Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


An yi karar wasu 'yan fim na Kano a kotun Abuja


A kan kaset na biki da rasuwar su Balaraba Mohammed

Taron sasantawa ya wanke Auwalu Marshal, kuma ya sakar wa Mu'azzam Boss mara

Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA a Abuja

KOTUN shiyya ta 2 (wato District Court II) da ke cikin unguwar Wuse Zone II a cikin babban birnin tarayya, Abuja, ba ta da wani bambanci da sauran kotunan da ke yawancin birane irin ta. Da shigar mutum zai tabbatar da haka idan ya fara yin arba da katifu, kekunan dinki, kujeru masu kushin, tsofaffin motoci, kyawaren dakuna masu tsada, tulin darduma, firji, da sauransu. Inda kawai za a iya cewa ta bambanta da ta wasu sassan arewacin kasar nan shi ne da yawa daga cikin ma'aikatan kotun ba Hausawa ba ne, sai dai suna dan fahimtar Hausa.

A kan titin Gaborone kotun take kuma tana daura da Sashen bayar da tallafin horo ga ma'aikata na Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya (Technical Aid Corps).

A wannan kotu ce a kuma rana ta 3 ga Afrilu, 2002 aka ajiye domin fara sauraren kara tsakanin mijin marigayiya Jummai (A'isha) yayar Balaraba Mohammed, Malam Adamu Umar, wanda shi ne kuma ma'aikacin ne a ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan al'amurran tsaro. Jummai dai tana daga cikin wadanda suka mutu a hadarin da ya jawo salwantar rayukan su amarya Balaraba. Mutumin ya kai karar shahararren dan fim din nan mai fitowa a mugu a fim, Malam Mu'azzam Boss, da kuma kamfanin shirya finafinai da ke Kano mai suna 'Tumbin Giwa Film Production' wanda Malam Auwalu Isma'il marshal yake jagoranta. Adamu Umar ya yi karar ne bisa cewa bai yarda su nuna mutuwar iyalinsa ba a cikin wani shirin fim na musammman (documentary) da yake zargin za su yi. A wurin biki da bayan mutuwar mamatan, an ga Mu'azzam da karamar kyamarar bidiyo (camcorder) yana daukar hotuna, tun daga isowar mahalarta daurin aure har zuwa binne gawarwaki da zaman ta'aziyya. Da yake bai koma Kano da wuri ba yana gidan su Balaraba aka kai gawarwarkinsu bayan sun yi hadari a kan hanyarsa ta zuwa Kano kwanan daya da daura aure. Wannan ne ya bai wa Mu'azzam damar sake yin amfani da kyamamar ya dauki wasu bangarori na hidima da gawarwakin tun daga saka su likkafani har rufe su a makabarta.

Ba wannan kadai ba, ya bi jama'a yana tambayarsu abin da za su ce kan bikin da kuma mutuwar. Daga cikin wadanda su Mu'azzam suka yi hira da su har akwai shi kansa mai kara, har ya dauko katin adireshinsa ya basu.

Rasuwar Balaraba ta ba da dama ga nau'in 'yan kasuwa daban-daban su fito da abubuwan sayarwa kala-kala a kan aure da mutuwar Balaraba, musamman ma dai kalandu, wadanda suka cika kasa suna dauke da hotunan bikin da na rasuwar. Su kuma mutane, suna kishirwar gani ko jin duk wani abu da ya jibinci wannan babban bakin labari da ya auku.

Wata majiya tamu mai tushe ta shaida mana cewa su Mu'azam sun tuntubi iyayen Balaraba domin su ba da izini a buga kaset din a sayar a kasuwa. Iyayen Balaraba da shi kansa Adamu duk ba su amince ba. Shi kansa Kumurci an tuntube shi don ya ba da goyon baya a saki kaset din a kasuwa. Majiyarmu cewa ta yi Kumurci gabansa faduwa ya yi da ya ji wannan magana "wadda shi ya dauka tamkar idan ya yi haka kamar cin naman Balaraba ya yi ko kuma sayar da gawarta". A karshe dai, in ji majiyarmu, Kumurci cewa ya yi shi ko kallon fim din ma ba zai iya yi ba.

Ana cikin wannan harda-harda sai ga sammacin bayyana a gaban alkalin kotun da ke unguwar Wuse Zone II a Abuja an aiko Kano wurin Mu'azzam Boss da kamfanin Tumbin Giwa. Wani bangaren sammacin mai lamba A2/DCII/CV36/2002 ya nuna cewa "daidai lokacin da iyaye 'yan'uwa da surukan iyayen Balaraba ke kidimewa taraddadi da jimamin abin da ya same su, wasu 'yan fim sun yi amfani da wannan dama suka dauki abubuwan da suka gudana a wurin domin su sayar su sami riba." Har ila yau cikin takardar kukan mai kara ta nuna bai yarda kowane bangare na iyalansa ya fito a cikin wannan kaset ba.

Lokacin da aka aiko da sammmacin a Kano, wasu daga cikin 'yan fim musamman su Mu'azzam Boss da aka aiko mawa, cikinsu ya duri ruwa, kuma an yi ta nuku-nuku da maganar ba a so wanda bai ji ba ya san da zancen. Sai dai kuma magana ba ta boyuwa a fagen harkar fim, don haka nan da nan maganar ta bi gari, duk inda aka tsuguna ana tusa ta. Da ma can baya ana ta ji-ta-ji-ta kan cewa wasu mutane ne suka yi wa Balaraba baki. To jin labarin an kai wasu kara kan mutuwar a Abuja sai kuma wata sabuwar ji-ta-ji-tar ta rika bazuwa, har wasu suna tunanin ko a kan waccan maganar yi wa Balaraba baki ne aka kai karar su Mu'azzam din.

Tun kafin a je kotun an yi yunkurin sasanta al'amarin. Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mohammed Mandawari, ya tsaya ka'in-da-na'in domin sasanta Adamu Umar da wadanda yake kara. A karshe sai aka tsaya kan cewa za a hadu a gidan su Balaraba a Kaduna a je da kaset din a gaban jama'a a kona shi. Amma sai labari ya sha bamban, domin ana saura kwana daya a tafi kotu sai wadanda ake karar suka samu labarin cewa ba zai yiwu a kashe magana a Kaduna ba, tilas sai an je kotun.

a ranar fara sauraron shari'ar, wato 3 ga Afrilu, wakilinmu ya isa kotun da misalin karfe 8:10 na safe. Bayan ya dade da zuwa ne sai ga Auwalu Marshal da lauyansu da kuma wani mai suna Faruk wanda ya zo a madadin Mu'azzam Boss da bai je kotun ba. Akwai kuma wani dan rakiyarsu guda daya. Daga nan kuma ba a dauki wani dogon lokaci ba sai ga wasu mutane biyu wadanda suka wakilci mai kara.

A 'yar tattaunawar da suka yi da wakilinmu, Malam Auwalu Marshal ya bayyana cewa shi ya zo kotun ne cike da mamakin yadda sunan kamfaninsa ya shigo cikin wadanda ake kara. Ya ce Tumbin Giwa ba ne ya dauki nauyin abin da Mu'azzam ya yi a wurin biki da mutuwar su Balaraba ba, ba da kayansa Mu'azzam ya yi aiki ba, kuma ba tare da shi Auwalu aka yi aikin ba. Ya kara da cewa ya je wurin bikin ne a matsayinsa na dan fim kamar yadda Balaraba take kuma ya tsaya jana'izar ne domin yana can aka yi mutuwar kuma shi ne shugaban riko na kungiyar 'yan wasan fim ta Jihar Kano wadda aka rushe jagorancin shugabanninta watannin baya da suka shude.

Tun kafin su iso kotun mujallar Fim ta bincika a ofishin mai tattara bayanan kotu (registrar), inda ta samu labarin cewa shi mai kara ya yarda a sasanta a wajen kotu muddin su wadanda ake karar za su amince da sharuddan da zai gindaya, wato na batun kona kaset ko kuma na cire fuskokin iyalansa kwata-kwata daga kaset din. An yi ta jiran lauyan mai kara har sama da awa daya da rabi bai zo ba, daga nan sai aka yanke shawarar zaunawa a da'irar sasantawa a daya daga cikin dakunan da ke kusa da ofishin alkali. An kuma zauna teburin sasantawar har da editan mujallar Fim.

Wanda ya wakilci mai kara ne, wani mai suna Malam Abdul Umar, ya fara magana. Ya nuna bacin ran wanda yake wakilta dangane wannan yunkuri da aka yi na yin kaset din auren da mutuwar Balaraba a sayar. Dalilin bacin ran nasa kuwa shi ne akwai matarsa da masu kyamarar bidiyo suka dauka lokacin da ake jana'izar mamatan. Abdul ya kara jaddada aniyar Adamu Umar ta cewa muddin matarsa ba za ta fito a cikin kaset din ba, to ba zai yi shari'a da su Mu'azzam ba. Batun Balaraba kuwa, wannan da ma 'yar fim ce, shi da iyalansa yake iko, wato Jummai da ta rasu da kuma 'yarsu Nana Khadija wadda ake jinya. Bayan ya yi dogon bayani ya kare sai lauyan da ke wakilar wadanda ake kara ya fara nasa bayanin.

Lauyan, wanda ya zo daga cambar lauyoyi ta 'Labaran and Co.' da ke Wuse Zone 4 kan titin Ladi Kwali a Abuja, ya furta cewa to shi dai a matsayinsa na lauyan wadanda ake kara ya yarda da wasu sharuddan amma bai yarda da wasu ba. Wasu daga cikin kalaman lauyan su ne:

1. Bai yarda a sasanta kafin a shiga kotu ba; kamata ya yi sai an shiga alkali ya kira karar an saurari bayanai, daga nan sai a nemi kotu ta ba da izini a sasanta a waje. "Amma ya za mu zo daga Kano, kotu ta kira mu har Abuja, mu zo kotu kuma mu koma ba mu shiga kotu ba?" ya yi tambaya;

2. yana kalubalantar takardar kiran da aka aika wa wadanda yake karewa domin a fahimtarsa akwai tsoratarwa da barazana a cikinta (intimidation);

3. da lauyan mai kara ya kamata ya fara tattaunawa. Tunda lauyan mai kara ba zo ba kuwa, kamar an wahalar da wadanda aka kirawo daga Kano ne;

4. ya yarda da batun goge kaset ko cire inda matar Adamu ta fito. Amma ya yi togaciya da cewa ai su Mu'azzam da suka dauki hotunan bidiyon sun sha wahala, sun kashe kudi, sun bata lokaci. Don haka sai dai a biya su ladar wahalar da suka sha;

5. Balaraba 'yar wasa ce, don haka duk wanda ya je wurin bikinta to ita ce ta gayyato shi, domin da a ce babu bikin nata, da ba za a taru ba. Wanda duk ya je wurin kuwa don ya shiga cikin kyamarar daukar hoto ba a take hakkinsa ko hakkin waninsa ba. Ita Jummai, ba a cikin gidan aurenta aka je aka dauke ta aka sa a kaset na bidiyo ba;

6. sa'annan babu ruwan kamfanin Tumbin Giwa da wannan magana saboda Mu'azzam dai da ya yi wannan aiki ba dan kamfanin ba ne kuma ba kamfanin ne ya ba shi kwangilar yin aikin ba.

Bayan lauyan ya yi wadannan bayanan da kuma wasu bayanan bayan wadannan, ya ce saboda Musulunci da kuma jimamin abin da ya faru a kan Balaraba da iyalin Adamu Umar, ya yarda ya daina kallon al'amarin a matsayinsa na lauya tunda sasantawa aka zauna za a yi.

A karshe dai an amince da wasu sharuddan da bangarorin biyu suka shata wa juna. Daga nan aka bukaci lauyan wadanda ake kara ya rubuta su saboda kowane bangare ya karanta ya sa hannu. An rubuta sharudda kamar haka:

1. Babu ruwan kamfanin 'Tumbin Giwa Production' da harkar daukar kaset na bidiyo a lokacin bikin Balaraba da kuma rufe gawarwakin. Kuma Auwalu marshal ya amsa kiran kotu ne domin jin yadda aka yi har sunan kamfaninsa ya shiga cikin sammaci;

2. ba za a nuna fuskoki ko wani bangare na iyalin Adamu Umar ba tun daga lokacin da aka kawo gawarwaki har lokacin rufe su;

3. idan har yiwuwar fitar da kaset din kasuwa ya faru, to kafin ya shiga kasuwa tilas a kawo shi gabansu su gani, su kuma suna da ikon yin korafi idan suka ga abin da bai yi masu ba don a cire;

4. da zarar an fitar da kaset din kasuwa, to maganar shiga zarafin masu alhakin kaset din bai taso ba.

A duk tsawon lokacin da aka kwashe ana sasantawar (awa uku da rabi), Adamu Umar ya rika bugo waya har sau uku don jin halin da ake ciki daga bakin wakilansa. Har gaisawa ya yi da Faruk, wato wakilin Mu'azzam wanda yana daga cikin wadanda suka tallafa wa Mu'azzam wajen dawainiyar daukar hotunan bidiyo din. Can baya kuwa kafin a shiga dakin sasantawar, Malam Faruk ya shaida wa mujallar Fim cewa, "Wallahi da muke daukar jama'a a bidiyo kyamara, mun sami Adamu Umar kuma muka ji dan bayani daga gare shi. Daga nan har ya ce idan mun dauka shi ma yana bukatar kwafe daya. To ni ban san yadda ake ciki ba sai na ji labarin cewa Adamu ya kai mu kara."

Tunda guguwar da ta nemi turnukewa ta kwanta, abin tambaya shi ne: shin ko Mu'azzam zai fitar da kaset din kasuwa? Da wane sunan kamfani zai fito da shi? Shin Shu'aibu Lawan da iyayen marigayiya suna da wani hakki a kan faifan ko a'a? Lauya dai ya ce idan Mu'azzam ya sa kaset din a kasuwa bai yi laifi ba.

Shi kuma wani malamin jami'a a Kano wanda ya yi nazarin al'amarin, cewa ya yi, "Su Mu'azzam sun yi dabara da suka tattara dukkan bayanan su Balaraba a kaset. Aiki ne wanda Kungiyar Masu Shirya Fim ko ta 'yan wasa ta yi inda tana da kyakkyawan shugabanci, ba domin komai ba sai don tarihi. Ina kira ga kungiyar da ta sayi kaset din ko da ba za a sayar da shi ga jama'a ba, ta aje shi a taskar kayan tarihinta (in tana da shi). In kuma sayar da shi za a yi ga jama'a, na tabbatar su Mu'azzam sun warke, domin za su sami riba mai yawa ta kudi."

To, sai mun gani.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin