Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 28   Afrilu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 3
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 4
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 5
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 6
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Hajjin Bana
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

 
If you had a new browser, you would be able to view this java applet. Akwai:  




Yadda bakin labarin ya firgita jama'a a Kano


MUTUWAR Balaraba ta firgita 'yan fim da yawan gaske a Kano da kuma wasu jama'a da dama. Da yammacin ranar da hadarin ya auku ne labari ya fara yaduwa a birnin Kano. A ranar Asabar din an shirya ana cikin bikin Gala a gidan sinima na Lale, sai labari ya zo na mumunan hadarin. Abokan ango, irin su Sani Musa Mai Iska, Tijjani Asase, Shu'aibu Idris Lilisco da Jazuli Kazaza, sun yanke shawarar kin shaida wa Ango halin da ake ciki.

Shi da ma Shu'aibu a ranar ya baro Kaduna, ya riga amarya zuwa Kano, daga nan ya zarce filin Gala. Da yake 'yan wasa da yawa, musamman 'yan mata, sun ji labarin, mafi yawa sun yi ta barza kuka. Ganin cewa mutane sun sauya fuska, babu alamun nishadi a gare su, Shu'aibu ya matsa lamba da tambaya inda daga bisani aka yanke shawarar fada masa cewa motar Amarya ta fadi. A nan Shu'aibu ya yanke jiki ya fadi.

Abokansa da sauran mutane ba su yi wata-wata ba, sai suka garzaya da shi asibitin 'Premier' da ke cikin unguwar Hausawa. Kafin sallar Isha'i labari ya game ko'ina cikin gari. Yayin da wasu ke kuka, wasu kuma na al'ajabi da dama daga cikin wadansu kuwa kin yarda suka yi da zancen mutuwar.

Ranar Lahadi tun da sassafe, wata matar wani hamshakin attajiri da ke makwabtakada gidan Editan mujallar Fim a Rijiyar Lemo, Kano, ta yi ta aiko yara domin jin tabbacin mutuwar Balaraba. Ko kafin a dauki wani lokaci kofar gidan ya fara cika da manya da kananan yara domin jin gaskiyar al'amarin.

Lokacin da wakilinmu ya je kofar gidan su Shu'aibu Lawan ya sami 'yan fim da yawa, daga mai jimami sai mai burbushin hawaye a ido. Da ya nemi ganin Shu'aibu, sai aka ce har yanzu yana asibiti. Can a asibiti kuwa jami'an tsaron da ke gadin wurin sun rika hana jama'a shiga wurinsa, wasu kuma akan ce masu, "Ai an sallame shi da safe." Duk wani kokari na ganin Kumurci a ranar ya ci tura.

Safiyar Litinin kuwa a cikin gidan su Kurmuci, mujallar Fim ta ji danginsa na cewa an sallame shi tun jiya da dare. Da aka tambayi inda yake, aka ce Shu'aibu yana gidan wani abokinsa saboda ya firgita da abin da ya faru matuka, don kada mutane su dame shi aka ce ya je can kafin wani lokaci. Jama'a da dama suka cika gidan suna ta'aziyya. A wurin ta'aziyyar kuwa akwai karamin littafi (exercise book) da mutum kan rubuta sunansa. 'Yan wasa da yawa maza da mata da kuma jama'ar gari duk sun je ta'aziyya a gidan. Mafi yawan wadanda aka tunkara don jin ta bakinsu duk sun ki yin magana saboda tunanin abin bai gama hucewa daga zukatansu ba.

Za a iya cewa shugaban kungiyar furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mandawari, ya gigita kwarai da jin wannan mummunan labari. Wata majiya ce mana ta yi, "Ina zaune Mandawari ya bugo waya a gidan Hajiya Umma Ali (furodusar Roman Rogo), hankalinsa a tashe matuka." Jin wannan labari ya sa hankalin Umma da sauran matan da ke dakin ya tashi matuka, suka rika kuka.

Ranar Lahadi, 17 ga Maris, Editan Fim ya je ofishin hada hotunan bidiyo na 'Kwality' da ke kan titin gidan 'Zoo', bai sami kowa a wurin ba sai mai kamfanin, DoktaUmar Faruk Jibril. Da ganinsa ka san yana cikin damuwa. Farkon abin da ya cewa editan shi ne, "Yaya hakurinmu?" Hakanan ofishin mujallar Fim da ke Kano ya zama wani dandali na jin gaskiyar labari. A kullum safiya daga mai zuwa ya yi ta'aziyya sai mai zuwa neman karin bayani.

'Fasaha Films' nan darakta Tijjani Ibraheem yake. A farfajiyar ofishin daga kasan benen an shimfida tabarma ana zaman jimami. Daga cikin wadanda ke kan tabarmar har da darakta Ishaq Sidi Ishaq. Duk inda ka zagaya kuwa babu wani dan wasa da za ka gani cikin raha ko annashuwa. Hajara Abubakar (Dumbaru) ta je ofishin mujallar Fim kwana biyu da yin mutuwar. Kowa ya san ta da fara'a da kuma wasa da dariya, amma har ta bar ofishin babu alamun murmushi a fuskarta, sai kawai tagumi.

A birnin na Kano, an yi ta yada jita-jita cewa hannun Balaraba ya fita daga jikinta lokacin da aka yi hadarin. Amma wani furodusa, Muktar M.D. wanda ya ce ya ga gawar kuma da shi aka rufe ta, ya karyata wannan zargin inda ya ce, "Gaskiya ina jin cewa buguwa ta yi a cikin jiki, don kuwa ba za ka ga raunuka a jikinta ba."

A daidai lokacin da ake rubuta wannan labarin sai ga wata tawaga ta zo ta'aziyya ofishin Fim da ke Kano daga garin Faskari ta Jihar Katsina. Tawagar ta zo a karkashin Malam Rabi'u Mohammed Gagarau, wanda shi ne dillalin mujallar Fim a kasar Faskari. Sauran 'yan tawagar sun hada da Idris Ibrahim Babangida, Adamu Sa'idu, Kabir Inuwa, Abashe Al-Hassan da Sanusi Mohammed Ggarau. Akwai kuma Sa'adu Rabi'u da Abdulmalik Bature. Bayan sun yi ta'aziyya sai suka zarce gidan su Shu'aibu Kumurci a cikin motocinsu masu lamba AA 306 JBY da AA 360 FSK.

ADDU'AR KWANA UKU A KOFAR GIDAN SU KUMURCI

Ranar da Balaraba ta cika kwana uku da rasuwa, jama'ar Gyadi-Gyadi, unguwar su Shu'aibu, 'yan fim da kuma 'yan'uwa da abokan arziki, sun taru a kofar gidansu don yin addu'a da misalin karfe 7 na safe. Manyan malaman unguwar ne suka yi adduo'i daga nan kuma wasu 'yan fim, ciki har da Mu'azzam Boss, suka yi 'yan jawabai. A nasa jawabin, Mu'azzam ya roki mutane da su yi wa Allah su daina fadar ji-ta-ji-tar. Babban dalilin da ya sa ya fadi haka kuwa shi ne saboda masu surutun cewa wai wasu ne suka yi wa Balaraba da Kumurci jifa.

Mu'azzam ya ce lokacin da aka je aka shaida wa malamin da ya daura auren Balaraba cewa ta rasu, malamin a gaban Mu'azzam ya furta cewa shi da ma tun lokacin da ake daura auren ya ji wasu alamomi a jikinsa kuma ya ga kamar gizo na dan saukowa cikin jama'a.

Daga cikin 'yan fim da suka je addu'ar akwai Sani Musa Mai Iska, Shu'aibu Lilisco, Aminu Shariff Momo, Ibrahim Sinana, Musa Jalingo, Abdullahi Zakari, Nura Imam da Hafizu Bello. Akwai kuma Tijjani Asase, Jazuli Kazaza, Mu'azzam, da wasu da dama.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin