Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 45   Disamba 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Dirama na da asali a Islam,

inji Sheikh Karibullah

Shaikh Karibullah
Shaikh Karibullah Nasiru Kabara

SHEIKH KARIBULLAH NASIRU KABARA, Shugaban darikar Kadiriyya ta Afrika ta Yamma, ya gabatar da wannan jawabin ne a wajen bude taron duniya kan finafinan Hausa wanda Cibiyar Nazarin Al'adun Hausawa, Kano, ta shirya a Kano cikin Agusta 2003.

Wassalatu wassalamu ala asharaful mursalina.

Masu girma manya-manyan baki, 'yan'uwa da muka halarci wannan taro, assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!

Na yi murna da gaske da Allah ya sa na samu halartar wannan taro wanda yake nuna irin gudunmuwa wadda wasan Hausa ko wasan kwaikwayo yake bayarwa da kuma irin yadda za a ciyar da shi gaba. To hakika wannnan dama ce wadda take mai amfani kwarai da gaske, kuma na yi murna, Allah ya sa na samu haduwa da 'yan'uwa a yau.

A takaice abin da nake so in dan tofa ni zan kalli abin ne kallo a addinance. Addinin Musulunci abu ne mai fadi, kuma mai yalwa; babu wata irin rayuwa da Allah bai sa ta ba a cikin addinin Musulunci, kowane irin ci-gaba da dan'adam yake nema akwai shi a cikin addinin Musulunci. To saboda haka ina tabbatar da cewa abubuwa irin wadannan, abubuwa ne wadanda idan muka yi kyakkyawan amfani da su to za su iya haifar mana da alkhairi. Samun nasararsu da rashin samun nasararsu ya danganta ga yadda muka yi amfani da su. Abin da na fada a farko na taba amfani da su ko na ta fada a wajen karatu da muke yi a gidan Mai Martaba Sarkin Kano na tafsirin Alkur'ani da azumi lokacin da muka zo inda Allah subhanahu wa ta'ala yake ba da labarin abin da ya faru tsakanin Annabi Dauda (a.s.) da kuma wani jaruminsa da ake kiransa Uruya'u. Lokacin da Annabi Dauda yana da mata dari ba daya, shi kuma wannan hadimin nasa yana da mata guda daya tak. To sai Annabi Dauda ya nemi wannan sahabi nasa da ya ba shi wannan mata tasa guda daya, shi ya zauna ba shi da ita, shi kuma ya cike dari. To a nan Ubangiji subhanahu wa ta'ala sai ya ba da wani darasi, ya ba da wani ilimi, ya yi wani hukunci amma hukuncin nan Allah sai ya aiko da shi ta hanyar wasan kwaikwayo. Annabi Dauda yana cikin masallacinsa, ga dogarai na gadin kofofin masallacin su sama da dubu talatin, babu ta inda wani zai shigo ba su sani ba. Amma kawai sai ya ga wasu mutane guda biyu sun fito sun tsaga bango kamar iska sun shigo gabansa, suka zauna a gabansa. Ya tsorata saboda ya tabbatar ta cewa ya ba da tsaron da ya tabbatar da ba wanda zai shigo bai sani ba, amma kawai sai ga mutum biyu sun zo, tsaron nasa bai tare su ba. Suka ce, "Mu mutum biyu ne muka zo mu kawo maka kara." Dayansu ya ce, "Ni ina da mata dari ba daya (casa'in da tara) shi kuma wannan yana da guda daya tal. Saboda haka sai wannan mai guda dari ba dayan nan sai ya ce sai in ba shi tawa guda daya, ya hada shi ya zamo yana da dari, ni kuma in zama ba ni da ko daya."

To a nan Annabi Dauda ya ce, "Gaskiya ya zalunce ka da ya ce ka ba shin nan kai ka zauna ba ko daya, shi kuma ya cike dari."

Shikenan, yana fadin wannan suka ce, "Kazarmijulu alanafsihi!" (mutum ya yi wa kansa hukunci). Sai ya ga 'mutanen nan' kamar tsuntsaye fir sun yi sama.

Saboda haka sai Annabi Dauda ya ga lallai cewa wannan hukuncin da ya yi, Ubangiji Allah subhanahu wa ta'ala ne ya ba shi gyara a cikinsa. Sai ya zauna ya yi ta istigifari, ya yi ta kuka, har dai Allah ya kawo karshen wannan maslaha.

To ka ga a nan nake cewa fadin addinin Musulunci da kyakkyawan tunaninsa ya shiga cikin kowace rayuwa. Ga shi a nan Ubangiji ya yi hukuncinsa, kamar kuma wasan kwaikwayon ne aka yi hukunci da shi. To saboda haka nake cewa wasan kwaikwayo yana da gudunmuwa mai fadi, wanda zai iya bayarwa a cikin rayuwa. Amma ya danganta ga yadda aka yi amfani da shi. A nan ya kamata mu yi kokari. Mun yi sa'a cewa Hausa tana da kyawawan al'adu a cikinta wadanda addinin Musulunci a lokacin da ya zo kasar nan ya tarar da Hausa a kansu ya kuma tabbatar da yawanci daga cikinsu. To mu yi kokari mu yi amfani da wannan wasan kwaikwayo ta wajen tabbatar da irin wadannan abubuwa. Alal misali, mun sani da Hausa za a ga cewa duk mai hankali dattijo a unguwa ya dauka cewa wata amana ce a kansa ta tarbiyyar 'yan unguwa, ko ya ga wani yaro zai yi ba daidai ba dole ne ya tsawata masa, ba wai sai 'ya'yansa kawai ba. To a hakika a yanzu ana sakin wadannan abubuwa kowa yana daukar cewa sai 'ya'yansa su ne 'ya'yansa, an bar 'ya'yan jama'a a sake wanda bai samu damar yin tarbiyyar ba 'ya'yansa kuma su suke zama 'yan daba 'yan shaye-shaye da kuma shiga halin kaka-ni-ka-yi. To irin wadannan ya kamata a farfado da su a fahimtar da su ta hanyar wasan kwaikwayon nan, amfaninsu da irin alkhairin da suke wa kasa. Akwai misalin yadda mutane suke sakin 'ya'yansu barkatai, sai ka ga mutum wato yana da 'ya'ya amma 'ya'yan nan sun fita ba su dawo ba har tsakar dare, wani lokacin har ma sai wayewar gari kuma bai san ma ina suke ba. Amma mutumin nan watakila yana da wasu dabbobi ko motoci da ake yi masa haya, ba zai iya yarda ya kulle gidansa ba sai ya tabbatar sun dawo gida lafiya, amma babu ruwansa da 'ya'yansa.

To irin wadannan abubuwa ya kamata a ce 'yan wasan kwaikwayo su rika fa'idantar da mutane kan irin wadannan da kuma jawo hankalin mutane domin gyara al'umma gaba daya.

Abu na karshe muna so abin nan ya yi nasara. Alhamdu lillahi, kusan al'ummar Hausa al'umma ce ta al'ummar Musulunci da tarbiyya. To lallai ne a kaurace wa wani abu guda daya, wanda akwai wasu 'yan kurakurai da ke faruwa a cikin wasan kwaikwayo da yake gudana yanzu, yadda wasu ke nuna yadda warwarewar tarbiyya take ta addinin Musulunci. A yi matukar kokarin kauce wa irinsu sai a ga abin yana samun ci-gaba har kasa ta amfana da shi al'umma ma su amfana da shi. Sai a samu irin wadanda suke da hange da tunanin irin na addinin Musulunci domin su rika ba da shawara a kan irin abubuwan da za su fita wanda in har ana tacewa to abin zai fita tangaran kuma ya zama alkhairi ga kasarmu baki daya da kuma al'ummarmu. Na gode. Allah ya saka da alkhairi.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin