Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 32   Agusta 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
MU LEKA HOLLYWOOD
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Aikin Darakta ba nawa bane

-Iyan-Tama

Hamisu da A'isha
A'isha B. Umar da Hamisu Iyan-Tama a cikin fim din

HAMISU LAMIDO IYAN-TAMA yana daga cikin 'yan wasa 'yan kalilan wadanda tauraruwarsu ta ki gushewa: an gan ta da dare, kuma an gan ta da rana, sa'annan an ci gaba da ganinta babu yankewa. Ba mamaki, shi ya sa wasu suke danganta dadewar kwarjininsa da ta jarumin Indiya din nan Amitab Bacchan. Kwanan nan sababbin finafinansa masu suna Buri da kuma Halak suka fito kasuwa. Shi Hamisu tare da wata 'yar wasan wadda ita ma tauraruwarta ba ta dushewa, wato Hauwa Ali Dodo (Biba), su ne jaruman fim din Buri. Fim ne wanda ya burge masu kallo. Za ma a iya cewa tun da kamfanin 'Iyan-Tama Multimedia' suke yin fim, ba su taba yin mai ma'ana da kuma cin kudi irin Buri ba. Manta da abin da aka ce game da Hakuri ko Fallasa, shi Buri ajinsa daban yake. Kafin fitowar fim din, Alhaji Hamisu, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, ya zanta da wakilinmu a Kaduna, Aliyu Abdullahi Gora II, kamar haka:

FIM: Alhaji Hamisu, ko za ka iya tuna yawan finafinan da ka shirya a karkashin kamfaninka zuwa yau?

IYAN-TAMA: E, ai ba mai maganar zan iya tunawa ba, sai in lissafa maka su domin ka sani. Da farko dai mun shirya fin din Badakala, da Kilu Ta Ja Bau, Wa Ya San Gawar Fari?, Saudatu, Kwai A Baka, Hakuri, Fallasa, A'isha, Dawayya, Gashin Kuma, ina fata ka fahimta. Sai wadanda ba su fito ba nan gaba, akwai Halak da kuma Buri, sai kuma wani Falaya, wanda na riga riga na gama, wanda shi ne ake kira Kullalliya. Wadannan su ne finafinan da 'Iyan-Tama Multimedia' suka shirya.

FIM: Daga cikin wadannan za ka bayyana wanda ya fi shigar maka rai?

IYAN-TAMA: Yo ai duk fim din da ka ga na riga na yi, na tabbatar da yana cikin zuciyata. Duk finafinan kamfanin 'Iyan-Tama' ina da dalilin da ya sa na yi su, kuma ba don in mora ba, a'a, don duk al'ummar durinya su mora.

FIM: Ka gutsuro mana kadan daga cikin labarin da Buri ya kunsa.

IYAN-TAMA: E, me zai hana, tunda abu ne wanda ko ban fada ba zai fito kuma duniya za ta gani? Shi Buri mun shirya shi ne domin ilimintar da al'ummarmu, musamman Musulmi Hausawa. Matanmu mafi yawancinsu sukan kasance masu kwadayi. Dukkannin wata mace, babba ko karama, talaka ko 'yar sarauta, mai kudi ko marar kudi, tana da bukatar ta ga ta auri wanda yake mutum ne mai adon zuci, sai dai in ba ta samu ba ta yi hakuri a haka. To Hajiya Maryam a cikin wannan fim ta kasance mai kwadayin mijinta ya zama mai arziki. Kuma tana yawan jawo mashi abubuwan da ba su kamata ba. Matsayin da ba ta kai ba, ta ce sai ta kai. Saboda haka ta rika addu'a, da kuma shi kansa, ta sa shi a gaba cewa ita dai tana so ta ga ya samu wata sana'a bayan aikin malanta da yake yi. To, burin ta dai da ma arziki, sai Allah ya azurta shi dare daya. Ya samu ya je aka dauke shi a ma'aikatar tace man fetur ta kasa, inda daga nan ne shi kuma ya samu hanyar budin arzikinsa. Da ya samu arziki, ya bude kamfanoni da sauransu, to waccan mata tasa, wato Maryam, sai ya kasance sai ta yi kamar wata biyu uku ba ta sa shi a ido ba. Saboda haka muna nuna wa mata cewa su daina sha'awar cewar dole sai sun auri hamshakin mai kudi: ki dai auri wanda zai kula da ke, ya ba ki hakkinki, ki ba shi nashi. Saboda haka mata su rage buri. Kuma duk matar da ta kalli wannan fim, ina tabbatar maka, ko wace iri ce, sai ta san cewar an shirya fim mai ma'ana wanda ya kamata a shirya tun ba ya ba a shirya ba. Sannan kuma wannan fim yana nuni ga irin masu kudinmu na kasar Hausa wadanda suka tara dukiya cewa ya kamata su rika hutawa, su bar kuma kannensu ko 'ya'yansu su nema. Abin da ya rage masu shi ne su dawo su koma ga Ubangiji. To amma mutanenmu ba su yin irin wannan.

Saboda haka a lokacin da shi Alh. Aliyu, wato mijin Hajiya Maryam ya samu arzikin nan, to a wannan lokaci ya gama tara dukiya, ya dawo gida domin ya faranta wa iyalinsa rai, sai Allah ya karbi ransa, bai ci dukiyar da ya tara ba. Matarsa ta zo ta gada ita da 'ya'yan. To, kuma likitan da ke kula da ita shi ya zo ya aure ta, ya kuma gaje dukiyar da mijinta ya bari, bayan wasu sharudda da ya kafa mata.

FIM: Da yawa ka fin son fitowa jarumin fim din da ka shirya, maimakon ka dauko wani daga waje. Me ya sa?

IYAN-TAMA: E, to ai in ka kula, in fim ya dace da ni maimakon in dauko wani, tunda ni ma jarumi ne, kuma ana biyana, kuma ni ma ina biya, bang a dalilin da ya sa na dace da fim kuma in fita in daukowani ba. Wanda ban dace da su ba, kamar su A'isha, Fallasa, su Gashin Kuma, in ka kula, ai za ka ga wasu na gayyato. Mu muna yin abu ne a kan cancanta.

FIM: To, akwai wani sabon yayi da ya shigo, furodusoshi suna rikidewa zuwa daraktoci,. Kai ma kana da wannan ra'ayin?

IYAN-TAMA: (dariya) In da ina da irin wannan ra'ayin ai da wani bai rabe niba. Da tuni na zama darakta, ko edita da sauransu, saboda na dade cikin wannan harka. Duk wani abu da wani darakta zai yi a fim ni ma na iya gwargwado. Amma ita harkar fim, harka ce da za ka ba wasu dama su zo su ci abinci. Saboda haka dole ka nemo wadanda suke kwararru, ku hada hannu, domin an ce taura biyu ba ta haduwa a baki. Saboda haka ni ban yarda da tsarin in zama darakta ba. Kuma ban tunanin zan zama darakta na wani fim. Ni ba abin da na kware a kai ba kenan. Ni furodusa ne kawai. Ina fatan an fahimce ni.

FIM: To, alhamdu lillahi, mun gode Iyan-Tama.

IYAN-TAMA: Ni ma na gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin