HUSSAINI Sule Koki yana daga cikin 'yan wasan fim din Hausa wadanda Allah ya tarfa wa garinsu
nono. Domin kuwa yana cikin ajin gaba na 'yan wasan da suka fi shahara, ake damawa da su, kuma suke cin moriyar harkar. Bayan haka Malam Husaini yana daga cikin dattawan industiri wadanda ake kallonsu a matsayin iyaye abin girmamawa. A yau shekararsa ashirin yana sana'ar wasan kwaikwayo, domin kuwa daga wasan talbijin ne wasan bidiyo ya riske shi, kuma ya rungume shi ake tafiya tare da shi.
Tunda dai da shi aka fara harkar fim, to yana da dimbin masaniya kan sana'ar. Ya yi fice a finafinai da dama, wadanda suka hada da wasu daga cikin finafinan marigayi darakta Tijjani Ibraheem da na kamfanonin HRB da FKD da sauransu, inda yakan fito a uba ko malami. Kwarewarsa ta sa yakan dace da matsayin da akan ba shi, kuma yakan yi wasa tamkar da gaske.
Abin mamaki, babu mujallar finafinai da ta taba ba da tarihin Malam Husaini, ga shi kuwa yana taka muhimmiyar rawa a harkar shirin fim. To, da yake komai da lokacinsa, kwanan baya wakilinmu SANI MOHAMED MAIKATANGA ya zanta da fitaccen dan wasan inda ya samo mana tarihin rayuwarsa da ra'ayoyinsa kan makomar shirin fim na Hausa. Malam Husaini bai boye abubuwan da ke cikin zuciyarsa ba game da harkar, musamman ra'ayoyinsa kan batun raguwar darajarta da kuma rawar da ya kamata gwamnati ta taka a cikinta.
Bismilla:
FIM: Da farko muna son mu san tarihinka a takaice.
HUSAINI: Ni dai an haife ni shekaru 47 da suka wuce, kuma na tashi na rayu a Koki cikin birnin Kano. Kamar shekaru 45 da suka wuce, kamar yadda kowane yaro Bahaushe yakan tashi a cikin Birni, na fara da makarantar allo, sannan makarantar Islamiyya ta dare, sai kuma na shiga wata makarantar Islamiyya primary wacce aka fi sani da Makarantar Dantata. Bayan na gama na zo na shiga wata makarantar musayar al'adu ta mutanen Misira, wato 'Egypt Cultural Centre.' Daga nan sai na shiga harkar koyarwa. Sai kuma na shiga makarantar horon malamai ta Arabiyya wacce yanzu take Hadeja, wadda a wannan lokacin ana kiranta 'Warure Arabic Teachers College'. A wannan lokacin ina yinta kuma ina koyarwa, wanda hakan ya saba wa ka'ida ta aiki da ta karatu. Daga baya aka ba ni zabi, sai na ci gaba da harkar koyarwa. Ina wannan koyarwar kuma ina tafiyar da harkokin kasuwancina kamar kanti a gida; na yi harkar keke, gyaran keke, saida keken dinki, aikin harhada keken dinki, da kuma gyaran shi kanshi keken dinki. To haka dai a yi wannan a bar wannan. Haka kuma na yi aikin tuka motocin haya daga kan bas zuwa taksi, a-kori-kura da makamantansu. Ina da mata biyu da 'ya'ya goma a yanzu.
FIM: Yaushe ka fara harkar wasan kwaikwayo, kuma me ya ba ka sha'awa ka shiga harkar?
HUSAINI: Na shiga wannan harka tun 1982. Kuma sha'awar tunanina da abin da nake ganin na gane, da kuma wasu nake ganin ba su fahimci abin yadda ya kamata ba, shi ne ya sa nake so in bayyana ra'ayina ta wannan fuskar, in ba da gudunmawa ga al'umma gwargwadon fahimtata. Kuma na fara ne da yin wasan a gidan talbijin wanda yanzu ake ce masa STV-67, wanda an kafa ta a 1982, sun fara aiki ka'in da na'in a 1983 'yan watanni bayan kafa ta. To shirin da aka fara yi a wannan gidan talbijin ta fuskar wasan kwaikwayo shi ne "Zaman Duniya". A wannan shiri ne na fara yin wasannin kwaikwayo a wata kafa ta watsa labarai ban da wasannin dandali haka kara-zube a gari, kuma wanna shirin na "Zaman Duniya" yana nan yana ci gaba a yanzu in ban da sauya masa suna da aka yi ya koma "Tsumagiya."
FIM: Ta yaya kuma ka fara fitowa a irin finafinan bidiyo na Hausa na yanzu?
HUSAINI: Na san dai duk dai wanda ya shahara a kan ita wannan harka ta wasan kwaikwayo to gaskiya dai ya fara ne daga kafofin yada labarai, su ne talbijin da bidiyo, saboda haka da wanda ya kware a wajen bangarensa na gudanarwa da kuma bangaren dan wasa wadanda kusan duk mun yi aiki da su kuma yanzu su ne ake kiransu shahararru, to duk an san juna. Ta wannan bangaren ne aka ga ya kamata a shigo da Husaini Sule Koki cikin wannan harkar, wanda har izuwa yanzu nake ba da gudunmuwata gwargwadon abin da Allah ya yassare.
FIM: Me za ka ce kan yadda ake kallon 'yan fim da wata manufa ta rashin kirki ko tarbiyya?
HUSAINI: Akwai wasu abubuwa guda uku wadanda dan'adam ya kamata ya fahimce su kuma kowane mutum yana fassara tunaninsa gwargwardon abin da shi ya fahimta, ba wai hakika ba. Idan kana son sanin hakika dole sai ka shiga cikin al'amari ka san ya yake tukunna. Amma in dai daga nesa kake ba za ka taba ganewa ba. Farko dai dabi'un 'yan wasan kwaikwayo da akan ga wadansu abubuwa wadanda akan fassara su da rashin tarbiyya ko kuma rashin sanin ya-kamata, sun samo asali ne daga nishadi da kuma kasancewar duk wanda yake sha'awar fim za ka tarar mafi yawansu mutane ne masu sha'awar barkwanci na wasa da dariya, domin abin da ya kunsa kenan. To ko ba fim ake yi ba idan duk ka tara mutum daya biyu goma masu sha'awarar barkwanci to za ka iya fassara su da irin fassarar da kake yi wa 'yan wasan kwaikwayo. Wannan shi ne dalili na farko da nake so mutane su fahimta a kan abin da ya sa 'yan wasa suke da wannan dabi'a. A cikin harkar gudanar da wasan kamar yadda kuka sani dukkanninsa barkwanci ne; mutum ne zai fito yana saurayi ya zo ya makale murya an shasshafa mar wata hoda an sa masa wasu irin kaya ya dawo tsoho a ce wai shi ne Malam Ya'u wani dattijo dan shekara saba'in, to ka ga duk wannan abu ne na ban-dariya. To duk mutanen da suke da wadannan dabi'u in ka duba, duk inda suka hadu suka taru wannan barkawancin ba za ka raba su da shi ba. Abubuwan da ake gani galibi ba wai shi ne hakikanin lalacewar ba, wani abin shirme. Iya wannan da ka gani iya nan abin ya tsaya. Abu na biyu kuma ba wai maganar 'yan fim ba ne suka lalace ni a fahimtata, Allah ya kawo mu karshen duniya ne wanda mafi yawan al'umma sun lalace. Idan ka shiga cikin kowane irin al'amari haka za ka gani kamar yadda kake gani a fim, bambanci kawai shi ne shi fim abu ne wanda kullum za a kalle shi da ido kuma kullum an sa. Amma misali yanzu in ka dauki makarantun boko, za ka je ka tarar da wasu masamman higher institutions (manyan makarantu) za ka ga 'yanmata irin shigar da suke kamar Chicago ta Amerika, yadda kuma suke cudanya da hulda da maza kai kanka ko ba ka kaunar Allah ka san ana yin abubuwa na rashin mutunci wadanda suka saba wa addini. Amma duk wadancan mutane masu maganar 'yan fim ba sa maganar wannan, wanda wannan wata tsokana ce wacce ba wanda yake ganin zai iya maganinta shi ya sa ba a ma kulawa da irin wannan. To wannan ni shi ne fahimtata. Ina fata an gane.
Abu na uku kuma, akwai wadanda gaskiyar magana ba su da tarbiyya kuma ba su san ya-kamata ba; da ka kalle su za ka gane da ma ba su da ko 'Ah' inda suka fito ba da'a ko tarbiyya kuma dole ka fassara su da cewa mutanen banza ne masu zunubi domin siffarsu da al'adun da suke yi yana nuna haka din. Wadannan su ne abu uku da nake so masu kallo ko karatun mujalla su yi la'akari da kowanne cikin abin da na fada.
FIM: Yanzu ka fito a finafinai kamar nawa?
HUSAINI: Gaskiya sai dai kiyasi, domin tun ina kirgawa har na gaji. Amma dai za su kai tamanin zuwa casa'in.
FIM: Ana cewa finafinan Hausa suna gurbata tarbiyyar addinin Musulunci. A matsayinku na dattawa kuma ana muku kallon malamai masana addini, wace irin shawara kuka taba bayarwa domin ganin an gyara bangaren tarbiyyar addini da ake surutun cewa ana gurbata ta a fim?
HUSAINI: Na farko dai su ma masu soke-soken wasu suna yinsa ne a jahilce, domin duk wanda aka ce wane fim suka gani sai su ce maka su gaya musu aka yi. To tunda mutane suka fada ka ga babu hujja kenan ta abin da ake magana a kai. Idan har ana maganar tarbiyya, yawancin abin da mutane suke magana dai shi ne wake-wake da raye-raye, amma idan suna maganar labari ne, na san kashi 95 cikin dari na labari ai ba shi da wata illa in dai ba an samu rashin kwarewar yadda za a tsara yadda za a tafiyar da shi ba aka samu tangarda koyarwa ta zama lalatawa. Tunda dai za a ce ne akwai wani ya yi kirki ga yadda kirkin ya kare, akwai wani kuma ya yi rashin kirki ga yadda ya samu sakamakonsa.
Ina ganin kusan kowane fim na Hausa abin da ya kunsa kenan. To amma rashin kwarewar dan wasa ko darakta ko furodusa wani lokaci tana sawa a samu matsala ta yadda za a kasa sarrafa abin yadda zai koyar da mutane sosai, sai ta zama matsala. To in ba irin wadannan ba ni ban ga wani abu sosai da za a yi magana ba. Idan kuma an samu shirmen kamar misalin fim din da aka tsara shi a kan wani layi da ya shafi shari'ar Musulunci in kuma har da mu a ciki kuma an nemi shawararmu ko kuma in mun ba da shawarar za a karba, to muna bayarwa kuma ana amfani da shi. Kamar yadda 'yan kallon suke gani suke yabawa, domin da yawa wasu abubuwan da mukan fada suna dan sabawa da ainihin abin da yake rubuce a cikin ainihin labarin wasan, musamman in ka kula cewa za a saki layi game da addini ko tarbiyya. To amma mutumin da ya sayi rariya ya san da ma za ta zubar da ruwa; duk mutanen da suke shirya fim din nan mafi yawa yara ne masu kuruciya, kuma babu wani abu da zai burge su a duniya sai abin da ya shafi nasu na kuruciya. To mutum ya fito da jarinsa, kai kana matsayin lebura ka ce za ka gaya masa yadda ya kamata a yi kuma har ya saurare ka, illa iyaka dai wadanda suka yarda kana da basira ka san abin za ka iya yi fiye da nasu illa dama ce suka samu to sukan nemi shawara.
FIM: Me za ka iya cewa kan raguwar darajar harkar fim a kan yadda take da da yanzu?
HUSAINI: Akwai abubuwa da yawa da za a kalla ba abu daya ba kai tsaye ka ce shi ne ya kawo raguwar harkar ba ta fuskar samu. Na farko dai tukunna da an shigo rambatsau, kowa ya shigo cewa harkarsa ce ya iya, da wanda ya iya da wanda bai iya ba, da wanda ya sani da wanda bai sani ba. To duk abin da aka cika akai masa yawa dole ne darajarsa da kimarsa za ta ragu. Daya kenan. Sannan su kansu masu labaran, kullum kana nuna wa mutum cewa ga wani tsari da kake ilimintar da shi a kai, to ka kasa kawo masa sabon tunani, sai kawai kullum magana ta soyayya kawai, ba wani abu na sabon tunani da zai zo, don haka sha'awar abin ta ragu daga wajen mutane ba kamar yadda take da ba, take da kaifinta, tunda abu ne wanda da can ba a yi to lokacin da ba a yi ka san ba sha'awar abin kuma aka zo a hankali abin nan ya shiga zukatan mutane da yawa, to yadda ya shiga da yawan nan haka yake raguwa da yawan nan saboda wadancan dalilai da nai maka bayani da kuma wasu.
Sannan akwai magana ta ha'inci. Ha'incin nan shi ne yawancin masu bidiyo kulob suna lalata harkar sosai sosai, saboda suna hana mutane sayen fim, duk mutumin da zai zo ya ba da naira ashirin kurum a ba shi fim ya je ya kalla in ya kalla ya dawo da shi, ka ga ba zai bata lokacinsa ya sai kaset a kan naira dari biyu da hamsin ba, sai wadanda suka dauka cewar dari biyu da hamsin a wajensu ba wata aba ba ce, kuma muhimmancin abin sadda duk suke so su dauka su sa su gani da iyalansu ya fiye musu zuwa a je a karbo wannan abu a wani waje, wanda wasu ma kamar zubar da mutunci ne da kima. To wannan shi ma ya taimaka wajen lalacewar harkar fim din, a fahimtata.
FIM: Amma kuma wasu sun nuna cewa ba laifin bidiyo kulob ba ne, laifin furodusoshi ne na yadda finafinan nasu suna fita inna rututu da kuma su sun ki su tsara yadda al'amarin zai kasance tsakaninsu da 'yan bidiyo kulob din, suka ce ko a kasar waje ma ai akwai gidajen ba da hayar kaset.
HUSAINI: Duk sa iya fadar komai tunda sana'arsu ce kuma hanyar neman abincinsu ce suke karewa. Amma a wannan kasar wadda babu doka da oda kwata-kwata sam, kawai doka da oda suna aiki ne a wasu 'yan kalilan din gurare, wanda za ka ga ita kanta gwamnatin kasar abin da take kuka da shi kenan - doka da oda, wanda wannan ya sa komai na gwamnati da na sauran jama'a ya zama ba ya da tasiri yadda ya kamata. Amma idan kana maganar kasashen duniya, akwai kasashe ma matalauta wadanda ba su kama kafar arzikin Nijeriya ba, amma idan ka je za ka ga cewa doka da oda suna aiki ba kamar yadda suke a nan Nijeriya ba. Saboda haka a nan Nijeriya duk laifin da ka yi, matukar za ka dau kudi ka bayar, kawai shikenan. Saboda haka wannan sana'a tasu tana da hadari a nan Nijeriya dangane da masu shirya fim da kuma su, domin kusan in ce kura da shan duka gardi da karbe kudin. Ni kawai ina ganin harkar bidiyo kulob ta taimaka wajen raguwar darajar. Ban ce ita ce komai ba, amma ta taimaka.
FIM: Wasu suna ganin rashin fadada harkar kasuwancin ne, wanda kawai su finafinan nasu iya Bata kawai suka tsaya, ba a san yadda za a fitar da su a yi tallarsu a sauran kasashen waje ba.
HUSAINI: Gaskiya ni nawa ganin ba haka yake ba. San da aka zo harkar ba ta lalace ba kuma ana samun kudi, ana da wata kasuwar da ta wuce Bata? Ai a lokacin babu wata kasuwar da ta wuce Bata. Da ma can da aka yi harkar iyakarta Bata, haka yanzu ma da ba ta ja a Batar take. Saboda haka ba wannan ne kadai ba, wannan kurum wani bangare ne da za a ce an kasa yin kokarin ciyar da harkar gaba. Amma wannan muna maganar tabarbarewarsa ne ma ya yi baya, ba maganar ci-gaba ba, saboda mutum ne zai sai kaset na dari biyu da hamsin sati mai zuwa wani zai iya fitowa, bayan sati biyu wani zai iya fitowa, ya gwammace ya je ya ba da naira ashirin a ba shi haya, da ya gani ya dawo da shi, wannan shi ne ainihin jigon da ya karya kasuwar kaset.
FIM: To ita maganar da ake yi kan fitowar finafinai inna-rututu fa ba tsari?
HUSAINI: Zai yi wahala a iya juyar da wannan saboda a tsarinmu na kasuwancin Bahaushe - ba ma sai fim ba ko ma me - babu maganar hada kai. Kuma kullum aka zo aka zauna za a tsara wani abu in ka ji wani na ta zakalkalewa cewa a zo a tsara din, to shi ne ya shiga cikin matsala kawai, amma ba kawai yana tunanin matsalar wasu ba ne cewa ya kamata baki daya a zo a zauna a yi wani tunani don a gyara lamarin. Da haka duk wanda ka ji yana ihun shi ya shiga matsalar, wanda bai shiga ba ba ruwansa, ta kansa kawai yake yi, ba ruwanshi da a zo a gyara wani abu. Kuma in an zo gyara akwai wadanda a shirye suke su kawo rudu, wane ba ya shiri da wane wane dan banza ne, su wane 'yan wofi ne, maimakon a maida hankali a ga cewa yaya za a yi a gyara kowa ya amfana, amma sai a je a rusa abin. Shi ya sa ko mutum yana da tunani ba zai tsaya ya fito da tunanin nasa ba domin ya yi amfani ga mutane ba.
FIM: Me za ka ce kan tururuwar 'yanmata cikin wannan harkar, wanda wasu ma ba su taba ko fitowa a fim ba ko sau daya, kuma suna kiran kansu 'yan fim, sai dai kawai daga ofishin wannan furodusa, sai wancan sai kuma yawon gala?
HUSAINI: Gaskiya ne yana faruwa, amma kuma mata mutane ne masu rauni a harkar rayuwa. Don haka su 'yan sharholiya ne, duk inda za a taru a yi wani shashanci su kawai suna sha'awar abin. Don haka ne suke fakewa da mu su shigo cikinmu su yi amfani da mu da wannan dama su yi abin da ya kamata su yi. To amma tunda harka ce ake yin ta ba babba ba yaro kowa ji yake ya isa, bare wanda yake jin shi a cikin abin ana yi da shi fiye da wasu, ba wani wanda zai iya tsawatarwa. Amma tururuwar yara cikin harkar nan ba ta da nasaba face rashin tsari da hadin kan su furodusoshin da suke da shi a junansu.
FIM: Menene maganin tururuwar tasu?
HUSAINI: In dai har an yarda ana so a yi gyara sai dai a danganta shi da gwamnati, domin tunda ku i ku ba za ku iya sarrafa kanku ba, saboda wadancan rikice-rikice, da nake ma bayani. To idan gwamnati ta shigo ta kawo wani tsari nata, wala-Allah wannan tsarin ya iya yin tasirin da kawai da karfi da yaji dole a hakura a bari. Kuma shi kansa fim din da ake yi, labaran da ake bayarwa na fim din yana ba da muhimmanci ne ga kananan yara fiye da masu dan shekaru. Alal misali, za ka ga akwai iyaye wadanda ba su wuce mutum hudu ba, akwai 'yanmata da samari matasa wadanda su ma ba su wuce haka din ba, sai kuma wadanda suke mara musu baya, to amma za ka ga yara kanana suna da sina-sinai arba'in ko hamsin a cikin fim kwaya daya, amma akwai fim din da za ka ga uba wanda dansa ne ko 'yarsa ake magana a kai za ka ga yana da sin biyu kawai ko uku saboda a tunaninsu wadancan yaran su ne ake nuna rayuwar a kansu. To saboda haka tunda su wadancan yara su ake son nuna rayuwarsu, don haka dole yara irin wadannan za su yi ta kwararowa cikin harkar kuma ba tare da tsari ba. Amma da akalla ka yi raba-daidai, kamar in ka kula a cikin gida ai ba yaranka ne suke tafiyar da al'amuran gidan ba, kai ne, wanda ya hada da tarbiyyar matan da yaran duk kai kake tafiyar da su. To amma a fim sai a nuna wadannan yaran su suke tafiyar da al'amuran rayuwa. To ka ga tunda haka ne dole su yi ta kwararowa cikin al'amarin.
FIM: Me za ka ce kan yadda wasu ke ganin cewa harkar nan da wani lokaci mutuwa za ta yi, har wasu na ganin wannan gwamnatin ruguje harkar ma za ta yi?
HUSAINI: Wannan shaci-fadi ne kawai irin na mutane da shashanci da rashin basira da rashin iya hangen nesa da rashin sanin abin da ka je ya zo. A wannan duniyar ta yau wacce duniya ce da za a iya kiranta sabuwar duniya ta bature, akwai abubuwa da yawa wadanda an riga an gabatar da su a duniya babu yadda za a yi yanzu a ce an kau da wadannan abubuwan sai dai in Mahadi ne ya bayyana ko kuma tashin kiyama ya zo. Domin kashi casa'in da tara cikin dari na rayuwar mutane ta ta'allaka ne da abin da bature ya zo da shi, ko a mu'amala ne ko a abubuwa na kasuwanci ko ma wane iri ne. To fim din nan in ka duba za ka ga gidajen manyan mutane a ko'ina a duniya akwai tashoshi na talbijin na kasashen duniya, wata ma sai dai ka gan ta a talbijin amma ba ka taba saninta ba ko jin ta ba a rediyo. Amma za ka ga kuma wadannan tashoshi kusan dari da wani abu ko dari biyu, to ya za ka yi da wadannan? Sannan finafinan da ake shigo da su daga kasashe daban-daban na duniya kuma ba ka isa ba ba yadda za ka yi da wadannan finafinan a kasa irin Nijeriya wadda ba ta da doka da tsari haka ta tabbata. To ka ga in kana maganar a daina fim, to wallahi matasa za su samu kansu a cikin wani abu wanda ya fi wannan 'Hausa film' din illa. Saboda haka zancen banza ne wai cewar wai za a daina finafinan Hausa. Wani tsari daga gwamnati wannan duk shirme ne. Ko ma waye zai zo da tsari wannan zancen banza ne, ba zai yi aiki ba.
FIM: Mecece shawararka ga masu yin wannan harkar?
HUSAINI: Shawara kawai mutum ya zama yana da tunani mai zurfi kuma yana da ilmi yana kuma aiki da shi, domin ka san ilimi kawai ba shi ne amsa a rayuwa ba. Ba ma harkar fim ba kawai, harkar Nijeriya ma gaba dayanta in ka lura ilimin da ake da shi ya isa a ce mun ma rike wasu kasashe a duniya na Afirka muna yi musu jagoranci, to amma ilimin bai yi maganin matsalarmu ta Nijeriya ba ballantana ta wasu kasar ta makwafta. To haka ma a harkar fim akwai masu ilimin to amma ilimin ba ya yi musu aiki. Wani abu da zan iya cewa da muka samu kanmu a ciki na yanayin rayuwa wanda ga ilimin ga komai amma kuma an ajiye ilimin kawai a zo a yi ta yin shashanci daidai da wanda ma bai san 'zo in kashe ka' ba cikin harkar ilimi. To kawai abin da ya kamata mutane su yi shi ne su yi amfani da iliminsu, a zauna a kau da zancen wani bambance-bambance, bambanci a kowane irin yare a duniya a kowace irin duniya akwai bambance-banbance na zama tsakanin wannan jinsi da wannan jinsi. Alhamdu lillahi.
FIM: A karshe shin yanzu ban da harkar fim mecece takamaiman sana'arka ko aikinka?
HUSAINI: Ni a yanzu halin da ake da ma ni dan kasuwa ne, babbar sana'ata shine dab'i (printing) ne, kuma nakan yi ayyuka kanana da matsakaita a kananan hukumomi daban-daban da kuma kamfanoni. Akwai kuma harka ta foreign exchange, wato canjin kudi da nake yi. Duk wadannan harkokina ne, kuma duk da dai cewa na fi ba wa harkar fim muhimmanci to ban tsaya a nan ba; nakan dan bugi kirji in bugi taiki wani lokaci.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin