Ni da ma ko? Haduwata da shi da rabuwata da shi addu'a nake yi. Kuma da ma ko iyaye na cewa suke yi Allah ya ba ni miji nagari wanda zan iya yin zaman lafiya da shi. Saboda haka don mun rabu, to ba alheri, shi ya sa Allah ya raba mu.
FIM: Me ya janyo har kika jefa wa Ali magana?
RUKAYYA: Misbahu ya je ya gaya wa wasu maganganu akai na. Nan na san Misbabu na bala'in sona. Duk da mun rabu, ya zo ya gaya min, ya ce, "Ali ya ce kaza ya ce kaza. Ki san zaman da za ki yi da shi." Wannan maganar sirri ne tsakanina da Misbahu; ka je can ka same shi ya gaya maka!
FIM: Misbahu ya ce iyayensa sun san zancen aurenku amma da naki iyayen da nasa ba su zauna kan batun ba. Ba kya ganin rashin zama a karfafa abin tsakanin manya na daya daga cikin abubuwan da suka lalata shirin naku?
RUKAYYA: Ni dai na san iyayen Misbahu sun san ni, domin har gidan su Misbahu na sani wurin mahaifansa. Amma tun da na je na fada wa mahaifina, ya ce Allah ya zaba mana mafi alheri, shi dai addu'a yake, duk abin da ya fi alheri a rayuwata da tashi, Allah ya zaba mana. Amma maganar ba mu yi kwari da soyayya ba don iyaye ba su kai ga shiga ba ko waye waye, duk ba haka ba ne. In Allah ya kawo rabuwa ai ko ranar da za a daura mana aure sai mu rabu.
FIM: Misbahu na zargin cewa samari na yawan yi maki waya. An ce ke ma watanni biyu da suka wuce kin taba samun "message" na wata yarimya a cikin wayar Misbahu. Wannan me za ki ce?
RUKAYYA: Wallahi ni ba abin da zan ce. Ni ba na zarginsa da neman 'yanmata. Shi ke zargina; domin ni duk wanda na sa ran zan aura, cire zargi nake da duk wani abu da zai kawo sabani tsakanina da shi. Ban taba zarginsa ba, kuma ni ban taba ganin wani message a wayarsa da zai bata min rai ba.
FIM: Ba ki ganin cewa ke ce mutane za su dora wa laifi domin ai ke ce kika bar wani kika koma wa wani, ba shi ne ya bar ki ya koma wa wata ba...
RUKAYYA: To, ni wallahi (dariya) ni dai addu'a nake yi masu kaunata su taya ni addu'a Allah ya zaba min abin da ya fi alheri. Don Allah ka kyale ni haka nan!
FIM: Akwai fa wadanda ke cewa a rabu da ke, Suleiman yaudararki zai yi don an ga yadda ya yi da Maijidda da Hindatu. Kuma ga shi ke kin dawo wurinsa.
RUKAYYA: Wallahi komai ka ga ya faru ga mutum kaddara ce daga Ubangiji. Ni ban taba tunanin don mun yi soyayya da namiji mun rabu ba, ya yaudare ni. A'a, Allah ne ya raba. Ni fa komai sai in zauna in yi istihara in yi salla, in durkusa in yi sujada ga Allah in gaya masa bukatata. Ni a rayuwata ba zan ce ya audare ni ba (Suleiman) tunda muna tare.
FIM: Sai kuma wakar da Misbahu ya shirya wadda ya ce za ta fito cikin kaset din wakarsa mai suna "Lalajo". To abin zai shafe ki?
RUKAYYA: In ya yi waka kaina ai ya tabbatar wa duniya cewa ni ne ya yi bakin cikin rabuwa da ni, ba ni ba. Don ni ma ina da kudin da zan biya a yi min waka da a ce ni na yi bakin cikin rabuwa da shi. Ka ga kuwa idan ya yi ya kara tabbatar wa jama'a da duniya da industiri cewa shi ne fa ya yi bakin ciki. Rabuwata da Misbahu kowa ya gan ni ba zai ce "Rukayya kin rame" ko "kin yi wani abu" ba. Sai dai ma ya ce, "Ke Rukayya kin kara kyau!" Shi kuwa ko wa ya gan shi ya rame. Ka ga kuwa shi abin ya dama. In zai je ya yi kaset dari ya zage ni a ciki na san so ne. Na tabbata kauna ce; ina ransa, shi ya sa zai je ya yi abu a kaina.
FIM: Ya yi magana kan kawarki Rashida (Rashida ta harari wakilinmu) cewa ita ce tsanin da kika taka kika tsallake Misbahu.
RUKAYYA: Gaskiya ya zargi Rashida sosai kuma Allah zai saka mata. Rashida sai da ta same ni ta ce, "Rukayya," na ce, "Na'am". "Ki kama Mishabu." Tana son Misbahu har abin ya yi yawa! Amma Misbahu da ya tashi bai fara zagin kowa ba sai Rashida. Ya kamata ya zauna ya yi tunani ya gane mai kaunarsa. Tunda kuma ya nuna ba ya kaunarta, to ita ma fa ba ta kaunarsa, ba ta sonsa. Duk wani zargi da zai yi wa Rashida na banza ne. Kuma duk wanda zai zagi Rashida sai Allah ya saka mata saboda ba ta da laifi.
FIM: Me za ki ce wa mutane kan wannan abu?
RUKAYYA: Duk mutum mai imani wanda ya yarda da kaddara idan ya ji wannan labari ba zai zage ni ba. Idan ka ga mutm ya zage ni, to bai yarda da kaddara ba. Masu kaunata kuma 'yan kallo da masu karanta mujallar Fim ina so don Allah su ci gaba da yi min addu'a; addu'ar nan dai ita nake ta bara. Komai kaddara ce.
FIM: Duk wanda ya kalli fim din Kansakali ya san za a yi kashi na 2. To za ki je idan aka kira ki?
RUKAYYA: A'a? Ni fa fim nake yi. Kuma a fim ya gan ni, a fim ya ce yana sona. Har ranar da za a yi shutin, da ni ce yarinyar fim din. Saboda (Misbahu) ya je gidanmu na ki fitowa sai ya canza (ya sa) wata. Ai ba mu fara soyayya da Misbahu ba sai bayan Kansakali. Ni fa yanzu Misbahu normal mutm ne a wurina. Idan ya rubuta labari ya kira ni ya ce zan yi fim, ba zan ki yi ba tunda sana'ata ce.
FIM: A karshe, ko kin yi maganar aure tsakaninki da Suleiman?
RUKAYYA: Ni yanzu 'tension' da ke kaina ya ishe ni. (mahaifinta na kwance a asibiti a lokacin). Muna zaune lafiya da Suleiman muna soyayya. Amma ba mu yi maganar aure ba. Ka san shi aure zuwa yake, kaddara ce. Yanzu haka kila ma ni ba matarsa ba ce, watakila ma kai za ka aure ni Ashafa! (Duk an bushe da dariya).
FIM: To Allah ya ba mai rabo.
Rukayya: Amin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin