Daga SANI MAIKATANGA
a Kano
FITACCEN dan wasa kuma furodusan nan Mudassiru Haladu yayi aure a ranar Lahadi, 7 ga Disamba, 2003. An daura aurensa da masoyiyarsa Zainab Sani Darma.
Tun da farko mahalarta daurin auren sun hallara a gidan Sharif Musa a unguwar Hanga kusa da makarantar Malam Mamman, daga nann suka nufi wurin da aka daura auren, wato gidan Alhaji Ibrahm Maigoro Agadasawa.
An daura auren na Mudassir, wanda ake kira Mudan ko Barkeke ko 'Young Producer', da misalin karfe 10:30 na safe a kan sadakin N5,000 kuma ya samu halartar 'yan'uwa da abokan arziki da dama; kusan duk wanda ke cikin harkar fim ya samu halarta ko da a makare ne. Daga cikin wadanda suka halarci wurin akwai ubangidan Mudassiru din na industiri, wato A.A. Sharif (Momo), da Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Chidi, da Ishaq Sidi Ishaq. Dimbin 'yan fim sun shiga gaggaisawa da juna tare da yin hotuna.
An tashi daga daurin aure lafiya, amma biki sai nan gaba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin