Finafinan Hausa suna gyara tarbiyya -A.A. Rasheed
A.A. Rasheed
| A. RASHEED ba bakon suna ba ne ga masu karanta mujallar Fim ko kallon finafinan Hausa. Yana daya daga cikin manyan dillalan sayar da kasakasan finafinai da kuma na wakokin rediyo a arewacin kasar nan. Shagonsa da ke cikin tashar mota ta Kawo, Kaduna, ba boyayya ba ce.
Da wuya ka ga mujallar Fim ba ka suna da hoton A.A. Rasheed a ciki ba yana tallata hajarsa. Haifaffen garin Hayin Danyi da ke cikin Karamar Hukumar Rimi a Jihar Katsina, A.A. yana zaune ne a Kaduna.
Kwanan baya wannan hamshadin dan kasuwa ya tattauna da wakilinmu ALIYU ABDULLAHI GORA II inda ya bayyana muhimman ra'ayoyi dangane da shirin fim na Hausa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
FIM: Yallabai, kamar yadda wannan san'a ta karbe ka, da ma can da ita ka taso ko daga baya ka koye ta?
A.A. RASHEED: Tun tasowata nake wannan sana'a. Na fara ne da zama a shagon yayana Alhaji Abdul Baki, wanda ke da shago a nan Babbar Kasuwar Kaduna. To muna nan tare da shi har na ga cewa na kware a harkar kasuwanci, kuma zan iya cin gashin kaina. Sai wata rana na yi mashi magana cewa ina son ya taimake ni da kudi don ni ma in kama sana'ar kaina. Na kuwa ci sa'a ya ba ni. To akwai wani wanda muka saba da shi, mai suna Idris, yana saida kaset ne, kowa ya riga ya san shi, a bakin Radah Cinema. To wani lokaci nakan je wurinshi mu zauna haka mu yi hira sannan in wuce gida. To a lokacin da yayana ya ba ni kudi in yi sana'a , sai na ji ba wata sana'a da nake son yi sai ta sayar da kaset. Ta hanyar wannan Idris din sai na fara sayar da kaset, har Allah ya kawo ni yadda ka gan ni a yanzu.
FIM: A da, kun saba da sayar da finafinan Indiya da na Turawa. Akwai wani bambancin kasuwanci da kuka samu sanadiyyar bullowar finafinan Hausa?
A.A. RASHEED: Alhamdu Lillahi na ji dadi da ka yi mani wannnan tambaya. Gaskiya na sami shekaru da dama ina wannna sana'a ta sayar da finafinai, tun lokacin ma ba a fara yin finafinan Hausa ba. A wancan lokacin mutane sun fi sayaen finafinan Indiya, sai kuma na Amerika. Amma da finafinan Hausa suka fara shigowa, a gaskiya fisabilillahi babu wani kaset da ya yi farin jininsu ga jama'a. Kuma sai ya zamana lokacin da mutane suka gane muhimmancin finafinan Hausa sai suka yi watsi da finafinan Indiya da kuma na Amerika. To a gaskiya mun ji dadin shigowar finafinan Hausa, saboda muna ganin ci-gaba kwarai da gaske, don haka mutane suka rungume su don kasancewar yadda finafinan ketare suke gurbata tarbiyyar yara. Amma duk mai kallon finafinan Hausa ya san cewa suna da amfani ga rayuwar yaranmu, sai dai ya bi son rai, ko yai suka maras tushe.
FIM: To yanzu a kan wannan sana'a akwai wata matsala da ku 'yan kasuwa kuke fuskanta tsakaninku da furodusoshi?
A.A. RASHEED: A gaskiya fisabilillahi tsakaninmu da furodusoshi babu wata matsala. Shi dai abin da furousa yake so in ya kawo maka fim din shi ran da ya waiwaye ka ka dauki kudinshi ka ba shi. To in ko ba ka ba shi ba dole ne matsala ta shiga tsakaninku da shi.
FIM: To amma da yawan furodusoshin suna kuka da cewa ku 'yan kasuwa biyan mugunta kuke yi masu. Wato da gutsun-gutsun kuke ba su kudi maimakon biyansu gaba daya. Menene gaskiyar al'amarin?
A.A. RASHEED: E, to ni ba zan iya cewa a'a ba. Domin kana iya haihuwar mutum amma ba ka iya haihuwar halinsa. A gaskiya ni babu wani furodusa wanda ya taba zuwa wurina in ce na dauki naira dubu daya, dubu biyu na ba shi. Abin da kawai na sani shi ne in ka zo zan duba abin da na sayar daga kayanka in kuma dauki kudinsu in ba ka. In kuma za ka bari a ci gaba da sayarwa to ya rage ruwanka.
FIM: Maganar dokar layin fitar finafinai, shin ku 'yan kasuwa kuna jin dadinta, ko ko dai akwai wata matsala da kuke fuskanta kamar yadda wasu furodusoshiA.A. Rasheedda ba ta yi ma dadi ba suke kokawa?
A.A. RASHEED: Na ji dadin wannan tambaya, domin ka sosa mani inda yake yi mani kaikayi. A gaskiya fi sabilillahi layi yana da amfani, sai dai wanda bai fahimce shi ba. Kamar mu 'yan kasuwa, mukan samu natsuwa wajen karbar fim, domin mun san wanda muka karba yau, mun kuma san wanda za mu karba gobe. In ko ba layi ake yi ba , za a iya kawo mana wajen ashirin a rana. Ka ga dole ka rasa ma wanda za ka karba. Su kansu furodusoshi sun fi samun kwanciyar hankali. Ko banza ka san ana jiran fitowar fim dinka a wani kayyadajjen lokaci wanda in ba layi, wani fim din ma sai ya dade a kasuwa mutane ba su san da shi ba. Amma duk wanda ka ji yana sukar layi, to bai fahimce shi ba ne.
FIM: Kana da ra'ayin zama furodusa kamar yadda wasu 'yan kasuwa takwarorinka suke yi, wato ka shirya fim na kanka?
A.A. RASHEED: A gaskiya ina da ra'ayin zama furodusa, to amma ka san abin sai a hankali. Nan ba da dadewa ba in Allah ya so zan shirya fim na kaina.
FIM: To Allah ya ba da sa'a.
A.A. RASHEED: Amin, na gode.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|