|
Watakila in dawo ruwa
Inji Dayyba Isyaku, bayan mutuwar aurenta
Daga ABDULLAHI NASIR Ability) a Zaria
Dayyaba Isyaku..ta fito daga 'auren dole'
| YANZU dai ta tabbata cewa auren fitacciyar 'yar wasan nan da ke Zariya cikin Jihar Kaduna, Dayyaba Isyaku, ya mutu mut, kuma jarumar ta shirin Asin Da Asin tana nan tana shirin dawowa harkar fim. Dayyaba ce da kanta ta tabbatar wa da wakilinmu haka a hirar da suka yi kwanan nan a gidansu da ke Kings Road, Muchiya, Zariya.
A ranar Alhamis, 18 ga Afrilu, 2002 alkali ya kashe auren a kotun Sabon Garin Zariya bisa hujjar rashin kulawar miji.
Dayyaba, 'yar shekara 21 da haihuwa yanzu, haifaffiyar Zariya ce wadda ta yi karatu a 'FGGC Zariya,' sa'annan ta yi aiki a wata makaranta mai zaman kanta mai suna 'Fahimta International School.'
Idan ba a manta ba mun taba ba ku tarihinta a Fim ta watan Satumba 2000, da kuma labarin aurenta a Fim ta watan Disamba 2000.
Ta fara shirin fim ne a 1999 da kamfanin 'Jari Film Production' da ke Zariya. Ta fara ne da fim din Mutum Ko Aljan?, wanda bai samu fitowa da wuri ba har sai da aka fara fim din Wasila . Ta shiga harkar fim ba tare da sanin mahaifinta Alhaji Ishaq Usman ba. Ta yi fice a finafinai da suka hada da Wasila 1 & 2, Asin da Asin, Mutum Ko Aljan?, Ana Bikin Duniya, da Jure Fari. A ranar da aka daura mata aure, Alhaji Ishaq ya yi hira da mujallar Fim inda ya nuna rashin gamsuwa da shigar 'yarsa fim. Ya ce, "Abin da ya sa nake kyamar in ga 'yata a harkar fim shi ne, duk da kasancewata ma'abocin kallon finafinan namu, nakan ji takaicin yadda jama'a masu kallon finafinan nan suke wa matan da ke ciki kallon 'yan iska ko ma su kira su karuwai kai tsaye tare da yi masu miyagun alkaba'i ga rayuwarsu." Alhaji Ishaq ya gaggauta aurar da 'yar wasan ga wani mutum a nan Zariya. A binciken da wakilinmu ya yi, ya gano cewa ita Dayyaba ba ta son auren da wannan mutumin. Ta dai bi umurnin iyayenta aka yi auren. Binciken ya dada nuna mana cewa tun da ta je gidan mijin abubuwa sun rika faruwa na rashin jituwa, domin har ta kona mijin ta taba yi da ruwan zafi.
Kwanakin baya sai rade-radi suka bazu cewa wai Dayyaba tana nan a gidansu, kuma sun duka shari'a da mijin. Wakilinmu da ya garzaya gidan ya tambayi wani yaro da ke kofar gidansu ko 'yar wasan tana nan? Sai yaron ya ce ba ta nan, ta je gidan yayansu a Tudun Jukun cikin Zariya. A bisa tambayoyin da aka yi masa, yaron ya ce Dayyaba ta fi karfin mako uku a gida.
Da yamma sai wakilinmu ya sake komawa gidan. Da ta ji shi ne nan da nan sai ga ta ta fito. Rabon da wakilinmu ya sa ta a ido tun ranar daurin aurenta da ya je. Kowa ya san Dayyaba yarinya ce kyakkyawa, ga siga ga kwarjini. Amma a ranar ya lura da cewa akwai damuwa a gare ta domin kuwa ta dan rame. Da fitowar ta ba abin da ta fara fadi, sai ta ce, "Ability mugun boss!"
Bayan sun dan tattauna sai wakilin namu ya waiwaye ta da maganar aurenta. Sai ta kada baki ta ce, "Ai an raba."
"Kamar yaya?" inji wakilinmu.
Sai ta ce, "Ability, kai ka san irin gwagwarmayar da aka yi da ni a gida a kan cewa ni ba na son shi, akwai wanda nake so daban amma babana ya ce shi fa ai wannan zan aura. To lokacin da muka yi aure na sha wahalhalu da yawa a gidanshi. Kai ma da kanka ka dube ni, a haka nake da?"
Ta ci gaba da cewa, "Don kada in bata ma iyayena rai shi ya sa na yi hakuri na zauna da shi. Amma duk da haka bai gani, sai rigima: na safe daban na yamma dabanb."
Tana cikin yin bayani ne sai kawai ta ce, "Kai ina zuwa. Daddy ya tashi! '' Ta shige gida.
Wakilinmu ya yi zaton mahaifinta ne zai fito. Can sai kawai ta fito da yaro jinjiri mai kimanin shekara daya, ta ce, "Ability, ga Daddy." Sai wakilinmu ya dauki yaron ya ce, "Ai ni da kika ce Daddy na zaci cewa babanki ne. To shi wannan fa dan wajen wanene?"
Sai ta fashe da dariya ta ce, "Ashe tun tuni ba ka ji labarin haihuwata ba? Ai wannan dana ne, sunan babana ne aka sa mashi, shi ya sa nake ce masa Daddy."
Shi dai Ishaq (Daddy), an haife shi ne a ran Litinin, 19 ga Nuwamba, 2001.
"Dayyaba ya maganr shirin fim?" wakilinmu ya tambaye ta.
Sai ta yi murmushi ta ce, "Kamar yaya?"
"Kamar yadda kike a da."
Ta kara murmushi ta ce, "Sai in na yi tunani zan zo in gaya maka."
Sai wakilinmu ya ce, "Ai tunda ga ni ai na tabbata cewa a zuciyarki tuni kin yanke cewa ko za ki koma wasan fim ko kuma ba za ki koma ba."
"Tunda ka matsa mani," inji Dayyaba, "to ni dai inada sha'awar dawowa harkar fim amma..." Sai ta yi shiru.
"Amma me?"
Sai ta ce, "Amma fa ban tsammanin babana zai bar ni ba in yi fim." Sai wakilinmu ya ce, "To me ya sa lokacin kina budurwa ya kyale ki kika yi fim ballantana yanzu da kike bazawara?"
Sai ta amsa, "Ai duk finafinan da na yi bai sani ba sai daga baya; mamana ne kakana kawai suka amince da na yi fim ko a wannan lokacin?"
Da wakilinmu ya lura magariba ta yi sosai kuma ga iskar ruwa ta taso sai ya ce, "To Dayyaba, ina sonzan tafi. Ko akwai abin da za ki gaya wa jama'a da masoyan finafinanki?"
Sai ta ce, "Abin da zan ce sai dai kawai Allah ya bar mu tare da masoyana, kuma ina shaida ma fans dina cewa ba da dadewa ba za a ji duriyata a wannan harka ta finafinan Hausa."
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|