Yadda hadarin ya faru
Tare da babban wan su Balaraba, Abdullahi Mohammed (wanda ake fi sani da lakabin Riskuwa) aka yi hadarin. A lokacin da motar ta yi kundumbala ta kife, shi kadai ne ya rage a ciki. Riskuwa, wanda soja ne a Kaduna, ya tattauna da mujallar Fim bayan kwana uku da hadarin.
FIM: Malam Abdullahi, mu 'yan mujallar Fim muna yi maka ta'aziyyar rasuwar 'yan'uwanka tare kuma da yi maku jaje ku da kuka ji munanan raunuka. Allah ya jikansu, kuma Allah ya ba su lafiya.
ABDULLAHI: Amin.
Bayan haka, me za ka fara cewa dangane da wannan al'amari?
ABDULLAHI: Ba wani abu. Wannan abu abu ne daga Allah. Kuma wannan abin pride (wato alfahari) ne wajenmu, saboda 'yar'uwarmu ba ta mutu haka nan a wulakance ba. Wannan abu ne na gadara a wajenmu, ya zama kamar soyayya ce Allah ya nuna mana. Sai dai dan'adam ka san zai iya rudewa saboda sabo. Amma ba wani abu.
Za ka iya tuna lokacin da kuka bar gida zuwa Kano a ranar da abin da ya faru?
ABDULLAHI: Mun bar gida karfe 3 saura minti biyar.
Za ka iya tuna wasu abubuwa ko wasu maganganu da Balaraba ta yi da iyayenku na karshe?
ABDULLAHI: E, babanmu ya kira mu, da ni da ita da shi Shu'aibu (angonta), ya yi mata magana, yake ce mata ta je ya yafe mata. Ta ce da shi, "Za mu je Kano amma za mu dawo tare." Ya ce ba komai, mu je ya yafe mata. Ta ce don Allah ya yafe mata. Ya ce, "Wallahi babu komai. Na yafe maki. Ku je sai kun dawo. Insha Allahu za ku je ku dawo lafiya." Shi ne sai shi babanmu yake tambaya, ya ce, "Shikenan Shu'aibu, hankalinka ya kwanta ko?" Ya ce e, hankalinshi ya kwanta. Ya ce, "To shikenan, ku tafi, a dawo lafiya. Ga babban yayansu nan zai bi ku, sai ku je tare ku dawo."
Lokacin da kuka tashi daga Kaduna, ba ku tsaya ko'ina ba kafin abin ya faru?
ABDULLAHI: Mun tsaya a gidan mai a nan Rigachikun, muka sha mai. Da muka sha mai na je na yi ma wadancan da ke cikin bas din magana, na ce su wuce su shiga gaba, sai mun sha mai mu ma za mu biyo su, da yake sun riga mu shiga gidan mai din.
Da kuka gama shan man, kuka kama hanya, za ka iya tuna irin hira kuke yi a cikin motar?
ABDULLAHI: E, kwarai da gaske, zan iya tunawa. Akwai hirar da muke yi wadda, ana hirar in mun je Kano, inda za mu sauka; da kuma ita kanwata tana cewa idan mun je Kano, don Allah, tana gaya ma shi direban kenan, tana cewa don Allah kada ya biye ni mu rika yawace-yawace saboda ba mu san Kano sosai ba. Shi ne sai ita kanwar mamana take ce mashi, wai! ni ne ban san Kano sosai ba? Lallai tana wasa da ni! Ana ta dariya, da sauransu. So that's it.
Ainihin shi direban, wato Muhammadu Sani, kana ganin rashin sanin hanyar ne ya sa ya fada wa ramukan?
ABDULLAHI: Rashin sanin titi... ko ya sani, ko bai sani ba, wannan duk ba shi ba ne. Abin karar kwana ne. Saboda in da a ce kwanansu bai kare ba, da haka duk ba ta faru ba.
Za ka iya tuna tantangaryar abin da ya faru, tun daga lokacin da hadarin ya soma zama karshe?
ABDULLAHI: Wato yadda aka yi har (motar) ta kucce ma direban, duk wanda ya fadi wani abu ban da abin da na fada, karya yake yi. Saboda ni ina zaune aka yi. Kuma na iya mota, ba wai ban iya ba. Na san yadda mota take. Kuma tun da aka fara hadarin nan har motar ta tsaya, ban fita hankalina ba, ina cikin hankalina. Abin da ni na lura da shi shi ne: ramuka ne guda uku a kan hanyar: daya a dama, daya a hagu, daya kuma a dama daga can gaba, duk kuma sun raba kansu. Da ya zo, bai hangi na farkon ba, wanda yake hagun, sai ya kauce. Da ya kauce sai ya ga na daman, zai kauce mashi kenan, sai motar ta kauce. Da ta kauce, sai ta fara tafiya a tsaye, a kan hanyar, ta karkace tana tafiya a kan kwaltar kamar za ta tsallaka ta je wancan daya layin. Ta yi tafiya a damar, almost zai kai rabin kilomita, tafiyar da muka yi kafin ta zo ta bugi wannan daya ramin na karshe. To shi ne sanadin tashinta sama. Ta yi juyi ina ji, ina ciki, juyi uku ta yi da mu. Sai da ta juya daya, biyu, uku sai ta dawo ta koma hannuna, wanda shi ya sa na samu targade a hannu. Da na ji na yi targade, shi ne na janye hannuna. Sai na rike, ni dai ina (cikin) seat belt (wato bel na kujerar mota) ban motsa ba. Shiru na yi ina jin yadda take yi da ni. Bayan ta fado ta bangarena, sai ta fara juyawa kamar fanka, tana juyawa, ina ji. Duk su ne dalilin da ya sa na samu raunuka. Ka ji yanda abin yake.
To, a lokacin da kuke cikin motar, kai kadai ne ka yi amfani da seat belt din?
ABDULLAHI: E, ni kadai ne na sa seat belt. Na san seat belt bai hana mutuwa. Amma da yake ni na riga na saba ne, in dai zan shiga mota sai na sa shi.
Da motar ta gama juyawa har ta tsaya wuri daya, taimaka maka aka yi ka fito, ko kai ka fito da kanka?
ABDULLAHI: Babu… Babu, don ba wanda ya dauka cewa akwai ma mutum a cikin motar. Ni na yi pressing … shi ne sanadiyyar jin ciwona ma a kai ai. Da na danna bel din na fado a cikin motar, na duba inda zan iya fita. Na kurda na fita. Mutane dai sun gan ni a tsaye ne kawai. Kawai iyakarta kenan. Amma ba wanda ya taimaka mani.
Lokacin da ka fito daga cikin motar, a wane irin hali ka tsinci 'yan'uwanka?
ABDULLAHI: An jefar da su kamar a layi ne. Tsakanin wani da wani zai kai kamar taki shida-shida ko bakwai-bakwai. Wannan ta hannun dama, wannan na bin shi, wannan na bin shi. Jummai ita ce a can ta karshe a hannun dama.
To, ita Balaraba, a kan kwalta aka jefar da ita, ko a gefen kwaltar?
ABDULLAHI: Duk ba wanda yake a kan kwalta sai Datti, shi ma ba kan kwaltar yake ba, a gefe yake.
Da kai aka taimaka wajen dauke su?
ABDULLAHI: Kwarai da gaske da ni aka taimaka, don Balaraba (yana hawaye) lokacin da na je na kama ta, tana dan numfashi. Na kama ta, na rike ta, abin da yake ya yi mani yawa …. (hawaye).
Da ka fito, wa ka fara kamawa daga cikinsu?
ABDULLAHI: Wajen ita Balaraba na fara zuwa.
Za ka iya tuna maganar da ka yi da ita a lokacin?
ABDULLAHI: Babu. Balaraba ba ta yi wata magana ba. Balaraba ko uhm! ba ta ce ba. Jummai, da ma ita tun farkon tsayawar motar a mace take, ta riga ta mutu.
Lokacin da ka samu Balaraba a kwance, me ka ce mata?
ABDULLAHI: Na yi mata magana.
Ta amsa maka?
ABDULLAHI: A'a. Na same ta, na tallabe kanta… (yana hawaye) ina cewa, "Balaraba, Balaraba, kina ji na? Kina ji na?" Ba ta yi magana ba.
Lokacin da aka dauko su Balaraba zuwa asibiti, an samu shiga da su asibitin kafin su rasu?
ABDULLAHI: An shiga.
Tare da kai aka kai su asibitin?
ABDULLAHI: Tare da ni, duk.
Wane asibiti aka kai su?
ABDULLAHI: Farko dai wato asibitin 'Road Safety' aka fara kai su, wanda yake nan kan hanyar Zariya. Aka je aka kwantar da su, suna rike da gawar shi kanina, wato Datti. Sai na zo na duba Balaraba, don Jummai na san ta mutu da ma; na san ba ta da rai. Na zo na duba Balaraba, ina rike da ita. Muhammad Sani kuma yana kakari. Sai na je na bude bakinshi, na hura mashi iska, ko wai Allah zai sa ya dan samo numfashinshi, amma ina!
Kafin a daura auren Balaraba, babu wasu dabi'u da ta yi, wadanda yanzu ka fahimci bankwana take yi, wato ta hango wannan al'amarin?
ABDULLAHI: Akwai alamu da yawa. Ni na ga alamu. Akwai alamu da yawa, wanda na yarda. Domin akwai lokacin da, that is ana gobe za a daura auren, ta same ni a daki ni kadai. Take ce mani, "Abdullahi." Na ce, "Na'am." Ta ce, "Ya za mu yi wannan abu?" Na ce, "Kamar menene?" Sai ta ce mani, "Kai, mts!" ita ji take wannan auren kamar ta fasa. Na ce mata me ya sa za ta fasa? Ta ce mani, "Haka kawai!" Ita ji take yi auren nan kamar a bar shi. Na ce, "Bai kamata ki fasa ba tunda kina son shi, ke kika kawo shi, ya kamata ki aure shi. Ba wani abu. Lokacinki ne na aure ya yi, ba wani abu." Ta ce ita ba ta son rabuwa da ni ne. Na ce mata, "Ba komai, don kin yi aure ai ba kin rabu da mu ba ne."
To gaskiya ne cewa wasu mutane sun taba gargadinta a kan auren?
ABDULLAHI: Ni dai kam, gaskiya ba mu yi wannan maganar da ita ba. Gaskiya ban da masaniya a kan wannan.
Lokacin da ta gaya maka cewa tana jin kamar a fasa auren nan, maganar ta je kunnen iyayenku?
ABDULLAHI: Ni dai kam tsakanina da ita kawai muka yi, ban gaya wa kowa ba, saboda ba ni son in tada ma iyayena hankali. Shi ya sa kawai tunda ma na yi mata magana na ga ba ta dauki abin serious ba, sai na bari. Ko ran da za mu tafi Kano din kuma muka ce mata sai ta shirya mu tafi, ta ce kai! Ita ba za ta je ba. A gaban Shu'aibu kenan. Shu'aibu yana ji. Na ce mata, "Ya kamata ki tashi mu tafi. Kin san ba za ki je ba kika sa mutane suka shirya, ga shi har da kanwar mamanki?" Sai ta ce shikenan, za ta je.
Ya kake ji a jikinka game da rasuwar wadannan 'yan'uwan naka?
ABDULLAHI: E, to alhamdu lillahi, ni bakin cikin da ka ga ina yi, ba wai don sun mutu ba ne. Wallahi kewa ce take damuna. Ina tuna irin shakuwar da na yi da su.
Me za ka ce dangane da zargin da wasu ke yi cewa akwai sa hannun makiya a cikin al'amarin?
ABDULLAHI: Kai fa Musulmi ne, ni Musulmi ne, kuma ka san ba abin da Allah bai iya kaddarawa.
To kana ganin cewa mugun gudu da direban ke yi shi ya jawo wannan hadari?
ABDULLAHI: Duk wanda ya ce ana mugun gudu karya yake yi. Idan kuma ya dage a kan haka, to Allah ya saka mana. A lokacin da abin ya faru, karkari malejin motar ya kai 130.
Wace irin hira kuke yi cikin motar, kafin faruwar hadarin?
ABDULLAHI: Muna labari ne, suna ce mani ya kamata idan muka je kada mu kai Balaraba wajen Galar da za a yi, ya kamata mu kai ta gidan da take a da, gidan su Balaraba 'yar'uwarta, wannan wadda suke zama tare (a Kano). Ina cewa, "Ai da ma ni na san abin da nike yi. Shi ya sa aka hado mu tare." A cikin motar kenan fa muna tafiya - kafin hadarin ya faru.
Za ka iya tuna kalma ta karshe da ka ji direban ya fadi?
ABDULLAHI: Ai da abin ya faru ba wanda ya yi magana cikinmu. Sai dai daga cikin matan na ji wata ta ce, "A'uzubillahi!" Na ji wannan.
Da ka fahimci motar ta kauce daga hannun direban, ba ka yi kokarin kama sitiyarin ba, don ka taimaka masa?
ABDULLAHI: Ban yi kokari na mika hannuna ba. Kuma ban... Na dai kalle shi kurum lokacin da ta kwace mashi din, in ga yadda zai yi da ita, amma ban sa hannu ba. Saboda na ga sharrin sa hannu ga sitiyari. Shi ya sa ko za ka yi tafiya, kada ka sa mai tsoro a gaba. Saboda ko abin bai kai haka ba sai ya ja ya kai haka nan.
Lokacin da motar ta kauce, ka fahimci cewa direban ya rude?
ABDULLAHI: Bai rude ba. Don ko da ni ne a yadda yake, haka zan yi. Inda na san na rude dai, inda na gaya dauke ta ta yi damar nan, ya dawo da ita. To wajen da ya dawo da ita din nan shi ne, amma ba wani rudewa ya yi ba. Na gan shi dai yana kokowa da sitiyarin ina kallonshi.
Ba ka yi mashi wata magana ba a lokacin?
ABDULLAHI: Komai ban ce mashi ba. Abin da na so in ce mashi, don ni da na daga kai da na ji ya kada na farkon, na so in ce mashi, "Kada ka yi kwana, kar ka ce za ka dauke mata kai! Daga kafarka kawai ka bi cikin ramin, za mu wuce insha Allahu!" To kafin in bude baki, har ya kai ga ramin, sai ya dauke kan. Ka ji yadda aka yi.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin