|
Wane hali Fatima Ahmed take ciki bayan mijinta ya sake ta saboda fim?
Fatima Ahmed
|
A FITOWARMU ta 21 ne muka fara buga labarin wata rigima tsakanin Fatima Ahmed da mijinta, wadda aka tafka a kotu tsawon watanni hudu. Fatima, wadda ta fara fim a lokacin, ta kai kara kan cewa Malam Ahmed ya sake ta, shi kuma ya tsaya a kan cewa bai sake ta ba har ta shiga harkar fim. A karshe dai mijin ya saduda, ya gaji ya rubuta mata takarda saki daya, ya ba ta. Daga lokacin zuwa yau, Fatima ta kara shiga harkar fim tsundum. Ga duk mai bin labaran mujallar Fim sau da kafafu, zai tuno cewa tun a farko an rubuta cewa Fatima 'yar kabilar Kalaba ce. Amma abin mamaki saboda Hausa ta ratsa ta matuka, ba kowane mutum ne zai iya gane cewa tana da wani yare ban da Hausa ba. Tuni ta zama Bahaushiya!
Gaskiyar magana ita ce iyayenta ba Hausawa ba ne, sai dai ita Hausa ce yarenta don kuwa dan abin da take iya fada da yarensu ba zai iya cika cokali ba. Kafin ta auri Ahmed, Fatima ba Musulma ba ce, amma ganin ta shiga Musulunci har ta daura aniyar auren Musulmi shekaru 10 da suka shude, a cewarta, sai iyayenta suka dora mata karan tsana. Yanzu kuma ta rabu da Ahmed ta koma gidan iyayenta. Abin takaici kenan! Amma abin sha'awa shi ne har yanzu ba ta rabu da Musulunci ba. "Ai sun hakura da ni, babu yadda za su yi, alkalami ya bushe," inji ta.
Za mu iya kiranta Fati mai abin mamaki. Dalili kuwa shi ne kan wata tambaya da aka yi mata na sunan da za a rika kiranta maimakon Fatima Ahmed tunda sun rabu da shi. A nan ne ta kada baki ta ce, "Fatima Abdulhalim." Fatima da wakilin mujallarmu sun yi ta-ja-in-ja kan wannan suna domin shi wakilin namu ya san Abdulhalim sunan dan ta ne. Haka ya hakura ya kyale ta ganin batun addini ya fado a cikin hirar tasu. "Na san Abdulhalim sunan dana ne, ni na fi so a hada sunana da na dana a kira ni da shi maimakon na mahaifina," cewar Fatima. Nata dalilin shi ne saboda bambancin addini da ke tsakaninta da mahaifin nata, wanda Kirista ne. "'Ya'yana su ne magada na. Tsakanina da mahaifina akwai bambanci saboda Musulunci," ta kara furtawa.
Da aka tambaye ta ko tana wani kokari domin ceto mahaifinta zuwa shiga Musulun ci, sai ta fito baro-baro ta ce, "Ai ba zai yiwu ba ne kawai! Ka san menene Hausawa suke ce wa idan mutum ya yi nisa ba ya jin kira?"
Kafin a fada maganar bambancin addinin da ke tsakaninta da mahaifinta, Fatima ta ba da labarin yadda kuruciyarta ta kasance: "To ni dai Fatima babana dan Kuros-Riba ne, mamata 'yar Imo ce. An haife ni a nan Nasarawa ranar 24 ga Disamba, 1976 a unguwar Badawa a Kano."
Karatu fa?
"A Race Ccourse na yi firamare, daga nan muka yi jarabawa na ci 'Hamdala Secondary School'. Ban gama ba ga gaskiya, maza suna yi min go-slow lokacin, na ga har an fara rigima a kaina, aka bula wa wani wuka a kaina, sai na yanke shawarar gara in yi aure shi ya fiye min. Mahaifiyata ta ce ba zai yiwu ba sai na gama makaranta. Ni kuma sai na ware mutum daya, shi ne Ahmed, na share duk wasu masu mota da ke so na, na aure shi. Shekarata goma da shi.
"Ko a yanzu da nake zawarci maza suna yi min gosulo, amma ba na son kowa."
Fatima ta rabu da Ahmed da 'ya'ya biyar a tsakaninsu. 'Ya'yan kuwa duk suna hannunsa, ya kai garinsu a Jihar Katsina ya rike, amma yana aikinsa a Kano. Da aka tambaye ta ko ta yi wani kokari don ta karbi wasu daga cikin 'ya'yan, sai Fati ta ce ba ta karba ba amma tana so a ba ta sai alkali ya ce mata sai dai ta shigar da wata karar sabuwa.
Yanzu dai ta dage wajen shiga finfainai. Wasu daga cikin finafinanta su ne Romon Rogo, Buri, Mugunta, da Daren Farko. Ganin yanzu babu wani rikicin igiyar aure kanta, furodusoshi da daraktoci da dama suna ta saka ta a finafinansu.
Ta gode wa Alhaji Hamisu Iyan-Tama da Hajiya Umma Ali wadanda ta bayyana da cewa, "Duk da halin da na tsintsi kaina a ciki, ba su yada ni ba. Ba zan taba mantawa da su b a."
Abin da ya fi ba ta sukuni a halin yanzu, inji ta, shi ne ba su tare da Ahmed. A karshe ta ce yanzu ta kara yin finafinai da yawa wadanda ba ta san sunayensu ba. "Ka san wasu furodusoshin suna boye sunan fim sai sun kammala za su fito da shi," inji Fatima Abdulhalim, wadda da wannan canjin sunan da ta yi ba a daina kiranta da Fatima Ahmed ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|