HIRAR MUSAMMAN, Fati Moh'd/ Sani Musa
RAYUWARMU A LONDON
Fati, Amaryar Sani
|
Daga birnin London, Fati Mohammed da Sani Mai Iska sun yi bayani kan ji-ta-ji-tar cewa wai sun rabu, kuma wai Fati za ta auri Bature. Jaruman sun karyata ji-ta-ji-tar, suka ce aurensu na nan daram-dakam DAGA IBRAHIM SHEME A KADUNA
Bayan mun gama gaisawa da Sani Mai Iska, sai muka ci gaba da tattaunawa da shi da Fati kamar haka:
FIM: Me za ka ce kan ji-ta-ji-tar da ake yadawa cewa kun rabu da Fati?
SANI: Da farko dai muna tare da Fati, kuma lafiyarmu kalau. Kuma maganar cewa zan yi aure kuma Fati za ta auri Bature, wannan magana ma ba ta taso ba. Dalilai kuwa Ingila kamar Najeriya take, illa dai kawai nisa ne. Ba yadda za a yi a samu cikakken sati ba a samu wasu mutane daga Najeriya sun zo nan ba ko kuma mutanenmu Hausawa sun je can. Kuma duk wani mutumin da zai gan ni ko Fati, to ina tabbatar maka da cewa ko dai mace ce ko namiji, to tare zai gan mu mun je kuma zai gan mu mun dawo. Saboda haka zancen cewa mun rabu da Fati ko kuma zan yi wani aure, wannan magana ma ka kyale ta.
Sannan kuma Ingila ba kamar irin mu nan gida ba ne inda za ka mutum zai yi mata biyu ko uku. Dole za ka ga irin mutanenmu da suke kamar shuwagabanni ko masu wadata wadanda suke da iyali daga daya biyu zuwa uku haka, sai dai ka ga matarsu daga su kawo ta daya nan wasu lokuta su maida ita sannan dayar ta zo haka. Amma hardly ka ga mutum ya zauna da mace biyu a nan.
Haka kuma har yanzu muna matakin mu zama 'yan gari ne. Don mu gaba daya wannan watan shi ne muka shiga wata na goma sha daya ko sha biyu a nan garin; to ka ga ba mu kai kafuwar da ma har wani daga cikinmu zai canza wani ra'ayinshi ko ya yi wani abu ba.
FIM: Menene dalilin da ya sa kai da Fati kuka tafi Ingila kusan a asirce, ba tare da kun yi sallama da jama'a ba?
SANI: Mun yi sallama da mutane, wala-Allah kai ne ba ka ji ba. Kuma … Mun yi sallama din. Kuma kafin ma mu taho nan gaba daya sai da na zo nan (Ingila) na yi kwana bakwai na gama shirye-shiryen da zan yi sannan na koma muka taho da ita. Saboda haka maganar cewa mun taho a asirce ba ta taso ba. Kuma jirgin sama muka zo iyafot inda akalla mun samu kamar minti arba'in ko hamsin haka; don mun yi mota akalla shida ko bakwai wanda muka zo iyafot. To ka ga cewa ba maganar cewa a asirce muka taho. Kuma sannan ba za mu sanar a rediyo misali cewa 'Sani da Fati za su yi tafiya' ba saboda muna son kowa da kowa ya sani. Kamar a tafiyarmu ta farko, wasu ma har muka je muka dawo ba su yarda mun zo ba. Sannan kuma yana daga cikin sunna ta Manzo cewa idan za ka yi tafiya kar ka zama mai barbadiya … kana da sirri a plan dinka. Saboda gudun bakin mutane ko kuma makiya haka, wanda na san ba za a rasa su ba. Akwai abin da za ka bude ma duniya, akwai abin da ba za ka bude ma duniya shi ba.
FIM: Zan so ka gaya wa mutane ainihin me kuke yi a London da kuka je kuka zauna shiru ba bayani.
SANI: To wannan tambayar sai in ce mu bar ta sai mun dawo Nijeriya.
FIM: To shikenan. Yaushe ne kuke sa ran za ku dawo?
SANI: Ka san tafiya ta Allah ce, sai dai mutum yana da wani buri nashi. Amma zai zama a kowane lokaci abin da kake tunanin za ka yi to kuma karshenta amma shi a lauhul mahfuz ba haka ya rubuta maka ba; ya rubuta maka wani abu daban. Amma dai duk da haka yanzu muna tunanin… da muna tunanin a Disamba din nan mu zo gida, to kuma sai wasu dalilai haka suka dakatar da mu. Ina ganin wala-Allah sai cikin sabuwar shekara. Shi din ma babu tabbas domin shi komai ka san dai Allah shi ne ke yin shi.
FIM: Shin kana tunanin idan kuka dawo za ka ci gaba da yin fim ne ko kuma za ka yi wasu abubuwan ne daban?
SANI: To ka san ni dai na farko fim ba shi kadai ba ne sana'ata; ina da sana'a wadda kamar gado ne zan ce na gada. Shi ne wanda a lokacin da aka yi bikin Balaraba har kuka yi gugar zana da cewa sai na tuna cewa ni ma tsohon dan tasha ne, ina buga wa tayar manyan motoci iska, da sauransu. To, wannan sana'a din, ita ce sana'ata da na yi gado. Sannan kuma bayan haka ina dan zuwa na sawo kayayyaki haka, ina da experience kadan na bizines haka - na saye-da-sayarwa wanda ya shafi karfe da sauran abubuwa haka. Sannan kuma harkar fim da kake magana, ai babu yadda za a yi harkar fim ta fita a raina domin ba zan manta da fim ba kuma ba zan manta da irin nasarori da na samu albarkacin fim ba. Saboda haka maganar cewa wai zan ci gaba da yin fim ko ba zan ci gaba ba, sai dai mu ce ka sa ido kawai ka yi kallo.
FIM: Yaya batun 'yarka? Ina take?
SANI: 'Yata tana hannun mahaifiyata.
FIM: Ba da ita kuka je ba kenan?
SANI: E to, ba mu taho da ita ba. Dalili kuwa domin ka san na farko ta kai kamar minzalin shekara uku ko biyar a nan gida lokacin da za mu taho. Sannan kuma tafiyarmu ta farko waccan, da ma ba a yi mata biza ba. A lokacin da wannan tafiyar ta tashi na san cewa bizarta ba za ta zama wata wahala ba tunda muna da biza ni da Fati, kuma yarinya ce karama, to amma sai nake ganin kamar bata lokaci ne in je hakanan in sa a yi mata biza da sauransu sannan mu zo. Sai nake ganin kamar tsarin tafiyarmu zai iya wargajewa, musamman da wajena da wajen mahaifiyata za ta fi samun walwala. Tunda da ma ko lokacin da suke nan gida ba tana hannunmu ba ne, tana hannun mahaifiyata ne. Kusan komai da komai a dakin mahaifiyata take yi tunda ba ita kadai ba ce, sun kai akalla su biyar wanda jikoki ne a hannun mahaifiyata, kuma kowa ya san Bahaushe yadda yake son zama wajen kaka, da sauransu. Shi ne nake ganin ya fi ma kwanciyar hankali tana tare da mahaifiyata. Dadin dadawa kuma idan muka ce mun zo da ita nan za mu iya samun matsala, kamar nan wurin suna da ka'idoji na cewa yaro karami yana da sharudda masu karfi wadanda suke kana da cikakkiyar kulawa a kan yaronka. Idan ka samu matsala, gwamnatin kasar za ta iya kwace shi. To kuma ka ga muna da burin mu yi abubuwa wadanda suke abubuwan nan idan da yaro muna ganin zai iya rage mana, saboda shi yaron a lokacin da yake bukatar wasu abubuwa sai ya kasance ba mu da lokacin. A takaice dai sai nake ganin ta ya fi sauki ta zauna tukuna; idan Allah ya yarda cewa mu kawo ta nan wurin to lokacin komai mun yi settling dinshi sai mu kawo ta.
FIM: Shin kukan yi magana da mutane a nan gida Nijeriya kamar ta hanyar waya haka?
SANI: E, kusan kullum sai mun yi magana da mutane akalla mutum biyar hudu shida. To amma babbar matsalar da take faruwa a gida, mukan so ma a ce kullum mun yi magana da mutane, to amma matsalar (ita ce) wannan GSM din; yawancin mutanenmu sun fi mu'amala da 'landline' haka nan. Amma mukan yi magana da mutane, don ko jiya da dare mun yi magana da Ali Nuhu, Lilisco, Umar Bawa Dukku, da Maikano na Kaduna, duk a jiya. Sannan mun yi magana da wasu masoyan Fati a Kaduna. Hakanan dai. Kuma ina son wannan lambar (ta waya) ta gida da na ba ka, za ka iya sawa a mujalla don wanda yake son ya yi magana da Fati ko ni kai-tsaye.
FIM: Me za ka ce kan masu yada ji-ta-ji-tar cewa lokacin da kuka isa London kai da Fati kun sha wuya sosai, wai kun yi ta rabe-rabe kun zama kamar wasu 'yan gudun hijira?
SANI: To gaskiya duk wani mutum da ya zo nan Turai, ko waye shi, in dai ba dan masu mulkinmu ba ne, irin 'ya'yan barayin Najeriya kenan, ko kuma 'ya'yan masu hannu da shuni wadanda suka zo don karatu, wato duk wanda ya zo nan gurin wanda zuwan kansa ne, to sai ya sha wannan wahalar ta farko. Ka fahimce ni? Saboda haka wai an zo ana yada ji-ta-jitar cewa muna shan wahala muna menene, ai duk mutumin da ya baro inda iyayensa suke da 'yan'uwansa da duk wani asalinsa, ya zo wani gari wanda yake ba dangin Iya ba ba na Baba ba, to dole sai ya fuskanci wasu matsaloli a farko. Akalla ko ba ka samu wata matsala ba to za ka samu matsala ta rashin sabo da mutanen da ka samu kanka a cikinsu, ba jinsinka ba ba jinsinsu ba, ba ka taba zama da su ba… musamman ma a nan Turai, za ka ga cewa wadanda suka zauna shekara ashirin, talatin, amma kawai suna zaune ne kawai Allah-Allah suke su koma gida, saboda rayuwar yadda take. Rayuwa ce mai dadi, amma kuma wani lokaci akwai wahala a ciki. Akwai takura a ciki, saboda babu ruwanka da kowa kuma kowa ba ruwansa da kai. Wani lokaci in ba mun je makaranta ba ko kuma mun je ziyara wajen Hausawa ba da suke zaune a nan London din, sai mu yi kwana bakwai ba mu yi magana da kowa ba, sai daga ni sai Fati, sai dai in mun je sayayya haka. Ka ga shi kanshi wannan matsala ce ga mutumin da ya saba zama irin na gida (Nijeriya) da za ka yi magana da mutumin da ranka yake so; wata sa'a in ba ka da lafiya a zo a yi ma sannu a duba ka. Kai, abinci a nan in ka yi sai dai ka zubar in ya ishe ka, ba wani wanda zai zo ya ce ka taimake shi ka ba shi. Ka ga rayuwa ce wadda wannan kadai wahala ce.
FIM: Wane sako ne kake da shi ga jama'a masoyanku a nan Nijeriya?
SANI: Ina ganin wannan tambaya zai fi kyau in yi alfarma in ba Fati ta amsa wannan tambayar, domin Fati ita ce take da yawan masoya, domin za ka ga duk wanda zai magana a kan ni da Fati, to kusan zai fi son ya ji maganar Fatin yake son ya ji ko kuma Fatin ta ce wani abu, domin ita ce kamar 'kankat!' inji Ibro.
TATTAUNAWA FATI
Lokacin da za mu fara tattaunawa da Fati Mohammed, na karanta wa Sani tambayoyin da nake son in yi mata, kamar yadda na karanta masa nasa tambayoyin. Kuma ya amince a yi mata wasu daga cikinsu, yayin da ya ki amincewa da sauran. A kan dalilin haka, ya ce tunda Fati matar aure ce yanzu, shi ya kamata ya amsa wasunsu. A cewarsa, Fati "mata ce ta kulle, irin tamu ta nan gida," don haka a cikin tambayoyin da aka tsara yi mata, "wani ma in ka tambaye ta ba ta san shi ba, sai dai in fita in je in dawo in ce mata an yi kaza da kaza, da sauransu." Ya ci gaba da cewa, "Duk wasu abubuwa da ake nema, da ma kafin mu zo na zo na yi kokarin na san wasu abubuwa kafin na zo mu taho. Saboda haka komai da ma mun yi shi ne a tsare, cewa ga yadda za a yi ga yadda za a yi. Don hatta ko ma menene wanda ya kama za a yi magana da Fati, ni ne nake zama kololuwa. Don ko a takardarmu da muke zaune a kasar nan sunana kawai a ciki. Sannan kuma abubuwa da yawa, ko kira aka yi a je wani intabiyu, to yawanci ni zan je in yi wadannan abubuwan. Saboda musamman a nan aka ce kai kana da iyali za ka ga cewa kana da mutunci a wurinsu, kuma za su iya amincewa duk wani abu ka wakilci matarka ka je ka yi har ma ya fi musu haka nan. Saboda haka da yawa, musamman yadda na san rauni kamar namu na matan gida, ba na ce mata lallai mu je mu yi wani abu in ba karatu kawai wanda ya zama dole ba, tunda ba za ka je ka yi wa mutum karatu ba, dole shi ma ya je. Amma duka irin wadannan abubuwan da kake tambaya, a gaskiya zan iya cewa Fati ba ta san wasu a ciki ba."
A karshe dai Sami ya amince ne Fati ta mika sako ne kawai ga masoyanta masu kallon fim da kuma 'yan wasa mata. Daga nan ya mika mata waya, muka tattauna kamar haka:
FATI: Hello.
FIM: Malama Fati, ina wuni?
FATI: Lafiya kalau. Ina gajiya?
FIM: Lafiya lau. Yaya azumi?
FATI: To alhamdu lillahi. An sha ruwa lafiya?
FIM: Lafiya lau. To kamar yadda muka yi magana da shi Sani, ki gaya mana sakonki ga masoyanki da suke son finafinanki lokacin da kike wasan fim.
FATI: To da farko dai zan ce assalamu alaikum wa rahmatul lahi wa barakatuhu. Ina farin ciki kwarai da gaske da godiya ga masoyana da suke Najeriya gaba daya. Ina gode musu saboda suna nuna bakin cikinsu a kan cewa abubuwan da ake cewa: "Fati aurenta ya mutu" ko kuma "za ta auri bature" ko kuma "Sani Mai Iska mijin Fati ya rabu da Fati zai auri wata." To gaskiya babu wannan tare da Fati bare shi Sani. Kuma ina so masoyana su sani, duk wannan ba wani abu ba ne hassada ce da kuma daukakar da Allah ya ba ni. Domin kuwa ba ma Fati ba, shugabanmu Annabi muhammadu sallallahu alaihi wa sallama shi ma ya samu mahassada ballantana kuma wata Fati wadda ba kowa ba ce. Don haka ni ina ga masoyana kawai su gode wa Allah. Kuma ba abin da nake yi illa addu'a; makiyana abubuwan da suke yi min sai in ce ni dai ba abin da zan ce illa Allah Ubangiji ya saka mani kan sharrin da suke min ni da mijina. Wannan abu daukaka ce ta kawo min shi ba wani abu ba. Kuma ina gode musu dari bisa dari. Allah ya bar mu tare, Allah ya bar dankon zumunci.
FIM: Wane sako gare ki ga sauran 'yan fim da ke cikin harkar a yanzu, musamman mata?
FATI: To masoyana 'yan wasa maza da mata ina yi musu fatan suna nan lafiya kamar yadda muke a nan Ingila lafiya. Da farko kuma zan mika gaisuwata ga wadanda suka yi aure, kamar babban yayana Ali Nuhu, ina yi mishi fatan alheri da matarsa Maimuna, Allah ya ba su zaman lafiya. Da kuma sauran 'yan wasa kamar Maijiddar 'Khusufi' da Maryam Mushaqqa, su Zahra'u Shata, da dai sauransu wadanda suka yi aure. Allah ya ba su zaman lafiya; kamar su Misbahu M. Ahmed, shi ma Allah ya ba shi zaman lafiya da matarshi Zainab. Su kuma sauran matan da ba su yi aure ba ina yi musu addu'a Ubangiji Allah ya ba su mazaje nagari. Kazalika mazan su ma Allah ya ba su mata nagari. Da fatan kuma suna nan lafiya kuma ina yi musu fatan alheri. Sannan kuma ina mika ta'aziyyata ga 'yan wasa na babban rashi da muka yi na Tijjani Ibraheem. Allah ya jikanshi Allah ya yi masa gafara, Allah ya sa ya huta, Allah ya sa aljanna ce makomarsa. Akwai kuma wannan 'yar wasanmu Hajiya Hassana 'Mama'; ita ma ina mika ta'aziyyar rasuwarta. Allah Ubangiji ya jikanta da gafara.
FIM: To na gode.
FATI: Okay, to, ni ma na gode. Ga Sanin.
Bayan mun gama tattaunawa da Fati, sai Sani ya yi tsokaci kan dalilin da ya sa mutane masu karanta mujallar Fim a intanet irinsa ba su ganinta a kai a kai. Na gaya masa dalilin, na ce insha-Allah zai ga canji kwanan nan, domin muna kan gyaran matsalar. Jin haka sai ya ce lallai ya kamata a gyara. Ya kara da cewa, "Musamman mutanenmu Hausawa a nan Ingila suna matukar son su rinka karanta mujallar. Kusan ma zan ce ba wani abu da suke son su karanta, wani harka na Hausa ba ma dirama kawai ba, kamar mujallar Fim."
Bayan haka Sani ya ba mu shawarar mu rika buga labaran wasu abubuwan a cikin mujallar, ba labaran shirin fim kadai ba; misali labaran siyasa a Nijeriya. A nan sai na amsa da cewa yin hakan ba zai yiwu ba domin manufar kafa Fim tun asali shi ne ta ba da labarin harkar fim din Hausa kadai, shi ya sa ma sunanta yake Fim. Na nuna masa yadda muka fito da filin adabi kwanan baya domin mun ga akwai alaka tsakanin marubuta da 'yan fim (marubuta ne suka kafa industiri din, kuma har yanzu akwai su da yawa a ciki). "To amma idan muka sa kamar labarin wasanni, to mujallar za ta zama wani abu kenan." Na kuma nuna masa cewa yawancin masu karatunmu sun fi son su ga labarin 'yan fim din.
Sani ya fahimci haka, ya ce da ma ra'ayinsa ne kawai ya furta.
Daga nan ya mika sakonsa ga iyalai da masoyan marigayi Tijjani Ibraheem da Hajiya Hassana kan babban rashin da aka yi. Haka kuma Sani ya mika sakon taya murna ga 'yan fim da suka yi aure, irin su Shu'aibu Lawan, Hajiya Hajara Usman, Ali Nuhu, Misbahu M. Ahmed, A'isha Ibrahim, A'isha Musa, Wasila, Hadiza Kabara, Maryam Mushaqqa, Maijidda Ibrahim da Zahra'u Shata. Ya yi fatan Allah ya ba su zaman lafiya baki dayansu. Ya ce idan sun zo Nijeriya za su bi su daya bayan daya su yi musu murna.
A karshe na yi wa Sani da Fati godiya kan yadda suka yi wannan tattaunawar da mujallar Fim, ina mai nuna da cewa hirar za ta taimaka wajen kashe ji-ta-ji-tar da ake yadawa game da su. Daga nan shi ma Sani ya gode mani kan yadda muka tsaya kai da fata wajen kare mutuncinsu shi da Fati, da kuma yadda muka ki yarda mu yi shaci-fadi kan al'amarinsu kamar yadda wasu mujallu suka yi.
Muna daf da yin sallama kuma sai Fati ta karbi wayar, ta ce ta yi mantuwa ne ba ta isar da sakon musamman don taya murna ba ga Mama Hajjo, Shu'aibu Lawan Kumurci, da Hadiza Kabara kan auren da suka yi. A karshe ta ce, "Sannan kuma ina yin addu'ar Allah Ubangiji ya kara daukaka mujallar Fim."
To, Fati da Sani, mu ma mun gode.
Lambar Tarhon Gidan Fati da Sani
Ga lambar wayar Sani Musa Mai Iska da Fati Mohammed a gidansu a London saboda mai bukatar yi musu waya. Ka jarraba ka gani: (44) 1733330197
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|