Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Ra'ayi Ba Gaba Bane
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Al-Amin da A'isha
Yanayin soyayyarmu

Ita zai aura ko Wasila? ·

Soyayya
Al'amin da A'isha

Daga ALIYU A. GORA II da IRO MAMMAN a Kaduna

BA kowace soyayya ba ce ake labarinta a fagen shirin fim irin wadda ke tsakanin darakta Al-Amin Ciroma da jarumar shirin Daren Farko, A'isha B. Umar. Wadannan 'yan fim su biyu sun sha tayar da muhawara a cikin fagen shirin fim na Kaduna, ba domin komai ba kuwa sai domin irin bayyananniyar sadaukarwarsu ga kaunar da ake ganin suna yi wa juna. A kullum tare suke, kuma duk inda ka ga zara, to babu shakka za ka ga wata.

Al-Amin Ciroma yana daga cikin daraktocin finafinai da ake ji da su a Kaduna. Da farko mun tambaye shi dalilin da ya sa su daraktoci sukan yi amfani da wata dama, idan suna soyayya da yarinya, duk fim din da za a yi sai sun tabbatar sun saka ta a ciki, ya-Allah ta dace da matsayin da suka ba ta ko ba ta dace ba. A ganin Al-Amin, "Gaskiya wannan ci-baya ne." Ya ce, "Na fada kuma na maimaita: ci-baya ne. Kuma gaskiya wannan shi ne ke karya mana kwarin gwiwa game da wannan aiki. Kowannenmu ya sani."

Ra'ayinsa shi ne, "Idan mace kana soyayya da ita, wannan ba za a iya hana ka ba. Amman idan aka zo maganar fim, to ka duba ka gani, shin matsayin da kake so ka ba ta a fim ya dace da ita? Wasu daga cikin abokan sana'armu sukan ce wai darakta yana iya tankwasa furodusa ya yi abin da yake so a fim. Wannan ba haka ba ne.

"To amma dai ba a ki ka yi soyayya da yarinya ba, in ka ga dama ma duk shot din da ka dauka tana kusa da kai-iyakar soyayya dai kenan ko? To amma ka dauko wadda ta dace ka sa a fim, wannan shi ne adalci."

Shi kansa daraktan yana daga cikin wadanda ake suka a bayan fage da cewa duk fim din da ya yi aiki a kansa, A'isha B. Umar ce take fitowa tauraruwar fim din. A kan wannan, sai ya amsa, "Ni ba ni ke zaben 'yan wasa ba. Yawancin finafinan da na yi daraktin dinsu nakan tambayi furodusa, 'Wa ka zaba, su wanene 'yan wasanka?' Ya kawo mani su a rubuce. Kuma kamar yadda ka ce, honestly a nan Kaduna yawancin furodusoshi ita A'isha B. Umar suke dauka, su ce ita suke so ta zama tauraruwar fim dinsu. To wannan ba zabena ba ne."

Wannan kam gaskiya ne. Domin kamar yadda wani furodusa da ya yi aiki da Al-Amin ya fada, shi furodusan da kansa ne ya zabi yarinyar domin ta fito a matsayin jarumar fim dinsa, ba Al-Amin ba. "Yarinyar ta iya wasa a fim, domin duk abin da aka sa ta ta yi za ka ga ta yi shi yadda ya kamata," inji furodusan, wanda ya ce a sakaya sunansa.

Da Fim ta tambayi Al-Amin batun soyayyarsa da ita A'isha, sai gogan naka ya wayance, ya ce, "Ba abin da zan iya cewa," sa'annan ya yi dariya.

Ban da A'isha, daraktan kuma yana yin wata soyayyar da fitacciyar jarumar nan Wasila Isma'il. Wannan ma ba boyayyen abu ba ne a fagen shirin fim na Kaduna. Hasali ma dai abin da ake cewa shi ne wai ruwan ido ne ya hana shi zabar wadda yake son ya aura a tsakanin matan biyu. Wani abu da ya daure wa jama'a kai shi ne duk da yake an ce ya kai kudin gaisuwa gidan su A'isha, to kuma wai ya kai kudi gidan su Wasila, ga shi kuma ba a jin biyu zai hada ya aura.

A kan maganar aurensu da A'isha, sai ya ce wa wakilinmu, "Na tabbatar kai kana daga cikin manyan abokaina. To ina ganin kai za ka ba wasu labari ba kai za a ba."

A hirarsa da Fim, Al-Amin ya ki fadin wadda ya fi so tsakanin A'isha da Wasila, amma ya ce shi ma ya "sha jin" ana maganar aurensa da Wasila a gun mutane.

"Kuma har yanzu ina ji. Amman abin da nake so, kamar yadda na fada a baya, kai abokina ne; insha Allahu duk abin da ake ciki nan gaba za ka sani... Allah ya sa alheri."

Batun cewar ya aika da kudin gaisuwa gidan su A'isha a kan maganar aurensu, Al-Amin ya ce, "A gaskiya wannan sirri ne. Ba abin da ya kamata mutane su sani ba ne a yanzu tukun."

Sa'annan batun ko dai har yanzu bai tantance wadda zai aura ba ne tsakanin 'yan matan, sai ya kada baki ya ce, "To duk dan Musulmi, duk sa'ar da ya yi salla yakan roki Allah ya yi mashi zabi na alheri." Ya kara da cewa, "Kwarai ba ka yi kuskure ba, ina nan ina rokon Allah ya zabar mani mafi alheri."

Wato dai da Wasila Isma'il da A'isha B. Umar ba wadda ta san matsayinta a wajensa kenan? Al-Amin ya yi dariya ya ce, "Gaskiya ba abin da zan ce maka a nan. Saboda, ka ga na farko muna tare da Wasila kusan shekaru da dama. Kusan tunda ta fara fim muke tare da ita a fim, har abin da kuke gani a zahiri... ana ta korafi a kai... To kowace daga cikinsu tana da nata matsayi a wajena."

Shin yana nufin daga cikinsu akwai wadda yake so da aure, akwai kuma wadda budurwa ce kawai ta waje? Al-Amin ya amsa: "Maganar auren nan mu bar ta kawai!" Ya yi dariya.

Sa'annan da ake cewa duk a cikin 'yanmatan da ke industiri Wasila da A'isha kawai zai iya soyayya da su, Al-Amin ya ce: "Ai ka gane, duk abin da ya fi kwanta wa mutum a rai shi zai yi."

Ga alama dai duk wannan abu babu mai warware shi dalla-dalla sai daya daga cikin 'yan matan daraktan. Wannan ko ita ce A'isha, wadda aka ji tana cewa ta fi kusa da shi fiye da Wasila.

Da farko dai, wacece A'isha? Menene tarihin rayuwarta? To bari ku ji. An haifi A'isha a cikin 1982 a Birnin Kebbi. A nan ta yi makarantar firamare, daga baya aka maido ta Kaduna ta karasa a makarantar je-ka-ka-dawo ta Rigachikun. Asalinsu 'yan Kebbi ne kuma 'yan kabilar Zuru.

Da fari ba ta son ta bayyana cewa ita 'yar Zuru ce, har ta ce wa wakilinmu a fusace, "To wannan kuma abin sirri ne, ina da yare ko ban da shi, wannan ba ta shafe ka ba!" Da aka matsa mata da tambaya ne sai ta amince: "Fadi da kari, ya wuce wai. Ni 'yar Zuru ce."

A'isha ta fara fitowa a fim ne a cikin shekarar 2000, lokacin da ta fito a shirin Rudani. Daga nan ta fito a wasu finafinan, kamar su Adali 2 inda ta fito a matsayin matar Ahmad S. Nuhu, sai Fauziya, Sassauci, Hikayah (wanda ya fito kwanan nan), sai kuma Daren Farko.

To me ya sa ta yi sha'awar shiga shirin fim?

A'isha ta amsa: "Ni gaskiya abin da ya sa na shigo harkar fim ra'ayi ne."

Kan batun aure, wanda 'yan wasa mata da dama suke son su yi, jarumar ta ce, "Ina da ra'ayin aure. Zan yi aure nan ba da dadewa ba in Allah ya so."

Wasu 'yan wasan, musamman mata, sukan samu matsala da iyayensu idan za su shiga harkar fim. Ita ko A'isha, cewa ta yi iyayenta "wayayyu ne."

"Sun san ba iskanci nake yi ba, kuma sun ga irin alheri da nake samu."

Mun tambayi 'yar wasan wane fim ya fi kwanta mata a rai daga cikin finafinan da ta yi. Ba tare da wata-wata ba, ta ce, "Daren Farko." Dalilinta shi ne , "Don shi ne aka fi ba ni dama na kuma hadu da gogaggun 'yan wasa." A shirin, wanda bai fito ba tukuna, A'isha ta fito ne a matsayin budurwar Ahmed S. Nuhu wadda aka hana ya aura, aka kuma ba da aurenta ga Hamisu Iyan-Tama. Ba shakka ta yi wasa da fitattun jarumai irin su Iyan-Tama, Ahmad, Maryam Mashahama, A'isha Musa, Sani Moda, da sauransu.

"Abin da ya sa fim din ya fi kwanta mani a rai," inji ta, "shi ne lokacin daukar shirin an nuna gwanintar aiki, ba a yi fada ko sa-in-sa da kowa ba, kuma har aka gama ba a bata mani rai ba. Kuma aka biya kowa hakkinshi a kan lokaci."

