Allah ya yi:
Wasila ce Al-Amin ya aura ba wata ba!
Ango bai je walimar aurensa ba, amma abokansa Nasiru Garba Funtuwa (a hagu) da A.S.Muhammad (a dama) sun halarta. Ga amarya nan a tsakiya
|
Daga WAKILINMU a Kaduna
DUK da yake an tsara cewa za a daura auren furodusan fim din Wasila, El-Sa'eed Yakubu Lere, a ranar Asabar, 6 ga Oktoba, 2002 a Zariya, amma ba labarin auren ba ne babban labari a wannan ranar. Babban labari shi ne na auren jarumar shirin na Wasila, wato Wasila Isma'il Ibrahim, wanda aka yi niyyar daurawa a daidai lokacin da hankalin 'yan fim ya raja'a kan auren Lere a Zariya. Tuni wakilanmu suka kyaro dabarar su Wasila, wato a daura mata aure a asirce da masoyinta Al-Amin Ciroma ba tare da wani dan fim ya halarta ba. Shi ya sa, maimakon wakilanmu su tafi Zariya, sai suka tsaya a Kaduna don su ga irin wainar da za a toya a kofar gidan su Wasila.
Don haka tun da misalin karfe 10 na safe wakilinmu da aka sa ya yi hira da wadanda al'amarin auren ya shafa, Aliyu Abdullahi Gora II, ya isa kofar gidan, yayin da sauran wakilanmu suka kafa kunne a wasu wurare da suke jin sun jibinci labarin auren na Wasila. Da Gora ya isa, bai ji da dadi ba, domin kuwa jarumar ta zazzage shi saboda tana hushi da labarin da ya yi a Fim ta watan jiya inda aka ruwaito Al-Amin da jarumar shirin Daren Farko, A'isha B. Umar, suna bayyana yadda soyayyarsu take. Wasila ta ji haushin yadda aka gaya wa duniya cewa ba ita kadai Al-Amin yake so ba, a'a akwai wata budurwar a cikin zuciyarsa (Dubi yadda suka yi, nan gaba a shafukan wannan mujallar). Abin da ba ta gane ba shi ne shi dan jarida abin da aka gaya masa ko ya binciko shi yake fadi. Labarin soyayyar saurayin nata da wata yarinyar ba zuki-ta-malle ba ce, gaskiya ne.
Shi ma labarin soyayyarta da Al-Amin, wanda dan wasa ne kuma daraktan fim a Kaduna, gaskiya ne. Sun fara soyayyar kusan shekara daya da ta wuce, bayan ya kwace ta daga abokinsa jarumin shirin Dare Daya, Yakubu Nuhu Danja. Wata majiya ta ce shi Danja shi ne saurayin Wasila, kuma Al-Amin ne ke raka shi zance, to amma wai Wasila ta yanke shawarar ta yi soyayya da abokinsa na kut da kut saboda ta dago cewa shi ma yana soyayya da wata yarinya da take ganin ta fi aji.
Da Danja ya gane cewa soyayya ta fara ruruwa a tsakanin budurwar tasa da abokin nasa, sai ya dan yi hushi; ya dauka ba inda abin za shi. Amma ina! sai wutar soyayyar ta yi karfi har kowa ma ya san halin da ake ciki. Shi kuma ya yi zuciya ya rabu da su. Ba a dade ba sai jarumar ta koma Kano, inda ta bude wani sabon shafin soyayya da dan wasa kuma darakta Zulkifilu Muhammad (Zik). Dalilin komawarta Kano shi ne farin jini da kuma daukakar da ta samu sanadiyyar fim din Wasila, mai dauke da sunanta; saboda haka a Kano ta samu fitowa a finafinai barkatai, yawanci saboda tsayawar da sabon masoyinta ya yi mata. A nan ma soyayya ta yi karfi, har ana maganar aure, to amma bayan kusan shekara daya, sai abin ya watse. Sakamakon batawarsu da Zik sai ta bar garin, ta koma gida Kaduna inda a nan ma ta samu yin finafinai, koda yake duk mai lura da al'amarinta ya san cewa tauraruwarta ta fara yin sanyi.
Dawowar Wasila Kaduna ta sa dankon soyayyarta da Al-Amin ya kara karfi har suka fara maganar aure. To matsalar abin ita ce, tun kafin ya fara soyayya da Wasila shi Al-Amin ya yi wa wata yarinyar alkawarin zai aure ta, kuma ta sadaukar da kanta kacokam gare shi. Wannan ko ita ce A'isha. A gaskiya, a fagen shirin fim na Kaduna ba a taba ganin wani yana yin soyayya irin wadda 'yan wasan biyu suke yi ba. Duk inda A'isha za ta, musamman in dai daukar fim ne, to sai ya raka ta. Abin mamaki, dan wasan ya kuma yi irin wannan sadaukarwar ga Wasila, wadda aka ce tana da tsananin kishi, amma duk kishinta ta kasa raba saurayin nata da A'isha. Haka aka yi ta tafiya, kowace daga cikin 'yanmatan tana fatan a ce ita ce zai aura. Shi kuma -ko ruwan ido ne? - sai ya kasa tsaida magana daya; ba ya nan ba ya can, duk 'yanmatan kowace kamar ta kama yizgar zuciyarsa daya tana ja.
Yakubu Nuhu Danja dai yana Katsina, inda ya koma da aiki a wani kamfani, kuma ya kafa kunne yana sauraron yadda wannan badakalar za ta wanye.
Sam, Al-Amin bai yi niyyar yin aure a yanzu ba, inji manyan abokansa. "Akwai matsalolin da yake son ya warware," inji wani da ya ce a sakaya sunansa. Ya ci gaba da cewa, "Ka ga dai yana da mata har da haihuwa. To kwanan baya sai ya yi gobara a dakin matarsa, lokacin da yake gasa kafarsa da garwashi. Ya fita yin ko menene? sai wuta ta tashi a dakin, ta kone dakin kaf, ba abin da matar ta dauka domin babu kowa a dakin. To, so yake ya dan mayar wa matar da wasu abubuwan kafin ma ya fara tunanin yin wata."
Akwai tsegunguma da aka rika yadawa game da daraktan da kuma wadannan masoya nasa, wasu ma babu dadin ji. Amma dukkansu ba su hana wadannan soyayyoyi kala biyu din nan su bunkasa ba. Har ma mutane suna mamakin yadda dan wasan yake soyayya da 'yanmata biyu a lokaci guda, ga shi kuwa Shata ya taba cewa, "Ba a yin damisa biyu a fage."
Wasila ta fi A'isha wayo, a ganin wasu. Domin ta fi jawo shi jika don ya aure ta. Tuni ta yanke shawarar cewa ita dai aure take so ta yi, musamman da yake sa'o'inta da ke wannan sana'a ta fim da yawa suna ta yin aure; tana so ita ma kada guguwar aure da ke kadawa a wannan zamanin ta wuce ta. Don haka sai ta matsa wa saurayin da ya fito su yi auren in dai da gaske yake yi. Majiyarmu ta ce sai ya dinga ce mata ta jira shi tukun. A gefe daya kuma ya rika yi wa A'isha alkawarin ita zai aura, har ma ya ce mata karya ne da ake cewa wai zai auri Wasila.
To, ashe ita ma A'ishar da wayonta. Hirar da ta yi da mujallar Fim ta watan jiya a kan soyayyarsu ta jawo wa Wasila rudewa. Domin kuwa A'isha ta nuna cewa ita ce Al-Amin zai aura. Wannan ya sa Wasila, wadda da fari ta yada a tsakanin jama'a cewa a ran 18 ga Oktoba za a yi aurensu, ta tada kayar baya a kan cewa lallai sai a yi aurensu "yanzu ba tare da bata lokaci ba," idan ba haka ba kuwa to ashe duk abin nasa bogi ne.
Ba ta tsaya a nan ba, sai ta dauki wasu matakan. Al-Amin yana zaune a farkon Oktoba sai kawai ga sako daga gidan su Wasila cewa ana nemansa. Aka ce ya turo magabatansa a sanya ranar daurin aure. Shi ko bai shirya ba. Kamar wasa, aka sa ran 5 ga Oktoba a matsayin ranar da za a daura auren. Wata kawar Wasila ta ce duk Wasilar ce ta kulla wannan ta yadda ana dawowa daga daurin auren Lere sai mutane su ji an ce, "Ita ma Wasila an daura nata." Wani abokin Al-Amin ya ce Al-Amin ya nemi ya bulke a kan cewa a dan bar shi ya shirya, amma aka share shi. Da ranar ta zo, wakilinmu ya isa gidan da ke kan 'Gwari Road', amma ba a daura auren ba domin yayanta da zai daura ya ki zuwa. Wasila dai mahaifinta da mahaifiyarta suna nan da ransu a gidan.
Washegari sai aka taru a kofar gidan wanta din da ke layin 'Yantukwane a Tudun Wada, aka daura auren da 'yan mutane kalilan. An yi duk yadda za a yi a boye al'amarin ga sauran jama'a in ban da wadanda ke unguwar, sai kuma kalilan da suka zo daga wani wuri. Musamman 'yan fim abokan sana'ar ma'auratan, an ki yarda su san ma za a daura auren. Wani abokin Al-Amin ma, Nasiru Garba Funtuwa (Mai Daukar Hoto), an ki yarda ya san inda za a daura auren koda yake da fari an bar shi ya dan san ranar da za a daura din.
Yin auren da garaje kuma cikin sirri ya tada muhawara a tsakanin jama'a inda ake tambayar dalilin yin hakan. Wasu gani suke akwai abin da ake kokarin a boye wa duniya, amma kuma ba a san ko menene ba. Wata 'yar wasa ta ce, "Wasila fa ba ta da kawa a industiri yanzu. Ina jin gani take mu duka munafukai ne, shi ya sa ba ta son ta gayyaci kowa. Amma ta yi kuskure." Wani sabon darakta kuma cewa ya yi, "Tsoro suke ji wai kada abin da ya faru a auren Balaraba ya faru saboda bakin mutane. Ka san akwaiwannan camfin banzan a industiri. Amma dai wannan ai jahilci ne. Kuma wai ma dakata, idan ban je daurin auren Wasila ba sai me? Sai duniyar ta tsaya?"
A wurin daurin auren, 'yan fim biyu ne kadai aka gani, daga shi ango sai babban abokinsa dan wasa A.S. Mohammed. Wadanda suka gan su a lokacin sun ce Al-Amin a rude yake. "Ko me ke damunsa? Oho!" cewar wani. An ce wai lokacin da aka daura din ma a guje angon ya bar wurin saboda kidimewa. Sai daga baya A.S. ya same shi ya hau bayan Besfar da suka je a kanta, A.S. ya tuka suka bar unguwar.
Bayan an daura auren kuma an so a yi tarewa ba tare da bata lokaci ba. Amma ango bai shirya ba; bai tanaji daki ba, kuma ba ya da isassun kudi. Don haka yana so a ba shi lokaci ya kimtsa sosai, ya gayyaci 'yan'uwa da abokan arziki wadanda suna hushi da shi a kan cewa bai sanar da su ko da wasa cewa zai yi aure ba, sai dai kawai suka tsinci labarin a gari. A lokacin, labari ya fara watsuwa a garuruwa, musamman a tsakanin 'yan fim, cewa wai Wasila ta yi aure. Duk dan fim din da ya ga dan'uwansa sai ka ji ya ce, "Wai da gaske Wasila ta yi aure?"
"Ni ma haka na ji," ita ce amsar da mutum zai samu.
Wasu sukan bayyana murnarsu da jin labarin, wasu kuma tsaki suke yi suna cewa, "Wasila da Al-Amin sun raina mutane; yaya za a yi a ce sun yi aure ba su gayyaci kowa ba? Wato dai sun yi irin na Momo kenan. To ai gara Momo da yake shi kasar waje aka tafi aka dauro auren. Wannan ko ba su da hujja."
Akwai wadanda suka ji haushin Al-Amin a kan kin auren A'isha da ya yi, suna cewa ya yaudare ta. Ba ma kamar wadanda suka san zurfin kaunar da yarinyar ta nuna masa. Wasu kuma na cewa ai a matsayinsa na namiji yana da damar ya yi haka, domin wata rana ai zai iya aurenta "idan matasshi ce."
Al-Amin yana sane da duk irin wadannan maganganun. Kuma abin na damunsa. Shi ya sa ya so a yi tarewar a nan gaba. Ga alama, Wasila na so a tare nan da nan domin kada a ce auren da ta tsara ta gudanar ya gamu da matsala. Don haka ita da 'yan'uwanta suka sanya sanarwa a rediyo cewa za a yi bikin tarewa a rana kaza. Ba su ma damu su tsara komai da angon ba. Shi ma a rediyo ya ji cewa wai za a yi tarewarsa. Don haka ma da aka yi walimar "tarewar" sai ya ki halarta, sai abokansa A.S. Mohammed da Nasiru Garba Dan Funtuwa ne suka je. Da aka gama biki kuma, maimakon a kai amarya gidan miji sai ta koma gidansu. Aka yi kwanaki sannan ita da angon suka hadu.
Bayan kwanaki dai an kai amarya gidan da ta kama masu haya, wanda aka nema a gurguje, wato gida mai lamba 12, 'Birnin Gwari Street', a unguwar Mando.
Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin, ba mu tabbatar ko angon ya tare a gidan ba, amma dai wakilanmu sun gan shi suna yawo tare da A'isha B. Umar, kuma an ji shi yana cewa ita ma aurenta zai yi ba da dadewa ba. Wato zai yi mata uku kenan - uwargidansa, da amarya Wasila da kuma amarya A'isha.
"Ni abin da ke ban mamaki," inji wani abokin angon, "shi ne yadda Al-Amin ya shiga rudu irin wannan, ga shi mutum mai sanyin rai kuma hafizi. Wallahi kai ka ce auren dole aka yi masa." Wani ko cewa ya yi, "Duk wadannan maganganun da kake ji, shirme ne. Aure dai an riga an yi, kuma abin da ya dace ne tunda raya sunnar Manzo ne. To mutane su kyale Al-Amin da amaryarsa su sake mana! Idan ma wuta ce ya kunno da kansa ai ya san inda zai nemi ruwa ya kashe ta, tunda shi ba karamin yaro ba ne."
Yanzu na san mai sona, na san makiyina
Inji Al-Amin
AL- AMIN CIROMA ya tattauna da wakilinmu ALIYU ABDULLAHI GORA II kan yadda surutai suka dabaibaye wannan aure, da kuma tunaninsa a kan makomar auren. Sau biyu angon yana tattaunawa da mujallar. A hirar farko jim kadan da daura auren, ya bayyana dalilin da ya sa aka yi auren kusan a asirce, da bacin ransa kan yadda wasu suke ta yada surutai a kan auren, da batun cewa budurwar abokinsa ce ya kwace, da sauransu. Bismilla:
HIRA TA FARKO (Jim kadan bayan daurin aure):
Al-Amin Ciroma: 'Mijin mace hudu'
|
Fim: Al-Amin, me ya sa ba ku gayyaci mutane zuwa wajen daurin auren nan ba?
AL-AMIN: To, am, ba gayyata ce ba a yi niyyar yi ba, sai dai kawai abin da ke faruwa shi ne, wata matsala ce ta cikin gida tsakanin iyaye, wadda suke ganin hanya mafi sauki da za su iya magance ta, ita ce su daura auren, sannan su ba da damar duk lokacin da za a shirya bikin tarewa sai a gayyaci 'yan'uwa da abokan arziki.
Fim: Da farko mujallar Fim ta binciko cewa kun shirya a yi daurin auren ne ranar 18 ga Oktoba, me ya sa kuka canza zuwa 6 ga watan?
AL-AMIN: Shi ne nake gaya maka, wata matsala ce ta cikin gida, tsakanin kuma iyaye, ya sa har aka sauya wannan rana, wanda kuma hakan zan iya tabbatar maka da cewa kowannenmu bai san hakan aka yi niyya ba sai da ranar ta zo. A gaskiya ba ni son in yi dogon bayani, amma ina so in tabbatar maka da cewa kusan dukkanmu, ni dai ta bangarena ban san cewa a wannan ranar za a daura auren ba. To matsala ce kamar yadda na fada a baya. Amma ina ba kowa hakuri game da rashin gayyata.
Fim: To yanzu yaushe ne za ku yi bikin tarewa?
AL-AMIN: E, shi ne kamar yadda na gaya maka, a yanzu haka tunda muna da hanyoyi da dama na sadarwa, musamman ma mujallar Fim, za mu sanar da kowa idan lokacin ya zo.
Fim: To kamar yadda kuka canza ranar daurin auren, wannan kun yi shi ne don gudun faruwar wani abu da zai iya hana daura auren in kuka jira zuwa 18 ga watan?
AL-AMIN: A'a, da ma ba wai an ce akwai... Ni dai a iya sanina ban taba tunanin cewa akwai wata matsala ba. Domin in ma akwai, Allah kadai ya bar ma kansa sani. Kuma in kana Musulmi, ka san cewa abin da za ka iya yi shi ne, in ka sa wani abu a gabanka ka roki Allah ya tabbatar maka da shi. Kuma duk sharrin da ke cikinsa Allah ya kiyaye shi. To ni dai na san ban yi tunanin cewa akwai wata matsala da ake hange shi ya sa aka dawo da shi baya ba, sai dai kawai wata matsala ce ta cikin gida.
Fim: Ka ce ba ka san za a daura auren a ranar 6 ga Oktoba ba, amma sai ga shi an gan ka a wurin daurin auren. Ya aka yi ka samu labari har ka halarta?
AL-AMIN: E, a lokacin da muka tafi da mutanen gidanmu aka je aka zauna. Manya suka zauna suka tattauna, to ina jin ban da ni din, in ba abokina na kut-da-kut ba, babu wani wanda zai kai su, tunda ni na san gidan da aka ce a hadu. To shi ya sa na kai su. To bayan sakamakon tattaunawar da suka yi, suna fitowa kawai suka ce to ga hukuncin da aka yanke.
Fim: An ce ita Wasila ce ta dauki nauyin daurin auren.
AL-AMIN: Ni sai yanzu nake jin wannan daga wajenka.
Fim: Kafin maganar daurin auren, ka dauke kafa daga industiri. Ka yi hakan ne saboda ba ka son a san abin da ke gudana tsakaninka da Wasila?
AL -AMIN: Ni yanzu ba a shirye nake da in yi dogon bayani a kan maganganun da ke tasowa ba. Ba irin abin da ba a fada ba. Wasu ma sun ce na haukace, wasu sun ce an yi mani asiri, wasu suka ce kurciya aka yi mani... kai, akwai ma wanda ya ce faskare ma nake yi domin don in tabbatar cewa an yi wannan aure. To ni ba a shirye nake da in yi wata magana a kan masu maganganu ba. Don suna yi ne, kuma ba barin yi za su yi ba. To amma abin da kawai zan gaya wa kowa shi ne, a cikin Alkur'ani mai girma, Allah cewa da ji, da gani dukkansu abin tambaya ne ranar alkiyama. To abin da kawai zan ce wa mutane shi ne, mutum ya fadi abin da yake alheri.
Fim: Me ya sa iyayen Wasila suka zaku da a daura auren cikin gaugawa ba ma tare da saninka ba?
AL-AMIN: Kamar yadda na fada a baya, matsala ce ta cikin gida tsakanin iyaye, su kuma suke ganin mafi saukin hanyar da za su bi su warware wannan matsala, shi ne su daura auren.
Fim: Wasu mutane suna cewa ka ci amanar A'isha B. Umar.
AL-AMIN: E, to, wadannan maganganu sun zo kunnena, kuma har sunayen, ...kai, kowa... duk wani wanda ya san ya furta wani abu a kaina, da A'isha ko da Wasila, ya sani cewa na sani, na samu labari kuma na san kowane ne. Na san wanda ya fadi alheri kuma na san wanda ya fadi sharri. Saboda haka "cin amana" suna ya tara. Na tabbatar cewa wanda duk aka ci amanarsa, ya san an ci amanarsa. To abin da nake gode wa Allah shi ne har yau babu wani wanda ya taba fitowa fili ya ce wai ni din nan na ci amanarsa. Saboda haka masu wadannan maganganu kamar yadda na fada a baya, su nemi abin ya don Allah.
Fim: Tun ranar da aka daura auren nan, ka taba kwantawa da tunanin makomar A'isha idan ka yi la'akari da matsananciyar soyayyar da ke tsakaninku?
AL-AMIN: Wannan ba abin da zan tattauna da kai ba ne. Ba abin da zan ce game da wannan.
Fim: Yanzu menene matsayin ita A'isha a wurinka?
AL-AMIN: mu je "next question" (tambaya ta gaba).
Fim: An ce duk da kasancewar an daura aurenka da Wasila, har yanzu kana nan a kan bakanka cewa sai ka auri A'isha.
AL-AMIN: Shi ne na ce maka ko a yanzu duk abin da ya shafi maganganu da rade-radi, ina jin su, don haka wallahi ba su sha mani kai ba.
Fim: Kana ganin ba za a ce ka auri Wasila ba ne domin ka yi suna saboda ka ga ta yi suna a harkar fim, ko kumaa ce ka kwaikwayi su Fati da Sani Mai Iska ba?
AL-AMIN (dariya): To zan maimaita abin da na fada a baya. Idan mutum ba zai fadi alheri ba, to ya ja bakinshi ya yi shiru ya fi. Ai in na dubi matsayina, shiga harkar fim ba nawa ba ne. Saboda a yanzu haka idan na je garinmu Adamawa to mutum ma zai yi tunanin cewa wani ne ma ya kamata ya rabu da ni ya karu.
Fim: To kai me ya sa ka yi sha'awar auren Wasila?
AL-AMIN: Ammm... Wannan tambayar tana bukatar dogon nazari. Abin da nake so in gaya maka shi ne, na farko, za ka iya sanin farkon abu, amma ba ka san karshenshi ba, ko ba ka gane ba? Yanzu ko haduwa ka yi da mace ka ce kana son ta, wannan son ba ka san yadda zai zama ba. To Allah ke hada zukata biyu lokacin da ya ga dama; Allah ke hada aure tsakanin wani da wata.
Fim: Yaushe ka fara soyayya da Wasila?
AL-AMIN: Gaskiya an dai dauki lokaci kawai.
Fim: Da farko abokinka ne ya fara nemanta bayan sun bata kai kuma ka maye gurbinsa ko?
AL-AMIN: To ai gara a ce ka auri budurwar abokinka da a ce ka nemi matar aure.
Fim: Ita Wasila ka yi mata akwatuna, ko ko dai duk ta dauke maka wannan dawainiyar?
AL-AMIN: Wannan tambayar ba ni ya kamata in amsa ta ba. Idan aka tambaye ta ita, kila za ta iya fadin cewa ga abin da na yi ga abin da ban yi ba.
Fim: Gida daya za ka ajiye ta da uwargidanka, ko gidanta daban?
AL-AMIN: Wannan matsalata ce.
Fim: Kana ganin ba za a zargi cewa akwai wani abu tsakaninka da Wasila da ba ku so a sani, shi ya shi kuka yi aure a boye ba?
AL-AMIN: To ai maganganu dai suna ta kaiwa da kawowa. Ni dai na yi imani da abu daya: ban taba nufin wani da sharri ba. Shi ya sa ma ni ban taba tunanin cewa ina da makiyi ba sai da al'amura suka bullo. Da ma ba za ka san wanene ke tare da kai ba sai in wani abu ya same ka. Ni yanzu na san su wanene ke sona so na Allah da Annabi, kuma na san su wanene makiyana.
Fim: Wasu na cewa wai asiri Wasila ta yi maka har aka daura maku aure ba da saninka ba.
AL-AMIN: To ai wanda aka yi wa asiri ba ya sani.
Fim: Bayan an daura auren, ka samu matsala da iyayen A'isha. B. Umar?
AL-AMIN: Shi ne nake gaya maka a tsarin tambayoyin da za ka yi mani wannan ba ya ciki.
Fim: Amma gaskiya ne cewa Wasila da budurwar abokinka ce?
Al'amin: Ammm... (dariya) Abokina, kamar wa?
Fim: Yakubu Nuhu Danja.
AL-AMIN: Yakubu Nuhu Danja..., ina ganin wannan tambaya... Uhm... ka gane ko Gora? Yakubu ya kamata ka samu ya ba ka amsa!
Fim: Da gaske shi abokinka ne?
AL-AMIN: Duk wanda muka shigo harkar nan ni na dauka ga baki daya kowa abokina ne; akwai amini, akwai aboki, akwai dan'uwa. To, duk wanda ke harkar fim abokina ne kuma dan'uwana ne.
Fim: Amma kana da masaniyar cewa Wasila da shi Yakubu sun yi soyayya?
AL-AMIN: E, na sani.
An ce tare da kai ma yake zuma tadi wajenta.
AL-AMIN (dariya): Ammm... to ba zan ce makaomai ba.
Za ka bar Wasila ta ci gaba shirin fim?
AL-AMIN: To ai wannan ba sai na fada ba, kai ka sani. Ba Wasila ta fara aure a cikin 'yan fim ba. Ka taba ganin wadda mijinta ya bari ta ci gaba da shirin fim? Ai inda akuyar gaba ta sha ruwa, ta baya ma nan za ta sha.
To Allah ya bada zaman lafiya.
Ba auren Wasila ne aka fara yi a boye ba
Inji madaurin auren
ALIYU ABDULLAHI GORA II ya tattauna da wan amarya Wasila, MALAM ISMA'IL UBA IBRAHIM, wanda shi ne ya daura mata aure da rabin ranta Al-Amin Ciroma. A hirar, ya fada mana yadda aka yi auren da kuma wasu abubuwa da ba a sani ba game da Wasila, Al-Amin, da shirin auren:
Isma'il Uba Ibrahim...Wan amarya
|
FIM: 'Yallabai, bari mu fara da samin cikakken sunanka.
ISMA'IL: Sunana Isma'il Uba Ibrahim. Ka ga ko Isma'il din nan da ka ji tana amsawa, sunan kakanmu ne. To ni kuma sai na gaji sunan, shi ya sa ake ce mani haka.
Fim: Ana rade-radin cewa kai ka daura wa Wasila aure da Al-Amin a boye.
ISMAIL: E, ba rade-radi ba ne; a gaskiya kam na daura mata aure ranar 6 ga Oktoba, 2002, wato ranar Lahadi kenan.
Fim: Angon ya ce ba ya da labarin cewa a ranar za a daura auren.
ISMA'IL: To ai ba zai ce bai sani ba tunda tun farko, mutumin da kai ka zo ka ce kana so, ka ji ka gani kuma ka nuna irin son da kake yi wa yarinya, ai ba wata maganar a ce bai sani ba. Tunda ni da shi mun yi magana na gaya mashi cewa ga ranar da za mu daura aure. To ina maganar bai sani ba kuma?
Fim: Amma ya nuna maku rashin amincewarsa kan ranar da kuka yanke hukunci daura auren?
ISMA'IL: Ba wata maganar nuna rashin amincewa, sai dai ka sanyawanci, sai da yawa idan, musamman ga ald'adarmu ta Hausawa, idan za a yi abu irin haka da yawa akan ce ana son a sanar da iyaye da abokan arziki, dangi da sauran mutane haka nan saboda a tattaru a zo a yi abu gaba daya. To misali yanzu kamar yadda ita Wasila fitacciya ce, an san ta, shi ma Al-Amin din ba boyayye ba ne kuma kusan dukkansu harka daya suke yi na sha'anin fim din nan, to ka san sau da yawa sukan zaci wani abu da suka raya ma zuciyarsu. Misali, yanzu yadda suke sanannu din nan suna so ya zamanto aurensu an san shi ko'ina, kamar yadda aka yi na Fati Mohammed. To amma abin da mutane za su fahimta shi ne, ba duka mutum ne yake so hayaniya irin wannan ba.
Kuma in ka duba, ka ga addininmu na Musulunci ai bai ce kada a yi murna ba, amma in abin ya zama kamar hananiya haka, wato ya zama kamar almubazzaranci za a yi ko barna da sauransu haka nan... Kuma ka ga ai, kuma irin aure a boye ai ba kanta aka fara ba; mun ji labarin Momo ya yi aure, ba a san ma ya yi auren ba, sai dai muka ji labarin ya yi. To ka ga da ma shi aure yana bukatar shaidun ango ne da kuma na amarya. To in aka samu wannan kuwa ai ya wadatar. Ake daura aure a masallaci ma… ka ga ko mutane biyu aka samu, in dai an samu shaidu, ai ya wadatar, aure ya dauru.
Fim: Wace matsala ta sa kuka canza ranar daurin auren daga 18 zuwa 6 ga wata?
ISMA'IL: Kamar yadda na gaya maka, ka san yawanci rayuwa ba ta rabuwa da matsaloli ko da yaushe. To sau da yawa da ma abubuwa kan zo, wadanda sukan danne wasu a wani lokaci. To a gaskiya wasu abubuwa ne suka dan taso da suka danne wancan din har aka canza ranar, ba wai ana gudu-gudu ba ne ko kuma sauri ko wani abu, a'a wasu 'yan matsaloli ne dai suka taso suka danne shawarar farko, amma duk da haka bikin tarewa za a yi shi ranar 18 ga Oktobar nan.
Fim: Ba ka ganin za a yi tunanin ko akwai wata matsala a tsakanin ma'auratan da ba ku so ta bayyana kafin a kai 18 ga wata, shi ya sa kuka zabge kwanakin zuwa 6 ga wata?
ISMA'IL: A'a to ai duk dan'adam yana tare da matsala. To misali kana mai gida ma, ai dole ne ka yi tunanin cewa ya za a yi ka je ka samu abin da za ka ba iyalanka su ci. Ka ga wannan ma ai matsala ce. Saboda haka don wai mutane sun je suna zargin ko akwai matsala, wannan ka san kowa yana da damar yayi tunanin abin da yake so.
Fim: Shin angon ya yi wa amarya kayan aure, wato kamar akwantuna masu taya da sauransu, ko ko sadakin kawai ya samu biya ku kuma kuka yanke hukuncin daura auren ko bai shirya ba?
ISMA'IL: Abin da nake so ka fahimta da shi shi ne aure ba ya daurawa idan ba a daidaita ba. Shin menene ma maganar aure? Ai sadaki shi ne maganar aure, in ya kawo sadaki ya ce a daura mashi aure da matarsa ko ko ya ce ga abin da zai iya bayarwa, kuma ta amince iyayenta sun amince… to, sai ya kawo mana Kaduna gaba daya? Mu ba ruwanmu da wannan. Mu abin da muke fata kawai shi ne Allah ya ba su zaman lafiya shikenan.
Fim: Wasu suna ganin ko kun boye auren ne saboda tsoron kar abin da ya faru lokacin bikin marigayiya Balaraba ya faru da su?
ISMA'IL: Kar ka manta, an ce tsoro fa gaskiya ne, yauwa. Kuma idan ma haka ne, ai ba kuskure aka yi ba. Kuma ba wai ana tsoron wani abu ya faru ba, duk dan'adam mai numfashi mamaci ne. Saboda haka tunanin ma cewa kana tsoron kar ka mutu, wannan shirme ne. To ba wai tsoron kar abin da ya faru da Balaraba ya faru da Wasila ya sa aka boye aurenta ba.
Fim: Wane bayani za ka yi mai gamsarwa a kan dalilin da ya sa ba ku gayyaci mutane zuwa wurin daurin auren ba?
ISMA'IL: To ka san sha'anin jama'a, duk abin da za ka yi ba za ka gamsar da wani ba. Amma duk mai tunanin cewa an saba mashi a kan rashin gayyatarshi, mun dauke shi masoyi; saboda haka a yi hakuri mun yi kuskure. Wadanda kuma suka zo mun gode masu, Allah ya saka da alheri.
Fim: Ganin yadda Wasila ta yi suna, ana ganin kamar sadakinta ba kowane namiji zai iya biya ba, shi Al-Amin akwai wani sauki na musanman da kuka yi mashi har ya samu ya biya? Ko kun tsauwala masa?
ISMA'IL: A'a to ai maganar tsauwalawa ba ta taso ba. Saboda ina ganin kamar cinikin dabbobi ne, idan ka je saye duk abin da mai su ya sara maka, ka ga dole ka biya. In ma ya ga cewa kai mai hali ne yana iya cika maka kudi. Amma dan'adam, a!, ko addinin Musulunci ma ai ya kayyade sadaki. Ai kamata ya yi a ce, ba ma mu kadai ba, ko wanene ma, ya yi tunanin cewa ba sai ka tsauwala mashi ba. To in ko ka tsauwala mashi ya kake so kuma ya je ya yi? A gaskiya ba wata maganar tsauwalawa tsakaninmu da Al-Amin. Abin da muka san zai iya yi shi muka sara mashi.
Fim: Sadakin da kuka sara masa ya kai naira dubu goma?
ISMAI'L: E, to, ba zai kasa naira dubu goma ba, kuma ba zai wuce ba.
Mun gode.
Wasila ba ta isa in kira ta 'Yaya' ba!
Cewar A'isha B. Umar
A'ISHA B. UMAR ce yarinyar da wasu suka zaci Al-Amin zai aura, har ita kanta ta bugi kirji a Fim ta watan jiya ta ce ita zai aura din domin wai ya yi mata alkawarin hakan, kuma ya ce mata ba soyayyar yin aure yake yi da Wasila ba. Shin an kasa ta kenan? Tana jin haushi? Wane mataki za ta dauka?
A'isha, wadda ta fito a matsayin jaruma a shirin Hikayah wanda ke kasuwa, ta gaya wa wakilinmu cewa ita ba a kasa ta ba domin har yanzu ba ta yanke kaunar cewa Al-Amin zai aure ta ba, wato ta zama matarsa ta uku. Kila wasunku su ce wannan magana tata bambami ce kawai ko borin kunya ko kuma furucin kananan yara. To amma A'isha ta san abin da ta taka, kuma in ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa, to tabbaci hakikan ya taka dutse ne. Wane irin dutsen ne ta taka har take wannan magana? Duk da yake 'yar wasan ta yi iyakar kokarinta na nuna cewa ba ta damu ba, idan mai karatu ya yi karatu da idon basira zai lura da makamai masu linzami wadanda ta harba wa Wasila a cikin kalaman da ta furta a nan. Me ta ce?
Al-Amin da A'isha
|
FIM: A'isha, me za ki ce game da auren da aka daura na Wasila da rabin ranki Al-Amin?
A'ISHA: E to, a gaskiya ni ma ina jin jita-jitar cewa wai wai wani an daura aure. To in ma an daura, sai in ce Allah ya ba su zaman lafiya. Ni ba ni bakin ciki da cewa ya aure ta kuma har ila yau ban cire tsammanin cewa Al-Amin zai aure ni ba saboda namiji mijin mata hudu ne. Ni dai na riga na san in ba zan kwace ma wata saurayi ba. Ba kwantai na yi ba. Saboda haka ni harkar aurensu ba wai ta dame ni ba ne saboda shi kanshi angon bai canza mani ba. Idan ya canza mani shi ne zan sai cewa ba ya sona, yadda muke da shi har yanzu muna nan a haka.
FIM: Kina nufin har yanzu maganar aurenki da shi tana nan?
A'ISHA: Akwai maganar aure a tsakaninmu.
FIM: Kin san cewa za a daura aurensu a ranar Lahadi, 6 ga Oktoba,2002?
A'ISHA: Ban sani ba. Ai ni dai wai na ji. Har goro aka kawo mani. A.S. Mohammed ya kawo mani goro, na kuma ci.
FIM: Ya kika yi a jikinki yayin da kika samu labarin cewa an daura auren?
AI'SHA: Wallahi tallahi in na ce na yi bakin ciki, na yi karya, saboda sunna suke rayawa, kamar yadda suke cewa. Saboda haka ni ban yi bakin ciki ba. Idan ya aure ta sun zama su biyu kenan a wajenshi; ka ga saura biyu kenan a bayanta, ni kuma in na zo ka ga na zama ta uku.
FIM: Yanzu haka kuna shirin aure da shi bayan ya auri Wasila?
A'ISHA: Akwai shirye-shiryen aure.
FIM: Kina ganin za ku yi zaman lafiya da Wasila idan Al-Amin ya aure ki ya kuma ajiye ku a gida daya?
A'ISHA: Ko daki daya za mu zauna da ita ba abin da ya dame ni da harkarta!
FIM: Shin ba ki jin kunya a idon mutane idan kika yi la'akari da hirarki da Fim ta buga kwanan nan inda kika ce ke Al-Amin zai aura ba Wasila ba, sai ga shi kuma ita ya aura ya bar ki?
A'ISHA: E, na fada kuma na kara fada din cewa ni Al-Amin zai aura ba Wasila ba. Saboda me kuwa na fadi haka? Wannan 'yar maganar da na fada wai ita ce ta tada bala'i a cikin gidansu, cewa sai an kamo shi an daura mashi aure (da Wasila). To, an daura mashi, ya ja akuyar mu gani!
FIM: A ranar da kika ji an daura auren wane mataki kika dauka?
A'ISHA: Gaskiya ni ban... To an dai daura aure, amma amarya dai tana gefe!
FIM: Za ki iya daukar abin da Al-Amin ya yi maki a matsayin cin amana?
A'ISHA: Gaskiya kar ku dauka a matsayin cin amana saboda mutumin da aka riga aka sha gabanshi, sai hakuri da addu'a; kuma sai dai mu roki Allah ya fidda shi daga kangin da ya shiga.
FIM: Yanzu menene matsayinki a wajensa?
AI'SHA: Yadda muke.
Zuwa yaushe ne za a yi aurenki da shi?
AI'SHA: Ni yadda aka boye nasu ni ba wai zan boye nawa ba ne; in lokaci ya yi za ku sani.
FIM: Yanzu ke kin dage cewa lallai lallai sai kin auri Al-Amin?
AI'SHA: Ban ce lallai lallai sai na aure shi ba. Aure nufin Allah ne, yadda Allah ya hada su ni ma ina sa rai, tunda yana sona ni ma ina sonshi.
FIM: Akwai wani fatan alheri da za ki yi wa ma'auratan?
AI'SHA: Next question! (tambaya ta gaba)
FIM: Ranar da aka daura auren, shi Al-Amin ya zo wurinki kamar yadda ya saba?
A'ISHA: Kwarai, Al-Amin ya zo wurina.
FIM: Da ya zo ya gaya maki da kansa cewa an daura masa aure da Wasila?
AI'SHA: Ban ji a bakinshi ba. Saboda na san mutum ne da yake gudun bacin raina.
FIM: Yanzu idan kika aure shi, duk wata matsala ta kare kenan tsakaninki da Wasila? Za ki yi mata duk biyayyar da ya kamata amarya ta yi wa uwargida?
AI'SHA: Bari in gama sakacen naman da Al-Amin ya saya mani don Allah... Ni (Wasila) ba ta da matsayin da zan ce mata 'Yaya'! Kuma ba ta da ajin da zan zage ta. Saboda ajinta bai kai na in zage ta ba. In na zage ta ma hakorina ciwo zai yi.
FIM: To A'isha mun gode, kuma Allah ya kyauta.
A'ISHA: Amin.
Al-Amin Bafillace ne, shi ya sa ya ruga!
Cewar babban aboki
A.S. MOHAMMED (wanda aka fi sani da suna 'A.S.' a fagen shirin fim, ma'aikacin shige-da-fice (immigration) ne a Kaduna. Ya fito a fim din Gagarabadau a matsayin dansanda, sannan shi ne jarumin shirin Maina, wanda bai fito ba tukuna, kuma akwai shi a wasu finfinai masu fitowa irin su Arziki da Ibro Soja.
A.S. ne babban aboki a auren Wasila da Al-Amin. A tattaunawarsa da Fim, ya kara zuba haske a kan harkallar wannan aure da aka yi shi cikin asiri.
A.S.Muhammad
|
Fim: A.S., a matsayinka na babban abokin ango, me za ka ce game da wannan aure wanda aka daura a boye?
A.S.: Alhamadu Lillahi. Aure tsakanin Al-Amin da Wasila Allah ya yi. Ba wani abin da zan ce illa Allah ya ba su zaman lafiya.
FIM: Me ya sa ba ku gayyaci kowa zuwa daurin auren ba?
A.S.: E, to a gaskiya an samu matsala ne ta bangaren iyaye. Don a hakikanin gaskiya ni kaina ban san cewa a ranar za a daura auren ba.
FIM: Kana ganin masu karatunmu za su gamsu da cewa wai ba ka san za a daura auren ba, bayan kuma kai ne babban aboki?
A.S.: E, to gaskiya wannan haka yake. Da farko dai, an sa ranar daura auren ta zama ranar 18 ga Oktoba, 2002. To ana nan, sai kuma dangin ita Wasila suka taru suka tattauna, sai aka ce an maida shi ya dawo 5 ga Oktoba. To, wato dai abubuwa suka dinga canzawa. Sai Al-Amin ya same ni a gida ya ce in raka shi ya gaida wan Wasila. To muna zuwa sai shi wan Wasila din ya ce a gaskiya sun yanke hukuncin cewa za a dauren a rannan. Muka ce to mu kuma ga shi ba wani shiri da muka yi. Su kuma suka tsaya kai da fata cewa lallai sai an daura auren a rannan.
FIM: A ganinka an yi wa angon adalci da aka yanke hukuncin daura masa aure ba tare da saninsa ba?
A.S.: To... (shiru)... a takaice ba zan iya ce maka shi bai sani ba, amma ni kam gaskiya ban sani ba. Amma shi ma a yadda ya nuna mani, cewa ya yi bai sani ba. Saboda haka a nan maganar adalci ba ta taso ba. Saboda ba mu gayyaci 'yan'uwa da abokan arziki ba. Kuma wannan gaskiya bai yi dadi ba. Don bayan an daura auren da yawa sun koka da rashin gayyatar.
FIM: Me ya sa ku ba ku ce ba ku yarda a daura ba tunda ba ku shirya ba?
A.S.: E, to, ni dai a bangarena gaskiya ban ji dadi ba. To amma tunda shi angon ban ga ya yi wani abu ba, ka ga ni ba ni da wani katabus.
FIM: A naka tunanin, me ya sa iyayen Wasila suka yanke hukuncin canza ranar daurin auren?
A.S.: E, to ni ina ganin suna tsoron abin da ya faru da auren marigayiya Balaraba ne.
FIM: An ce kai ne ka dage cewa sai Al-Amin ya auri Wasila maimakon A'isha.
A.S.: A'a, ba wai na dage ba, shi dai abokina ne, kuma duk abin da ka ga abokinka na so-matukar bai saba ka'ida ba-ai ka ga kai ma dole ka so shi. Musamman tunda ka ga akwai maganar aure, ka ga ba zan ce kar ya aure ta ba. Shi ya ga abin da ya hango.
FIM: Wace shawara ka taba ba shi dangane da soyayyarsa da A'isha da kuma ita Wasila?
A.S: To gaskiya yana tare da A'isha kafin ita Wasila, kuma ka san shi aure nufin Allah ne. Maganganu sun taso game da wannan. To amma tunda ban ga ya motsa ba, ka ga ni ba wani motsi da zan yi. Shiya san wadda ta fi dacewa da halinshi.
FIM: To kana ganin akwai yiwuwar aure tsakaninsa da A'isha, duk da cewa ya auri Wasila?
A.S.: Kwarai da gaske. Ai shi namiji ne, kuma shi mijin mata hudu ne.
FIM: An ce lokacin da aka daura auren, shi angon rugawa ya yi, sai da aka kamo shi.
A.S.: (dariya) To, ka san shi Bafillace ne, ka kuma san su da kunya. Ba mamaki kunya ce ta sa ya ruga!
Fim: Amma kai ka taba ganin inda aka je daurin aure ango ya ruga?
A.S.: To, (dariya) ka san na gaya maka Bafillace ne, kila kunya ta sa ya ruga.
FIM: To Allah sa alheri.
Amin.
'Ba a gayyace ni bikin aurena ba!'
Ango ya ce wannan aure ya jawo masa matsala da abokai, dangi da iyayensa
A karshe dai an yi bikin tarewa ba tare da ango ba; amarya ta koma gidan iyayenta. Ango bai ji dadi ba, yana ganin iyayen amarya da ita amaryar sun fara daukarsa mijin hajiya. Sakamakon wannan tunanin, ango Al-Amin ya tattaki zuwa wurin wakilinmu Aliyu abdullahi Gora II inda ya bayyana abin da ya kira da rashin adalci, tare da cewa iyayensa da danginsa sun yi hushi da shi saboda ya "share" su a bikinsa. Amma ya kamata mai karatu ya sani cewa bayan wannan hirar da Al-Amin, Wasila dai ta tare a wani gida da suka kama ita da mijin nata a unguwar Mando a wajen garin Kaduna, inda take fatan za su yi zaman kwanciyar rai da shi.
Fim: A lokacin da aka daura aurenku, ba ku gayyaci kowa ba, amma daga baya ka yi alkawarin gayyatar 'yan'uwa da abokan arziki idan za a yi bikin tarewa. To sai ga shi an yi bikin a ranar 18 ga Oktoba, 2002 amma ba ku gayyaci mutane ba. Me ya kawo haka?
AL-AMIN: E, na yi alkawarin. To a gaskiya da ban so in ce komai ba, amma sai na ga ya zama wajibi in yi magana. Wato abin da ya faru shi ne, ni dai na san cewa an bada damar idan aka daura auren nan a haka, za a bari zuwa lokacin da aka ga ni na shirya, na gama duk tsare-tsaren da ya kamata in yi, sannan sai mu sanar wa mutane cewa za a yi biki lokaci kaza. A haka muka ajiye magana. Sai kwatsam a cikin satin da ya gabata, a lokacin ma ni ina gida kwance ba ni da lafiya, a ranar Laraba, sai mutane suka rika gaya mani cewa wai sun fara jin sanarwa a rediyo cewa za a yi bikinmu a ranar 18 ga Oktoba. Na ce masu, "To, ni ban sani ba." Aka yi ta tafiya a haka. Sai da ita kanta Wasila ta zo gaishe ni a gida, na ce mata, "Ni fa ga maganganun da na fara ji. Menene gaskiyar al'amarin?"
Sai take ce mani to kila iyayenta ne ke son a yi bikin a ranar 18 din. Na ce, "A'a, to ya za a yi haka, bayan mun samu matsala an daura aure mutane ba su sani ba?" Kuma na nuna mata cewa ni ga yadda na san mun ajiye magana. Kai, har dai ta kai ga mun tashi mun tafi gidansu a ranar.
Da ni da A.S. Mohammed muka samu babban wanta wanda ya daura mata aure da ni, muka tattauna da shi, na gaya mashi duk abubuwan da na ji. Sai ya ce, "A'a, to yaya za a yi haka bayan an ajiye magana?" Sai yake cewa to ai tunda ma ga shi an zo gab da azumi ga hidimomin Sallah a gaba, ai kila ya kai Disamba". Sai muka ce mashi, "To ai mu abin da muke so kenan saboda mu samu isasshen lokaci mu shirya." Sai ya ce to zai je gida ya tattauna da su. To ran da ya je ya tattauna da su, sai ya ce in je in same shi in ji yadda suka yi. To na je a kan hakan. Sai ya ce mani su fa suna nan a kan bakansu cewa ranar 18 za a yi biki. Ni kuma na ce mashi, "Gaskiya ba zai yiwu ba, saboda ban shirya ba!" Sai ya ce mani to shikenan zai je su sake tattaunawa. Duk da haka sai na ci gaba da jin sanarwa, ban daddara ba na sake komawa na gaya masu cewa a gaskiya fa, musamman ni da nike da 'yan'uwa a nesa, ga abokaina da yawa, ina da bukatar in fitar masu da hakkinsu.
Ranar 17 ga Oktoba, kwatsam, sai ga Wasila ta same ni a gida ta gaya mani cewa, "To gobe ne fa!" Na ce mata, "Wai ku kuna nan a hakan bayan na gaya cewa ban yarda ba tunda ban shirya ba?"
Muka dai rabu a haka. Mutane suka yi ta yi mani surutu ina gaya masu cewa ba ni da masaniya. Kawai sai dai na ji wai an yi biki!
FIM: Ya kake ganin mutanen da ke kallonka da mutunci za su dauke ka? A ce ka yi aure amma tun kafin ta tare abin da take so shi ake yi!
AL-AMIN: To ka san wani duk rantsuwar da za ka yi mashi ba yarda da kai zai yi ba. Amma dai ni kam a zahirin gaskiya abin da 'yan gidan su Wasila suka yi mani ba haka na so ba!
FIM: Ka taba dauka cewa abubuwan da ke faruwa tsakanin ka da su Wasila akwai yaudara, tunda kuna ajiye magana daga baya su canza ba tare da sani ko yardarka ba?
AL-AMIN: Ni dai a gaskiya ba zan iya cewa komai ba, domin tunda an riga an daura auren ai na zama nasu, na kuma zama dan gidansu. To dan gidan kuma ai yana da hakkin ya yi magana a saurare shi. Ni haka na dauka. Amma Allah shi ne kadai ya fi sanin sirrin da ke cikin wannan al'amari!
FIM: Yanzu tunda an yi bikin tarewa, Wasila tana gidanka kenan?
AL-AMIN: To ni dai tun ranar da aka ce an yi biki, har yau ban sa Wasila a idona ba. Don haka ni ma ban san abin da ake ciki ba.
FIM: Ko maganar auren nan ta jawo matsala tsakaninka da 'yan'uwanka ko iyayenka?
AL-AMIN: A gaskiya akwai, babba ma. Domin idan na takaice maka, yanzu haka a gidanmu 'yan'uwana sun sanya mani ido ne kawai. In ma na wuce kallona kawai ake yi. Abokaina haka. Gaskiya wannan abin ya jawo mani zagi, wasu tsine mani suke yi, ana cewa na yi auren bariki, maganganu dai ga su nan iri-iri.
FIM: Yanzu idan 'yan'uwanka suka juya wa auren baya, wane mataki za ka dauka?
AL-AMIN: To har ila yau dai duk abin da ya shafi 'yan'uwana ina bin su ina gaya masu. Idan Allah ya sa sun fahimce ni yadda da ni da ita za mu samu kwanciyar hankali, to alhamdu lillahi. In kuma hakan ba ta samu ba to ina ganin su ne ya kamata su dauki matakin da ya kamata.
FIM: Za ka iya daukar abin da iyayen Wasila suka yi maka a matsayin rashin adalci?
AL-AMIN: Wuce wannan tambayar!
FIM: Idan mai karatu ya yanke hukuncin cewa ba a yi maka adalci ba, ya yi daidai?
AL-AMIN: Ya yi daidai. Domin ka san wani ba zai yarda a yi mashi haka ba.
FIM: To Allah ya kyauta.
Yadda muka yi da Wasila:
Na so in yi tonon silili a kan Zik da kuma Yakubu Nuhu Danja,
Inji Wasila
Arangamar Wasila Isma'il da wakilinmu Aliyu Abdullahi Gora II misali ne guda daya na irin wahalar da wakilanmu suke sha wajen samo wadansu labaran a fagen shirin fim na Hausa. A saboda wani dan dalili wanda bai taka kara ya karya ba sai ka ga dan fim ya botsare ya zama abokin gabar wannan mujallar tuburan. Sai ka ga ya manta da duka wani aikin alheri da muka taba yi masa. Sai ka ga ya nuna kauyanci da gidadanci da jahilci, ya manta da yadda mujallar ta taimaka masa a baya, ta fito da shi, ko ta fito da wata bajinta da ya yi. Haka dai ya faru a kan batuna auren Wasila.
Ita Wasila dai ta yi fushi da mu ne saboda hirar da muka buga ta Aisha B. Umar, jarumar shirin Daren Farko. Mu abin da ba mu sani ba a lokacin shi ne a tsakanin 'yanmatan biyu akwai matsanancin kishi da gaba wadanda suke yi a kan darakta Al-Amin Ciroma. A ganin Wasila, da yake ta fi A'isha yin tashe, A'isha ba ta isa ta ja da ita ba. Saboda haka don me Fim za ta daga A'isha ta nuna wa duniya ita a matsayin masoyiyar wanda take kauna? Kada a manta, kafin mu buga waccan hirar da A'isha da Al-Amin sai da muka tuntubi Wasila a gidansu domin ita ma ta fadi ra'ayinta, amma ta ki domin tana ganin A'isha ba ta isa ba!
Matar mutum kabarinsa: A nan tsohon saurayi Yakubu Nuhu Danja ne da Wasila suke yi wa juna kallon soyayya a wani lokaci can baya
|
Ga alama, ALIYU ABDULLAHI GORA II bai san zurfin kishin Wasila ba har sai da suka gamu lokacin da ya yi gigin zuwa gidan su jarumar da niyyar tattaunawa da ita kan aurenta. A nan ga labari daga bakinsa kan artabunsu:
WASILA Isma'il ba bakuwa ce a gare ni ba, haka ni ma ba bako ba ne a gun ta. Mun dade da sanin juna tuna shigowarta fagen shirin fim.
A kokarina na tattaunawa da ita a kan maganar aurenta da Al-Amin, na yi tattaki zuwa gidansu a ranar Alhamis, 19 ga Satumba, 2002, da misalin karfe 10 na safe. Da shigata muka yi ido hudu da ita, sai na ga ta murtuke fuska, alamar ba ta ji dadin ganina ba. Ko magana ba ta yi ba sai ta jiya kawai ta shige daki. Ni ko da yake ba bako ba ne ko a wurin iyayenta sai na bi ta har cikin dakin, na nemi wuri da zauna.
Na san dalilin wannan karbar da ta yi min. 'Yan kwanaki da suka gabata, Fim ta watan da muke ciki ta buga tallar labarin soyayyar A'isha da Al-Amin inda muka ce shin a tsakanin ita A'isha da Wasila wacece ta fi rike masa zuciya? Na san Wasila ba za ta so wannan tallar ba. A ofis, mun samu labarin cewa ta ji haushin musamman hoton da muka sa na A'isha da Al-Amin suna zaune dab da dab, har ya rike mata hannu. Wannan hoto dai A'isha dakanta ne ta kawo shi ofishinmu ta ce shi take so a buga a cikin labarinta da Al-Amin. Daga baya mun fahimci cewa ashe dabara yarinyar ta yi, tana so ta tsokano Wasila. Abin da ba ta sani ba shi ne ashe ganin shi hoton da kuma karanta labarin zai sa Wasila ta kidime har ta bukaci a daura auren ba tare da bata lokaci ba. Ni ko a wannan rana na zo ne domin in samu nata ra'ayin a kan soyayyar, musamman da yake na dauke ta wayayyiya mai karanta mujallu irin wadannan, ciki har da na Turanci kamar su Hints da Hearts. Kaico, ashe ban sani ba, ramin kura na fada!
To, zaunawarta ke da wuya sai wata yayar Wasila mai suna A'isha, wadda ke zaune a dakin, ta dube ni ta fashe da dariya, sannan ta dubi Wasila. Sa'annan kuma ta juyo ta tambaye ni, "Aliyu Gora II, me ya kawo ka? Ko ka zo tsegumin ne?"
Karf, sai Wasila a fusace ta ce, "Gulma ta kawo shi mana."
Sai na amsa, "Wace irin gulma?"
Fushinta na ta karuwa, Wasila ta ce, "Ai ka san abin da ka yi! Menene na daukar hoton wata karamar yarinya ka buga a mujalla tare da Al-Amin? Kuma har da sa sunana! Ai ni ba ruwana da ku."
Na yi dariya na ce, "To Wasila ki manta da duk wannan. Ni yanzu na zo ne in yi hira da ke game da soyayyarku da Al-Amin".
Fadin haka ke da wuya, sai ta bude mani wuta, tana cewa: "Ai ni da mujallar Fim har abada, na yanke hulda da ku! Kuma a da na yi maku tanadin labari, amma ba zan ba ku ba. Kuma bari in gaya maka: kayan dakina yanzu haka an gama". Ta ci gaba ta ce, "Labarin da na so in ba ku shi ne na yadda muka yi soyayya da Zik da yadda muka rabu da shi, da kuma irin soyayyar da muka yi da (Yakubu) Danja da kuma abin da ya sa na koma wa abokin shi Al-Amin. Don haka kun yi missing!" Sannan ta kare da cewa, "Ko ranar aurena wallahi kar ma ku zo, don ko kun zo ba zan saurare ku ba".
Da ta dire, sai na yi dariya na mike na ce, "To ni zan koma."
Sai ta daka mani harara ta ce, "To da ma wa ya kira ka? Don Allah malam ka fita daga gidanmu!"
Na kama gabana na tafi. Ana nan kuma sai labari ya same mu a ofis cewa za a daura auren 'yar wasan da Al-Amin a ranar Asabar, 5 ga Oktoba 2002, da misalin karfe 2 na rana, amma wai a cikin gida za a daura shi, kuma ba a son kowa ya sani daga danginta sai na angon. Abin ya ba mu mamaki, domin mun dauka sai ran 18 ga wata. Ana zaton wuta a makera sai ga ta a masaka kenan! Mu kuma aiki ya samu; ko Wasila na so ko ba ta so sai mun gaya wa jama'a labarin!
A ranar, karfe 10 na safe daidai na yi ina gidansu. A lokacin iskar wani bakin hadari tana bugawa. Da zuwa sai na fada ciki. Shigata ke da wuya muka yi arba da amaryar. Wayyo Allah! Ai sai ka ce an aiko mata da mala'ikan mutuwa! Ba wata-wata sai ta fara zunduma mani zagi tare da tambayata, "Me ya kawo ka gidanmu? Algungumi! Munafiki! Ka kama gabanka kawai!"
Na ce, "To a yi mani arziki in fake saboda ga hadari ya taso."
Sai ta ce, "Ba dai a nan gidan ba. Ka fita kawai!"
Wai ni dabara, sai na ce mata, "Al-Amin na zo nema."
Sai ta ce, "Ka je gidan su A'isha B. Umar. Nan ba gidansu ba ne…. Malam, na ce ka fita daga gidan nan!"
To gudun kada a ji ni ina sa-in-sa da amarya, sai na fita. Fitata ke da wuya aka fara ruwa. Kafin in a samu wurin fakewa, na jike sharkaf. Haka na dawo ofis sharkaf da ruwa.
To ka san abinka da dan jarida, ban yi hushi ba. Ban manta da cewa karfe 2 za a daura auren ba. Karfe 1:30 na yi, sai na tasar wa gidan. Na samu wani wuri daga nesa na labe, ina hangen duk abin da ke faruwa a kofar gidan. Ashe sanadiyyar zuwana gidan da safe ya sa aka canza wurin daurin auren, kuma aka ce sai gobe za a daura. Karfe 2.05 daidai na auka cikin gidan, amma ban ga alamar za a yi daurin auren ba.
Sai na aika aka kira mani A'isha yayar Wasila, muka yi ta hira har zuwa karfe 2:31. A cikin hirar ne sai na ce, "Ke A'isha wai ko ba za a yi daurin auren nan ba ne?"
Aliyu Abdullahi Gora II, Wakilin mujallar Fim
|
Sai ta ce, "Ai ba yau za a daura ba, sai gobe, saboda ba a ga Al-Amin ba."
Kwatsam, sai ga Wasila ta shigo gidan, ta kure adaka. Tana yin arba da ni sai ta yi kamar an watsa mata wuta. Ta ce, "Wai kai ba ka da zuciya ne? To wallahi kar ka kara zuwa gidanmu. Hirar ba dole ba ce! Ka fita ka ba ni wuri!"
Kai, da dai na ga ta tubure, za ta tara mani mutane, sai na hakura na kama gabana. Ga alama, masu karatunmu ba za su samu ganin hirarmu da Wasila a kan aurenta ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|