Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 46   Junairu 2004
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Tsigai: Ina Ta Fito, Ina Za Ta?

tsigai
Hajiya Husaina Gombe (Tsigai)

HAJIYA HUSSAINA GOMBE (TSIGAI) tana daga cikin manyan 'yan wasan fim na Hausa wadanda da jibin goshinsu aka kwaba bulullukan da aka gina harkar da su. Kamar yadda muka sha gaya muku a hirarrakinmu da ita a baya, ta fi yin fice ne a finafinan Ibro, koda yake ta yi wasa a wasu finafinan kamar "Dan'adam Butulu" da "Darasi." To, an dan jima ba a ji duriyarta a wannan mujallar ba, ga shi kuwa al'amura da dama sun wakana daga lokacin da kuka karanta hirarta da ta gabata zuwa yau din nan. Harka dai ta yi kasa, kuma akwai abubuwan da su kansu jama'a suke son su sani game da ita Tsigai. Misali, me ya sa har yanzu guguwar aure da ke ta kadawa ba ta wuce da ita ba? Mecece babbar nasararta a sana'ar fim? Da gaske ne cewa yaron nan mai suna Salisu dan'uwanta ne kamar yadda wasu ke cewa ko kuwa danta ne ko kuma dai kawai dauko shi riko ta yi? Me za ta ce kan irin kallon da wasu mutane ke yi wa 'yan fim? Wadannan tambayoyin, da ma wasu, su ne wakilinmu na Jihar Kano, SANI MOHAMMED MAIKATANGA, ya yi wa Hussaini kwanan baya lokacin da suka tattauna a Kano. Hirar ta bayyana mana inda Tsigai ta fito a wannan harka, da kuma inda ta dosa. A sha karatu lafiya.

Fim- Husaina, za mu so muji shin meye gaskiyar dangantakarku da Salisu wanda wasu ke cewa dan ki ne, wasu kuma na cewa kaninki ne?

Tsigai- Alhamdu lillahi. Ala kulli halin ka san shi bawa bai isa ya ce kar ka yi da shi ba; in har ka ga ba a yi da kai to ba ka kai ba. To tsakanina da Salisu ni dai mahaifiyarmu ta haife mu mu goma sha uku a cikin garin Gombe, kuma ni ba tsinto Salisu na yi ba. Duk wadanda suka je wasa (a Gombe) sun je gidajenmu, kamar Kumurci, Ahmed S. Nuhu, Fati Mohammed, sun je sun ga mahaifiyarmu kafin ta rasu, kuma ba inda ba su je sun gaisa da 'yan gidanmu ba. To ko wa ya je Gombe ya ya tafi gidan Sarkin Fulani a cikin Bolari, Layin Waziri, hanyar gidan Sarkin Bolari, idan har ya tambaya zai ga ubanmu. Mu ba boyayyu ba ne, kuma ba a waje na samo Salisu ba, duk wanda yake shakka ban taba rike kaina kamar Zainab (Solani) ai a hannuna ta zauna har take abu, amma ai ban taba cewa 'yar'uwata ba ce. To ni ba na boyo ba na shakka domin dan da yake bai da asali yake tsoron asalinsa. To muna da asali, don haka ni na fada cewar uwarmu daya ubanmu daya.

FIM: Kusan 'yan wasu lokutan da suka wuce kuna tare da Solani, wato ita Zainab din da kika ambata, amma kun rabu, an ce kun samu wani sabani wanda ya sa yanzu ta bar wajenku. Mecece gaskiyar lamarin?

TSIGAI: To alhamdulillah lokacin dai ban san yarinyar nan ba, an ce tun "Sangaya" take garin nan, kamar yadda ta yi min jawabi. Ni mun zo mun tafi Nijar gaba daya mu da su Aleebaba, Misbahu, Katakore, Danwanzan. Da muka je sun je gidan iyayenta su darakta su Hankaka suka je, yarinyar nan ake kawo mata abinci daga gidansu. Da muka dawo Nijeriya da ita domin mun saba a nan, sai su Hankaka da Danwanzan ba na nan ina gida suka turo ta suka ce don Allah in rike ta tamkar kanwata. Za ma yai zama tana zaune a gidanmu. Ni dai alhamdu lillahi, Zainab 'ya ce 'yar halak domin ni bana taba ba ta ajiyar wani abu ko kudi da zummar ta cuce ni ba ko ta zage ni. Tsakanina da ita ba mu taba yi ba. Da kanwar mamanta ta yi aure a nan garin tana da gida ita kadai sai ta gaya min ta ce za ta koma ta taya ta zama. Suka zo har nan gidan, ta koma. Kai kullum akan zo mu gaisa kuma ni ma ina zuwa inda take, amma ni da ita ba mu taba musu ba, amma ni ban san wani abu ba sai dai kuma halin dan'adam na rayuwa.

FIM: Menene gaskiyar lamarin Ibro da sauran abokansa da suke harkar fim wanda kusan kullum suna tare a da amma yanzu ba a ganinsu tare, wato kamar irin su Danwanzan, Katakore da dai sauransu, tunda kusan ke za ki iya sanin dalili.

TSIGAI: To, ka san mutane akwai su da zato, wanda kuma Allah ya haramta zato. Gaskiya dukkannin mutanen da Ibro yake tare da su, duk wanda ya daga hannu ya ce Ibro sun yi fada da shi ko ba ya tare da shi, to ni a zatona karya yake yi. Ba ina so in yi wasa da hankalin mutane ba ne. Da, Danwanzam da Katakore suna da kungiyarsu, abokantaka muke yi. Danwanzam suna 'Hikima,' Hotoro, Katakore yana 'Nurul Zaman.' Da ma abin da ya sa mu da muka fara fim shi ya sa muke kiransu, sakamakon shi Ibro ba shi ya bude kungiyar da ake ciki ba, wadda take dauke da suna 'Hamdala Film Productin,' wanda kuma yanzu mun maida ta 'Ibro Film Production.' Kuma ni na bude kungiyar nan da Cinnaka. Da na bude na samu Cinnaka ya samo suna, har na jawo Ibro muka zo muka shigo, su ma abokanmu muka zo musu wasa, su ma suka je mana, har muka taru muka zama daya. Da man tun can ba tare ake ba, to ka san duk wanda ya yi suna dole ya je ya ja ragamar yaransa, tunda da ma kowa mun same shi da yaransa a kungiyarsa yana wasa, don haka ba rabuwa aka yi ba. Kulu kuwa kafin mu fara wasa da ma yana wasa sama da shekara ashirin, yana da 'yan wasa, kuma dan rawar koroso ne da su suka fara bude wasanin Hausa a Legas. Kuma shi dan Saminaka ne a Unguwar Bawa. Don haka babu wanda aka taba samun wata matsala da shi har da aka yi baram-baram. Don haka a gobe in ka tara mu za ka gan mu a hade.. Amma duk wanda ya yi suna yana so shi ma a zo a dauko shi. Yanzu haka wasan ya zama ko a ina ne; ka je ka yi ciniki da mutum. Amma ina tabbatar da zumunci a dai industiri da ake yinsa babu wanda ya kai mu, don kowa ya san gidan kowa, mun zama daya, kuma ba a taba musu ba, don in ka gan mu muna fadan doke-doke to ka yi shirunka za ka gan mu tare. Kuma ku kanku 'yan mujallar Fim ba ku taba samun wasu matsalolinmu ba sai dai kawai a ce muku 'wai wai', amma za ka gan mu a hade, sai dai in wanda yake da wasansa ne ya zo ya yi 'casting' din wani bai yi na wani ba, amma in dai namu ne to sai ka ga kowa a ciki.

FIM: Wadanne irin matsaloli da nasarori kika samu a cikin wannan harka ta fim tun daga farawarki zuwa yanzu?

TSIGAI: Gaskiya alhamdu lillahi don ni ina jin ba abin da zan yi wa Allah sai godiya domin ni na samu babbar nasara a wannan harka kuma na samu dukiyar da ko mai kudin da ya shahara da kudi, kowaye a duniya, ita yake nema. To alhamdu lillahi wannan dimbin arziki da na samu kuma wanda nake ganin ni ba wata ba ce, amma Allah ya kai ni, shi Allah Ubangiji ya ba ni dan'adam kuma ni ba wata ba ce, kuma ni ba 'yar wani ba ce amma yau alhamdu lillahi dukkanin inda na fita a duniya zan ga jama sun taru suna kiran sunana, wasu ma ban taba tunanin ganinsu ba amma su karbe ni. To ni gaskiya wannan shi ne babban arzikin da na samu a cikin wannan harka wanda nake ga ya fi dukkan abin da zan mallaka a duniya na kudi, domin kudi ba zai saya min dan'adam ba. To alhamdu lillahi Allah ya ba ni arzikin dan'adam: ko'ina ka je a ce ana sonka, ai maka abu don mutuncin wannan harkar; don haka ina godiya ga masoyanmu baki daya kuma ina rokonsu duk abin da muka yi na kuskure don Allah su dinga aiko mana ba tare da sai sun zage mu ba, in ma ba mu gyara ba sai mu ba su hujjar da ta sa muka yi wannan abin, domin in ka ga mutum ya yi abu watakil yana da hujjarsa.

FIM: Bangaren irin matsalolin da kika samu fa?

TSIGAI: To matsaloli ba wani abu ba ne shi tunda mu muke wayar da kai kullum dole ne dan'adam mai rai dama ya samu matsala. Mutane sukan dan fuskance mu a juye, har kullum tunaninsu idan kana wannan harka yadda suke ganinmu daban. Mu ma muna da uwa da uba kamar yadda kowa yake da su, yawancin 'yan fim kuma matsalolin da ake samu idan ka ji ana zagin wannan, to ba haka ba ne. Mutane muna so su gane cewa wannan ba halayyarmu ba ce, kuma fadakarwa ce. Kamar akwai wata tambaya da aka taba yi min ba zan manta ba a wajen Tage wasu sun zo da tambayarsu na samu a mujallu wasu sun ce shin ai in ba ka tafiya ce to ka ji irin wannan matsalar. Na ce musu e. Wasu ma suka zo su uku, daya ya ce don Allah an ce ni arniya ce, na ce e. Wani kuma ya ce don Allah an ce ke Bayarabiya ce wai musulunta kika yi, na ce musu e! To ka ga wannan da mutane suna bi su fuskanci abin da muka fada a fim, kai ko mutum ba 'yancinka ba ne ai dai wasan nan dai ta zagaye duniya. Ka ga irin wadannan duk matsaloli ne da muke samu. Kamar lokacin da na yi "Dan Adam Butulu" na samu matsala da yawa a wajen mutune. Kuma haka mutane sun dame ni a (kan) fim din "Darasi". To duk abin da aka yi to ina jin dan'adam ya yi shi. Sai ka ga wadansu suna jin tsoronka suna gudunka. To sam ni ba haka nake ba, kuma ni ba halayyata ba ce abubuwan da nake yi a fim; ina fadakar da mu ne gaba daya da mu da ku domin duk mu taru mu gane. Don haka Allah ya taimake mu.

FIM: Wane irin darasi kika koya a zamanki a wannan harkar ko sana'ar ta fim?

TSIGAI: Alhamdu lillahi, ka san duk wanda ya ce 'ni ni ne' to ba shi din ba ne, haka Manzon Allah (s.a.w.) ya ce. Ni dai duk abubuwan da nake koyar da mutane duk don Allah su yi tunani yadda Tsigai take fitowa, in yi wa mutane, ko Ibro duk mace, masifarki da abinki bai ba ki dama ki kai ga nasara a gurin mijinki face ladabi; idan duk na yi karshe ba sa gani ina kaiwa ga nasara. Da a ce mata za su lura kar su yarda su yi koyi da halin da nake yi a fim marar kyau, su dawo su yi koyi da mai kayu, idan suka yi mai kyau din to za suga mai kyau. Kuma ladabi shi ne yake bai wa mace komai a rayuwarta; ba mace ba, dukkanin dan'adam. To ni abin da nake yi a fim ina nuna musu ne cewa idan ka yi kazan nan fa ba zai kai ka ga cin nasara ba, kuma idan su ma sun bi za su ga a karshe ba na cimma nasara ko da da farkon an ci nasara, domin an ce gaskiyar mutum ba ta karewa sai karyarsa. Ina fatan za su gane.

FIM: Daga shekara ta 2000 zuwa 2003 an samu yawaitar aure a cikin industiri inda 'yan fim ke yin aure kuma wasu su shigo. To ana surutun ku manyan matan industiri kun yi shiru maimakon ku yi aure ku bar yaran, musamman ke da Biba da irin su Saima da sauransu. Shin ku yaya wannan guguwar auren take yawo ba ta tafi da ku ba?

TSIGAI: To alhamdu lillahi wannan gaskiya ne, amma an ce mai daki shi ya san inda yake masa yoyo. Gaskiya ne shi kuma aure nufi ne na Rabbih. A takaice, ni a wadanda ka fada din nan ni na taba aure kuma na haifi 'ya'ya biyu; Saima ta yi aure ta haihu; to cikinmu ina jin Hawwa ce za a ce ba ta taba auren fari ba; kuma in an duba duk sa'anni ne. Ko irin su Lubabatu Madaki duk za a ce sun taba aure. To aure nufi ne na Ubangiji; babu 'ya macen da Allah ya dauke mata aure. To don haka nan dukkanmu duk wanda Allah ya kawo ranar aurensa da izinin Allah duk wacce Allah ya bai wa miji, kamar yadda mu ma muke zuwa na 'yan kananan yaran mu yi biki insha Allahu mu ma za mu yi. Ba wanda yake burin ya zauna ya tabbata ba shi da aure, babu shi. Duk ko wace ce Allah ya kawo mata miji za ta yi aure.

FIM: Mun dade da samun labarin cewa wai Hussaina Tsigai za ta yi aure, har yau kuma anawa ce za ta yi auren a karshen shekarar nan ta 2003. Shin menene gaskiyar lamarin?

TSIGAI: To ni ma na dade ina jin haka din kamar yadda ka ce kai ma ka ji, ni na ji ma har wasu sun yanke min ranar auren! Duk na ji. To alhamdu lillahi ni na tabbatar ana min fata irin na masoya ne. Kuma ni ma ina fatan Allah ya sa haka ya tabbata, Allah ya sa in samu miji in yi aure, ni ma ban ki ba.

FIM: Wane abu ne kika yi a zamanki na industiri wanda ba za ki taba mancewa da shi ba?

TSIGAI: Shine ai na ce ni kuwa na cimma burina tunda na samu jama'a gabas da yamma, kudu da arewa, kuma na samu masoya, duk da ba za a rasa makiya ba. Annabi ma yai fama da su bare mu da ba kowa ba. Shi ne babbar nasarata da na cimma wanda rayuwata har jikokina ba zan taba mantawa ba, kuma abin alfahari ne a gurina. Ina godiya ga masoyana har ma makiyana gaba daya.

FIM: Ana cewa 'yan fim suna samun kudi musamman mata, amma kawai yana tafiya ne ta wata hanyar, ba kasafai suke sayen wani abu su ajiye ba wanda in sun gan shi za su tuna da harkar ko bayan sun yi aure.

TSIGAI: Alhamdu lillahi arziki shi sirri ne kuma ba za ka taba cewa wani bai yi wani abu don rayuwarsa

ba. Ka san idan Allah ya ce ka ajiye za ka ajiye, idan kuma bai kudirta maka za ka ajiye ba duk zafin nemanka bai kawo samu. Amma tunda dai za a ci a ba wani har kuma ai wani abu to alhamdu lillahi. Da ma 'ya mace mijinta ke ci da ita ya shayar da ita ko? Mu ne yanzu a al'adance muka kawo mace sai ta yi sana'a ko ki yi sana'a ko kar ki yi, Allah dai ya ba ki mijin aure zai ci da ke. Kuma arziki sirri ne. Ni dai godiyata da nake yi (ita ce) wadannan mutanen da na samu su ne babban arzikina, su ne na tanada na ajiye su, saboda farkon duniya ai in an haife ka a tara jama'a, kana in ka mutu ka yi jama'a. Alhamdu lillahi su ne dukiyar da na tara.

FIM: Mun samu labarin cewa kin sayi mota. Amma wasu kuma sun ce ba ki aka yi. Meye gaskiyar maganar?

TSIGAI (ta yi dariya): Kin ji Baba! To alhamdu lillahi na gode wa Allah ni dai Tsigai a tsakaninmu ko ni ko su Hawwan da muka sayi mota a industiri ba wani abin burgewa muka yi ba, tunda ai an samu alkhairi kuma da mu aka kafa harkar nan. Ni ba wani ya ban mota ba, ni na sayi motar. Kuma ba wani abu ba ne don yanga ko don wani abu, a'a, harkokinmu ne suka zamanto dole zuwa wuraren da za ka yi harka; kuma ba wani abu ba ne. Don Allah mutane su yi hakuri, ni ba wanda ya ban mota.

FIM: Me kike tunanin zama a wannan harkar nan da wasu shekaru?

TSIGAI: Alhamdu lillahi dukkannin abin da zan zama a industiri yanzu hakana ta cimma ruwa. Burina yanzu Allah ya ba ni mijina in yi aure in zauna gidan mijina. In ma ina cikin gida in rubuta fim in kawo in ci gaba da ba da gudumunuwata a wannan harkar. Amma abin da ni nake buri ala kulli halin ni Tsigai na kai shi, duk inda na gitta ba sai an ce "wacce ta yi fim kaza" ba; ana cewa "Tsigai," to ba alfahari ba na yi cikin hukuncin Allah shi ne burin da na cimma a rayuwata. Kuma har yanzu ina cin arziki domin duk inda ka je za ka samu alkhairi kuma a mutunta ka. Ba abin da za mu ce sai dai Allah ya saka da alkhairi.

FIM: Shin kina nufin ko da kina gidan miji za ki ci gaba da shirya fim?

TSIGAI: Gaskiya ni ban cimma burin barin harkar fim ba har karshen rayuwata. Abin da ya sa na ce haka, ina so kowa ya saurare ni da kunnen basira, ka da a yi min mummunar fassara, shi ne ko ina gidan miji zan rubuta fim zan kira dukkanin da indusiri za ta yi min, ba wai ni in fito in yi fim ba, a'a, zan dai ci gaba da ba da gudummawata saboda 'ya'yanmuda jikokinmu da kuma kannenmu da za su zo, domin mu ba mu son durkushewar wannan harkar, don ka ga ko da hakori daya dole mu yi wa wannan harkar dariya.

FIM: Me za ki ce kan raguwar darajar harkar fim ba kamar yadda take a da ba, har wasu suna ganin cewa wadanda suka kafa harkar ne suke lalata ta domin ba su dauke ta sana'a ba, sai dai kawai don su yi suna a san su a duniya?

TSIGAI: Alhamdu lillahi ka san ni Tsigai da Ibro mu 'yan kauye ne, ba za mu gane cewa harkar fim tana tafiya ko ba ta tafiya ba, tunda mu illa iyaka a zo a dauke mu mu yi fim a biya mu, kuma mu kullum muna aikinmu kamar yadda muke yi da. To amma shi lokaci da zamani Ubangiji ne ke kawo shi; samu da rashin samu duka kuma canji da yake an danyi damina yanzu kuma ba za mu taba cewa akwai kasuwa ko babu ba domin mu muna ta sana'a; 'yan kauye ne mu. Wannan 'yan birni za a tambaya: su suke shiga kasuwanni, tunda ka gan ni nan ko Bata ban taba sani ba, ina cikin kauyenmu; an dai ce a nan ake saida fim.

FIM: Ya batun kwararowar 'yan mata cikin ita wannan harkar? Shin ku ma 'yan kauye kuna fuskantar hakan?

TSIGAI: Ka san mu ba za mu samu irin wadannan matsalolin ba, domin duk yarinyar da ta fito ba ta shafa 'dangwali yaba' ba ba za ta zo wajenmu ba. Yawancin wadannan matsaloli yana wajensu ne a birni, mu dai 'yan kauye ne, babu wanda zai zo gurinmu. Mu duk wadanda muke fim da su mun san gidajensu. Yanzu ma duk sauran sun yi aure, in ka kula ba ka ganinsu a fim tunda yanzu a nan kauye muna da yara mata da suka yi aure sun kai goma sha hudu, duk kuma suna gidan mijinsu, daya ma ba da dadewa ba ta mutu da ciki a gidan mijinta. Ka ga mu ba za mu sani ba domin yanzu fim din ya zama in furodusa ya sai labari a gurinmu ya je ya kawo 'yanmatan da yake so ya hada da mu mu yi fim mu ba shi. Don haka mu ba mu san duk wadannan matsalolin ba.

FIM: Me za ki ce kan yadda 'yan fim ke ikirarin cewa su fadakarwa suke yi, musamman matan, amma kuma masu kallo da masu karatun mujalla sun nuna cewa wannan abin da 'yan fim ke fada ba haka ba ne, kawai suna dada lalata tarbiyya ne, ta yadda suke shigarsu da kuma sauran mu'amalarsu?

TSIGAI: Ka san duniya an ce wai akwai wata dama da aka bai wa mutane wanda aka fada kuma har gobe mutane suna kokari maimakon su yage shi, sai su ce sai sun yi koyi da shi. Ana cewa ka yarda da fadar malam amma kar ka yarda da aikinsa. To abin da nake so in sanar da mu 'yan fim da kuma masu kallonsa, akwai ran da wata mata ta samu lambar wayata ta yi gayyata ta a lokacin muna cikin Abuja muna wasa. Na taka na je gidanta da ni da 'yan'uwana. Amma abin da ta ce mana wai ta tsani 'yan fim. Magana ce ta gaya mana, amma saboda ni 'yar wasa ce, na san fadakarwa nake kuma so nake in gaya mata kuma in nusar da ita hanya, kawai sai na bar ta, sai cewa take yaransu suna koyon wakoki suna koyon shirme ita ba a sa fim a gidanta. Amma burina da ya tashi cika, 'yar Hausawa ce ita, sai danta ya fito a daki wanda bai wuce dan shekara hudu ba, sai ya zo yana wakar "Mandako," kuma mijinta wani ne a kasar nan. Sai da yaron nan ya kai daga farko har karshe. Sai ta yi shiru. To amma su tuna, 'ya'yanmu suna wakar gumaka. Kuma duk wanda ya ce ba waka a fim, ai da ana fitowa a yi waka a dandali 'yanmata da samari har saurayi ya zuba kudi sai an daure yarinya, sai wani ya zo ya ba da kudi ya ce ya kwance ta, su fito a yi rawa 'yanmata da samari. To jama'a idan ba mu canza zuwa ga zamani ba... da ana cin tuwo a kwarya yanzu ana ci a kwano har da wani wai 'ci ka duba silba' ko? ... To idan ba mu fito da zamani ba babu yadda za a yi mu yaki wakar gumaka da Indiya suke yi, kuma manya ana sa kebil 'ya'yansu a cikin gida suna kallon duk tashoshin da suke so. To ba su gyara ba. Shin idan da mutanen nan sun kawo mana gyara sun zuba kudinsu a wannan harkar idan ka ce fim ka za ba shi da kyau to ka zuba kudinka ka yi mai kyau din da zai kawo gyara, muna gani ana koyi da shi. Mu dai kullum fadakawa muke yi. Amma akwai yaran da suka zo yanzu za ka ji an ce 'yar fim ce amma kai ba ka san ta ba, watakil in ka bibiya ba ta yi wani fim ba, in ma ta yi ko a cikin 'yan rawa ta fito ba za ka gane ta ba, ta yi ikirarin 'yar fim ce. Daga yarinya ta yi abu sai ta zaga ta ce ita 'yar fim ce, yawanci mu ma ba mu san su ba. To ina kira, duk mai son ya shigo cikinmu, mu na da, da kuma 'yan kallo don Allah don Annabi zargin da suke mana mu taru mu gyara, kuma na yarda da cewa dole kai mai fadakarwa ya zamanto kai ka fadakar kuma ka fi kowa dauka. Gaskiya muna ba mutane hakuri idan mun yi laifi Allah ya gyara. Da ma mutum bai taba zama daidai ba. Su kuma mummunar fassarar da suke yi mana don Allah su yi hakuri. Mu dai ikirarinmu masu fadakarwa ne, kuma Ubangij ya ba mu hakurin jure magangamun da muke sha a gurin mutane, domin ko dan da ke cikinka sai ka yi hakurin zama da shi, bare mu masu yi wa duniya gaba daya.

FIM: A karshe mecece shawararki ga duk wani mai yin harkar fim, kauye da birni?

TSIGAI: To ni abin da zan ba mu shawara shi ne, da wanda ya zo yau da wanda ya zo jiya duka uwarmu daya ubanmu daya, ba wane ya fi wane, kuma ba a gwani sai da makoyi, kar ka ce don ka ga wannan sabon zuwa ne, to ba ka san baiwar da Allah ya ba shi ba, kuma wane ya fito ya zagi wane, a ce wane ya yi fada da wane, ko kuma ka ji ana zagin dan'uwanka a wannan harkar to ba shi ake zagi ba har da kai. Kada kuma wani dan fim ya ga dan'uwanshi ya yi wani abu na muni ya fara murna wai ya samu wane, to ya same mu ne gaba daya saboda in an tashi "industiri" za a ce, gaba daya 'yan fim ya shafe mu. Mu ci gaba da bai wa junanmu shawara da hakurce wa juna.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin