|
Ina Maryam Aliyu ne?
Maryam Aliyu
|
Daga MUHAMMED NASIR da IRO MAMMAN a Kano, Zariya da Kaduna
MARYAM Buzuwa. Ko ka ce Mushaqqa (wato fim dinta na farko). Ko kuma ka ce yarinyar da jarumi Ahmed S. Nuhu yake son ya aura. Ko kuma ma dai, ka ce yarinyar da ta fito a fim din Mushaqqa da fim din Sharadi a bana. Shin tana ina ne?
Ga masu kallo, Maryam Aliyu tana nan daram-dakam a fagen shirin fim. To amma ga 'yan fim, Maryam ta dade tun da ta bace bat, kuma babu wanda ya san inda take; watanta daya yawancin abokan sana'arta ba su san inda take ba.
Da fari, an fara yada ji-ta-ji-tar wai ba ta da lafiya, an tafi da ita Nijar, kasar mahaifiyarta. Aka ce jifarta aka yi (wato sammu), wai barin jikinta ya shanye, an tafi neman magani. Kuma aka ce a'a, wai cikin shege ta yi aka gudu da ita domin a zubar. Sai kuma aka ce a'a, mahaifiyarta, wadda a Zariya take aure, ita ce ta zo ta dauke ta daga Kano inda ta zauna a gidan mahaifinta tana harkar fim, ta tafi da ita domin da ma can ba ta son 'yar ta ta yi fim. Shin me Maryam ke ciki?
Wadannan surutan sun yawaita a fagen shirin fim, musamman a Kano. Duk wanda ka gani abin da zai gaya maka daban ne da na dan'uwansa. Wani matashin dan fim ya zo ofishin mujallar Fim a Kano a cikin zumudi ya ce wa 'yan ofis din, "Jiya na je gidan su Maryam na same ta a kwance ba ta lafiya, ana yi mata karin ruwa." Da aka tambaye shi me ya sa yake zaton ba ta da lafiya, sai ya kada baki ya ce, "Eee to, ni dai na gan ta a kwance kuma an makala mata ledar ruwa, kuma babu ruwa a cikin ledar. Idan lafiya lau take me zai sa a yi mata karin ruwa?"
A fagen shirin fim, ba abin da ya fi dadi kamar ji-ta-ji-ta. Ita ko mujallar Fim, a kullum so take ta ji kwakwaf, kuma daga gindin maganin. Wannan ne ya sa wani wakilinmu ya niki gari daga Kano ya tafi Zariya a tsakiyar watan jiya, domin an gaya masa cewa kyakkyawar jarumar tana can a wurin babarta.
Da ya isa gidansu da ke unguwar Tukur-Tukur a birnin na Shehu Idris, yamma da gidan attajirin nan Alhaji Tsoho Abdullahi kuma arewa da makarantar 'Lawal Ali Academy,' ya zaci zai tarar ana yi mata girka, ga 'yan bori sun takarkare suna kada garaya a kofar gidan. Amma maimakon haka, sai ya ga babu wani taro a kofar gidan. Sai ma wata budurwa 'yar kimanin shekara 13 da haihuwa wadda ta ce ita kanwar Maryam ce ta fito daga gidan suka yi magana.
Yarinyar ta ce Maryam ba ta nan, wai ta tafi Kano. Daka tambaye ta yaushe, sai ta ce, "Ranar Asabar, yau kwana goma sha biyu." Mahaifiyar Maryam kuma ba ta nan, inji ta, lokacin da 'yar wasan ta tafi. "Mu ma ba mu nan, sai wadannan yaran kadai (ta nuna wasu 'yanmata kanana biyu da suka fito daga gidan), ta zo ta kwashi kayanta tai tafiyarta."
A Kano, wakilanmu sun fahimci cewa cikin furodusoshi da dama ya duri ruwa domin jarumar ta fara yi masu fim amma ba ta kammala ba ta bace. "Idan aka hana Maryam yin fim ai ni na dibga asara," inji wani sabon furodusa.
Da wakilinmu bai same ta a Zazzau ba, sai ya bincike ta a Kano. Ya tuntubi daraktan da ya daure mata gindi a birnin na Dabo, wato Tijjani Ibraheem. Tijjani, wanda mabiyansa ke kira Oga, ya roki mutane da su daina yada ji-ta-ji-ta. Da aka tambaye shi halin da jarumar ta shiga kuwa sai ya tabbatar da cewa Maryam ta hadu da wani mummunan rashin lafiya wanda ya nanata cewa "was very very terrible." Ya ce, "Wato abin da ya faru, Maryam ta hadu da ciwon zuciya ne inda har zuciyarta ko murfin zuciyarta ya fada. Ganin halin da take ciki ne sai mahaifiyarta ta dauke ta ta maida ita wurinta a Zariya don akwai irin maganin da akan yi mata a can."
A kan batun hana ta yin fim, shahararren daraktan ya ce shi bai san mahaifiyarta ta hana ta yin fim ba. "Kuma Maryam ta dawo, domin jiya da shekaranjiya duk ta zo ofishin nan."
Da gaske ne jarumar ta dawo shirin fim. Wani wakilinmu ya gan ta kwanan nan a Kaduna suna shirya wani fim, har ma akwai saurayinta Ahmed S. Nuhu a ciki.
A hirarsa da Fim, Tijjani Ibraheem ya bukaci wakilinmu ya tsaya ya dauko masa wani jadawalin finafinan da 'yar wasan za ta karasa tare da shi wadanda ba ta yi ba lokacin da ciwonta ya tashi.
A ranar Alhamis, 20 ga Yuni, wani wakilinmu ya samu Maryam a gida, inda ya waiwaye ta kan maganganun da ake yi game da ita. A lokacin, an yi mako daya da fitowar sabon fim dinta mai suna Sharadi, wanda Ali Nuhu ya shirya, kuma ta fito a matsayin budurwar Ahmed S. Nuhu.
Ga hirar da suka yi da wannan mujallar:
FIM: Maryam, da kika bar Kano kwananki nawa kika dawo? Kin yi wata daya?
MARYAM: A'a. Na dai yi kwana ashirin da wani abu.
FIM: Wasu sun ce asiri aka yi maki.
MARYAM: Ba wanda ya yi mani asiri. Kana ji ko? Ni ciwon zuciya ne ya same ni; (zuciyata) ta rika ciwo. Toka san mutum mai neman magani, duk abin da ya ji an ce shi ne magani ai sai ya jaraba. To sai aka yi mani kaho a daidai santar zuciyata (ta nuna kirjinta). Ai wannan kaho ne da aka yi min, maimakon in sami sauki, sai ciwon ya karu, kuma zuciyata ta fada. To sai na koma wurin mahaifiyata aka yi min magani.
FIM: Yanzu zuciyar taki ta dawo daidai?
MARYAM: Sosai! Ai wata mai magani ce ta zo ta sa hannu ta dago ta sama.
FIM: Da ganin ba ki nan ana ta cewa mahaifiyarki ce ta hana ki yin fim, wai ta ce ba za ki dawo ba.
MARYAM: Ni mahaifiyata ba ta hana ni yin fim ba; addu'a take yi min ta alheri.
FIM: Kin fara yin fim bayan dawowarki?
MARYAM: E, na yi wani amma ba a sa masa suna ba; ban san sunansa ba.
FIM: Ga shi ba ki gari har Halima Adamu Yahaya, wadda ta kawo ki shirin fim, ta yi aure. Wace nasiha za ki yi mata?
MARYAM: (Cikin mamaki) Da gaske ne ta yi auren?
FIM: Kwarai kuwa! Yau kwana ashirin da daura auren.
MARYAM: Ina yi mata fatan alheri. Ta daure. Allah ya ba su zaman lafiya.
Maryam da Ahmed: Yaushe Za A Yi Aurensu?
AN dade ana yada ji-ta-ji-ta a kan soyayyar fitaccen jarumi Ahmed S. Nuhu da 'yar wasa Maryam Aliyu (Mushaqqa), amma a duk lokacin da maganar da dawo ga masoyan biyu sai su ce ba haka take ba.
Duk da haka, mujallar Fim ta ji daga wata kwakkwarar majiya cewa lallai ne akwai soyayya a tsakanin 'yan wasan, kuma ma sun yi nisa a kan hanyarsu ta zama miji da mata.
Yanzu an yi watanni ana ce-ce-ku-ce a kan wannan al'amari. Kwanan baya lokacin da kamfanin 'Mandawari Enterprises' zai shirya Mu Shakata na 4 an gayyato wadanda shi Mandawari ke ganin cewa "aurensu ya matso.'' Akwai A'isha Ibrahim daga Kaduna, Rabi Mustapha, Balaraba Mohammed da Kumurci da kuma Maryam tare da Ahmed. Mazajen A'isha da Rabi ba su halarta ba saboda ba 'yan fim ba ne. Tambayar da 'yan fim suka rika yi a lokacin shi ne idan batun Maryam da Ahmed bai tabbata ba, to yaya aka yi aka kira su a shirin, wanda yanzu ya fito?
Shin me ya sa masoyan suke nuku-nuku? Kwanaki kadan bayan an dauki shirin Mu Shakata 4, mun nemi jin ta bakin Halima Adamu Yahaya, wadda ita ce ta gabatar da shirin. Ta yi wa A'isha, Rabi da Balaraba tambayoyi kan zancen aurensu. Amma "na yi iyar kokarina in ji gaskiyar lamarin da ke tsakanin Ahmed da Maryam amma duk wanda na tambaya sai ya ce min abin sirri ne,'' inji Halima, wadda kuma ita ce ta kawo Maryam fagen shirin fim na Kano.
To, yanzu dai maganar ta tabbata, har Ahmed da Maryam din sun fara bayyanawa a fili. Lokacin da rashin lafiyarta ya taso kwanan nan, kar ka so ka ga yadda jarumin duk ya kidime. "Fadi da kari," inji wani abokin Ahmed, "aurensu ya kusa. Nan da 'yan watanni kadan insha Allahu."
Labari na baya-bayan nan da Fim ta tsinta shi ne har Ahmed ya tura waliyyai sun kai kudin gaisuwa gidan su kyakkyawar masoyiyar tasa, wadda ta taba yin wani aure na dan gajeren lokaci.
Wani dan wasa cewa ya yi, "Mu idan Ahmed ya auri Maryam murna za mu yi, domin zai kara nuna wa jama'a cewa 'yan fim suna da mutunci, kuma ba su kyamaci junansu ba tunda har suna auren juna."
E, mun yarda. Kuma kada mu manta, jarumin zai more da kyakkyawar mata mai kawaici da alkunya. Ita ma haka.
To, Allah ya nuna mana.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|