Lilisco da Zulai
Auren Ban Mamaki
Lilisko (rike da hannun zulai ) suna cashewa a wurin piknik
|
"Tun da na tashi a unguwar nan, ban taba ganin daurin auren da ya yi armashin wannan ba!"
WANI dattijo ne aka ji ya ambaci haka a cikin taron daurin auren fitaccen dan wasan fim kuma gwanin koyar da rawa, wato Idris Shu'aibu (Lilisco) da fitacciyar jarumar finafinai, Zulai Dalhat. An dai daura auren ne a gidan iyayen amaryar wanda ke kan titin Bida a cikin garin Kaduna, a ranar Asabar, 13 ga Disamba, 2003 da misalin karfe 2:30 na rana. Daurin aure ne wanda ya burge mahalartansa, ya ba da mamaki, har ya sa wasu matasa (maza da mata) suka rika cewa, "Da ma a ce mu ne!"
Wannan aure, ya faru ne bayan dimbin tsare-tsare da gayyata wadda ango da amarya da abokansu da iyalansu. Lilisco da abokansa sun dinga zuwa Kaduna, sa'annan ita ma Zulai, wadda ta yi fara yin fice ne a fim din "Illah," takan dan leka Kano gun angon domin su tsara yadda za a yi. Wannan tsarin ne ya sa Lilisco da abokansa suka shirya bikin kalankuwa na 'yan fim, wato 'gala,' a Kano, kwanaki kadan kafin ranar daurin auren. Kwamitin abokai da kamfanin shirya fim na 'Handsome Chico Production,' Goron Dutse, sun shirya bikin a gidan sinima na Lale a karkashin jagorancin shugaban kamfanin, wato gwanin kidan finafinai din nan Muktar Musa Kwanzuma. A bikin, wanda aka fara da karfe 4:30 na yamma, an fara da gabatar da raye-raye daga 'ya'yan kungiyar ta 'Handsome Chico'. Daga nan aka gayyaci abokin ango, Muntari Tholes tare da A'isha Mika'il suka yi rawar wakar wakar "So Salo-Salo, kauna Salo-Salo" ta cikin fim din farko mallakar Lilisco, wato "Salsala." Wannan wakar ta kasance taken wannan bikin baki dayansa tun daga farkonsa har karshensa.
Sauran wadanda suka yi rawa a wajen sun hada da Danmage shi da A'isha Superstar wadanda suka yi rawar fim din "Ja'iza", sai Aminu Mai Dawayya da Rahama Isa da suka yi rawar fim din "Hasken Ma'aurata," sai kuma Ahmed S. Nuhu da Maryam suka taka rawa fim din Adamseyalo. Daga nan sai Rabilu Musa (Ibro) da Hussaina Gombe (Tsigai) suka gabatar da wani wasan ban-dariya da suka gutsuro daga cikin fim din "Kauran Mata." Shi ma ango tare da A'isha Superstar, wadda ake kira "A'ishar Lilisco" saboda zumuncinta da shi, sun taka rawar "Kauna Salo-Salo." Bayan nan kuma sai shi da A'isha Mika'il suka taka rawa wakar "Bazar Kowa" ta cikin "Salsala".
A karshe Lilisco da Muntari Tholes da Maijidda Abbas suka taka rawar sabon fim din nan wato "Cashewa." Mawaki mai suna Adamu Mohammed ne ya gabatar da taron. Bikin ya kayatar sai dai a karshe 'yan kallo sun yi cirko-cirko suna jiran sai an bude musu kofa sun ga 'yan wasan, musamman Ibro. Da kayar aka fitar da 'yan wasan ba tare da 'yan kallon sun sani ba.
Wannan gala ta bude kofar bikin, ta gabatar da shi ga jama'a. Daga nan ne sai hankali ya koma Kaduna, inda a tsarin da aka yi an nuna cewa a can ne za a gwangwaje sosai. Abin da 'yan fim kan tambayi kansu a Kano shi ne, "To, yaya, za ka je Kaduna din?" Abin da ake sanyawa a rai shi ne yawon 'picnic', wato kilisar auren zamani ta 'ya'yan zamani, inda akan ci direshi na kece raini, 'yanmata da samari su fice daga gari zuwa wani kebattaccen wuri a bayan gari, su cashe. A ranar 11 ga Disamba, 2003, ne aka yi fikinik din bikin na Lilisco da Zulai. A wannan ranar, a gaskiya in da a ce bako zai dira Kaduna daga wata jiha, to zai iya zaton watakila sau biyu aka yi bikin Karamar Sallah a garin na Gwamna. Tun misalin karfe 10:30 na safe, 'yammata da samari suke ta karakainar shirye-shiryen zuwa kilisar bikin Lilisco da Zulai, wanda aka yi a wani wurin shakatawa na musamman da ke kimanin kilomita 25 daga Kaduna zuwa Abuja, wanda ake kiria 'Bush Farm.'
Kusan duk wanda yake ji da kansa a industiri bai yarda an bar shi a baya ba, musamman 'yan Kano. Launin fata kawai ya kawo cikas, amma da sai ka rantse da Allah turawa ne suka shirya wannan bikin. 'Yan fim mata da wadanda ba 'yan fim ba, mafi yawanci zanzaro suka yi da wandon jins wanda ake ya yi da kuma irin rigar nan 'yar mitsil wadda ake kira 'body-hug'. Wasu kuma siket suka matse jikinsu da shi, suka yi irin shigar nan da suke yi wa lakani da 'gani-nan-bari-nan'. Wata ma da ta zo da wani dan gyale a wuyanta, fizge gyalen wasu 'yanmata suka yi, suna cewa za ta bata musu biki.
'Bush Farm' dai ya fara dibar baki tun daga misalin karfe 4:30 na yamma. Kafin ka ce kwabo, wuri ya cika makil da jama'a. Ango da amarya ba su samu isowa ba sai wajen misalin karfe 7:30 na yamma. Da zuwansu, babu wani bata lokaci, sai darakta Salisu Mu'azu ya fara gabatar da Ali Nuhu da darakta Saminu Mohammed Mahmud. Bayan nan sai ya wuce kai tsaye ya kira ango da amarya, suka shigo tsakiyar fili. Amaryar ta yi wata irin shiga ta turawa da wasu tsadaddun kaya, irin shigar nan da mata ke kira "Ina-na-rage?" Lilisco yana rungume da ita, aka gabatar da su. Bayan an gama murnar shigowarsu, sai mai gabatarwa ya nemi a goce da kidan wakar "Kauna salo salo" ta cikin fim din "Salsala" (wakar da Lilsco da Zulai suka rera a fim din), su kuma su rera waka. To, ka san mutum da sana'arsa, Lilisco dai ko karar zubar kudi ya ji a kasa sai ya taka rawa. Ai fa sai suka goce da rawa da waka shi da Zulai. Sun sha likin kudi kamar ruwan sama daga 'yan'uwa da abokan arziki.
Bayan sun gama, sai sankiran bikin ya fara kiran fitattun 'yan fim suna taka rawa; kowane dan fim da yarinyar da ta kwanta masa a rai. Misali, Ali Nuhu ya fado fage rike da hannun A'isha B. Umar, jarumar "Daren Farko", suka gwangwaje da rawa kai ka ce su ake yi wa bikin. Saminu M. Mahmud shi ma ya shiga fili da wata wai ita A'isha Superstar, suka baje kolinsu. Haka dai shagali ya yi ta tafiya har zuwa lokacin da aka tashi wajen karfe 9:30 na dare. Taro kuma ya tashi tafiya, kowa na sambarka, musamman 'yan Kaduna, wadanda suka ce wannan shi ne biki na farko da ya shafi 'yan Kano wanda aka nuna an san da su, wai saboda duk sa'ilin da aka nemi 'yan Kano biyu, to sai an nemi dan Kaduna daya.
Washegari kuma aka yi lancing ('luncheon'). Ga duk wanda ya samu halartar wannan lancin di, to ya san akwai bambanci da wadanda aka taba yi a baya. An yi bikin a wani dandalin shakatawa da wasannin gargajiya da ke unguwar Barnawa, Kaduna, wato 'Space 2000'. Akalla mutum dubu daya sun halarci wurin.
An fara gudanar da bikin da misalin karfe 6:43 na yamma. Shigowar ango da amarya ke da wuya sai wuri ya dauki ihu da shewa na masoya, musamman ganin irin shigar da ma'auratan suka yi. Lilisco ya sanya manyan kaya na farar shadda, wadanda babbar rigar aka rangada wa wani irin aiki da bakin zare, da alamar ma a ranar aka gama shi. Ita kuma amarya ta sha wani leshi mai tsada na kece-raini mai ruwan madara da adon digon koren zare a kansa, sa'annan ta rangado wani irin gwaggwaro mai sa mahassada cizon yatsa. Bayan sun zauna sai masu gabatarwa, Tijjani Paris da Yahuza A. Ilu suka shiga aikinsu. Daraktan daraktocin Jihar Kaduna, Saminu M. Mahmud, shi aka kira ya bude taro da addu'a. Daga nan sai aka gabatar da Ali Nuhu a matsayin babban abokin ango, yayin da aka kira Zainab Mohammed a matsayin babbar kawar amarya. An kuma gabatar da fitattun 'yan fim kamar Rabi'u Ibrahim HRB, Hafizu Bello, Ahmed. S. Nuhu, Baballe Hayatu, Misbahu M. Ahmed, Ibrahim Mohammed Mandawari, Muhibbat Abdussalam, Safiya Musa, Yakubu Lere, Usman Kabara, A.S. Mohammed, Aminu Bala, Hawwa Maina, Umar Binta Investment, Salisu Mu'azu, Barrister, Rabi'u Rikadawa, Abubakar Yusuf Ladan, Aminu Mirror, Lawal Ahmed da kuma Aliyu Abdullahi Gora II. An cashe da kade-kade da raye-raye, musaman na wakokin finafinai kamar su wakar "Kauna salo-salo" da wakar "Ba ji ba ji ba" ta cikin shirin "Kauna."
Wata kuma tawagar 'yan koroso da suka zo daga Kano wadda aka ce ta Lilisco ce, su ma ba a bar su a baya ba, domin sun bar mutane da baki hangame suna mamakin wata irin rawar sai da rai da suka rika yi. A wurin, Lilo, wanda aminin ango ne, ya ba da sha'awa da rawarsa.
Bayan nan kuma an kaddamar da kalandar ango da amarya. Babban mai kaddamarwa shi ne furodusan fim din "Rimi-Rimi," wato Bawa Chocho, wanda ya sayi kalanda a kan N30,000. Rabi'u Ibrahim ya saya a kan N20,000. Sauran sun hada da Ali Nuhu -N10,000; Hawwa Maina - 2,000; Yusuf Barau - N2,000; Salisu Mua'azu - N4,000; Amina Garba (Dumba) - N2,000; Aminu Busy - N3,000; Ibrahim Mandawari - N1,000. Jimillar kudi N84,000.
Da aka kare sai masu gabatarwa suka umurci ango da amarya da su shigo tsakiyar fili su rera wakar "Kauna salo salo". Sun fito sun rausaya, kuma sun sha liki, abin sai wanda ya gani. Wani abin ban sha'awa shi ne, duk da yawan taron ba a samu tashin hankali ba ko miskala zarratin. Motoci 48 aka halarci bikin da shi.
Da misalin karfe 9:47 aka tashi, kowa ya kama gabansa.
Da gari ya waye ne aka daura auren. Wani mutum mai suna Malam Hassan ne waliyin amarya yayin da Malam Muhammad Sabi'u ya kasance waliyin ango, ya kuma karbar wa Lilisco mata a kan sadaki N10,000 lakadan. An kuma raba wa jama'a huhun goro daya, da katan daya na minti tare da mudu daya na dabino. Irin dimbin mutanen da suka halarci daurin auren ya kara tabbatar wa jama'a da cewa lallai Lilisco mutumin mutane ne. An kwashe kimanin minti 30, da yawa ba su san ana gama daura auren ba.
Duk wani dan fim da yake ji da kansa ya halarci taron, wanda ya jawo cinkoson mutane masu so su su gan su har da matan aure daga gidaje mazajensu. Furodusoshi, daraktoci, 'yan wasa da kuma 'yan kasuwa da suka halarci daurin auren sun hada da Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, wato Hamisu Lamido-Iyan-Tama, da Shugaban Kungiyr Furodusoshi ta Jihar Kano, Ibrahim Mandawari, da Ya'u Koli, Mohammed Amge, Hafizu Bello, Kabiru Karama, Dan'azimi Baba Chediyar 'Yangurasa, Yakubu Lere, Kabiru Maikaba, Kabiru Nakwango, Mohammed Garba Kabara, Abdurrasheed Kankia, Hussaini Sule Koki, Mu'azzam Boss, Tijjani Paris, Barrister Ali Lawan, Saminu M. Mahmud, Mahmud Hameed, Ibrahim Sheme, Haruna Danjuma, Magaji Mijinyawa, Jibril S. Fagge, Adamu Kwabon Masoyi, A.A. Kurawa, Misbahu M. Ahmad, Mamuda Isyaka, Tukur Aliyu, Nata'ala Aliyu, Galin Money, Adamu Bello Ability, Rabi'u Koli, Umar Muh'd Binta Investment, Labaran Ali, Rabi'u Ibrahim, Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, da sauransu.
Jim kadan da gama daura auren, ana cikin rugundumin bikin, sai 'yan asharalle suka goce da kida, mata na gwangwajewa, wuri ya yamutse. Kwatsam, sai ga ango ya keto taro a cikin wata kwankwatsetsiyar mota kirar Honda, mai lamba EJ 659 KJA. Yana sanye da wata tsadaddar shadda mai ruwan bula, babbar riga da jamfa mai gajeren hannu, an rataya masa wani koren tambari mai dauke da hotonsa da na amaryar.
Fitowarsa ke da wuya sai jama'a suka yi masa caa, kowa na kokarin ganin sun hada hannu an gaisa. A cikin wannan halin ne, yana kyalla ido sai ya hango sahibarsa cikin fararen kayan Fulani, tana cashewa da rawa a gaban mai asharalle. Gogan naka, bai tsaya wata-wata ba sai ya tunkari wajen. Da zuwansa, sai ya farke wani bandir na sababbin kudi 'yan naira goma goma, bai sauke hannun ba sai da suka kare.
Gidan iyayen amaryar kuwa cike yake dankam da mata ba masaka tsinke. Tsananin murna da jin dadi ya sa uwar amaryar kuka, musamman idan aka yi mata gaisuwar taya murna. Haka dai bikin ya yi ta tafiya, har zuwa misalin karfe 4:00 na yamma, jama'a ba su tsunke daga kofar gidan ba. Daga cikin masoyan ma'auratan da suka halarci bikin kuwa, wasu har daga kasashen ketare suka zo, kamar Nijar, Kamaru da Chadi,
Da yamma kuma aka shirya wata gasar kwallon kafa ta musamman a filin wasan kwallon kafa na Ranchers inda aka kara tsakanin 'yan fim na Kano da na Kaduna. Tun da misalin karfe 3:40 filin ya fara cika da jama'a maza da mata, ciki kuwa har da 'yan wasan nan da suka yi aure, wato A'isha Ibrahim da A'isha Musa, kowace tana rungume da 'yarta. 'Yan fim sun yanke hukuncin shirya kwallon ne tsakanin garuruwan biyu musamman a kan dalilai biyu. Na farko don karfafa zumunci, na biyu kuma don kara armashi a bikin auren 'yan'uwansu Lilisco da Zulai.
Duk da cewa an tsara cewa za a fara kwallon da karfe 4:00 na yamma, hakan ba ta samu ba sai wajen karfe 5:15, lokacin ma har an soma buga wasan. Karfe 5:35 daidai ango da amarya suka shigo fili, inda aka dauke su kai tsaye zuwa tsakiyar filin, bayan an dan dakatar da wasan na dan wani lokaci musamman don a girmama zuwansu.
Ba tare da bata lokaci ba sai alkalin wasan, Malam Abdurrahman Tonga, ya umurci ango da amarya su sa albarka. Lilisco ya fara sa albarka, inda ya harba wa Zulai kwallon, ita kuma ta mayar masa. Fili ya dauki tafi. Bayan ma'auratan sun fita daga tsakiyar filin sai aka ci gaba da fafatawa.
Duk da cewa wasa ne na nishadi, jaruman Kaduna sun tagayyara, wanda ya sa tilas suka surka da kwararru, wasu ma daga sanannen kulob din nan suke, wato Rancher's Bees, amma duk a banza. Da wuta ta yi wuta, sai 'yan Kaduna suka rika tura 'yan wasa ta bayan fage, wanda ya sa mutum 14 ya buga wa Kaduna, yayin da 'yan Kano ke da mutum 11.
Kanawa sun nuna wa 'yan Kaduna cewa lallai ko da me ka zo sun fi ka, domin duk da yake dai ana daukarsu kamar 'yan baragada, can daidai karfe 5:57, sai gwanin rawar nan Lilo ya kwace kwallo. Bayan ya gama koya mata rawa a tsakiyar fili, sai ya cilla ta zuwa barayin 'yan Kaduna, inda Saraki bai tsaya wata-wata ba ya tafka ta a raga. Sai ihu ya cika wurin. 'Yan Kaduna sun dauki duk matakan da ya kamata don ganin sun rama cin, amma hakan ba ta samu ba, har zuwa lokacin da alkalin wasa ya busa usur karfe 6:04 daidai. Nan da nan fili ya cika. Kanawa suka goce da kidan koroso, su Ali Nuhu suka cashe. Har zuwa lokacin sallar Magariba dai wurin cike yake da jama'a maza da mata.
Lokacin da ake watsewa, an ji wani furodusa mazaunin Kaduna yana ce wa Saraki, "Haba Saraki! Ai ba ku kyauta ba. Ci biyu fa kuka yi mana." Da ya ga dan wasan bai fahimce shi ba (domin kwallo daya rak ya san sun jefa a raga), sai ya ce masa, "Na farko dai mun ba ku kyakkyawar mata za ku tafi da ita Kano; sa'annan kuma sai ku ci mu a kwallo? Wannan ai shi ne ci biyun!"
Wannan dai shi ne shagali na karshe da aka shirya a bikin a Kaduna. Washegari, ranar Lahadi, 14 ga Disamba, da misalin karfe 12:30 na rana, angwaye suka dauke amaryarsu zuwa Kano.
To, sai dai kuma ba a nan shagalin ya kare ba, domin fa can ma a Kanon ana jiran a zo da amarya domin a ci gaba da rugundumin bikin. Da tawagar ango da amarya suka rankayo zuwa Kano an dada cashewa a karo na karshe a kulob din 'Alliance Francaise' wanda ke kan titin Magaji Rumfa. Tun da misalin karfe 7:30 na Magariba aka fara shirya wannan gida don yin taron walima. 'Yan'uwa da abokan arziki sun fara halartar wajen tun wajen karfe 8:30. Tawagar Kaduna ta iso wurin da karfe 9:00. Sun hada da Al-Amin Ciroma, Saminu M. Mahmud, Rabi'u Koli, sai kuma wasu gungun sojiji da aka yiwo guzurinsu daga Kaduna don yin tsaron kofar shiga kulob din (domin ba a ma son wani a Kano ya san sojan da ke wurin ballantana ya yi masa tsaurin ido ko kuma ya roke shi alfarmar shiga ba tare da ka'ida ba). Mahalarta daga Kano sun hada da Hafizu Bello, Ali Nuhu, Sani Danja, Yakubu Muhammad, Hussaina Tsigai, Amina Garba, Fati Baffa, Baballe Hayatu, da sauransu.
An fara raye-raye tun kafin isowar ma'auratan. Aminu Mai Dawayya ya fara washe filin da wakoki daban- daban. Bayan isowar Lilisco da Zulai ne kuma sai aka ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka kamata. Fitaccen dan wasa Malam Isa Bello ne ya bude taron da addu'a, bayan nan aka gabatar da manyan baki da za su zauna a kujerun manyan baki. An fara da kiran Ibrahim Mandawari, sai shugaban kungiyar 'yan wasan Kano, wato Shu'aibu Yawale, sai Rabi'u Koli, Ali Nuhu, Umar Mohammed Binta Investment, Balaraba Ramat Yakubu, Umma Ali, Jamila Haruna, Amina Garba, da babbar kawa Zainab.
Daga nan sai aka ba Shu'aibu Yawale fili ya ba da takaitaccen tarihin ango, na amarya kuma Zainab ce ta ba da shi. 'Yan koroso daga karamar hukumar Wudil sun cashe a wajen, da suka kare kuma sai aka ci gaba da rera wakokin finafinai, inda Saima Mohammed Raga da Baballe Hayatu suka yi wakar nan ta Kumbo, sai Ali Nuhu da Fati Baffa Fagge suka yi wakar "Shan koko." Shi ma Sirajo Mai Asharalle Katsina, ba a bar shi a baya ba, domin ya cashe da wakokinsa. A wurin, akwai shahararren mawakin nan Sa'adu Bori, wanda aka gabatar tare da maidakinsa da 'yarsu (amma bai yi waka ba). Sai aka yi wakar "Eba-ebana" wadda Sani Danja da 'yanmata suka yi. Jarumin shirin "Ruda," wato Abba El- Mustapha, Ali Nuhu da Fati Baffa sun yi wakar fim din "Makamashi", har ango da amarya suka rika bin wakar a kan kujerunsu a zaune. An kuma cashe da wakar "So salo-salo," taken da ango da amarya suka yi ta bi daga zaune har suka kagara suka shigo filin, suka dan taka. Ko da Zulai ta ga Lilisco ya zake sai ta janye shi suka koma suka zauna. Haka dai aka yi ta biki har zuwa karfe 1 na dare sa'annan kowa ya nemi inda ya fito, na nesa kuma suka koma masauki.
A Kaduna, babban abokin ango, wato Ali Nuhu, ya bayyana farin ciki kan wannan biki na Lilisco. Ya fada wa mujallar Fim cewa, "A gaskiya wannan biki ya kayatar da ni kwarai da gaske, ba don komai ba sai ganin yadda aka tsara shi, da kuma yadda aka gudanar da shi lami lafiya. Kuma ina so in ja hankalin ango da amarya a kan hakuri da zama da juna. Domin hakuri shi ne ginshikin kowane aure. Sannan kuma irin hadin kan da 'yan fim da kuma dangin amarya suka ba da ya ba mu mamaki, ya kuma burge mu. Allah ya bar zumunci, su kuma ma'auratan Allah ya zaunar da su lafiya."
To mu ma mun ce amin summa amin. Bikin I.S. Lilisco da Zulai Dalhat kenan. Yanzu dai komai ya lafa, ba abin da ya rage sai su ci gaba da cin duniyarsu da tsinke a cikin dumin aurensu, tare da hakuri da juriya da kai hankali nesa. Mu kuma sai mu ce Allah ya ba su zaman lafiya tare da karuwar arziki, amin.
Ba zan nuna bambanci tsakanin Zulai da uwargidata ba - Lilisco
Idris Shu'aibu Lilisco ya jima yana fafutikar ganin ya auri 'yar fim. Akwai 'yan fim mata da yawa da ya so ya aura, kamar su fitacciyar jaruma Maijidda Abdulkadir, amma Allah bai yi da shi ba. A yanzu da rabonsa ya tsaga a Kaduna, ya gaya wa Mataimakin Edita ALIYU A. GORA II asalin soyayyarsu da Zulai Dalhat da kuma fatansa kan wannan auren:
FIM: Lilisco, muna mika sakon taya murna a gare ka.
LILISCO: To, na gode kwarai da gaske.
FIM: Zan so mu fara da jin ta bakinka game da wannan muhimmiyar rana ta bikin aurenka da Zulai Dalhat.
LILISCO: Babu shakka wannan muhimmiyar rana ce a gare ni da ba zan taba mantawa da ita ba. Domin ko ba komai, na san dai ina da aure na farko yau misalin shekara biyar kenan, kuma muna zaune lafiya da matata Sa'adatu, kuma muna da da daya mai suna Shu'aibu, wato sunan mahaifina, wanda saboda haka ne ma muke kiransa Abba. To kuma ga shi Allah ya kawo mu wannan rana zan kara aure, wanda ba zan iya misalta iyakar farin cikin da ke cikin zuciyata ba. Sai dai in ce Allah ya kara tabbatar mana da alherinsa.
FIM: Za ka iya tuna sanadiyyar huduwarka da Zulai?
LILISCO: Haduwarmu da Zulai haduwa ce wadda sai dai mu ce ikon Allah ne. Zulai ba ta taba ganina ba sai ta harkar fim, ni ma inda na fara ganinta shine a fim din "Illah", amma babbar sanadiyyar haduwarmu ita ce a lokacin da mujallar Fim ta ba mu kyaututtukan karramawa.
FIM: Ya za ka iya kwatanta farin cikinka a kan wannan auren da kuma aurenka na farko?
LILISCO (ya yi dariya): A zahiri a lokacin da na yi auren farko, duniya ba ta san ni ba, ina harkar fim amma ba na fitowa a fim. To ka ga kuma a wannan lokacin ba ni da jama'ar da suka san ni, na yi fice kuma ake son ganina kamar yanzu, to ka ko ga akwai bambanci.
FIM: A wane gari za ka aje Zulai?
LILISCO: A'a, kai ma ka san Kano zan kai ta. Idan mutum ya je farauta ya samo ba gidansu zai kai ba? Ni ma gidanmu zan kai!
FIM: Amma kafin zuwan wannan rana, ka taba samun labarin ana cewa ba aurenta za ka yi ba, wai yaudararta kawai kake yi?
LILISCO: Na ji wannan labari ya fi a kirga. Ina ganin ko a nan Kaduna akwai 'yammata guda hudu wadanda suka furta cewa ba aurenta zan yi ba, yaudararta kawai nake yi. Kai har cikin mazan ma akwai, kai har Kano ma.
FIM: Yanzu menene matasayin sauran dimbin 'yanmatanka wadanda Zulai ta kasa?
LILISCO: To, ka san dai yadda abin yake, kuma shi aure ai nufi ne na Allah, sai dai mu ce Allah ya hada kowa da rabonsa.
FIM: Ka taba samun matsala da 'yanmata game da soyayyarka da Zulai?
LILISCO: E, matsaloli da yawa gaskiya na fuskanta. Domin ka san shi halin rayuwa, duk mutumin da kake so har zuci, kuma ka ga wani na sonsa, to dole kishi ya shiga. Wajen sau uku ina samun matsala, amma da yake Allah ya nufi ita ce matata, ka ga na aure ta.
FIM: Me ya sa ka tsallake Kano ka zo Kaduna ka yi aure?
LILISCO: Ina so ka fahimci wani abu daya, da dadewa na taba gaya maka cewa na nemi Maijidda Abdulkadir, kuma a lokacin burina shi ne in aure ta, Allah bai yi ba. Kuma cikin 'yan fim na Kano a cikin goma, ina tabbatar maka duk wadda ka gani sai ka yaba, kuma sai ka so ta a zuciya. Amma da yake shi aure nufi ne na Ubangiji ka ga sai ya kaddaro a Kaduna zan yi auren.
FIM: Idan muka yi la'akari da abin da ya faru ga Sani Mai Iska da kuma Hamza Mohammed Danzaki, wadanda duk abokanka ne, a lokacin da suka sabunta mata duk sai suka kori na da. Shin kai ma haka za ka yi?
LILISCO: Wallahi har ga Allah, ni a zuciyata, idan da misali zan ba ka dama ka je ka samu matata uwargidana, ka yi mata tambaya, ta san ni mutum ne mai adalci daidai gwargwado, kuma ta san duk wadda zan auro in kawo mata, ba zan nuna bambanci a tsakaninsu ba. Dukkansu daya ne gare ni, ba wadda ta fi wata, ni ba ra'ayina kenan ba. Kuma kamar Sani Mai Iska da ka ambato, ai ba Talatu kawai ya taba aure ba, matarsa ta farko ita ce Habiba, wadda ya saki a lokacin da ya auri Talatu. 'Ya'yansu biyu da ita, ita kuma Talatu ya sake ta lokacin da ya auri Fati.
FIM: To maganar fim fa, za ka bar Zulai ta ci gaba ne ko za ka hana?
LILISCO: Ka san zamanin yanzu, in kana da sana'a, kuma in har za ka iya barin matarka ta taya ka wannan sana'ar, in dai ba haram ba ce to ba laifi ba ne. A kan sana'ar nan aka san ni, ita ma haka. Saboda haka idan na ga zuciyata ta ba ni in bar ta ta yi, sai in bar ta.
FIM: Me za ka ce game da gudunmawar da 'yan'uwa da abokan arziki suka ba ka a kan wannan al'amari?
LILISCO: Ni dai wallahi abin da jama'a suka yi mani a gaskiya ya wuce in ce na gode kawai, sai dai in hada su da Allah ya yi masu sakayya da alherinsa. Allah kuma ya mayar da kowa gidansa lafiya.
FIM: To Lilisco Allah ya zaunar da ku lafiya.
LILISCO: Amin amin. Na gode.
Na sha wahala kan Lilisco,inji Zulai
Amaryar Lilisco, Zulai Dalhat, ita ce har wa yau jarumar shirin Salsala, fim din farko da shi Lilisco ya shirya kuma ya mallaka, inda suka fito tare a matsayin masoya. Ita ma ta tattauna da ALIYU A. GORA II a kan soyayyarta da jarumin nata, da fatanta game da auren:
FIM: Malama Zulai, muna taya ki murnar zuwan wannan rana ta aurenki da Lilisco.
ZULAI: To na gode kwarai da gaske, na ji dadi wallahi.
FIM: To, ga shi yau Allah ya kawo mu wannan rana kin tabbata matar Lilisco. Me za ki ce, musamman in za ki iya tuna abubuwan da suka wakana tun daga ranar haduwarku zuwa yau?
ZULAI: To, ni dai ba abin da zan ce, sai dai... Ka san shi aure nufi ne na Allah. Tun farkon haduwata da Lilisco zuwa yau, ba irin abin da ban ji ba, ba kuma wanda ban gani ba, to da yake Allah ya yi mijina ne, ka gani ga shi an yi.
FIM: Za ki iya tuna yadda kika hadu da shi kuka fara soyayya har ta kai ga aure?
ZULAI: E, akwai bikin da mujallar Fim ta taba shiryawa a Kano inda ta ba da kyaututtuka ga mawaka da makada. To muna cikin mota a kan hanyar zuwa Kano, su kuma (su Lilisco) suna cikin motarsu daban, to ashe da ma shi ya taba ganina a inda aka yi editin fim din Illah, to tun daga lokacin, suna tare da Umar na Binta Investment, ni a lokacin ma ban san shi ba, ban san ma dan fim ba ne, sai na ga ana daga mani hannu. To a cikinsu Umar kawai na sani, sai suna nuna ni; ni ma sai na daga masu hannu. To bayan mun isa Kano, muna cikin dakin da ake bikin, sai na ga ya zo ga gaishe ni har sau uku, ni kuma ban san shi ba. To sai da muka fita waje sai ya same ni ya shaida mani cewa yana sona. Nan dai ya ba ni adireshinsa, ni ma na ba shi nawa. Ka ji haduwata da shi.
FIM: Kin taba fuskantar wasu matsaloli a kan soyayyarki da shi?
ZULAI: Gaskiya akwai matsaloli da yawa, saboda wallahi na sha wahala! Tun fa daga Kano ake yo takakkiya zuwa gidanmu a nan Kaduna wai za a ci mani mutunci in ban rabu da shi ba. Amma da yake Yaya Gora ka san ni ba na fada, ko dangina in sun taso ni ke tausarsu. Da kuma masu nuna mani cewa su masoyana ne a fuska, masu zuwa su ce mani wai Lilisco ba aurena zai yi ba, yaudarata kawai yake yi, saboda haka in fita harkarsa kawai... Kai, ba irin zagin da ban sha ba a kan Lilisco!
FIM: Ashe kin sha artabu da 'yanmatansa?
ZULAI: Babu shakka ina kishin Lilisco, to amma saboda na san 'yanmatan su suka kawo kansu wajensa, ba shi ya ce yana son su ba, don haka ban samu wata matsananciyar damuwa ba. Suna nuna kishi a kaina sosai, don har barazanar dukana sun sha yi.
FIM: Maganar da kika ce ana gaya maki game da Lilisco cewa yaudararki yake yi, hankalinki ya taba tashi a kanta?
ZULAI: A gaskiya ta tayar mani da hankali, tunda har gida ake zuwa a gaya mani.
FIM: Yanzu me za ki ce wa masu gaya maki wannan magana?
ZULAI: Sun ji kunya, ai an kashe bakin tsanya, kuma wallahi har yanzu da su ma ake hidimar bikin nan!
FIM: Ga shi ke ba ki taba yin aure ba, kin zo kuma kin auri mai mata. Ke ba ki da ra'ayin 'yan zamani ne?
ZULAI: To ai aure nufi ne na Allah, kuma shi na ga ya dace da ni... (ta yi dariya)
FIM: Za ki iya tuna ko mutum nawa Lilisco ya kasa kafin ya aure ki?
ZULAI: A gaskiya idan na ce ga yawan samarin da ya kasa na yi karya, domin ni kaina ban san iyakar yawan samarina ba wallahi. Wasu ma sai mun hadu su tuna mani cewa ai su samarina ne.
FIM: To yanzu kin yi bankwana da shirin fim kenan ko za ki ci gaba bayan bikin aurenku?
ZULAI: E, gaskiya na daina, amma ina da burin zama furodusa nan gaba.
FIM: Za ki iya tuna fim dinki na farko da kuma na karshe?
ZULAI: Fim dina na farko shi ne Illah, amma na karshen a Zariya na yi shi, kuma gaskiya ban san sunan da za su sanya mashi ba.
FIM: Me za ki ce wa 'yan'uwa da abokan arziki da suka halarci wannan biki naki?
ZULAI: Ni dai ba abin da zance sai dai in ce wa masoyana na gode Allah ya saka da alheri. Su kuma makiyana sai in ce don Allah su yi hakuri... (tana dariya) ... su ma su rika sona tunda yanzu dai bakin alkalami ya bushe.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|