Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Sharri ne aka kulla mana

A'isha
A'isha B. Umar (Amani)

BABBAN abin da yawancin jama'a suka fi tunowa game da soyayyar daraktan nan da ke tashe a Kaduna da A'isha B. Umar, jarumar fim din Daren Farko wanda ya fito kasuwa kwanan nan, shi ne artabun da suka yi a kan batun auren Al-Amin din da fitacciyar jaruma Wasila Isma'il. Labarin da aka sani shi ne, A'isha da Wasila sun yi goyayya a kan wa za ta aure matashin Bafillanin, inda a karshe kaddara ta riga fata, aka daura wa daraktan aure da Wasila.

Ko shakka babu, da wuya idan Al-Amin ya taba yin soyayya da wata 'ya mace irin wadda yake yi da A'isha (domin fa har yanzu din nan suna nan tare). Idan muka ce za mu bayyana maku yadda soyayyar take, to mun yi wauta, domin fa sai mu cika shafukan nan 48 da labarin ba mu kare ba.

To, wani labarin wanda yawancin jama'a masu kallon fim ba su sani ba shi ne wata bakar furofaganda da ake ta yadawa yau kimanin shekara daya (tun cikin Fabrairu 2002) cewa wai Al-Amin da A'isha sun haifi wani yaro nasu na kansu a asirce, kuma sun boye yaron a wani wuri. Wannan labari kusan kowa ya san shi a fagen shirin fim. Wasu sun ce sun ga yaron da idonsu; wasu suka ce sun ji labarin yaron; wasu kuma suka ce an yi masu kwatancen gidan da aka kai yaron aka boye-wai a gun wata tsohuwa, ana shayar da shi. Abu dai kamar almara.

Shi ko Al-Amin, abin ya fi karfin almara a gunsa, domin kuwa a kullum da wannan abu yake kwanciya yake tashi; yana tunanin irin kallon da ake yi masa. Har sai da ta kai ya samu matsala da iyalinsa a kan al'amarin.

A yayin da abin ke damunsa shi da A'isha (wadda ta ce karya ake yi mata), har yanzu an kasa samun takamaimaiyar hujjar cewa akwai dan, ko kuma an haihu din. Mujallar Fim ta yi duk iya bincikenta ta kasa gano gaskiyar lamarin, don haka a yanzu ta dauki labarin a matsayin karya maras amfani, irin mai kai wanda ke yada ta Wuta.

A'isha dai ta ce ita ma labarin ya zo mata ne kamar daga sama, ta dauke shi labrin kanzon kurege kurum, wato irin wanda akan kirkira game da 'yan fim - misali a ce wane ya yi hadari ya mutu ko an sace Ibro ko auren Fati ya mutu, da sauransu. Ta fara jin labarin a ranar da Balaraba Mohammed ta rasu. da farko bai dame ta ba sai da ta ga yana ta ci gaba har kusan kowa ya san shi.

Mun waiwayi Al-Amin da nufin ya warware mana zare da abawa game da al'amarin da ba a son a yi masa maganarsa kai tsaye, sai dai a je bayan fage ana zundensa a kai. Ya amince ya tattauna da ALIYU ABDULLAHI GORA II a kan al'amarin, inda ya nuna dai sharri akae yi masa shi da A'isha. Bismilla:

Fim: Menene gaskiyar rade-radin da ake ba zawa wai A'isha B. Umar ta haihu, kuma wai shi ya sa ka ki yarda a daura maka aure da ita?

AL-AMIN: To, gaskiya ni ma na ji wannan magana. Amma a zahirin gaskiya ni iyakar abin da na sani shi ne, lokacin da aka gaya mani maganar na yi mamaki. Ina tunanin ta yaya za a yi wannan abu ya kasance a haka? To, ni ta bangarena dai na san babu wani abin da ya yi kama da cewa A'isha ta haihu. To in ma ta haihun, ni ba ni da wata masaniya ta wanene ke da hakkin abin.

Fim: Lokacin da ka samu wannan labarin, akwai wani bincike da ka yi don ka gano gaskiyar al'amarin?

AL-AMIN: E, na yi bincike. Abin da ya sa na ce maka na yi mamaki (shi ne) a lokacin da muka dade sosai, muka dan fara soyayya muka dan samu matsalA, mun dauki kusan shekara guda da wasu watanni ba mu ko ga maciji a tsakaninmu; kowa ya kama gabansa. To sai kwatsam, muna dandalin gala, aka zo aka ce mana ai ga zance ga magana cewa A'isha ta haihu. To, ni a lokacin, abin ya zo mani ana tsakiyar wata magana makamanciyar hakan. Akwai wata ma 'yar fim da ta taba haihuwa, wadda muna tsakiyar daukar shirin wani fim, wanda ni ne daraktan fim din, da muka fara fim din, sai washegari aka zo aka ce mana ai wance ta haihu. To (hakan) ya sa dole muka dakatar da daukar fim din.

To da aka gaya mani wannan zance, sai na ce afi ai ya yi kama da waccan maganar. Da farko ban yarda ba. To daga baya sai na ji maganganun sun yi yawa. Na ce to in dai wannan A'ishar ce, na san zan iya zuwa har gidansu in bincika. To, muna tashi daga Gala, da aka yi sallar Isha'i sai na je gidan, na yi sallama da ita.

Ta fito. Ta yi mamakin ganina, saboda a iya saninta dai ba mu ko ga-maciji da dadewa. Sai na tambaye ta, bayan mun gaisa, na ce mata, "Na ji wata magana ne, shi ya sa na zo da kaina in bincika."

Sai ta ce, "Game da me?"

Na ce mata, "Na ji an ce kin haihu."

Sai ta yi shiru na dan lokaci. Ta ce, "Don Allah wa ya gaya maka wannan maganar?"

Na ce, "A'a, ni ba na zo ba ne don in kalubalance ki, sai dai..."

Wannan shi ne abin da ya sa har muka samu matsala da ita na tsawon kwanaki. Na nuna mata cewa, "A rayuwa yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba. Sannan duk abin da da namiji ya yi, to ado ne a gare shi, amma mace fa?"

Ta ce wallahi karya aka yi mata. To ni ma a zahiri, lokacin da na ga abin a haka na ce to ta yaya za a ce mace ta haihu sannan ta fito tangaram? Har ma washegari, bayan mun yi wannan magana da ita, akwai wani fim da nake yi mai suna Fauziyya, to ita ce yarinyar fim din, sai furodusan (Sadisu Mohammed) ya zo ya same ni ya ce ya ji an ce A'isha ta haihu. To, ban ce mashi kala ba, na ce mashi ya je gidan tunda yau muna da wasa, ya je da mota su dauko ta, in ta haihun in ya je can ya ji. Da ya je sai ya dauko ta. Muka je kuma muka ci gaba da daukar shirin. Iya binciken da nayi kenan. Kuma wannan zuwa na gidan shi ya kara karfafa soyayyarmu har ma muka dinke. To, manta da abubuwan da suka faru, ni na ma manta da su, muka ci gaba da tafiya haka nan da ita. To amman har zuwa yau, maganganun daga wannan ya ce kaza, sai wancan ya ce kaza, amma ni dai Allahu ya'alamu.

Fim: A lokacin da aka fara yada wannan magana, hankalinka ya tashi?

AL-AMIN: Gaskiya hankalina ya tashi matuka, saboda a duk lokacin da za a yi maganar, ni ne na farko da ake danganta ma cewa ina da da tare da A'isha! To, kullum maganar kenan. Daga nan har Kano har ko'ina, duk dai inda aka san A'isha aka san ni, za a ce ina da da da ita. To ni kuma akwai lokacin da ma na fito nake gaya wa mutane cewa don Allah duk wani wanda ya san... ni dai na ce ban san komai ba, kuma ga zahirin abin da ya faru, in kuma za a lissafa lokacin da muke tare, da kuma abubuwan da suka faru, kowa ya sani. To amma in wani ya san cewa ga dan, ya fito da shi in gani.

Fim: Yanzu duk da irin yadda maganganun suka bazu, har yanzu ba ka ji kanshin gaskiyar al'amarin ba?

AL-AMIN: E, ai batun kanshin gaskiya bai taso ba. Domin fa na zaunar da ita, na ce mata, "Duba nan A'isha, ni ina so in tabba tar maki da abu daya. Soyayya Allah ke hada ta. Dangantakata aure Allah ke hada ta. Saboda haka ni tunda na gan ki na ce ina son ki, idan yau aka ce duk Kaduna 'ya'yanki ne gaba daya, zan iya aurenki a hakan. Kai, karshen ma maganar, idan ma a gidan karuwai kike zaune, idan na ji ina son ki zan iya zuwa gidan in dauko ki in dawo da ke in aure ki. Zaman aure zaman ibada ne." Na zaunar da ita na ce ta gaya mani tsakaninta da Allah, menene gaskiyar maganar haihuwar da aka ce ta yi? Ta rantse da Alkur'ani cewa ita wallahi FADI SONKAhi, na farko ba ta san da maganar ba, na biyu kuma ba ta taba haihuwa ba.

To ban tsaya nan ba. Sai na tafi har gidansu ni da aminina A.S. Mohammed (jarumin shirin Maina). Muka yi magana da mahaifinta. Ni na kasa ma fitowa in ce ga abin da yake tafe da mu. A.S. ya ce, "To Baba, abin da ke tafe da mu shi ne, ana yada cewa A'isha ta haihu. Shi ne muka zo mu ji matsayin maganar".

To shi ma mahaifin sai ya yi shiru na dan lokaci. Can ya ce gaskiya shi ma wannan zance ya zo kunnensa, amma ya yi iyakar bincikensa a matsayinsa na mahaifinta, har ma ya sa jami'an asibiti su bincike ta. Ya shaida mana cewa an bincike ta, amma har yanzu ba su ga wani alamun haihuwa tare da ita ba.

Fim: Akwai masu ganin kila boye maka gaskiyar al'amarin ta yi.

AL-AMIN: To ai bisa tsari, idan mutum ya fito ya fadi magana ya ce kaza ne, har ya yi maka rantsuwa kana Musulmi, ai dole ka ba shi uzuri. To wallahi, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kai in gaya maka, mun dauki lokuta da daman gaske ni da ita muna magana, ba abin da nake boye mata nawa. To ban ga dalilin da zai sa ita kuma in wani abu na damunta-ko kuma wani abu ya faru da ita-ta boye mani ba.

Fim: Yanzu idan ya kasance daga baya ka gano cewa lallai gaskiya ne ta haihu, akwai wani mataki da ka yi shirin dauka?

AL-AMIN: A, to ai da ma duk wanda ya yi abu, in har boyewa ta yi ai da ma ramin karya kurarre ne. Karkari, kai duk tsiya wata rana gaskiya za ta yi halinta!

Fim: Ka taba tunanin za ta iya lika maka dan ta ce naka ne?

AL-AMIN: A'a, ban taba tunani ba, saboda ta nuna mani cewa ita ba ta yi ba. Kuma abokaina da na gaya masu su ma sun bincike ta, ta ce ita ba ta haihu ba, babu wannan magana.

Fim: Yanzu wannan maganar ta je har kunnen iyalinka?

AL-AMIN: Ba inda ba ta je ba. Saboda ni din nan har ma an taba yi mani kawanya haka a gida aka zaunar da ni, aka ce mani ga maganganun da aka ji-cewa ina da da da wannan yarinya, me na sani? Na bayyana masu gaskiyar abin da ni na sani. Ban da wannan, abokaina wadanda maganganun ke bata masu rai sukan zo su same ni su ce ga abin da suka ji, amma ya aka yi haka? In na bayyana masu suka gane za su ce to gaskiya su abin da daurewar kai. To in takaice maka labari, wallahi har yanzu kullum shiga cikin rudu nake. Ta ce ba ta haihu ba. Ni kuma iya gaskiyata na sani, in ma ta haihu to ban san wani abu a kai ba. To amma, jama'ar gari, ... Kai, akwai wanda ya ce mani ya ma san sunan dan! Wani ya ce mani shi kuma ya ga dan! Wani ya ce kaza, wani ya ce kaza. Shin wannan abu, Allah kadai ya... Ni ban san... In fact, I am confused! (A gaskiya, a rude nake!).

Fim: To ita A'isha tana da wani saurayin wanda suka shaku kamar yadda ta shaku da kai?

AL-AMIN: E, ai... Ka san... Shi... Bari in ma misali. Yanzu abin da ya shafi ciki, shigar ciki bai wuce lokacin da namiji ya kwanta da mace, ... shi kanshi ba zai san a lokacin ne ciki ya shiga ba. To, tana da samari kafin mu hadu da ita. Kuma har bayan yadda muke da ita din wasu sukan kawo mani rade-radin kaza da kaza. To amma... ni dai ba zan iya nuna wani mutum in ce shi ne saurayinta ba. Kafin mu hadu da ita tana da samari da dama wadanda yake suna tare kut da kut kamar yadda muke da ita.

Fim: In har gaskiya ne ta haihu, kana ganin me ya sa take boye maka al'amarin?

AL-AMIN: In dai gaskiya ne to, ni kaina ba zan san dalilin da ya sa take boye mani ba. Amma ta ce ba gaskiya ba ne.

Fim: Ka taba samun matsala da matarka game da wannan al'amari?

AL-AMIN: Na samu matsala da iyalina sosai.

Fim: Wadanne irin matakai ka dauka na ganin ka gano gaskiyar wannan matsala?

AL-AMIN: Matakan dai ni dai nawa sun kare. Kullum nakan roki duk wani wanda ya san zai iya ba ni masaniya domin in gano gaskiyar wannan abu, saboda in wanke kaina. Saboda yanzu har duniya ta nade, wasu suna ganina da wannnan abu.

Fim: Me ya fi tada maka hankali game da wadannan maganganu?

AL-AMIN: Abin da ya fi tada mani da hankali shi ne, cewa ake yi wai ni ne uban dan. Shi ne abin da ya fi tada mani da hankali. Sannan abin yana zubar da darajata; ni wannan shi ne ya fi damuna.

Fim: Ko wannan magana ta taimaka wajen kin yiwuwar aurenka da ita?

AL-AMIN: Ni dai ban kalli abin a haka ba, saboda... Abin da kawai na duba shi ne idan lokacin abu ya yi, ko an ha-maza ha-mata za a yi shi.

Fim: Yanzu kana ganin idan da za ka auri A'isha ba za ka samu matsala da iyalinka ba?

AL-AMIN: Ai kamar yadda na gaya maka, matsala ce idan aka warware ta, ba wani abu, amma matukar ba a warware ta ba, to ko da nan gaba ne abin sai ya taso, kuma idan taso, kowa ba zai ji dadi ba.

Fim: Me ya sa ba ka ce wa wadanda suka ce maka sun ga yaron, su kai ka kai ma ka gan shi?

AL-AMIN: Wato ka san yadda abin yake ne, duk wadanda suke maganganun, da zarar sun gan ni, katse maganar suke yi. Sai su boye mani, suna ganina, sai su ce, "Ga shegen nan zuwa!" Amma ni da yanzu zan samu mutum guda da zai ce mani shi ya ga dan, wallahi rike shi tsaf zan yi, kuma ba zan yarda mu rabu da shi ba sai ya nuna mani inda yaron yake.

Fim: In har gaskiya ne A'isha ba ta haihu ba, me ya sa ba ta dauki mataki a kan bata mata suna da ake yi ba?

AL-AMIN: Mun sha yin wannan maganr da ita. Ta ce mani ita duk ranar da ta ji wani ya fito fili ya ce mata ta taba haihuwa, to ba abin da zai raba ta da shi sai kotu.

Fim: Me kake sa ran zai faru in har nan gaba aka gano da gaske ta haihu?

AL-AMIN: Zan ji dadi, saboda a lokacin da aka gano ta haihu ko ba ta haihu ba, to daga nan kowa ya san matsayinsa, idan aka yanke maganar kuma jama'ar gari da dangina za su daina kallona da abin, kai har ma nata dangin.

Fim: Kana ganin idan tana tsananin son ka ba za ta lika maka yaron ba ko da ba naka ba ne?

AL-AMIN: To ai wannan ba a taba yin haka a tarihi ba. In ko an yi, sai dai inda babu ilimi.

Fim: To misali idan ta yi kuskuren makala maka dan, ya za ka yi?

AL-AMIN: To, ai maganar kuskure ma ba ta taso ba. A Musulunci ana amfani da zahiri ne. Don haka, ba ma za ta yi wannan kuskuren ba.

Fim: To Al- Amin, Allah ya kiyaye.

AL-AMIN: Amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin