Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Wai Balaraba za ta dawo!

Marigayiya
Marigayiya Balaraba
Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna

IDAN kana da rai babu abin da ba za ka ji ba. Kuma babu abin da ba za ka gani ba. Abin da al'ummar kasar nan suka ji a cikin ''yan makwannin nan, daga tsakiyar watan jiya zuwa yau, shi ne wai shahararriyar 'yar wasan fim din nan Balaraba Mohammed, wadda ta rasu a ran 16 ga Maris na bana, za ta dawo duniya! Wai ba ta mutu ba! Wai wani Banufe ne ya dauke ta, ya musanya ta da wata gawa mai kamanninta! Wai idan za a ba shi aurenta zai iya dawo da ita!

Wannan ji-ta-ji-ta ta yi kamari, musamman a tsakanin mata, har ta kai ga wadansu sun manta da hukuncin Ubangiji sun gaskata ta.

An yada wannan labari cikin nau'o'i daban-daban. A dukkan jihohin kasar nan inda ake kallon finafinan Hausa da kuma wasu kasashe makwabta, ana cewa wai an fadi labarin a cikin wani shiri mai farin jini na gidan Rediyo Nijeriya na Kaduna mai suna "Jakar Magori". Abu kamar wutar daji, da labarin ya watsu ko'ina sai mutane maza da mata yara da manya suka yi ta yin tafiyayya zuwa ofisoshin mujallar Fim na Kano da Kaduna don jin gaskiyar labarin ko akasin haka. Kai, har gidajen wakilanmu aka je domin tuntubarsu kan wai Balaraba ta dawo ko za ta dawo a rana kaza. A ofishin na Kaduna ma akwai wanda ya zo takanas yana shaida wa wakilinmu cewa shi ya ga wanda ya ji wannan labarin ma a BBC London.

Ita dai wannan ji-ta-ji-ta ta kasu kashi-kashi; wasu suna cewa wai lokacin da motar su marigayiyar ta yi hadari, ita ba ta mutu ba sai wani Banufe masoyinta ya dauke kurwarta ya musanya da siffar gangar jikinta wanda aka binne a kabari, amma ita sai ya je ya boye ta a dokar daji inda yake kula da rayuwarta har zuwa lokacin da ya zo ga iyayenta ya shaida masu cewa Balaraba fa tana nan a hannunsa, amma in suna son ganinta sai sun yi masa alkawarin za a ba shi aurenta, kuma wai in aka je aka tona kabarin babu abin da za a gani sai gungume ko ayaba. Wasu ma suka ce wai mutumin ya ce taya za a gani cikin kabarin. Cikin masu yada wannan bakinlabarin har akwai wadanda suke gaskanta cewa an je an tona kabarin kuma an ga abin da wai Banufen ya fada. Wasu kuma cewa suke yi wai ta ma bayyana ga iyayenta cikin tabin hankali kuma ba za ta samu waraka ba har sai iyayen sun amince da ba da aurenta ga shi masoyin nata wanda ya boye ta.

Akwai wasu wuraren da akan sarke da gardama kan sahihanci ko shirme da wannan labari ya kunsa. Don akwai wanda ya ba mu labarin wai ya ga wasu da suke yin irin wannan musu sai guda ya kada yatsansa guda a gaban wani talbijin, kawai sai ga Balaraba tsugunne a gindin wani dutse, jimawa kadan sai ta bace.

Irin wadannan shaci-fadin mabambanta ba su da iyaka, sai dai wanda ka ji kawai za ka iya karaswa.

Don binciken yadda aka yi wannan karyar ta faro, wakilinmu ya yi takakkiya zuwa gidan su Balaraba da kuma gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna.

A gidansu marigayiyar, wakilin namu ya lura cewa iayayenta da sauran danginta sun shiga damuwa mai yawa dangane da yadda ake ta yada wannan labari na karya. Yayanta Abdullahi Mohammed ma (wanda ya kubuta daga hadarin), ya shaida wa wakilinmu cikin fushi cewa duk wanda ya sake tunkararsa da batun wai Balaraba za ta dawo, to zai tokara masu wata maganar da zai dade bai manta da ita ba. "In ba jahilcin mutane ba, Shafi'u, uban wa ya taba mutuwa ya dawo?" inji shi.

A gidan rediyon kuwa, su ma kansu jami'an gidan mamaki ya cika su kan yadda ake ta cewa wai an ji labarin ne a "Jakar Magori." Madugun shirin tare da dukkan abokan aikinsa da wakilinmu ya gana da su sun karyata duk mahalukin da ya ce wai daga shirinsu aka ji labarin. "Wannan karya ce mummuna aka yi mana," inji daya daga cikin ma'aikatan.

Wakilinmu ya tuntubi Limamin masallacin Jumma'a na Unguwar Kaji inda aka haifi 'yar wasan, Malam Abdullahi Ibrahim, don ji ta-bakinsa a kan wannan al'amari. Tun kafin tattaunawarsu da wakilinmu, malamin, wanda a hannunsa Balaraba ta yi karatun Islamiyya kuma shi ne ya sallaci gawarta ita da 'yan'uwanta da suka rasu a hadarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, ya bayyana matukar mamaki da takaici a hudubarsa ta Jumma'a a ran 21 ga Yuni, 2002, kan wannan al'amari mai rikitarwa.

Hasali ma dai wakilinmu, wanda ya halarci sallar Jumma'arsa a masallacin, ya yi la'akari da cewa limamin ya yi hudubar ne domin mutane sun yada karyar cewa wai a wannan ranar ne marigayiyar za ta dawo ko ta ma dawo. Liman Malam Abdullahi Ibrahim ya ce shi kansa har gida an rika zuwa wajensa ana tambayarsa yiwuwar dawowar Balaraba gidan duniya cikin motoci daga wurare daban-daban. Hakan, inji shi, ya ba shi mamaki da haushi kan yadda yawancin al'ummar Musulmi suka jahilci rayuwa irin ta addini.

Bayan idar da sallar sai wakilinmu ya tuntubi malamin dangane da tunanin inda wannan labari ya samo asali ko dalilin da ya sa ake yi wa wasu mutane da suka daukaka irin wannan hasashen bayan sum mutu. Malamin ya ce shi bai san yadda wannan mummunan labari ya samo asali ba, amma tun zamunna da dama da suka shude akan samu irin wadannan labarurruka kan mutane da suka daukaka wajen aikin kwarai ko na banza bayan sun mutu, kawai domin jahilcin rayuwar wasu masoyansu ko makiya.

Babu mahulukin da zai dawo bayan ya mutu, inji limamin. Ya ce ayoyin Alkur'ani da hadisan Annabi (s.a.w.) sun tabbatar mana da wannan.

Bisa maganar fatalwa kuwa da aka ce tana bayyana bayan mutum ya mutu, Malam Abdullahi, wanda ke zaune a Unguwar Kaji (NDC), Kaduna, ya ce a fahimtarsa babu fatalwa a Musulunci, amma akwai wani tsuwa da ake cewa shaidan wanda ake samunsa wajen bokaye da 'yan bori. Limamin ya hori mutane don Allah masoyan wannan yarinya da makiyanta su daina yada wannan labari haka nan, domin Manzo (s.a.w.) ya hori Musulmi in za su yi magana to su fadi alheri ko su yi shiru.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin