Abu kamar wasa..
Maryam Mushaqqa ta yi aure!
Maryam Mushaqqa
|
MARYAM ALIYU, daya daga cikin shahararrun jarumai ta bar fagen shirin fim. Wanda ta aura din dan Nijeriya ne mazaunin kasar Kamaru. 'Yan fim sun sha biki. A'ISHA ABBA AHMED, ABBAS SA'ID KIRU, da SANI MAIKATANGA ma sun halarci bukukuwan, kuma ga rahotonsu. SANI MAIKATANGA ya dauko mana hotunan bikin
GABA dai gaba dai 'yan fim! Da ma dai Hausawa sun ce komai ya yi zafi maganinsa Allah. Idan mai karatu na biye da al'amuran da suke zuwa da komowa, ya san labarin soyayyar da aka dade ana yi tsakanin fitacciyar jaruma Maryam Aliyu da shahararren dan wasa Ahmed S. Nuhu wadanda batun aurensu ya cika gari, masoyansu suka yi ta zuba ido don ganin ranar ta zo, amma daga baya abin ya watse.
An daura auren Maryam a ranar Asabar 19 ga Yuli, 2003, to amma ba da Ahmadu ba. Wani dan kasuwa da ke harkokinsa (mun ji an ce dan canji ne) tsakanin kasashen Kamaru, Faransa, Ghana da sauransu, mai suna Alhaji Auwalu Mohammed, shi ne ya sure jarumar ta shirin Mushaqqa, Sharadi, Asiya, da dimbin finafinai. Yanzu ta zama matarsa, har ma a daidai lokacin da muke rubuta wannan labarin ana shirin kai ta can kasar Kamaru inda mijin nata yake zaune da iyalinsa. Wannan ne aurenta na biyu, shi ma angon nata yana da mata daya a yanzu.
Wani abu da ya ba da mamaki, kuma ya burge jama'a, shi ne tun a katin gayyata zuwa shagulgulan auren, an rubuta cewa mahalarta daurin auren za su hadu a kamfanin shirya finafinai na FKD (kamfanin su Ahmed, tsohon saurayin Maryam), domin da yawa an dauka cewa ai ba sa shiri. Wannan matsayi da aka ba Ahmed da dan'uwansa Ali Nuhu, girmamawa ce daga Maryam, da kuma nuna cewa komai ya wuce sai dai labari.
Da karfe 9:30 aka ce a hadu a FKD din d ake titin Zoo Road don yin kwamba zuwa gidan su amaryar don daurin auren, to amma har karfe 9:56 ba wanda ya zo, sai ma'aikatan kamfanin kadai ne ke shawagi. Da wakilan mujallar Fim suka ga haka, sai suka yanke shawarar tafiya kai tsaye wajen daurin auren.
An daura auren da misalin karfe 10:57 na safe. Dimbin 'yan fim sun halarta. Daga cikinsu akwai Sir Hafizu Bello, Ishaq S. Ishaq, Aminu Mohammed Sabo, Ibrahim Maishinku, Tijjani Paris, Bashir Abubakar, Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Suleiman Gambo Awaisu (Alaqa), Isa Bello Ja, da Nasiru Dorayi da sauransu. Maijidda Ibrahim kadai ce wakilan wannan mujallar suka gani daga cikin 'yan fim mata a gidan, ana ta hidindumu da ita.
Bayan an daura auren, jama'a suka zarce gidan ango da ke unguwar Sallari don cin abinci, amma sai suka tarar ba a kawo ba. Da yake abokan angon suna gudun jin kunya, nan take sai suka yi odar abinci da lemon kwalba daga fitaccen gidan cin abinci din nan mai suna 'Al-Amir Restaurant'.
To amma tun kafin ranar da aka daura auren, an yi abubuwa da dama na al'ada da kuma wadanda zamani ya kawo. Daga ranar Laraba, 16 ga Yuli, 2003, aka fara shagulgulan bikin inda aka yi kamun amarya. An kama amaryar ne a gidan su fitacciyar jaruma Saima Mohammed da ke unguwar Brigade. Kamun, wanda aka yi a daren ranar, ya samu halartar 'yan fim mata da kuma 'yan'uwan amarya da dama, duk da cewa an yi ruwa a ranar. Haka kuma al'ummar unguwar sun taru, wasu ma sun je ne domin ganin 'yan fim kawai.
A ranar Alhamis kuma aka taru a gaban kamfanin editin na 'Kwalitiy Audio-Visual' da ke kan titin zuwa gidan Zoo domin a dunguma zuwa kauyen Tiga, a inda aka shirya yin kilisar zamani (picnic). Kamar yadda aka bayyana a jikin katin cewa shiga irin ta Turawa (English wear) ake bukatar kowa ya yi, haka aka yi kuwa. Duk wanda ba shi da mota a ranar 'yanmata ba sa ma ko kallonsa, wasu kuwa har dan waken zagaye suke yi wa wadanda ba su da kudin tafiya bare mota. Sai a ce da mutum bari a je a shawo mai, to sai dai ya ji a salansa.
Lokacin da aka isa can wurin an dan yi ciye-ciyen abin kwalama sa'annan aka shiga harka. Duk wanda ya sake ya tafi wurin ba tare da wani ba sai an jefa shi ko ita a ruwa. Aminu Mai Dawayya har da gudun mutuwa wai sai ya dauko angon ya jefa shi a ruwa. Wayoyin tafi-da- gidanka (GSM) sun sha ruwa a ranar domin ba zato ba tsammani ake rungumo mutum a wurga shi cikin kandami. Abokin ango kuma shahararren darekta kuma dan wasa, Ishaq Sidi Ishaq, ya batar da makullin motarsa - ko a ruwan ne ko yaya ne, oho! Hauwa Ali Dodo (Biba) tana ta fada, tana cewa ba ta son kowa ya jefa ta a ruwa; haba, ai sai gwanin tsara rawa a fim, Shu'aibu Idris (Lilisco), ya debo uwa a fanteka, ya biyo ta bayanta, ya kwara mata shi. Wata yarinya mai suna Hadiza har ciwo aka ji mata, sai kira take yi. "Kalli yadda suka sa nake bleeding," jini kuwa sai zuba ya ke daga goshinta.
Wannan harka ta yi armashi domin har sarkin ban dariya, Rabilu Musa Danlasan (Ibro) ya halarta, amma shi ya roki kada a jefa shi a ruwa saboda yana da ciwo a hannunsa. Aka kyale shi. Lokacin da amaryar ta ga zuwan Ahmed sai ta kama kukan karya, to ko tsohon ciwo ta tuna ne wa ya sani.
Da za a tafi gida, wata yarinya ta so ta wulakanta saboda ba ta san kowa mai mota a wurin ba; ko yaya aka yi ta je, oho! Daga karshe sai wani shahararren mawaki ta like wa duk da cewa ba shi da mota sai da ya samu ya makala ta a motar da za su taho. Motar su Ahmed S. Nuhu ta daki wani dustse, amma dai Allah ya kiyaye ba a ji ciwo ba.
An dai tashi daga wajen da misalin karfe 10:30 na dare.
Washegarin ranar da aka yi kilisa, wato Jumma'a, 18 ga Yuli ne aka yi walimar zamani a dandalin shakatawa na matasa da ke unguwar Panshekara (Sani Abacha Youth Centre), a ci gaban da ake yi da shagulgulan bikin.
Tun da karfe 5 na yamma mutane suka fara tururuwa zuwa wurin, maimakon karfe 3 da aka rubuta a jikin katin gayyata. A ranar, Ibro yana yin Gala a wani bangare na wurin, saboda haka duk wanda ya zo wurin ya tarar ba a fara komai ba sai ya fada wurin kallon Ibro. Lakacin da sarkin barkwancin ya gama wasansa ne kowa ya yi tururuwa zuwa wurin shagalin auren Maryam Mushaqqa, ciki har har ma da wadanda ba a gayyata ba. Wasu samari sun more da wanka a dan ruwan da ke filin shakatawar. Gurin ya zo abin tsoro ne lokacin da samari daga waje suka yi kwamba zuwa wurin, wasunsu kuma suka yi ta busa tabar wiwi, wasunsu ma suka yi ta kokarin fada da 'yanmata da ke wurin, duk da matakan tsaron da aka tanadar na 'yan sanda.
Wata kawar amarya ta shaida wa wakilinmu cewa amaryar ba za ta samu damar zuwa wurin ba saboda ba ta jin dadi, haka ma angon ba zai zo ba. Can zuwa karfe 9 na dare sai ga ango da amaryar tasa sun diro filin, suna ta walkiya. Maryam, wadda Ba'abziniya ce, tana ta kyalli, kuma harafin 'M" (na sunanta) da aka tsaga a goshinta ya fito radau. Da shigowarsu nan da nan mutane suka yi musu caa domin su gan su. Masu daukar hoton kati da na bidiyo suka shiga aiki, kowa yana gwada nasa kokarin, amma gurin ya cushe. Nan ma 'yansanda suka shiga nasu aiki.
Lokacin da ma'auratan suka iso filin ne kuma sai mawakin na asharalle, wato Alhaji Surajo Mai Asharalle Katsina, ya kara kaimi. Amarya da ango sun shiga fage sun cashe, mutane kuma da ma aljifai suna ta kaikayi, nan da nan suka shiga liki. Ana ta wannan sha'ani kuma sai aka yi abin ban haushi, aka dauke wutar lantarki. Nan take sai masu wayoyin selula na GSM suka shiga haska fitilar wayoyin nasu domin a ga haske, kada bata-gari su yi halinsu. Ai kuwa ba a tsira ba, domin duk da wanna kokarin samun haske sai da aka sace wa wata wayar GSM dinta. Da aka dawo da wuta aka yi ta cigiya ko Allah ya sa wayar ta fada hannu nagari, amma ina!
An tashi daga wajen da misalin karfe 10 na dare. 'Yan fim da suka halarci gurin b asu kirguwa, to amma sun hada Ibrahim Sinana, Shu'aibu Lilisco, Ali Nuhu, Misbahu M. Ahmad, Aminu M. Ahmad, Dan'azimi Baba, Suleiman Sa'eed da sauransu. A 'yan fim mata akwai irin su Rahma Isa, Maryam Mashahama, Yahanasu Sani, Zulai Dalhat, Saima Mohammed, Hauwa Ali Dodo, Hadiza Kabara, Rukayya Dawayya, da suaransu.
A yammacin ranar da aka daura auren an yi walima. Da, a gidan su amaryar aka yi niyyar yin walimar, to amma daga baya sai aka canza aka koma gidan su Saima Mohammed. Aka kuma dawo kusa da gidan su amaryar inda a karshe aka yi walimar. 'Yan'uwa da abokan arziki sun taru, an kuma yi addu'o'i da karatun Alkur'ani mai girma. Bugu da kari, a wannan ranar an yi pati na tsakar dare wanda ba a so kowa ya sani ba saboda gudun surutun mutane. Wannan wuri ya samu halartar 'yanmatan amarya ne da angwaye zalla. Da alamu da dama cewa ba a so musamman ma dai 'yan jarida su halarci bikin na Maryam baki daya saboda yawo da hankali da kawayenta suka rika yi musu na cewa an canza wuraren yin shagulgulan. Abin tambaya shi ne, idan har ba a so su je menene ya sa aka yiwo tattaki aka gayyace su?
A ranar Lahadi, 20 ga watan, an yi liyafar cin abincin dare a otal din Ni'ima, wadda abokan ango da kawayen amarya suka shirya. An yi wannan liyafa ne a gidan wanka (swimming pool) da ke otal din. Jama'a sun yi ta tururuwa amma aka ce sai mai kati ne zai shiga. Tun karfe 8 na dare ake fara hallara wanda har karfe 9:30 babu alamar 'yanmatan amaryar, irin su Biba da Saima. 'Yan fim sun taya mutane shakatawa tun kafin zuwan angwayen. Tuni su Kumurci da Rukayya suka fara cashewa, sai Ahmed S. Nuhu da Maijida Ibrahim, sai Baballe Hayatu da Farida Jalal, sai Sani Danja da 'yan matan fim suka cashe da wakar "Eba Ebana" ta cikin Harsashi; sai kuma Ali Nuhu da Rahama Ahmed su ma suka cashe da wata wakar cikin fim din Khusufi 2, wanda bai fito ba tukuna.
Sai wajen karfe 10 tukuna abokan ango suka iso tare da 'yanmatan, sun sanya angon a tsakiya, suka shigo wajen, amma kuma babu amarya a tare da su. Rashin zuwan Maryam ya haifar da surutai a tsakanin mahalarta wannan bikin. Wata kawarta ta shaida wa Fim cewa wai mahaifiyarta ce ta hana ta zuwa. To amma wata majiyar kuma ta ce wai wata yarinya ce ta shirya ci wa amaryar mutunci domin ta ari kayanta ba ta mayar mata ba, wai ta sha alwashin cewa idan Maryam ta yi gigin zuwa wajen sai ta sa 'yansanda sun tafi da ita.
Ana cikin wannan cashewa ne, wato bayan angwaye sun iso, sai Sani Dan Indo shi ma ya fara nasa kidan. Su kuma 'yan fim suka dada kure kayan kidansu. Nan dai aka dan yi hayaniya tsakanin 'yan fim da mutanen Sani Dan Indo, a kan waye ya dace ya yi wasa a lokacin. Da kyar aka aka shawo kan takaddamar. Ana gama wannan kuma sai can kuma samari 'yan fim suka kwaso tasu da wasu samari da aka gayyata wajen a dalilin wani daga cikin samarin gari ya ingiza wani yaro cikin wajen, wanda duk da yake bai ji ciwo ba kuma babu ruwa a ciki. Nan take Adam User ya yi kansa ya cakume shi, suka rukume. Su ma da kyar aka shawo kansu. Haka kuma mahalarta bikin sun yi wawar abinci a kan teburin angwaye duk aka dauke musu su lemon Five-Alive da ruwan sha da sauran abincin da aka kawo aka fara rububin rabawa. Nan dai angwaye suka ja kujerunsu baya. An dauke sauran abincin an boye. Ganin haka ya sa wani yaron Sani Dan Indo ya shiga habaici yana cewa, "Wasu sun zo wajen nan da ledoji sun kwashe abinci, mu kuma muna taya su murna". Har wa yau an sace wa wata wayar G.S.M Shi kuma Sani Dan Indo ya ci gaba da cashewarsa inda 'yan fim mata suka cashe. Su ma su Ahmed. S. Nuhu da Baballe Hayatu da sauransu sun cashe. Biki dai ya yi ta tafiya har wajen karfe 2 saura na dare. Haka dai aka gudanar da wannan liyafa lami lafiya babu amarya.
Daga cikin wadanda suka halarci wannan shagalin akwai Hajiya Balaraba Ramat yakubu, Hajiya Umma Ali, Saratu Gidado, Lubabatu Madaki, kai har ma da matan aure masu alaka da industiri, wato irin su Maimuna Ali Nuhu, Maryam Aminu Sheriff Momo, Maryam Shu'aibu Lawan Kumurci da amaryar Aminu Garba Mai Dawayya.
Wannan shi ne abu na karshe da aka tsara a shagulgulan auren. An shirya cewa za a kai amaryar gidan mijinta a can kasar Kamaru a cikin makon. Wata maciya ta shaida wa Fim cewa anguna sun tanaji motoci da za a kwashi 'yan kai amarya Kamaru din.
Muna yi wa Maryam da Auwalu fatan alheri a wannan aure nasu, tare da fatan samun zaman lafiya da karuwar zuri'a dayyiba.
Na yi murna, Allah ya sanya mata albarka Inji uwar amarya
Kafin wannan aure, Maryam ta shafe sama da shekara daya ba ta shiri da mahaifiyarta HAJIYA HAUWA. To amma wannan auren ya wanke Maryam, domin mahaifiyar tata ta yafe mata, kuma ta sanya mata albarka, a tattaunawarta da mujallar Fim:
FIM: Hajiya muna taya ki murnar wanna shagali.
HAJIYA: Na gode. Allah ya saka muku da alheri.
FIM: Wane irin farin ciki kike yi a ranki a yau?
HAJIYA: Ina murna da godiya ga Ubangijina ne.
FIM: Wane fatan alheri gare ki ga 'yar taki?
HAJIYA: Ina yi mata addu'a. Allah ya shiryi halayenta. Allah ya sa mata albarka. Allah kuma ya sa ta yi amfani da nasihohin da aka yi mata.
FIM: Wane sako gare ki ga angon na Maryam?
HAJIYA: Gaskiya ni ban san shi ba, ita ta hada ni da shi. Don haka in rokon shi arziki don Ubangiji da ya halitto mu ya rike min diyata amana kuma ya zama cikakken Musulmi.
FIM: Abokan arziki fa, musaman kawayenta 'yan fim?
HAJIYA: Ina gode musu da suka zauna da diyata lafiya. Allah ya saka musu da alheri, kuma ku yi mata alheri.
FIM: Me za ki ce dangane da halayenta?
HAJIYA: Sai dai in ce Allah ya shirye ta, domin gaskiya da farko mun yi tashin hankali da ita amma yanzu da Allah ya kawo mu wannan rana, na gode wa Allah, kuma Allah ya shirye ta shirin na Musulunci.
FIM: Kafin wannan rana, ta sami daukaka a fagen fim, kowa yana sonta. Yaya kike ji a ranki?
HAJIYA: Ni ban sani ba. Ka san shekarata biyu da ita ba ma shiri; magana ta Allah kenan.
FIM: Me za ki ce dangane da matsayin da take kai a yanzu na daukaka kuma ga shi za ta yi aure?
HAJIYA: Da farko da yake abin da ba gadonka ba kuma kake da jahilci a kai, da raina ya baci sosai, to sai daga baya na fahimci abin da yake akwai. To na yi wa Allah godiya sosai.
FIM: To Hajiya mun gode. Allah ya sanya alheri.
HAJIYA: Amin.
'Wasu ba su so na aure ta ba'
Jim kadan da daura auren, mun waiwayi sha-guda, wato ango, Alhaji Auwalu Mohammed, don jin ta bakinsa. A hirar, ya bayyana matsayinsa, haduwarsu, matsalolin da ya fuskanta da kuma sako ga abokin takararsa da ya sha kaye, wato Ahmad S. Nuhu:
FIM: Haji Auwal, muna taya ka murnar wannan rana. Wane farin ciki za ka bayyana a yau?
AUWALU: Ina godiya ga Allah da iyayen amarya da ku da kuka halarci wannan taro na daurin aurena da Maryam. Allah ya saka wa kowa da kowa.
FIM: Da muna da labarin aurensu da wani dan fim, amma daga baya mun ji an ce wani dan Kamaru ya kada shi.
AUWALU: To! Ni dai gaskiya a da ban san Maryam ba. Haduwata da ita da Babbar Sallah ne lokacin da na dauke su na kai su Kamaru wasa. Kafin in ci gaba, ina son a sani cewa ni dan Nijeriya ne; mahaifiyata a Legas take, mahaifina dan Bauchi ne. An haife ni a Legas amma a Kamaru na zauna shekara goma sha uku, don haka rayuwata ina yinta tsakanin Najeriya da Saudiyya da Kamaru, don haka in na zo Najeriya na yi aure sai dai a ce na zo gida na yi aure.
FIM: Daga lokacin da ka fara sonta wadanne matsaloli ka samu?
AUWALU: Lokacin da na ce ina sonta, ba ta ma yarda da gaske nake ba, sai bayan sun dawo Najeriya na biyo ta, muka sami iyayenta muka sanar da su. To a nan ne ma na ji cewa akwai wani dan fim da yake sonta, to amma ban yi binciken menene a tsakaninsu ba, na ci gaba da nemanta har kuma Allah ya yi.
FIM: Ba ka sami tsegumi da kushe daga wajen abokan sana'arta ba?
AUWALU: Da farko an so a samu, to amma idan aka ce ka girma dole za ka kai munzalin da za ka dauki mataki a kan irin wadannan abubuwan. Domin da yawa wasu ba su so a yi ba. To da yake mutum ba ya auren matar wani, sai ga shi Allah ya tabbatar.
FIM: Ga shi kai ba harkar fim kake ba, lokacin da ka ce za ka auri 'yar fim ba ka sami matsala a gida ko wajen abokai ba?
AUWALU: Akwai wadanda a gaskiya ba su so ba, to amma idan aka ce mutum wayayye ne, to za ka ga abin da wasu suke ganin yana da wahala to kai sai ka yi shi ba da wahalar ba. Kuma akwai wadanda ke zuwa kasashen waje su auri Turawa alhali ba su san usulinsu ba. Kuma ai addini bai ki fim ba, jahilci ne ya sa wasu suke kyamatar masu yin fim din.
FIM: Tun yaushe kuke soyayya da ita?
AUWALU: Ba na jin mun yi wata shida da ita; watanmu biyar.
FIM: Wane sako gare ka ga wanda ka kasa?
AUWALU: Sai dai in ce ya yi hakuri, don wallahi a cikinsu babu wanda na sani lokacin da na fara nemanta, sai bayan na yi karfi a wajenta da gidansu nake jin labarinsa. To ya dauki kaddara; wani ba ya auren matar wani.
FIM: Kasancewar tana da dubban masoya, ga shi kuma yau ka raba su da ita, me za ka ce musu?
AUWALU: Su yi hakuri su yi ta yi mana addu'ar zaman lafiya. In dai masoyan nata ne na hakika, to za su fi son ta yi zaman auren a maimakon ta ci gaba da yin fim kawai.
FIM: Da ka taba aure ne?
AUWALU: Maryam ita ce ta biyu; ina da mace daya da da guda daya.
FIM: Ga shi za ka kai ta inda ba uwa ba uba, wane kira za ka yi gare ta?
AUWALU: Ta yi hakuri ta bi aure mu zauna lafiya. Idan mun je ni ne uwa da uba a wajenta, ta san cewa aure ne ya kai ta.
FIM: Mun gode. Allah ya sanya alheri.
AUWALU: Amin, Allah ya taimaka.
Sakon Maryam ga masoya
Mako biyu kafin a daura mata aure, MARYAM ALIYU ta je Kaduna, inda ta sadu da Mataimakin Edita ALIYU ABDULLAHI GORA II, inda suka tattauna kan auren da za ta yi. Kamar wata daya da ya gabata a lokacin, sun yi wata hirar (wadda muka kawo muku a cikin wannan watan) inda jarumar ta karyata labarin da ya cika industiri cewa aurenta ya kusa. To amma a nan, ta bada kai bori ya hau, domin fa ta hango cewa ba makawa aurenta nata za a yi. Bismilla:
FIM: Maryam, ga shi Allah ya kawo mu lokacin da za a daura maki aure da wani dan Kamaru, wanda kika taba karyata ji-ta-ji-tar cewa za ki aura a wata hira da muka taba yi da ke. Shin shi ne za ki aura ko wani dan Kamaru din ne daban kuma kika samu?
MARYAM: E, to, gaskiya dai, ina fatan da masu kallon finafinanmu da kuma masu karanta mujallar Fim suna sane da cewa shi fa aure nufi ne na Allah. Saboda haka yanzu shi dai Ahmed (S. Nuhu) ya zama wana. Shi kuma zancen wannan Auwalu na Kamaru da kake magana, gaskiya a da ban sa ran zan aure shi ba; kawai Allah ne ya kaddara kuma ya ce sai an yi da shi.
FIM: Da ma sunan angon naki kenan Auwalu?
MARYAM: E, sunanshi kenan.
FIM: Amma yanzu ba a fi wata daya da ya wuce ba da kika gaya mani cewa ba ma maganar soyayya tsakaninku da shi ballantana maganar aure. To daga wancan lokacin ne zuwa yanzu kuka daidaita har kika amince za ki aure shi?
MARYAM: E, gaskiya bayan tattaunawarmu da kai ne.
FIM: Yanzu daurin auren naku ya tabbata ranar Asabar, 19 ga Yuli, 2003 za a yi?
MARYAM: Kwarai kuwa.
FIM: Yanzu shi Auwalu ya kammala duk shirye-shiryen da ake bukata daga bangarensa ?
MARYAM: E, to, to dai kudin zance ake cewa ko kudin menene dai, da su waye, duk an kawo. Da kayan sa rana duk an kawo. Sadaki kuma ai ka san wasu sai za a daura aure ake bayarwa.
FIM: A can kasarku Nijar za a daura auren ko a Kano inda mahaifinki yake?
MARYAM: A gaskiya ni mahaifina a Kano yake. A nan za a daura auren.
FIM: A nan Nijeriya Auwalu zai bar ki ko tafiya zai yi da ke can Kamarun?
MARYAM: A'a, inda duk mace take ai gidan mijinta ko a ina yake shi take bi.
FIM: Yanzu shi kenan kin bar shirin fim, ko zai bar ki ki ci gaba da sana'arki?
MARYAM: A'a, zan bar fim. Sai dai kuma a bar wa 'yan baya su zo su ma su dan yi nasu yayin.
FIM: To idan ya amince ki ci gaba da yin fim din fa, za ki yarda?
MARYAM: Gaskiya sai in ce ba ya kishina. Ba zai ma bari ba. Kwata-kwata wannan ma ba zata yiwu ba.
FIM: To wace sana'a za ki yi bayan kin tare gidan mijinki? Ko zaman aure kawai za ki yi, sai abin da mijinki ya ba ki?
MARYAM: To ka san ban san yanayin yadda can garin yake ba. Wa ya sani, kayayyakin sanarsu daya suke da na Kano ko Kaduna? Sai dai na je can tukun na gani. Amma in Allah ya yarda, zan zauna ba sana'a ne?
FIM: Ahmed S. Nuhu ya san za ki yi wannan auren?
MARYAM: Ahmed ya san komai. Kusan ma in ce sh ine ma babban abokin amarya a ranar bikin in Allah ya so!
FIM: Wace irin rawa yake takawa game da auren naki?
MARYAM: Yana ba ni shawarwari. Sannan kuma ya na ba da tasa gudunmuwar.
FIM: Wace irin gudunmuwa?
MARYAM: E, to wannan kuma tsakaninmu ne, ba ruwanku…(dariya)
FIM: Shi angon naki sana'ar me yake yi?
MARYAM: Kasuwanci yake yi.
FIM: A can asalin garinku na Nijar ake shirye-shiryen aure ko a Kano?
MARYAM: A nan Nijeriya aka yi komai.
FIM: Ku Abzinawa an ce ba da kudi ake biyan sadakinku ba, da rakuma ake biya. Ke ma sadakin naki da rakuma za a biya?
MARYAM: Gaskiya haka ne, da rakuma ake biya. Kuma rakuman da ake biyan sadaki da su, misali a ce yanzu…tun dai daga iyaye ne abin... idan da rakumi goma aka biya sadakin uwar yarinya, to ita ma yarinyar da rakuma goma za a biya sadakinta. To amma gaskiya wannan dai na Hausa aka yi.
FIM: Me ya sa ba ku bi na al'adarku ba?
MARYAM: To ai ka ga su yanzu iyayenmu sun dade a nan kasar. Ka ga kuma shi wannan ba dan can garin namu ba ne. Sannan kuma mafi yawancin al'adar... Yanzu to ina ma zai samo rakuma saboda Allah? Ai ba zai yiwu ba!
FIM: Kafin a daidaita maganr aure tsakaninki da shi, kun tura shi Nijar ya gaida danginku?
MARYAM: Gaskiya danginmu suna Nijar. Ba su je Nijar ba, yana dai kan hanyar zuwa. Amma ai akwai dangin babana a nan, ya je sun gaggana da su.
FIM: Me za ki cewa masoyanki, kasancewar da yawa daga cikinsu ba su san za ki yi wannan aure ba?
MARYAM: E, to gaskiya ni kaina ban gaskata auren ba a da. Amma yanzu na tabbatar da in Allah ya so za a yi. Saboda haka ina rokonsu da don Allah don Annabi su yi hakuri. Abin ne ya zo a kurarren lokaci, amma su dai ci gaba da taya ni addu'a kawai Allah ya zaunar da mu lafiya.
FIM: Da kamar kin nuna ba ki son shi Auwalu da aure. Ya aka yi to kuka sasanta har ta kai ga ga shi yanzu za ku yi aure?
MARYAM: E, to sun biya... (dariya) ... Gaskiya ni kaina ban sani ba, to abu ne in aka ce maka dai da ikon Allah, kawai an gama komai. To Allah ne ya kaddaro hakan za a yi.
FIM: Mecece gaskiyar maganar cewa kin taba yin aure, wai har ma kin haihu?
MARYAM: E, a gaskiya na daura mani aure. Ban tare ba sai aka samu rikici, har Allah ya sa aka raba auren. To amma ban taba haihuwa ba. Ban ma zauna ba.
FIM: A ina ne kika yi auren?
MARYAM: A Kaduna ne. A Badarawa.
FIM: Me ya sa kika yanke hukuncin yin aure a Kamaru maimakon ki auri dan'uwanki Ba'abzine ko Buzu, ko kuma abokin san'arki dan fim a nan Nijeriya?
MARYAM: Gaskiya na yi niyyar auren dan fim din, Allah ne bai yi ba, kuma Allah ya san zuciyata, kuma kowa ya san niyyata. Ko da mutum bai ji daga bakina ba, ya karanta a mujalla. Saboda haka Allah ne ya yi da wannan din za a yi.
FIM: Kina ganin mutane ba za su yi tsammanin kila don ki nuna wa Ahmedu kin fi shi aji ne ya sa kika yi aure a kas ar waje ba ko don ya ji haushi?
MARYAM (tana dariya): A'a, ba haka ba ne wallahi. Ai duk yadda aka dauki abin da zafi, fadanmu da Ahmed bai kai haka ba. Saboda ni ban taba wata hayaniya da shi ba. Kuma wallahi ko da zan taho nan yanzu ma sai da muka yi magana da shi ta waya. To me ya yi zafi?
FIM: Dangantakarku da shi za ta dore ko bayan kin yi aure, ko kuwa daga ranar da aka daura auren kin yanke hulda kenan?
MARYAM: Ni da yayana ya za ka ce a yanke saboda Allah. Ga waya nan. Kuma ai zai iya zuwa gidanmu a matsayinshi na wana, tunda gaskiya yanzu kwata-kwata babu zancen wata soyayya a tsakaninmu sai ta Musulunci kawai. Amma a matsayinshi na wana zai iya zuwa gidanmu ya gan ni.
FIm: Shi mijin naki ya san kun taba yin matsananciyar soyayya da Ahmed?
MARYAM: Ya sani mana. To amma shi ma ai yana da hankali, kuma na san yana da isasshen ilimin da za a ce ya fahimci duk abubuwan da suka gudana a tsakaninmu.
FIM: Amma kamar yadda kuka shaku da Ahmed, kina ganin idan yana zuwa gidan da kike aure wata ran ba zai kashe maki aure ba?
MARYAM (dariya): A'a. Hakan ba za ta kasance ba. Ya za a yi ina gidan wani kuma in rika tunanin wani abu? Ai ba zai yiwu ba.
FIM: Maryam, tunda ga shi kina bankwana da wannan sana'a ta fim, wadanne irin nasarori kika samu a cikinta tunda kika fara ya zuwa yau?
MARYAM: Gaskiya na samu nasara a cikin wannan sana'a. Sai dai in yi wa Allah godiya. Saboda duk wahalhalun da dan fim ke sha idan yana sabon shigowa ni ban sha su ba. Don kwata-kwata dirata a Kano ban yi sati daya ba na fara fim. Kuma na sha samun alheri da kyaututtuka daga masoyana, ga abokai na yi. Wadanda ban sani ba a da, yanzu sun zama aminaina. Ka ga wannan babbar nasara ce. Ga shi kuma zan bar industiri lafiya.
FIM: Wanne ne fim dinki na farko, wanne ne kuma na karshe?
Maryam: Fim dina na farko shi ne Mushaqqa, na karshe kuma shi ne Salmat, wanda Dokto na Iyan-Tama ya shirya.
FIM: Amma kin taba tunanin za ki yi aure a cikin wannan shekarar ki bar shirin fim?
MARYAM: Gaskiya, ina dai rokon Allah ya sa hakan ta faru, amma... ina dai roko sai ga shi Allah ya kawo.
FIM: Ba ki taba jin ba dadi ba a zuciyarki, ganin za ki yi aure ki bar sana'arki da masoyanki da kuma abokanki?
MARYAM: To, ko ma ya tashi ai dole hakuri zan yi, tunda ya kamata kuma a bar shirin fim kuma a nemi wata sana'ar.
FIM: Me zai hana ki rikide ki zama furodusa, tunda kin riga kin san sirrin san'ar?
MARYAM: A'a. A haka ma ana hada mani zafi ballantana na zama furodusa! Ba zan iya ba gaskiya.
FIM: Wane sako ne gareki zuwa ga 'yan'uwa da abokan arziki?
MARYAM: Da farko dai ina godiya ga iyayena da kuma 'yan'uwana da dukkan masoyana. Sai kuma Halima Adamu Yahaya, Antina. Ba zan taba mantawa da ita ba tunda ita ta kawo ni fagen shirin fim. Ina yi mata godiya. Allah ya raya mata 'ya'yenta. Sannan kuma sai marigayi Tijjani, shi kuma Allah ya jikansa.
FIM: Maryam, muna yi maki fatan alheri, kuma Allah ya ba ku zaman lafiya.
Maryam: Ni ma na gode na gode. Allah ya kara daukaka ku.
MUNA MUTUNCI DA MARYAM HAR TA YI AURE, INJI ALI NUHU
AN jima ana ruwa kasa na shanyewa a zarge-zarge na cewa ALI NUHU ne musabbabin rabuwar Misbahu da Rukayya, haka tsakanin Ahmed da Maryam. A duk lokacin da ake ta yada wadannan surutai, Ali dai ya koma gefe guda yana kallon me zai je ya komo. 'Yan jarida sun tuntube shi a kan wadannan zargi amma ya ce shi ba shi da ta cewa.
A lokacin auren Maryam Mushaqqa ne wakilinmu ya tinkare shi Ali da maganar, shi kuma ya amsa tambayoyinmu kamar haka:
FIM: Ali, yaya aka yi ku da ake ganin kun samu sabani da Maryam amma sai ga shi an sa FKD ne wurin haduwa tafiya daurin aurenta?
ALI: Hakikanin gaskiya da farko zan yi gyara. Wannan "sabanin" da kake fada ni ba na tunanin akwai wani sabani; har Maryam ta tafi, fim dinmu na karshe wannan ne Khusufi, akwai Maryam a ciki. Ka ga kuma wanda kuke sabani da shi za ka yi fim da shi? Babu wannan zancen. To shi ne dalilin da aka sa FKD (ya zama) meeting point ba wani abu ba ne. Da a ce marigayi (Tijjani Ibraheem) yana da rai, to ina ganin da Fasaha za a sa, to amma tunda marigayi ba ya nan, ai ya rasu ya bar Maryam a hannunmu, tunda dai kusan za mu ce Allah ne gatanta kuma shi ne gatanta. To saboda haka babu kuma wadanda suke hulda da kuma alaka da take mafi kusanci da ita wanda za su shige mata gaba a kan wasu abubuwa a industiri shi ne tana ganin mu ne wadanda za su fi saukin gane gidansu domin zuwa wajen. Kuma ita tana ganin babu wani kamfani a wajenta kamar FKD. Wannan shi ne dalili.
FIM: Me za ka ce kan zargin da ake yi cewa kai ne ummulhaba'isin rabuwar Maryam da Ahmed?
ALI: To ai ni wannan maganar taku maimaici kuke yi; kun tambayi Ahmed S. Nuhu, kun tambayi Maryam ta ba ku amsa, kuma kun zo kuna tambayata, amma ba abin da zan ce ni.
FIM: Ana so ne ka kare kanka kan wannan zargin.
ALI: In ka ji ana maganar kare kai ai ka yi laifi ne. To ai ni ban san komai game da wannan maganar ba, amma ana ta cewa in kare kaina kamar na yi laifi kenan.
FIM: Ai yanzu mutane da yawa sun dauka duk wani laifi na rabuwar a kanka ne.
ALI: Ai ba ka san wani abu ba, ai da ma mutane ba za su rasa magana ba, ka gane? Ai da ma Annabi Muhammad (s.a.w.) ya ce in ba za ka fadi alkhairi ba ka yi shiru, ko ba haka ba? Da (mutane) za su yi aiki da wannan hadisin da an zauna lafiya a duniya; mutane will always talk. Ni ban ga wani abu na kare kai kare kai ba. Maryam da Ahmed su ya kamata su gaya muku abin da ya sa suka rabu, ba Ali Nuhu ba; in suka gaya muku dalilin da suka rabu, tunda sun fada sun kara fada, to ku sai kun san dalilin da ya sa suka rabu, amma ni ban san me ya sa kuke jawo ni cikin maganar nan ba, don ni ba wanda ya taba tunkarata da wannan maganar sai ku 'yan jarida. Zan ce ku ne kuke so ku gaya wa mutane wannan maganar.
FIM: Me za ka ce kan batun Rukayya da Misbahu wanda Suleiman Sa'eed ya ce kai ne ka yi kutu-kutun rabuwarsu?
ALI: To ai ba ka san wani abu ba, harshe ai ya gama magana da ya ce, "Akuyar da ta isa ita ake daga wa kara". Suleiman Sa'eed bai isa in yi magana da shi a mujalla ba saboda ni ci-baya ne a gare ni in na zauna ina yin magana a kan shi, ka gane? Kuma bayan haka, ni dai ka ga ban taba yin magana a mujalla a kan maganar su Misbahu da Rukayya ba; su da abin ya sha fa sun yi magana a kai. Duk wani da yake cusa kai da karfi da ya ji so yake a san shi, ni kuma ba wannan nake nema ba saboda alhamdu lillahi daidai gwargwado an sanni, ko ba haka ba? Ni ba zan so in bata wa masu kaunata rai ba ina cacar baki da wani a mujalla, ba zan iya ba wallahi. In shi dabi'arshi ce, ni ba dabi'ata ba ce.
FIM: To yanzu ga shi Maryam ta yi aure. Ko wace nasiha za ka yi mata tare da angonta?
ALI: Nasihata gare su (ita ce), don Allah zan roke su da su riki junansu amana. Su yi hakuri da juna, domin zaman aure in ba hakuri ba za a ji dadi ba. Kamar wata wakar Khusufi inda ake cewa, "Ginshiki na aure kauna ce". Don kaunar ita ya kamata ta yi aiki a tsakaninsu wanda in har aka yi hakan za a zauna lafiya. Allah kuma ya ba su zaman lafiya, ya ba su zuriya tagari.
FIM: Ali, mun gode.
ALI: Ni ma na gode.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|