|
'Yan fim sun zama 'yan dambe
Kishi kan samari, gulmace-gulmace, kyashi da bakin ciki sun sa
Shugabannin shirin fim sun zuba ido mabiyansu suna zubar wa kansu mutunci a titi
Daga WAKILANMU
A YAU an wayi gari a cikin wannan shekara da wuya ka ji an yi wata biyu wani abin takaici bai faru a cikin masu harkar fim ba. Ba kuma wani abu ba ne illa yawan fadace-fadace da ake yi tsakanin 'yan fim, kuma mafi yawansu mata. Wata sa'a gulma ce ke haifar da rigima: a ce wa wance wai wance ta ce kaza game da ke; wata sa'a kishi kan samari ke haifarwa: a ce wance tana rabar saurayin wance ko kuma an ga wane da wance bayan ko yana neman wance; wata sa'a jin haushin wance ta yi fice fiye da wance ko kuma wance ake yayi sai ka ji wata ta tsane ta har tana yada kalamai marasa dadi game da ita; wata sa'a dan wasa ne zai nemi yarinya amma da ya ga ba ta da sauran moriya a gare shi sai ya watsar da ita, ya koma wa wata. Har yanzu ba mu ji wani namiji da wani namiji sun dambace ba tukuna, amma a yadda al'amura suke tafiya da wuya a dade ba ka ji an ce wane da wane sun kwafsa ba. A yanzu, su mazan sai dai su rika cin naman juna, amma suna yin kokari matuka wajen kin yarda a ji su suna dambe da juna.
Wasu sun ce duk rashin kyakkyawan shugabanci a fagen shirin fim ne ya sa ake fadace-fadacen. Shugabannin kungiyoyin shirin fim kamar Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano da Kungiayr 'Yan Wasa da Kungiyar Furodusoshi Mata da kuma uwa-uba Kungiyar Furodusoshi ta Arewa duk sun zama hoto a wannan al'amari, domin a yayin da girmansu ya zube a idon 'yan wasan da ke fadace-fadacen, su kuma sun kasa yin wani hobbasa don ganin an daina wannan mugun abu wanda ya fara zama ruwan dare. Ga shi kuwa sun san cewa idan wata 'yar wasa ta yi fada da wata, dukkan 'yan fim ake gani da abin.
Idan aka bi dalla-dalla, fadan da ya faru tsakannin Hindatu Bashir da Maryam Mashahama shi ne za a ce ya dan dade, domin kuwa ya kai watanni shida da faruwa. Baya ga shi kuwa, sauran duk a cikin watanni hudu da suka gabata suka faru, abin kamar annoba. Ban da na Maryam da Hindatu, n yi fadace-fadace kamar wadannan:
Ko shakka babu, matsalolin da suka jibinci kishi, gulma, tsegumi, bakin cikin juna da kuma uwa-uba rashin kyakkyawan shugabanci su ne ummul-haba'isin tafka mummunar bahallatsa tsakanin 'yan fim din. Ya zuwa yanzu, wadanda suka kwafsa a Kano da Zariya su ne:
1. Hindatu Bashir da Maryam Mashahama;
2. Hindatu Bashir da Maijidda Abbas;
3. Aina'u Ade da Hadiza Kabara;
4. Saratu Gidado da Hadiza Kabara;
5. Sulaiman Sa'eed da Maijidda Abbas;
6. Ummi Nuhu da Ali Nuhu;
7. Ummi Nuhu da Fati Baffa Fagge;
8. Rukayya Umar Santa da Maimmuna Husaini;
9. Nasiru Danmaliki da Hadiza Kisisina.
Lokacin da muke rubuta wannan rahoton, yawancin wadanda aka yi fadace-fadacen da su sun ki yarda su ce wani abu, sai kalilan, saboda dalilan da suke a bayyane. Wasu ba su so ma a bayyana labarin fadan, domin wai "komai ya wuce." Wasu kuma suna kallon abokan fadan nasu a kaskance ta yadda ma ba su son a tuno masu da abin kunyar da suka yi na yin fada. Da wakilinmu ya tuntubi Rukayya Umar Santa me za ta ce kan fadansu da Maimuna Husaini a Zariya, sai ta ce ba za ta ce komai ba. Amma da ta ji labarin cewa Maimuna ta yi magana da Fim, sai ta ce wa wakilinmu, "Kai rabu da ita! Yaushe zan biye wa karamar yarinya? Ai ni ba ajina ba ce; na fi karfinta!"
Wasu kuma ba su garin lokacin da muke hada labarin. Misali, Fati Baffa Fagge ta tafi Legas kan wani shirin fim, inji wata majiya, don haka babu halin a ji ra'ayinta kan dambenta da Ummi Nuhu, wadda ita din ma ba a gan ta ba don jin ta-bakinta kan fadansu da Ali Nuhu da kuma Fati din.
Sulaiman Seed ya so ya yaudare ni shi ya sa na so a kulle shi -Maijidda
Soyayyar Maijidda Abbas da Suleiman Sa'eed (daraktan manyan finafinai kamar Maula da Tarzomar Shahada) misali ce ta irin abubuwan da kan faru a fagen fim na Hausa. Za ka taras furodusa ko darakta ko dan wasa ya aje mace suna soyayya. Wata sa'a shi da ita za su yada a fagen shirin fim cewa aure za su yi, wata sa'a kuma su yi mirsisi. Idan an yi dace, wata soyayyar takan kai ga an yi aure (Fati da Mai Iska, Abida da Hamza, da sauransu). Idan kuma ba a yi sa'a ba sai ka ga an tashi baram-baram, dutse a hannun riga. A duk lokacin da aka ce wane shi ne saurayin wance, to shikenan sai ta kasa ta tsare, ba ta son kowa ta rabo mata kusa gona. Idan wata ta yi gigin shigowa kuwa, to za ta kwashi kashinta a hannu. Fada yakan kaure musamman idan saurayin yana da ruwan ido. Irin wannan ta faru ga Suleiman Sa'eed, wanda ban da aikin ba da umarni yakan fio a matsayin jarumin fim. Farkon zuwansa Kano daga Jos, da Hindatu Bashir suka yi samartaka, har ana maganar aure. To kuma sai Maijidda ta bullo daga Zariya. Sai mutuminka ya karbe ta hannu bibiyu. Da fari, suna abinsu a boye don kada Hindu ta sani. Ita ko Maijidda ba ta son a boye soyayyar domin tana son ita ma ta kai ga matsayin kasawa da tsarewa. Don haka ta dinga yi masa hidima a bayyane. Ita ce ma ta kama masa gidan haya a unguwar Kabuga, ta biya kudin, sa'annan ta ware wata rana guda daya ta je gidan ta dingi aikin wanke gidan da gyara shi. A gun makwabta, Suleiman da Maijidda miji da mata ne, sai daga baya suka gane duk karya ce. Kuma takan dafa masa abinci ya ci, ba sai ya aika an karbo daga 'Saudat Restaurant' ba, wato gidan abinci na su Hindatu, kamar yadda yakan yi. Da labari ya kai ga kunnen Hindatu ne sai bala'i ya tashi. Hindatu ta je har gidan ta kama su da Suleiman, ta ko yi wa Maijidda dan karen duka, ita kuma ta sha zagi da tsinuwa a gun Maijidda.
A karshe dai Hindatu ta "bar wa Maijidda" Suleiman, duk da yake abin ya yi mata ciwo matuka. A ranta kuma ta ce in Allah ya yarda su ma za su rabu. To, Allah ya amsa addu'ar Hindatu cikin watan Yuli, domin kuwa Suleiman sarkin ruwan ido ya ga wata yarinyar mai suna Rahama (mai bille). Rannan sai Maijidda, wadda a da ta dauka ba yarinyar da ta isa ta kwace mata shi, ta je gidan ta kama su da hannunta. Da ma an yi kawo masa gulma game da mutumin nata amma tana sharewa. Shin me ta yi masa da ta kama su?
Mujallar Fim ta tuntubi darakta kuma dan wasa Sulaiman Sa'eed kan rikicin da Maijidda ta ce sun yi. Suleiman, damo sarkin wayo, ya tsaya tsayin-daka cewa shi sam bai ma san ko wacece Maijjidda Abbas ba. Duk wani kokari da wakilinmu ya yi domin ya amsa zargin da ta yi masa ko da guda daya ya ci tura domin ya nuna bai san da wata Maijidda a fadin duniya ko a cikin duniyar fim ba. Sai dai kuma daga baya ya gamu da editanmu, ya ce masa shi dai ya ce bai san Maijidda ba ne domin wai ba ya son a buga labarin rikicin nasu.
Ita kuwa a hirarta da Fim, Maijidda ta fara da ba mu tarihin rayuwarta kafin ta kai ga gaya mana yadda suka yi da tsohon rabin ranta:
Maijidda Abbas
|
FIM: Maijidda daga ina kike?
MAIJIDA: Ni dai 'yar Zariya ce, ubana kuma soja ne. An haife ni a cikin 1980, yanzu ina da shekara 22. Na taba yin aure. Da na yi aure muka sami matsala da mijina sai muka rabu. Ina da da daya da shi (mijina na da) amma haihuwata biyu. Daya ta mutu dayan kuma yana nan da rai sunansa Abbas, sunan babana. Na yi firamare da sakandare, yanzu kuma ina School of Hygine, Kano.
Me kike karantawa a can?
MAIJIDDA: Ina karanta Environmental Health Assistant, E.H.A.
A wace makaranta kika yi karatunki na sakandare?
MAIJIDDA: Na yi makarantar sakandare a Barrack, barikin can Zariya, da kuma na yi na gama sai aka samo min aikin asibiti. Da na fara sai mamanmu ta ce ta fi so in je in karanci aikin asibitin, saboda in karanci yadda aikin yake. To shi ne ta turo ni nan in zo in zauna a gidan kakata domin in ci gaba da karantuna. Bayan na zo kuma shi ne na yi sha'awar harkar fim sai na fara yi, sai na bar karatun. Sai (mahaifiyata) ta nuna ranta dai bai baci ba dai.
Har yanzu mahaifinki yana aikin soja?
MAIJIDDA: Ya yi ritaya a yanzu.
Rayuwarki kina karama duk a bariki kika yi ta?
Kwarai da gaske. Rayuwata a bariki na yi ta, amma da yake ina yawan bin dangi, dangina suna yawan daukana, amma dai a bariki na yi rayuwata.
Daga wace shekara kika fara fim, kuma sanadiyyar wa kika fara yin fim?
MAIJIDDA: A shekara ta 2001 na fara yin fim, kuma a sanadiyyar fim din Al'ajabi part 2, gaskiya a nan ya ba ni sha'awa yadda aka shirya fim din, na ce insha Allahu sai na yi wasan Hausa, sanadiyyar dai farawata kenan.
To da kika shigo, kin dade ba ki fara ba? Kuma wane fim kika fara yi?
MAIJIDDA: E to, ni dai da na shigo harkar fim a gaskiya ban dade ba dai ina zuwa na fara aka kai ni 'Welfare.' Ina zuwa 'Welfare', rannan kwatsan sai aka zo aka dauke ni za mu fara wani fim wai Laila, to sai na yi fitowa daya a Laila, shi ne fim dina na farko, sai kuma na biyu Rantsuwa, na fito yarinyar fim din.
Daga shi fa sai wane fim din?
MAIJIDDA: Daga Rantsuwa gaskiya na yi finafinai da yawa wanda a yanzu gaskiya ba zan iya kawo su ba sai dai in kawo kalilan; ka ga kamar su Yaqini, Mushaqqa, su Hamayya, Jirwaye, Darasi 2, Ruda, Matsala, dai da sauransu.
To me ya sa ake samun matsala da ke, ko kuwa rayuwarki ce ta barikin soja kike nunawa a cikin ta farar hula?
MAIJIDDA: Ka san dai an ce dai a san mutum a san cinikinsa, in ya daina a san ya daina. Ai ka san gado ne gara ma a fara sani, domin ka san mu 'ya'yan sojoji don mu ba ma son a rika nema a kawo mana wata gada-gada, ah-ah yanzun nan sai mu yi maganin mutum...! Ina gani wannan haka ne!
Shin yanzu shigowarki, akwai wani darasi da kika koya game da harkar shirin fim?
MAIJIDDA: E a gaskiya shigowata na koyi darasi, sosai kuwa, saboda idan ka shigo ka yi masu lako-lako sai a tafi da kai haka, idan kuma ka nuna zafinka ma sai a tafi da kai a haka. Kuma gaskiya da na shigo harkar fim na samu na gaba da ni kuma har yanzu ina yi masu biyayya, amma akwai wadanda yanzu ni kawai daya muke da su ba wani saurarawa.
Kina nufin su ma 'yan zafin kai ne shi ya sa ke ma ba ki saurara masu?
MAIJIDDA: Kwarai kuwa 'yan zafin kai ne.
Cikin finafinan da kika yi guda nawa ne kika fito a matsayin yarinyar fim din?
MAIJIDDA: Yanzu dai wanda ya fito akwai Rantsuwa sai Jurwaye mu uku ne 'yan matan fim din, sai kuma Darasi na 2, sauran dai ba su fito ba.
Lokacin da cika shigo harkar fim ba ki dade ba har kika yi suna. Shin menene sirrin abin?
MAIJIDDA: Gaskiya dai wannan sirrin daga Allah ne, Allah ne kawai ya san sirrin wannan abin.
Ke kin ce kina zaune a hannun kakanninki wasu kuma sun ce kina zaune a hannu Hajiya Amina Garba (Dumba). Menene gaskiyar al'amarin ?
MAIJIDDA: Gaskiya a gidanta nake zaune, amma a yanzu ina hostel a zaune yan zu karatu nake yi ina makaranta idan fim ya samu in fita in yi. Amma kuma a gidan Amina nake, daga gidanta ne na koma makaranta, shi ne gaskiyar.
Ita Amina meye alakarku da ita ?
MAIJIDDA : Alakarmu da ita shi ne ta bangaren mahaifiyata; da mahaifiyata da ita kawaye ne kuma ma lokacin da mahaifiyata ta rasu ina nan kuma (ita Amina) 'yar Zariya ce, mun sai juna tun ba a nan ba wajen fim. Shi ne na dauke ta kamar yayata ita ma.
Wasu suna ganin yawan fadace-fadace da matan fim ke yi ya nuna cewa suna janyo wa kansu zagi. Ke me za ki ce a matsayin wadda aka taba gwabzawa da ita?
MAIJIDDA: Gaskiya yawan fada daga 'yan matan fim yana kawo zagi, to amma ai wani abin ne idan akai maka idan ba wai ka kai zuciya nesa ba... kamar ni idan akai min abu in har na tafi ban mayar masa ba to sai na yi ciwon zuciya, to amma idan ka yi min a yanzu na mayar maka to wallahi ko a gobe muka hadu sai mu gaisa. Kawai ni haka zuciyata take, amma ban san sauran ban.
Abin har ya wuce da an kwana?
MAIJIDDA: Ina! ai ba za a kwana ba. Gara inda mutum yayi min a lokacin in mayar masa.
Kwanan nan an ce kin yi rigima da wani darakta kuma dan wasa wanda da an ce nan da shekara dubu hakan ba za ta taba faruwa ba a tsakaninku. Amma ya aka yi hakan ta faru?
MAIJIDDA: E to, waye wannan?
Sulaiman Sa'eed
|
Suleiman Sa'eed.
MAIJIDDA: Kwarai haka ne, saboda shi mayaudari ne kuma sai Allah ya kama shi da hakkin yaudara da yake na 'ya'yan mutane. Kuma ni ba fadan da muka yi da shi ne ya dame ni ba. Har zuwa na yi na same shi da wata yarinya Rahama, mai bille, na kulle su a daki da kwado. Kuma kashegari na dauko masa dansanda aka kulle shi saboda yaudarata da ya yi. Tunda Sulaiman Sa'eed har mahaifiyata ya sani, ba abin da bai sani ba a dangina. Kuma ni ma na sha zuwa Jos. Amma da yake mayaudari ne ya rika kawo 'yanmatan mutane yana yaudara. Lokacin da na zo ban san halinsa haka yake ba. Da na ga haka halinsa yake na ce ya bari, in bai bari ba... Rannan na je na same shi da wannan yarinyar, muka kama fada har ma ya kai ga ya mare ni. Wannan gidan da yake zaune ma ni na kama masa haya (lokacin) ba shi da gida. Daga baya kuma aka ga yana kawo 'yanmata sai makwabta suka ce ni ba mijina ba ne.
Da ya ce ke matarsa ce? Makwabtan sun ga kuna kwana tare ne ko kuwa?
MAIJIDDA: Dalilin da ya sa ya ce matarsa ce (shi ne) lokacin da muka je neman gidan tare muke zuwa da shi, yana bina muka je muka tambaya. To da suka gan ni da hijabina sai suka dauka ni matarsa ce. To da kuma aka samu gidan sai suka ga kuma ba sa ganina. Kuma ni na je na cire hijabina nasa ruwa na wanke dakin na na share.
Wane police station ne kika kai su?
MAIJIDDA: Police station din 'Fagge Division' na kai shi za a kulle shi. Sannan aka ce tunda soyayya ce mu dan fita mu sasanta. Muka fita. Ya dinga ba ni hakuri. Aka ce na hakura. Na ce na hakura.
An kai ga sakaya shin ko a'a?
MAIJIDDA: Har an tafi za a sakaya shin sai dai aka tausaya masa, sai ('yansandan) suka ce in na hakura shikenan a kyale shi, kuma in ban hakura to a kulle shi.
To ga shi ana fim a Zariya. Ko an taba kiranki Zariya ki je ki yi fim?
MAIJIDDA: E akwai wani fim da aka taba kirana to amma lokacin muna wani fim a nan ban je ba. To amma yanzu akwai wani fim da za mu je Kaduna ran ashirin ga watan nan (Yuli) na su Salisu Ma'azu. Amma 'yan Zariya gaskiya ban masu fim ba.
Ban da wannan fim din wadanne finafinai ke gabanki?
MAIJIDDA: Nan gaba a gaskiya ina da fim kamar hudu ban san kuma wanda Allah zai kawo ba. Nna san ina da su presently a hannuna.
Maijidda, lokacin da Balaraba tarasu akwai wata yarinya Hadiza wadda ta saci kudin Balaraba kuma an ce a gabanki aka yi abin. Shin meye gaskiyar abin?
MAIJIDDA: E gaskiya ne ta saci kudin, saboda a lokacin da hatsari ya faru an ce in dauki kayan Balaraba in rike. To kafin in dauka sai ita ta dauka. Da ma ni ba wannan ba ne a gabana saboda ban san a inda muke ba saboda kidimewar wannan hatsarin da ya faru. To ita kuma yarinyar sai ta fara suma, kuma da ma da aka kawo mu sai na ga ta yadda jakar, a cikin jakar kuma akwai wani turare ya fashe, sai na dauka ina ta kuka. To tana cikin suman ne sai na ga kullin abu a siket dinta. Sai na ce bari in dauke kar a sace mata to sai na ji kanshin turaren Balaraba. Sai na ce "A, to ai wannan ma kudin na Balaraba ne." Sai na ce, "Jama'a don Allah ku shinshina min wannan." Sai aka shinshina aka ji aka ce iri daya ne da wancan danshin.
Sai aka ce wannan kudin Balaraba ne. Sai na tambaya cewa "Da kudi a cikin jakar Balaraba?" Sai aka ce akwai, kudi sama da dubu ashirin a cikin jakar. Sai na ce, "To ni ga wanda na gani." Sai aka duba aka ga dubu biyu ne. Ashe akwai sauran kudin a cikin siket dinta. Bayan ta farfado muka tambaye ta sai ta ce nata ne wai. Muka bude mata wuta, sai ta ce wai na Balaraba ne ajiye mata ta yi, wai ba ta dauka da wata niyya ba ne.
To ita kenan sumar karya ta yi?
MAIJIDDA: In ma dai da gaske ne mu dai ta saci kudin Balaraba, ba za mu iya ce wa na karya ba ne don ba wanda abin bai buge shi ba. Amma mu dai mun ga kudin a siket dinta.
Ita wannan Hadiza din ta taba yin fim?
MAIJIDDA: Ta taba yin wani fim har ma na ga fostar a ofishin Tahir, amma bai fito ba kuma na mance sunansa, kuma ta yi fitowa daya a cikin wani fim da muka yi da ita mai suna Matsala; shi ma bai fito ba.
Dawayya ta mare ni, ni kuma na rama
MAIMUNA Husaina ba ta yi ficen Rukayya Umar Santa ba, to amma wannan bai hana su ba hammata iska a Zariya ba. Fadansu ya faru ne lokacin da su Rukayya suka je yin shirin Dawayya 2, wanda ita ce jarumarsa. To bayan an gama Dawayya 2 sai Rukayya ta shiga fim din Manufa 2, wanda ake yi a lokacin. A nan ne suka hadu da Maimuna.
An haifi Maimuna a Albarkawa cikin birnin Zariya a cikin 1983. Duka duka a watan Fabrairu na bana ta shigo harkar fim. Ta yi wasa a finafinai kamar su Gundura, Janhuru, Maina, Manufa 2, da sauransu.
A Zariya, ta fada wa wakilinmu yadda ta samu matsala da Rukayya:
Rukayya Dawayya
|
FIM: Me ya hada ki da Rukayya?
MAIMUNA: E, na taba samun matsala da Rukayya Dawayya. A lokacin daukar shirin Manufa 2 ne muka hadu, ana gobe bikin Balaraba. Da muka hadu muna ta wasa da dariya. Sai aka tafi daukar wakar Hadiza Kabara da Galin Money. Sai ita Rukayya ta tafi ta bar kanwarta. Muna nan zaune sai wani mutum da ake kira 'Game Super' ya fara yi mana dabon kudi. Sai yarinyar, wato kanwar Rukayya, ta ce tan so ya yi mata dabon alewa. Sai ya ce ba zai yi mata ba.
Shikenan sai ta ce mu je cikin Zariya in zagaya da ita ta ga kasuwa. Ta dai dame ni. Sai kuma ta ce in kai ta inda su Rukayya suke shooting (daukar fim). To, muna cikin tafiya sai muka hadu da Mustapha Ibrahim. Sai muka dawo, to ashe ma sun riga sun dawo daga shooting din. Muka tarar ita Rukayya tana ta wasu maganganu.
To, na fito daga cikin mota kenan sai ta hau ce mani wai me ya sa na tafi yawo da kanwarta. Sai na ce, "Ban gane me ya sa na tafi maki yawo da kanwa ba!"
Kawai sai na ji saukar mari.
Ni kuma da haushi ya debe ni sai na rama marina. To a lokacin ne su Aminu Asali da Abubakar Ishaq suka zo suka raba mu.
Kafin kuma mu iso (ofishin) Jari, muna ta cece-ku-ce, zan shiga cikin shagon kenan sai ta sa hannu ta ci mani kwala, sai ni ma na cakume ta. Sai muka fara dambe. Aana raba mu, sai ga Galin Money. Gali ya zo ya raba, yana zaginta. To a wannan lokacin Hadiza Kabara tana goyon bayanta. Amma da Gali ya zo aka maida jawabi sai ta ba ta rashin gaskiya. Daga nan sai ita Rukayya ta fara kuka, ta kuma nade kayanta ta ce ita gida za ta koma. Daga baya sai Hadiza ta zo tana ba ni hakuri.
Zuwa yawo da kanwarta dai ya jawo abin kenan?
MAIMUNA: E, wai na dauki kanwarta zan koya mata iskanci. Ni abin da ya fi ba ni haushi shi ne inda take cewa wai da ma 'yanmatan Zariya ba su da tarbiyya.
Yaya sunan kanwar tata?
MAIMUNA: A'isha.
To yanzu kun sasanta?
MAIMUNA: Har yanzu ba mu shirya da ita ba; ko da mun hadu ba mu magana. In ta nemi mu shirya za mu shirya. Amma ni ba zan yi mata magana ba, sai dai in ita ta fara yi mani magana.
Hadiza ba ta sa an kulle ni ba Inji Danmaliki
NASIRU Danmaliki shi ne furodusan da aka ba da labarinsa a Filin Malam Zurke lokacin da ya yi rigima da wata yarinya a Zariya wai ita Hadiza Kisisina, aka ce jarumar ta sa an kulle shi a caji ofis bisa laifin ya yi mata kage. To, bayan mun buga labarin sai kura ta tashi, inda Nasiru ya karyata abubuwan da suka faru, musamman da aka ce an kulle shi. A cewarsa, shi dai ya san sun yi fada da yarinyar, to amma ba a sakaya shi ba. Ya dora laifin a kan wanda ya ba mu labarin, ya ce bai ba mu shi daidai ba. Hasali ma dai sai da furodusan ya yi barazana a wata hira da aka yi da shi a mujallar Annur cewa zai kai maganar kotu.
To, mun nemi Nasiru domin mu ji ta-bakinsa a kan al'amarin, wato ya gaya mana abin da ya faru a nasa bangaren. Ya kuma amince ba don komai ba sai don a bari a cikin tarihi cewa ga fa yadda abin ya faru daga nasa bangaren. Bismilla:
FIM: Menene gaskiyar musabbabin fadanku da Hadiza Kisisina ?
DANMALIKI: Kamar yadda na bayyana a wata mujalla, ganin yadda aka buga labarin yadda ba haka yake ba, shi ya sa na yi bayani. Wato abin da ya faru, muna zaune a ofishinmu na 'Ya-Kareem Ventures' da ke nan Zariya, ana hira ana jiran fita zuwa lokeshin daukar wani fim, sai ake maganar wushirya. Sai na ce, "Ai wushirya iri-iri ce, amma duk wushiryar da ta wuce irin tawa to gaskiya ta zama gibi." To, Hadiza tana zaune, sai ta ce, "E, gaskiya kuwa, amma ga wushirya sai dai ba fasali." Sai na ce, "A, to ke kina da fasali ne har kike kushe mutane?"
Wannan kalma da na gaya mata bai mata dadai ba. Sai ta fara maganganu haka. To wannan shi ne ya jawo rigimarmu da ita, har ya kai ga mun yi fada da ita. Ta tafi police station ta yi kara ta. To a lokacin ina 'Ya-Kareem,' kuma ina tare da shugaban wurin, wato Adamu Bello Ability. Na sauko kasa kenan, sai na gan ta tare da wani mutum cikin fararen kaya. Sai ya yi mani bayanin cewa Hadiza ta yi kara ta a wurin 'yansanda, saboda haka ana nemana.
To, da muka je kowa ya yi bayani, sai su 'yansandan suka dauki abin ma wasa, suka ce, "A, kai ai ba haka ake yi ba; in kana son ta ne ka bayyana mata mana!" Na ce, "A'a ai ba maganar haka ne ba, tunda muna tare da ita kuma muna harkokin yau da kullum". Sai ta gaya wa 'yansanda cewa na mare ta. Na ce, "A'a, ni ban mare ta ba. In na mare ta ina shaida?"
Sai aka tambaye ta cewa za ta iya kawo shaida? Ta ce e, amma sai ta kasa kawo shaidar. Sai suka ce to ai wannan abu mai sauki ne, muna iya sulhuntawa. Nan ko take muka yi magana da ni da ita muka sasanta kanmu, muka dawo. Ba kamar yadda aka taba bugawa a mujalla ba, cewa wai an kulle ni har wasu furodusoshi sun yo belina ba. Ni ba wanda ya kulle ni ballantana a ce wani ya yo belina.
Su wa suka raka ka wurin 'yansandan lokacin da aka tafi da kai?
DANMALIKI: Ba wani wanda ya raka ni.
To maganar da ka gaya wa ita Hadiza har ta bata mata rai, da gangan ne ka yi don kawai ta ji haushi ko kana nufin wasa ne?
DANMALIKI: Wato ka san idan aka tafi lokeshin, akwai wasu abubuwa da suke faruwa, wadanda idan ba mutum ya cika kama kansa ba, idan an ga dama ana iya yi mashi gori da wannan. To da zaran ka kushe mutum, shi kuma zai iya dauko wata maganar ya yi maka gugar zana. To ni na yi mata gugar zana ne da wani abin kunya da ta yi a lokacin daukar fim din Janhuru, to shi ya sa, kuma ni wurin kawai na fada, da yake ita ta san maganar, sai ya bata mata rai, to abin da ya kawo rigimar kenan.
Wane irin abin kunya ne ta yi?
DANMALIKI: Yanzu dai ba ni son in fada, saboda bayan na yi magana a mujallar Annur, Hadiza ta zo ta same ni, ta ce ya za a yi in yi wannan maganar? Na ce, "A'a ai waccan maganar ita ta jawo wannan." Ta roke ni cewa don Allah don Annabi, wannan abu tunda an yi ya wuce to in rufa in bar shi a hakanan. To ka ji dalilin da ya sa ni kan kaina ban yi bayanin ainihin cikakken al'amarin ba. Amma da abin ya kai mu zuwa kotu, kotu ta bukaci in bayyana zan bayyana, tunda na gani da idona.
Yanzu wane irin hali ake ciki tsakaninka da ita?
DANMALIKI: Mun shirya da ni da ita. Ba wata matsala tsakanina da ita.
To Danmaliki mun gode.
DANMALIKI : Yauwa, to ni ma na gode.
Zuciya ce ta debe ni na doki Hadiza Kabara Inji Saratu Gidado
FADAN Saratu Gidado (Daso) da Hadiza Mohammed Kabara yana daga cikin fadace-fadacen da aka yi ta ka-ce-na-ce a kansu. Daya daga cikin mafadatan, Saratu, ta yarda ta bayyana mana abin da ya hada su har suka yi wannan abin tereren. Ga bayaninta:
Hadiza Kabara
|
FIM: Saratu, yaya aka yi kuka kwashi 'yan kallo ke da Hadiza Kabara?
SARATU: To, gaskiya ni dai na san ina mutunci da ita tun da Allah ya hada mu da ita. Haka kawai sai aka wayi gari na ga ba ta yi min magana. Idan ta zo wuri idan muna da yawa, za ta kira sunan kowa (amma) ba za ta kira sunana ba. Sai na ga me yai zafi? A ka'idar Musulunci ma idan mutum ya zo wuri, kowa zai yi wa magana. To ganin haka, ni ma sai na daure mata.
Haka muke, sai a kira mu mu yi fim tare, mu tafa hannu mu yi wasa mu yi dariya. Amma ana cewa "Cut!" (wato a dakata da wasa), kowa sai ya daure fuskarsa. To, ana haka sai a ranar da mujallar Fim da aka yi hira da Mohammed Kabara ta fito, ni kuma na sayi mujallar ina karantawa, ranar sai abin ya zame mata kamar hauka. To, ko ganin ina karanta wannan hirar da Kabara, shi ne sai ta fara yi min habaici. Da, duk gabar da muke yi ba ta yi min habaici. Sai ta fara yi min habaici da mata; a wani otal ne inda muke fim. Muna kallon satalayit a wata tasha, wata tsohuwa na rawa. Sai Hadiza ta ce, "Mu ma a nan Industry dinmu akwai irin wadannan tsofaffin da ba su da kamun kai." To, kuma ni kadai ce babba a wurin, na san kuma da ni take. Shikenan, ni kuma sai na kalli daya daga cikin abokan aikinmu na ce, "Ah! S. Bello kai fa kwage ne, bar ganinka busasshe, yadda ake ganinka fa, to idanunka da tafin kafarka da tafin hannunka suna nuna tsoho ne kai."
Tun daga nan sai ta yi shiru. Kuma na kara cewa, "Na ma yi imanin ka girme ni tunda ina da sirrinka!" Sai ta yi shiru.
Ka ji abin da ya hada mu.
Saratu Gidado
|
Rannan sai muka sake haduwa a wurin daukar fim, inda muka hadu a Kwality. Nan ma sai ta fara habaici: "Duniya ta juya wa wadansu; yanzu sin daya sin biyu suke yi; an daina ba su principal character!"
Ni kuma sai na juya na kalli wani na ce, "Kai wai mutumin da ke cin tudu uku - ya yi aikin gwamnati a biya shi, ya saida shadda leshi ya samu riba, kuma yai fim - yau ko cewa aka yi an daina fim da ni ai ina nan ina cin tudu biyu."
Yanzu zancen fada dai ya zama gaskiya kenan ko?
SARATU: Ya zama gaskiya. Da ta kai ni kara wurin daraktan fim din sai ya kira ni ya ce don Allah, don Allah mu daina. Na ce masa, "Wallahi ni ban san abin da na yi mata ba take yi min habaici." Sai ya ce bari ya kira ta ya yi mana sulhu. Na ce shikenan.
Sai ya kwala wa Iliya Tantiri kira, ya ce ya kira Hadiza. Muna tsaye mu hudu - darakta (Mohammed Kabara), ni, Tantiri, da Hadiza. Ya ce, "Yanzu na yi wa Saratu fada kan maganarku. Don Allah ban son jin komai. A yi hakuri."
Sai ta buda baki ta ce, "Wai wannan matar ce ina ganinta da mutunci take buda baki take cewa wai kana kwana da ni."
Sai na ce mata, "Ni na fada maki haka?"
Ta ce, "Kwarai. Ba ki fada wa Hauwa Ali Dodo ba? Ko ba ki fada wa Zahara'u Shata ba? Ko ba ki fada wa Maikaba ba?"
Na harzuka. Sai na ce, "To karya ake? ... Na fada, in da abin da za ki yi!"
Sai ta ce min, "Banza!"
Sai na ce, "Ni ce banzar?"
Sai na cire takalmina na bai wa wani almajiri ya rike min.
Tantiri cewa yake, "Don Allah ku rufa mana asiri!"
Na ce ya ba ni wuri. Ya ki. Yo, da na cafki kafadarsa na hankadar da shi, ya fadi a kasa. Na hankade Kabaran shi ma ya fadi, na cakumo ta, na tadiye kafarta, na hau kan ruwan cikinta ina duka. Aka taru, da kyar aka cire ni daga kanta ina dukanta.
Allah ya kiyaye gaba. Sai dai kuma ke Saratu masu kallon finafinanki za su ce me ya sa babbar mace kamarki za ta yi fada a kan titi a gaban jama'a?
SARATU: Wallahi wallahi ban taba yi ba! Kuma duk 'yanmatan fim muna shiri. Zuciya ce ta debe ni, saboda a gaban jama'a ta ce min banza, na ji ba zan hakura ba. Na san ban da hakuri!
Wannan fadan, tsautsayi ne kenan?
SARATU: Tsautsayi ne. Kuma ni a gare ni ya wuce, don idan mun hadu muna gaisawa irin ta Musulunci. Ko a yinin bikin Abida da muka hadu mun gaisa, a lokacin kuwa ba a fi kwana shida da yin fadan ba.
Allah ya kara wa abokarku danko a daina fada.
SARATU: Amin amin.
Yaran ba su jin maganarmu - Ramat
Me shugabannin shirin fim ke ciki don magance irin wannan tijara da ake tafkawa a kan titi? Ko 'yanmatan fim suna jin nasihar na-gaba da su? Fim ta tuntubi Sakataren Kungiyar Furodusoshi Mata, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu. Hajiyar dai ita ganau ce ba jiyau ba a fadan da aka yi tsakanin Hindatu Bashir da Maryam Mashahama a cikin gidanta.
Balaraba Ramat
|
FIM: Hajiya, me za ki ce ganin cewa cikin 'yan watanni hudu an sami yawaitar fadace-fadace tsakanin matan fim?
BALARABA: Abin da zan ce shi ne, yara ne kuma ba su gama mallakar hankalin kansu ba. Shi ya sa har za su tsaya su yi fada, su yi zagi su yi duka a kan titi. Duk inda aka san 'ya mace, an san ta da kame kai, da martaba, da daraja, kuma duk ana tunanin wanda ke kewaye da ita yana yi mata kallon wannan kwarjini. To amma har yau aka ce ga 'ya mace wacce ta mallaki hankalin kanta tana sana'a kuma mai daraja irin ta fim, amma a ce yau ga ta tana kokawa da zage-zage da fada - kan namiji ne, kan kudi ne, kai ko a kan menene - ni ina ganin duk inda aka ce 'ya mace ta yi fada, ta zubar da mutuncita.
Akwai wani abin da za ki iya cewa tunda ku ne ake kallo a matsayin shugabanni mata?
BALARABA: Gaskiya mu mu ne shugabanni mata saboda a cikin 'yan wasa da furodusoshi muna daga cikin tsofaffin da ke ciki, ka gane? Yaran ne ba su cika daukarmu da wata daraja ba wadda har za mu iya yi masu fada su ji. Ko da ganinmu suka yi suna yin wani abu na shashanci, maimakon su kau da kai su ji kunyarmu, a'a sai su ci gaba da yi. Tun ina fada har ya zamanto zai zama sun tsane ni. Sai na tattara su na watsar.
Amma idan da za ka tambayi Fati Faka (Fati Bappa Fagge), yarinyar nan da ta yi Mashi, da wasu 'yan mata guda biyu, idan suna yin abu idan na tsawatar masu za su daina. Amma abin mamaki sai na ji an ce wai ga Fati ga Ummi sun yi kokowa - ko a ina ne? a Kwality?, a'a, a HRB! Abin ya ban mamaki.
Ya ci a ce duk wata budurwa ta gane cewar da furodusa da dan wasa da duk wani saurayi nan na waje wanda bai shafi industiri ba in ya zo yana son kawarki, to ki tattara ki bar masa. Abin da ya sa ya daka tsalle daga kanki ya koma wurinta shi zai sa daga can ya koma wurin wata. Kun ga kun maida shi shashasha kenan.
In har za a zo a tsakanin mace a yi kokowa saboda namiji, to ni ba wani namijin da ya isa 'ya mace ta yi kokowa don shi har a daki lafiyata. Sai dai shi ya daki lafiyarsa.
Samari ke haddasa rigingimun - Nata'ala
Alhaji Nata'ala Aliyu shugaba ne a cikin masu shirya finafinai a Jihar Kaduna. Shi ne furodusan finafinai kamar su Mutum Ko Aljan? da kuma Janhuru. Kuma shi ne shugaban kamfanin 'Jari Video Centre' da ke cikin Birnin Zariya. Saboda haka duk abin da ake ciki game da harkar fim ya sani, musamman fadace-fadacen 'yan fim. Hasali ma dai shi ganau ne ba jiyau ba a fadace-fadace biyu da aka yi a Zariya, wadanda watakila su kadai ne wadanda aka fi sani a Jihar Kaduna, jiha ta biyu wajen yawan fadace-fadacen 'yan fim, wato fadan Rukayya Umar Santa da Maimuna Husaini da kuma na Hadiza Kisisina da Nasiru Danmaliki. Fim ta waiwaye shi a Zariya.
FIM: Me za ka ce kan yawaitar fadace-fadacen 'yan fim, musamman mata?
NATA'ALA: A zahirin gaskiya yawan fadace-fadace da ke faruwa a industiri tsakanin 'yanmata kila a kan samari, to ba laifin matan. Ba azzalumai irin samarin. Duk su suke haddasa fadace-fadacen, saboda sau da yawa za ka ga saurayi daya ya tara kamar 'yanmata biyar, kowacce budurwasshi ce shi kadai. Kuma su 'yanmatan, kowacce tana takama cewa ita ke da shi. To da zaran ta gane cewa akwai soyayya tsakaninshi da wata sai ka ga ba sauran zama lafiya. Duk halin da za ta bi ta raba su za ta yi. To, sanadiyyar haka ne za ka ga ana rigima tsakanin 'yanmatan. Amma wallahi duk laifin mazan ne.
Wace hanya za a bi a magance irin wadannan matsaloli, kuma su wa ke da hakkin magance matsalolin?
NATA'ALA: To ai hanyar gyaran abu ne a bayyane. Kamar yadda na gaya maka, dukkanmu da za mu daina abubuwan da muke yi, to da za a samu gyara.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|