|
Abin da Ali Nuhu da Ahmed S. Nuhu suka yo a Saudiyya
Ali Nuhu a Saudiyya
|
HAUSAWA kan ce Allah ya gama kowa da masoyinsa. A bana, 'yar wasan nan da ta yi aure, Fati Mohammed, ta je London inda ta yi wata tallar talbijin a kan cutar kanjamau. To, abin kamar shiri, jim kadan da dawowarta sai kuma labari ya bulla cewa su ma tsofaffin abokan sana'arta din nan, wadanda su ma fitattun jaruman shirin fim ne, Ali Nuhu da Ahmed S. Nuhu, za su tafi Saudi Arebiya don yi wa wani kamfani talla. Wakilanmu sun yi magana da 'yan wasan masu kamfanin 'FKD Production' na Kano a kan wannan tafiya, to amma sai suka bukace su cewa su bari su je su dawo tukuna, daga nan za su yi wa jama'a bayani a cikin mujallar da aka fi karantawa, wato Fim.
To, sun je sun dawo din. Don haka yaya wannan tafiya ta kasance? Wce wainar suka toya a can Kasa Mai Tsarki?
Ali da Ahmed sun bayyana mana komai. Wani kamfani mai suna 'Al-Tayyar Sudan Air Cargo' shi ne ya dauki nauyin tafiyar tasu da biyansu hasafin abin da suka je suka yo. Kamfanin irin na cargo din nan ne, wato mai yin dakon kayayyaki a tsakanin kasashe daban-daban kamar Nijeriya, Chadi, Nijar, da Sudan. A birnin Jidda na kasar Saudiyya ne yake da hedikwatarsa kuma yana aiki ne da kamfanin jiragen sama na kasar Sudan, wato 'Sudan Air.'
Wani mutum mai suna Alhaji Bako Sakatare, wanda ba bako ba ne a wurin masu karatunmu (domin mun sha buga wasikun da yake aiko mana daga Jidda, inda yake zaune da iyalinsa), shi ne ya dauki nauyin tafiyar ta su Ali, domin dai shi masoyinsu ne wanda ya amince da yadda suke yin wasansu a fim. A cewar Ali, babu wani mutum da ya shiga tsakaninsu ya yi masu 'hanya' ta tafiyar. "Gaskiya ba wani agent (dillali) a tsakaninmu," inji shi. "Shi da kanshi wanda ke da reshen (kamfanin) na nan Nijeriya kuma yake can Jidda yana gudanarwa, shi ya zo ya same mu."
Kuma kada ku dauka cewa ganin Fati ta je London ne aka kai su Ali waje. Ali Nuhu ya bayyana wa wannan mujallar cewa tun wajen cikin shekarar 2000 aka soma maganar. "Abin fa ya kai wajen shekara biyu, amma Allah bai tabbatar da abin ba sai yanzu," inji shi.
Wani abin sha'awa game da wannan tafiya shi ne 'yan wasan sun yi amfani da damar da suka samu suka shirya wani fim a can mai suna Kusufi. Ahmed ne furodusan shirin, yayin da shi Ali ya kasance daraktansa. Da ma Ali ya taba furtawa a mujallar Annashuwa cewa ba da dadewa ba zai zama daraktan finafinai. A lokacin, an dauka a nan Nijeriya zai fara yin wannan aikin, to sai ga shi Allah ya ba shi sa'a a kasar waje ne ya soma yin aikin. Duk da yake akwai bangarorin fim din da suka rage, wadanda za a dauka a Abuja nan gaba kadan, wannan ba karamar nasara ba ce a fagen fim inda wuraren daukar fim suka yi karanci a kasar Hausa. Bayan dawowarsu, ASHAFA MURNAI BARKIYA ya sadu da Ali da Ahmed, inda suka yi masa karin bayani a kan tafiyar tasu, kamar haka:
Mutanenmu na Saudiyya sun nuna mana kauna
-Ali
FIM: Ali, yaya ka ji da ka tsinci kanka a birnin Jidda, garin da ba ka taba zuwa ba?
ALI: Abu na farko shi ne, kafin mu sauka, lokacin da jirgi ya kusa sauka, na kallo garin ta taga, na ga wutar lantarki ta haske garin gaba daya. Gaskiya wannan ba karamin burge ni ya yi ba saboda sai na ga canji, sabanin mu a nan inda za ka ga wani wuri babu wuta, da sauransu, amma can na ga ko'ina da wuta.
Da kuka isa, an dauki kwanaki kafin a ba ku fili ku yi abin da kuka je yi?
ALI: Gaskiya ba a dau lokaci ba. Farko dai sai da suka ce mu je mu fara yin umra. Da muka yi muka gama sa'annan suka yi ta dawainiya da mu daga Madina zuwa Makka. Muka dawo Jidda muka samu kamar kwanaki biyu muka huta, sai muka yi abin.
A filin jirgi kuka yi tallar ko a wani gidan talbijin?
ALI: A'a, a can ofis dinsu ne inda suke daure kaya su hada su sa'annan kuma a kwashe su a taho da su filin jirgi inda za a kawo su Nijeriya ko kuma wasu kasashe.
Yaya tallar take?
ALI: Da ni da Ahmed S. Nuhu tunda fitattun 'yan wasa ne, an nuno mu a matsayin mun je Saudiyya mun sayi kaya, kuma mun ba da kayan an shigo mana da su Nijeriya lafiya lau. Akwai karashen tallar da za mu yi a filin jirgin sama na nan Kano. Ka ga kenan nuna aminci da yarda da wannan kamfani ba tare da kayanka sun salwanta ba, shi muke nunawa.
Da wadanne irin na'urori ne kuka yi tallar?
ALI: Da kyamara ce digital, amma fa sabuwar fitowa ce, koda yake dai a nan ma Tijjani Ibraheem ya taba amfani da irinta. Ai ka san an shirya abin ne don jama'a masu kallon finafinan Hausa, don a cikin finafinan Hausa za a rika saka tallar.
Da kuka gama, sun nuna gamsuwa da aikin da kuka yi masu?
ALI: Hakika sun nuna.
Sun fada maku lokacin da za a fara sa tallar a finafinai?
ALI: A'a, ai tsarin tallar ma ni na ba su shi. Kuma ni zan yi editing gaba dayansa; basirata ce. Kuma ta hanyarmu za a rika saka tallar a cikin finafinai.
Da kuka sauka a can ko ka ci karo da wanda ya gane ka har ya ce, "Ai ga Ali, ga Ali!"?
ALI: E. Wannan ai tun daga cikin jirgi muka fara fuskantar irin wannan. Saboda bayan mun yada zango a Ndjamena, (babban) birnin kasar Chadi, an sauke fasinja, na tashi zan tafi bandaki haka, ina tashi sai na ji an rike min wando. Ina juyawa sai (wata mace) ta rika ce min, "Jamilu! Jamilu!" Shi ne sai mijinta yake tambayata, "Menene?" Sai take yi masa bayani da yarensu; ni ban ma san yaren ba. Na ba su hakuri, na ce ina zuwa. Da na fito sai ta rika yi min tambayoyi, take cewa in zauna nan kusa da su. Ni ba na jin abin da take fada. Shi ne har mijinta ya kule, ya ce to bari ya tashi ni in zauna. Sai na ba shi hakuri, na tafi na zauna. Sai kuma dubban mutanenmu da yawansu sun nuna mana sani sosai.
Wace irin tarba 'yan Nijeriya mazauna can suka yi maku?
ALI: Ai wato irin tarbar da aka yi mana a Saudiyya … Shi ya sa nake ganin kmaar ma a gida ba son mu ake yi ba. Saboda idan aka kwatanta irin son da mutanen Saudiyya suke yi mana da kuma na gida ... koda yake dai su na Saudiyya suna nesa ne ba ganinmu suke kullum a ba ... ai ba zan iya misalta abin ba! Amma fa an nuna mana karamci sosai.
Kun je da niyyar tallata wani kamfani, amma sai ga shi kun ciwo tudu uku: ga tallar kun yi, ga umra, ga kuma fim da aka ce kun shirya a can. Haka ne?
ALI: Gaskiya da ma ina da shiryayyen labari (script) da ya shafi kasar waje. To amma da ma ka san mu matsalar finafinanmu na Hausa ita ce rashin kudi, da sauransu. To, da Allah ya kai mu kawai sai na ce ah, to da ma wannan fim din, Kusufi, Ahmed ya taba fadarsa a hirar da aka yi da shi a mujallar Fim, sai na ce, to mu yi shi mana (a can). To ka ji yadda aka yi kenan muka fara yinsa a can.
An ce wai idan mutum yana shirya fim a Saudiyya askarawa kan zo su damke shi. Ku ya aka yi kuka sami nasarar yin naku?
ALI: Ai da ma duk kasar da take da doka, idan ba ka bi dokarta ba, tilas ka shiga matsala. Gaskiyar magana ita ce, mu mun yi shooting din mu da izinin hukuma. Idan kana son kwafen takardar izinin da aka ba mu, sai in nuna maka. Ba wai haka kawai kai-tsaye muka je muka kafa kyamara muka fara daukar fim ba. Amfanin ofishin jakadan wata kasa kenan a wata kasa. To ta ofishin jakadanci muka bi.
Tunda daga kai sai Ahmed kuka tafi, yaya aka yi kuka yi fim ku biyu?
ALI: Abin da ke faruwa shi ne, gaskiya fim din nan mun yi shi musamman kan ni da ahmed da kuma 'yan tsirarun mutane da suke zaune a can. Sa'armu ita ce da muka je sai muka taras da wasu 'yan wasan fim da ke can Saudiyya wadanda suka tafi daga nan. Gaskiya wadannan 'yan wasan ban san irin godiyar da zan yi masu ba, saboda su suka taimaka aka samu nasarar wannan abu; kamar Safa Ahmed ta cikin fim din Kowa Da Ranarsa, Habiba ta cikin Sa'a ta Fi Gata, Rabi Sulaiman, su Abdullahi Dankurma, su Ladidi Fagge, da Fati Al-Amin.
Duk a cikin gida kuka yi kuka gama ko kuwa kun fito waje kuna yi jama'a na kallonku?
ALI: Mun fito waje kan titi, kuma jama'a kowa yana harkokinsa babu ruwan wani da wani, amma jefi-jefi wasu za su zo su yi tambaya: shin fim ne ake yi? Idan aka ce masu e, sai su ce to su ma a nuna su a nuna su. To har ma mun dan yi wani da irin wadannan mutanen. Sa'annan kuma mun shiga cikin kantuna da kasuwanni, da sauransu.
Me za ka ce game da mutanen kasar?
ALI: Gaskiya ni dan zuwan da na yi sai na fahimci mu ne nan muke ganin Larabci kamar yana ba mu tsoro. Amma iya dan zaman da na yi na fahimci (cewa) yare ne wanda ba shi da wuyar fahimta. Na fahimci abubuwa da dama. Idan za ka ji kalma yau, ka ji ta gobe, sai ka rike ta. Abu na biyu kuma shi ne gaskiya saboda ibadar da na yi a can, shi ya sa da muka dawo sai na ji hankalina ya kwanta, kuma sai na ji kamar an warkar min da wani cajin kai da yake damuna na game da cakudewar ayyukan harkar nan (ta shirin fim). Abin da zai sa kenan in yi marmarin komawa wannan gari. Kuma za ka ga yadda mutum Musulmi ke nuna wa dan'uwansa Musulmi kauna.
Me za ka ce dangane da Alhaji Bako Sakatare?
ALI: Gaskiya ni ban san irin godiyar da za mu yi masa ba. Gaskiya da muka je sai ya maida mu tamkar kannensa ne suka zo daga gida, ba maganar an dauko mu ne mu yi wani abu. Duk wani abu da ya kamata, irin dawainiya da mu da zirga-zirgarmu, duk shi ya dauki nauyi.
Shin, shi Alhaji Bako, gaba dayan harkokinsa a Jidda yake yin su ko kuwa yakan zo Nijeriya ya koma?
ALI: Yakan zo Nijeriya. Kuma shi Allah ya yi shi mutum ne mai son wasan Hausa, don ko a mujallar Fim na sha ganin wasikunsa. Da muka zauna, ya ba mu shawarwari da dama da suka shafi sana'armu. Yana nuna mana (cewa) yana kishin sana'armu. Ya nuna mana (cewa) daya daga cikin matsalolin da harkar fim din Hausa ke fuskanta ita ce ba a dauke ta da daraja ba kamar yadda a kasashen waje aka dauke ta.
Tunda ka dandana dadin fim a Saudiyya, nan gaba idan bukatar haka ta taso za ka iya komawa can ka shirya wani fim da 'yan wasan da ke can?
ALI: In kasuwar fim ta bukaci haka, idan na yi haka na kai kasuwa zan samu riba, ko da ba mai yawa ba ce, sai in yi.
Menene zai fi kwanta maka a rai game da wannan tafiya?
ALI: Gaskiya yadda aka karbe mu da hannu bibiyu.
A Saudiyya akwai lokeshin kamar jamfa a Jos!
-Ahmed
FIM: Ahmed, yaya labarin tafiya?
AHMED: Alhamdu lillahi, domin tun a filin jirgi na nan Kano muka fara haduwa da mutane wadanda ba su taba haduwa da mu ba ido-da-ido har suna nuna mana cewa idan mun sauka a can za su ba mu masauki. To sai muka nuna masu ai mu ma ba tafiyar kanmu ba ce, gayyatarmu aka yi.
Ahmed S. Nuhu
|
Masu masaukin naku sun tarbe ku da kuka isa can?
AHMED: Mutane masu dimbin yawan da ba mu zata ba sun zo tarbarmu. Muka yi ta gaisawa da su, kowa na so mu shiga motarsa. Da muka sauka a masauki kuwa nan ma mun samu mutane da yawa. Haka suka rika kawo mana abinci iri daban-daban. Kai, a takaice dai sai da muka kai safiya guda cur muna zaune muna hira.
Ashe ka ga wasu 'yan fim wadanda suka koma can da zama.
AHMED: Ban yi tsammanin zan ga wasu a can ba sai bayan da na sauka na ga har da ma wadanda ban ma san ashe suna can ba.
Ka yi ziyarce-ziyarce kuwa?
AHMED: Mun kai ziyara a Madina, muka je kabarin Manzo (s.a.w.), kuma muka yi harami, muka je Makka da dare. A can na yi addu'o'i, na yi Safa da Marwa. Ni sai abin ya yi ta ba ni mamaki, don kawai abin na san daga Ubangiji ne: ga ni a Kasa Mai Tsarki! Gari ne kayatacce, wallahi!
Ka dan taba yawo a cikin gari?
AHMED: Na yi yawo a kasuwanni, kamar babbar kasuwa ta Muhammad Sa'eed wadda ake ji da ita, da kuma kasuwar Badadiyya inda ake sayar da kayan bal; za ka samu iri daban-daban. To na je can na sayi jersey (rigar kwallo).
Ka shirya fim a can. Ashe kai dai riba uku kenan: ga talla , ga umra ga fim!
AHMED: (dariya) Ka san da farko mun shirya za a yi fim din ne a Legas. To da muka je Saudiyya sai muka ga lokeshin kamar kasa, ga su nan wurare daban-daban. Sai muka nemi izini, muka fara. To yanzu ka ga babu zancen zuwa Legas kenan, sai dai mu je Abuja mu karasa.
Ali ne daraktan shirin a can; shin ka ji wani bambanci ganin cewa shi sabon darakta ne?
AHMED: Ai ka ga da yake kwararren dan wasa ne, mutum ba zai gane sabo ne ba. Sai dai kawai Ali kan nace ya ce sai ya samu abin da yake son ya samu kafin a dora wa mutum kyamara. Kuma karfin gwiwar da muka samu shi ne yadda Ali ke bai wa Larabawa umarni kansa tsaye.
Da wasu 'yan fim mazauna can kuka hada kuka shirya fim din, ko?
AHMED: E. Kuma na gode masu saboda karamcin da suka nuna mana, da kuma yadda suka saki jikinsu tamkar ba su dade da barin Industry ba. Wallahi da, ni na dauka sun manta fim. Wadannan 'yan wasa suna da yawa, sai da muka canza tsarin labarin na Kusufi, yanzu har Larabci akwai a ciki.
Ashe za ka dade ba ka manta da wannan tafiya ba.
AHMED: Musamman yadda mutane a can suka dauke mu. Kai har yanzu din nan muna samun labari wai wasu ba su yarda mun taho ba. Yadda ka san shugaban kasa haka mutanenmu na can suka dauke mu. Wallahi mun gode masu!
Alhaji Bako Sakatare fa?
AHMED: Ai sai dai godiya kan yadda ya rike mu, da yadda yake hulda da mutane da yadda yake aiki. Kafin mu iso gida har wasu kayanmu sun riga mu isowa. Allah ya kare Bako Sakatare daga sharrin mutane! Wani abin da na yi mamaki shi ne yadda suke samun labaran abin da harkar fim ke ciki, tamkar suna Kano. Suna kallon finafinan Hausa sosai, suna aiki da e-mail kuma har kungiya gare su ta masu karanta mujallar Fim a intanet, suna kuma yin wasiku ta e-mail ga mujallar Fim.
A karshe me za ka ce?
AHMED: Ba zan manta da Malam Isa Sakatare ba wanda shi ne sakataren Bako Sakatare, da Sima, da Kabiru Isa. Na gode wa kowa da kowa, ba ma su kadai ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|