Wani abu da mahalarta daukar fim din suka yi la'akari da shi shi ne irin soyayyar da A'isha da Al-Amin suka rika bayyana wa juna a fili a wurin daukar shirin. Lokacin hirarmu da ita, jarumar ba ta boye batun soyayyar ba. Gatso-gatso ta ce, "Maganar soyayya tsakanina da Al- Amin Ciroma ba karya ba ne. Muna soyyaya..." Ta kara da cewa, "Ya aika gidanmu da gaisuwa kuma an amince mashi. Shi ya sa ka ga duk lokacin da zan je lokeshin in ba da shi ba, zai yi wuya ka gan ni a wajen. Kuma ni yanzu a rayuwata ba ni da wani saurayi a industiri da wajenta sai Al-Amin Ciroma."

Ita a ganinta ma, sam manemin nata ba ya da wata budurwa a cikin 'yan fim sai ita. "A gaskiya ni kadai ce," inji ta.

A takaice, ba ta ma yarda da cewa Al-Amin yana soyyaya da Wasila ba.

"Wannan kuma sai ka je ka tambayi ita Wasila da shi Al -Amin din. Amma ni a sanina, Al- Amin ya gaya mani cewa da shi da Wasila abokantaka ce kawai ke tsakaninsu."

Tarayyar Wasila da Al-Amin, inji ta, ba ta taba sosa mata rai ba.

To shin yaya za ta yi idan soyyayar da Fim ta san tun tuni ta sarke tsakanin Al-Amin da Wasila ta zama aure fa?

A'ISHA : "Ai za mu iya zama tare, in dai mun fahimci juna."

Akwai wasu abubuwa da suke ba yarinyar sha'awa game da Al-Amin dinta har ta ga ba ta son kowa da aure sai shi. Na farko, "saboda yana da mutunci da rikon amana. Kuma ya tsare mani mutuncina, duk abin da nake so yana yi mani. Kuma saboda mutuncinshi duk inda na je ana karrama ni. Daga shi har matarshi ta gida."

Af, har matarsa? Ashe dai matarsa ba ta damu da cewa mijinta yana neman ya auro 'yar fim ta zama kishiyarta ba kenan. A'isha ta gaya mana abin da ta fahimta da matsayin matarsa kan wannan al'amarin, tana cewa matarsa ba ta da kishi. "Ba ta kishi, tunda ina zuwa har gidan, in dauki danta in tafi da shi ya wuni a gidanmu sannan in maida shi."

A'isha dai ta fi son ta auri mutum mai mata irin Al-Amin, domin "masu auren sun fi tabbas, kuma sun fi mutunci."

Game da batun Wasila dai, A'isha ta ce ita kam ta san abin da ta taka, in dai ana maganar Al-Amin ne. Ta ce, "Saboda na riga na san matsayina da shi, duk wadda ke son shi, ta yi ta gama fafarniyarta ta kara gaba ta bar ni da shi." Ta ce abin da ya sa ba ta nuna kishi da Wasila ba shi ne wai saboda "ni bai gaya mani suna soyayya ba."

Ita ko mujallar Fim, ta ji daga wata kwakkwarar majiya cewa Al-Amin dai Wasila zai aura, wai a ran 18 ga Oktoba din nan ma za a daura auren. Har an ga Wasila tana raba kayan anko a Kaduna, kuma tana cewa A'isha dai "mafarkin auren Al-Amin kawai take yi."

Da wakilinmu ya tuntubi Wasila a gidansu kan wannan al'amari, hushi ma ta nuna kan yadda mujallar Fim ta bayyana a watan jiya cewa akwai soyayya tsakanin Al-Amin da A'isha. A ganinta, A'isha ba ta ishe ta kishi ba, kuma wai aurensu da Al-Amin yana nan daram dakam za a yi shi. Ta ki ta yi bayanai a kan al'amarin.

Shin ko dai ita A'isha tana jin tsoron nuna kishinta a kan Wasila ne don ganin ta fi ta daukaka a fagen shirin fim? A nan, sai A'isha ta hasala, ta ce, "To ai mu ma Allah zai daukaka mu kamar yadda ya daukaka ta."

Wannan gaskiya ne, kuma kowa akwai lokacinsa. Yanzu dai finafinan A'isha sun fara fitowa, musamman ma dai Hikayah, inda take jaruma. Nan gaba kadan kuma za a gan ta a Daren Farko a matsayin jarumar shirin. Idan har aka dade ba ta yi aure ba, to ga alama za a dama da ita sosai a fagen shirin fim. To Allah dai ya nuna mana ranar.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin