Daga ABDULLAHI NASIR ABILITY, a Zariya
SABON salon yaudara, cuta da zamba, ba ya kare wa mutane, shi ya sa mutane kan ce, "mai son abinka ya fi ka dabara".
Idan ba ku manta ba, can a watannin baya mun ba ku labarin yadda 'yan damfara ('yan '419') suka yaudari Bashir Bala (Ciroki) suka raba shi da Besfarsa a Kano. To ga alama 'yan damfara suna hangen akwai romo a fagen shirin fim na Hausa, domin kuwa kwanan nan sun kutso kai a Zariya cikin Jihar Kaduna.
Abin bakin cikin ya faru ne a kan furodusan nan mai suna Malam Abdullahi Yahaya Maizare, shugaban kamfanin buga littattafai na 'Maizare Publishers & Printing Press,' kuma shi ne babban edita kuma mawallafin mujallar finafinai ta Annur. Har ila yau, shi ne sakataren Kungiyar Furodusohi ta Jihar Kaduna.
Abin ya samo asali ne a yayin da wani makwabcin shi Maizaren mai suna Malam Ahmadu ya tunkare shi da batun wani malami mai suna Malam Usman wanda a cewarsa yana dalibta ne a wajen wani malami a nan Zariya, kuma shi (Usman) Bakano ne. Ya ce malamin yana son ganinsa don ya ba shi wani albishir game da wani mutum mai suna 'Major' Jibo dan kasar Nijar, wanda yake son su yi harkar kasuwanci da shi.
A cewar Malam Ahmadu, wanda ya ce Malam Usman ke gaya masa, wai shi Major Jibo soja ne a zamanin shugaban kasar Nijar wanda aka kashe, watau Baare Mainasara, shi kuma Major Jibo yana da kudi da yawa kuma yana son ya fara kasuwanci a Nijeriya, domin in ya yi kasuwanci a can Nijar to hukumar bincike ta kasar za ta tuhume shi, shi ya sa ya fi son ya sami wani mai amana su yi kasuwanci.
"Da aka shirya ranar zuwansu," inji Maizare, "sai duk wasu harkokina na dakatar da su, domin mu tattauna yadda za mu bullo wa abin. Kwatsam, sai ga su sun iso har ofis dina, da Malam da shi Major Jibo, shi Malam Usman ya yi shiga irin ta malamai; shi ko Major ya yi shiga irin ta attajirai. Da muka gaisa, sai shi Usman ya gabatar da shi Major Jibo gare ni, sannan shi Major Jibo ya fadi dukkan kudirorinsa na yadda za a fara kasuwancin. A cikin kudirorinsa kuwa yana son ne a je can kasar Benin, watau Kwatano, su sayi kayayyaki har da motoci, wanda ni zan zabi wuri a nan Zariya inda za a fara sayar da wadannan kayayaki".
Da Maizare ya ji kudirorin sai ya gasganta masa cewa don wuri za a samu. "Watau abin da ya sa na dulmiya cikin zancen wadannan mayaudara shi ne, dukkansu suka ce kafin a fara wannan yarjejeniya za su yi alwala su rantse da Alkur'ani cewa idan sun yi niyyar yaudarata ne, to Kur'ani ya ci su. To, saboda Allah ko wanene ai zai yarda, saboda dukkansu Musulmi ne; kuma a dauka cewa shi Major Jibo ban san shi ba, ai shi Malam Usman na san shi a lokacin yana almajiranci a nan Zariya. Sai dai wani abu bai taba hada mu ba.
"To, da na amince a haka sai dukkanasu suka dauki buta, suka yi alwala a gabana. Da ma a ofishina akwai Alkur'ani a rataye a cikin gafaka, sai na dauko na ba su, dukkansu suka dafa suka rantse da cewa idan sun yi niyyar yaudarata ne a cikin wannan al'amari, to Kur'anin nan ya ci su."
Daga nan ne fa, sai shi Major Jibo ya ce wa Maizare wai yana son zai je Abuja da Legas. Domin a cewarsa yana son ya yi clearance na wadansu kukudade domin kudaden da ke tare da shi ba na nan kasar ba ne, wai kafin ya samu canjinsu zai dan sami matsala. A nan take ya ciro su, shi kuma Maizare ya gan su. Ya ce saboda haka yana son Maizare ya ba shi N50,000 domin ya je ya aiwatar da wadannan ayyuka a Abuja da Legas, in ya dawo dai ya biya shi, sa'annan a ci gaba da harkar kasuwanci. Daga nan ne sai Maizare ya ce shi dai bai da wadannan kudin a yanzu.
"Sai suka koma waje suka yi shawara," inji Maizare. "Daga nan Malam Usman ya ce mani nawa ne a hannuna? Sai na ce, 'Dubu ashirin da shida ne' (N26,000). Sai Major Jibo ya ce babu damuwa in kawo.
"Sai na dan tsaya na yi tunani. Sai na tuna da rantsuwar da suka yi, sai na ciro kudin na ba su. Sai Major Jibo ya ce bayan sati daya in saurare shi, shi kuma Malam Usman ya ce ya kamata in zo mu je in ga inda yake zaune a Kano."
"Shin kun je tare da shi Kanon?" inji wakilinmu.
Sai ya amsa, "Mun je mana."
"A wace unguwa yake?"
"Tudun Maliki yake. Kuma bayan mun je tare da shi, na kara komawa bayan na ga lokacin da shi Major Jibo ya diba cewa bayan sati daya zai dawo ya yi."
"To da ka koma kai daya me ya faru?" inji wakilinmu.
"Da na koma can Kanon ban tsaya ko'ina ba sai layinsu a nan Tudun Maliki. Sai na tarar da shi da almajirai yana ba su karatu," inji Maizare.
Daga nan fa wannan furodusa bai kara jin duriyarsa ba. Hasali ma bayan wata guda da yin wannan abu, ya kara komawa Kano, yana zuwa layin da gidan, sai ya ga ba almajiran ba kuma Malam Usman din. Da ya tambayi jama'ar wurin, sai suka ce masa ma ba su san Malam Usman din ba, kuma ma ba a taba yin wani malami a gidan ba. Shikenan, ya juyo yana cizon yatsa.
To, Allah ya kare mu da irin wadannan masharrantan, amin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin