Mutuwa ce kadai za ta hana aurenmu da A'isha, inji saurayin Saliha
Daga IRO MAMMAN,
a Kaduna
SHIN me ake ciki game da auren nan da aka yayata za a yi na fitacciyar jaruma A'isha Ibrahim (Saliha)? An fasa ne ko kuwa?
Wadannan tambayoyin ne mutane da dama a ciki da wajen fagen shirin fim suke ta yi a cikin 'yan watannin nan, ganin cewa an shafe watanni tun lokacin da aka ce za a yi auren amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.
Abin da ya kara ruruta wutar shaci-fadin da ake yi kan al'amarin shi ne babban labarin auren wanda Fim ta buga a fitowarta ta watan Janairu da ya wuce, inda har A'isha Ibrahim ta fito a matsayin yarinyar bangon mujallar. A labarin, an yi hira da A'isha da saurayinta Atta Oumaten, wani dan kasuwa dan kasar Nijar wanda ke zaune a Amerika, suka nuna kamar gobe-gobe ne za a yi bikin auren.
Wata majiya ta gaya mana cewa Atta ya riga ya biya kudin sadakin kyakkyawar yarinyar wadda a yanzu take karatun digiri a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya.
Haka kuma wata majiyar ta fada wa Fim a asirce cewa ita kanta A'isha ta damu kan rashin yin auren, musamman tunda an yayata har duniya ta sani.
"Ita yanzu ta kosa mijin ya zo a yi auren a gama hankalinta ya kwanta. Ka san Film Industry da kananan maganganu," inji majiyar. "Wasu za su rika cewa mutumin ya fasa, da sauransu."
Mujallar Fim ta waiwayi ma'auratan biyu don jin abin da suke ciki, musamman da yake rade-radin sun yawaita.
Mun fara da tuntubar A'isha, wadda ta ce lallai batun aurenta da Malam Atta yana nan, kuma ba fasawa aka yi ba. Ta ce, "Kawai wasu ''yan matsaloli ne suka taso daga bangarensa, wadanda da zaran ya warware su za a yi bikin."
A'isha ta kuma bayyana cewa akwai lokacin da angon nata ya ba da umurnin a daura auren kafin ma ya zo Nijeriya saboda kosawar da ya yi, to amma iyayenta suka ce a dai yi hakuri har zuwa lokacin da zai samu damar zuwa.
Mujallar Fim ta ji labari daga wata majiya cewa har yanzu soyayyar ma'auratan biyu ba ta yi sanyi ba kamar yadda wasu ke zato, "sai ma abin da ya yi gaba." Majiyar ta ce a kusan kullum sai Oumaten Atta ya bugo wa masoyiyar tasa waya, ko kuma ya aiko da i-mel.
"Abin ma yana ba ni mamaki; ita ma Madina (A'isha) a kullum ba maganar da take yi sai ta wannan mutumin na Amerika," inji majiyar.
Don kara tabbatar da maganar, Babban Editan mujallar Fim, Ibrahim, ya aika wa da Malam Atta da wasika ta hanyar intanet (i-mel) inda ya fada masa rade-radin da ake yi a Nijeriya, tare da bukatarsa ya kara haske a kan al'amarin.
A ran Asabar, 30 ga Maris, 2002, Atta Oumaten ya aiko da amsa, inda ya yi watsi da rade-radin, kuma ya kara tabbatar da kosawar da ya yi kan a yi auren.
A sakon nasa, Malam Atta ya fara da yi wa mawallafin mujallar Fim, Ibrahim Sheme, jaje kan satar da aka yi masa a gida kwanan baya. Ya yi addu'ar Allah ya kiyaye gaba, ya kuma mayar da alheri.
Daga nan Malam Atta ya amsa tambayar da wakilinmu ya yi masa a kan ko batun aurensa da A'isha yana nan. Ya ce: "Maganar aurena da A'isha tana nan daram dakam. Insha Allahu za a yi."
Ya kara da cewa mutuwa kadai ce za ta iya hana wannan auren da suka kudiri niyyar yi. "Ka shaida ma masu tambayarka cewa idan sun ga ba a yi ba to watakila ta Allah ta kasance a kan daya daga cikinmu: ni ko ita."
Haka kuma malamin ya yi bayani kan dalilin da ya sa aka ji shiru kamar an shuka dussa. Ya ce, "Abin da ya sa kuka ji shiru (shi ne) ina cikin wasu ayyuka ne wadanda suka shafi zamana a nan Amerika. Ban kammala su ba. Da zaran na kammala su za ka ga e-mail dina take yanke, insha Allahu. Amma maganar fasawa ai ba ta taso ba, kuma Allah kada ya kawo abin da zai kawo cikas a cikin wannan auren namu! Wai ana cewa na fasa? Ina! Ni da na kosa, har ba iyaka.
"Kuma watakila nan zuwa 10/04/02, za ka samu cikakken bayani."
Bayan wannan wasikar da ya aiko, Malam Atta Oumaten ya kuma sake aiko da wata inda ya yi tsokaci kan wani sharhi da muka yi a filin "Waiwaye" a cikin Fim ta watan Maris inda aka yi shagube kan aure-auren da 'yan fim ke yi ko ake cewa za su yi. A cikin shaguben, an tabo shi shi da A'isha. A cikin annashuwa, angon na A'isha Ibrahim ya ce, "Malam Sheme, bayan na tura maka e-mail sai na shiga cikin www.Kanoonline.com, shi ne sai na fara karanta mujallar March 02. A ciki sai na karanta labarin 'sabuwar jami'a' wadda kuka bude ta 'yan fim mai suna A.B.U,wato 'Aure Bautar Ubangiji.' Wannan gaskiya ne. Kuma na ga kun zana sunayen wadanda suka ci jarabawa, a ciki har da amaryata, wato A'isha Ibrahim. Na ga an ce 'sai dai ba ta karbi takardar sakamako ba.' To, insha Allahu kwanan nan za ta karbi takardar sakamako!"
Muna gab da za mu tafi wurin buga mujallar wannan watan kuma sai ga wata sabuwar wasikar i-mel Atta ya rubuto daga Amerika, wadda ta kara nuna cewa ana ci gaba da kammala dukkan shirye-shirye don yin aurensa da A'isha.
Cewa ya yi, "Malam I. Sheme, ina sanar da kai cewa zan bar nan kasar ranar Laraba mai zuwa, wato 24/04/02, zuwa gida Nijar. Daga can kuma sai gida Nijeriya. A takaice dai da zaran na je Nijar za ka samu cikakken labarina, ta hanyar waya ko kuma Intanet, sannan ne za ka samu tabbacin ranar daurin aurena, insha Allahu."
Saboda haka dai yanzu a tabbace yake cewa maganar auren Atta Oumaten da A'isha tana nan "daram dakam," kamar yadda Atta ya fada, kuma kamar yadda wadannan sakwanni na malamin suka nuna, nan ba da jimawa ba za a yi bikin. Allah ya kai mu.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin