Na makara ban zo ba, suka tafi suka bar ni
In ji Babbar Kawar Amarya
A AL'ADA, idan za a yi aure a kusan kowace al'umma a duniya, ma'auratan sukan nada Babbar Kawa da Babban Aboki. Aikinsu shi ne su tsare sirrin ma'auratan, su zama manzanni a tsakanin ma'auratan, kuma su ne manajojin shirin auren, wato masu wakiltar ma'auratan. SAFIYA MU'AZU ce Babbar Kawar Balaraba Mohammed a wannan auren. Wakilinmu IRO MAMMAN ya same ta a gidan auren yarta inda take zama, a unguwar Kurmin Mashi a Kaduna, domin jin yadda aka yi aka tafi Kano ba tare da ita ba a matsayinta na Babbar Kawa, da kuma wasu abubuwan da suka jibinci kawancensu da Balaraba, da shirin auren, da kuma mutuwar da ta auku.
Ita ma Safiya, 'yar wasan fim ce. Ta fito a finafinai da suka hada da Tasiri 1 da Rigar 'Yanci (duk tare da Balaraba). Bayan haka, wasu finafinan nata wadanda ba su fito ba su ne Harsashi; Nasaba; Guza; da Nufaka. Hasali ma dai ita ce jarumar shirin Nasaba. A cikin Harsashi, inda suka yi wasa tare, Balaraba ce ma jarumar shirin.
FIM: Safiya mecece dangantakarki da marigayiya Balaraba?
SAFIYA: Dagantaka da marigayiya Balaraba ba wata boyayyiya ba ce, 'yar'uwata ce a Musulunci kuma babbar kawata. A 'yan wasa ban da kowa kamarta.
Ya aka yi kuka hadu da ita har kuka fara kawance?
SAFIYA: Wata ran na je Kano ana wani taro na artistes a (gidan sinima na) Lale, muka hadu da ita. Ta ce min ita ma 'yar Kaduna ce, na ce mata ni ma 'yar Kaduna ce. Sai ta nuna mani sani, na ce ai ni ma na san ta a Kawo. Daga nan muka fara kawance har aka zo lokacin shirin wani fim mai suna Tasiri, sai kawancenmu ya kullu sosai-sosai.
Da fara kawancenku yanzu ya kai wata nawa?
SAFIYA: Za a yi shekara daya.
Kina da masaniyar komai kan soyayarta da Shu'aibu har zuwa lokacin auren?
SAFIYA: E. A gaskiya wasu abubuwan ina sane da su, don ta ba ni labari. Ko farkon zuwanta Kano, da tana wurin Dan Zariya, amma sai suka hadu da Ibrahim Sinana. To daga nan da suka hadu da Shu'aibu sai suka fara soyayya, kamar yadda ta gaya man.
Ta hanyar Sinana suka hadu da Shu'aibu kenan?
SAFIYA: Ba zan iya sani ba. Ta gaya mani ita dai ta fara sanin Sinana kafin Shu'aibu.
To lokacin da bikin ya zo, a matsayinki na kawa wadanne shirye-shirye kuka yi don bikin?
SAFIYA: A gaskiya tun bikin yana sauran kwana 30 muka zauna da ita, na ce mata ya kamata mu zauna mu yi shirye-shiryen biki. Amma sai take ce mani ai ita ba ta damu da a yi wani biki ba. Nake tambayarta, "Ba za yi luncheon ba?" (wato walima) Shi ne ta ce mani in na ga za a yi to sai a yi. Har ni ina ce mata, "Wannan wace irin magana ce?" Ta ce mani ita dai burinta kawai a daura auren. Bayan mun yi haka, sai kamar mako uku sai muka hadu, ga ni ga ta, ga shi Shu'aibu. Sai nake tambayarshi maganar biki. Shi kuma ya ce ba ga ni ga amaryar ba? Da muka koma gefe sai na ce mata ya kamata mu fita da anko. Ta ce mani ita ta rasa wanda za ta fitar saboda kowa yana kawo irin nashi wanda yake so. Da ta ce mu fitar da leshi, ni kuma na ce, "A'a, ba kowa ke da kudin leshi ba. A fitar da kamfala." Ta ce to in je gun mamanta in karbi N1,200 in sayi wannan anko, ita kuma za ta koma Kano don za su yi wata tafiya har da Shu'aibu zuwa Nijar. Ni kuma Allah bai sa na je gidansu ba har sai ana jibi dauren aure.
A lokacin da ake hidimomin auren, akwai wasu maganganu da ta fada maki wadanda suke da alamun kamar bankwana take maki ba ta sani ba?
SAFIYA: A gaskiya akwai wata magana da ta fada mani a ranar daura auren da daddare, bayan rasuwar (maganar) ta ba ni tsoro. Don mun raka su Shu'aibu za su tafi (cikin gari shi da su Sani Mai Iska), ta kamo hannuna muna tafiya. Na ce mata mu je ta sa goggoro a yi rawa, saboda da daddare ne. Ta ce mani ita ta gaji ba za ta iya rawa ba. Ta ce, "Shin masu kidan ma wa ya kira su?" Na ce mata, "Watakila sun ji sanarwa a rediyo ne suka zo." Ta ja ni muka shiga dakin mamanta. Sai na ce mata ni zan tafi gida. Ita kuma yarta Jummai san da za a yi tafiyar take ce mana ita tun da aka fara bikin take jin kanta ya yi mata nauyi ba ta jin dadin jikin, kila ma ciwonta ne zai tashi. Na ce mata,"Hayaniyar mutane ne."
Mu yi magana kan batun hadarin, wanda mun samu labarin da ke aka shirya za a yi tafiyar tare da amarya a cikin motar. Me ya faru ba ki bi su cikin motar ba?
SAFIYA: Mun rabu da misalin karfe 10:30 na safe a kan zan je gida in shirya in dawo. Na fito kofar gidansu har wanta yake ce mani, "Ku yi sauri fa ku dawo don a yau za mu tafimu dawo." Da na dawo gidanmu sai na ji duk jikina ya yi mani nauyi, har na kwanta, har wajen karfe 2 ban yi wanka ba. Sai da yata ta dawo daga makaranta nake ce mata, "Za mu tafi party a Kano." Ta ce ya za a yi a ce zan tafi party a Kano, za mu kwana kenan? Ta ce ba za ni ba. To akwai wasu kawayena da muka dinga rokonta har ta amince. A takaice har karfe 3 ban baro gida ba. Don haka muna zuwa (gidan su Balaraba) wata kanwarta ta ce ai har sun tafi. Amma a kan hadarin ban san komai ba kan abin da ya faru.
Da gaske ita ma an ce ba ta son ta tafi a ranar?
SAFIYA: A gaskiya ba ta son ta tafi.
Saboda me?
SAFIYA: Haka nan kurum ta ce ba ta son ta tafi.
Kuma iyayenta ma ba su son ta tafi din?
SAFIYA: E, gaskiya mahaifinta ma ba ya so, don har wanta da kuma ita yarta da ta rasu suke cewa mu je mu roki baban.
Kina nan lokacin da Shu'aibu ya yi sallama da ita da safe ya tafi Kano?
SAFIYA: Ba na nan.
Kina da masaniyar wai wasu mutane sun fada mata cewar in aka daura mata wannan auren za ta mutu?
SAFIYA: Ni ba ta taba gaya mani haka ba.
A dazun kin ce a daren da aka daura aure ta kama hannunki tana son gaya maki wata magana. Me ta gaya maki?
SAFIYA: Ba ta gaya mani komai.
Saboda me?
SAFIYA: Saboda mun zauna kenan sai ta ce mani ita ma kanta ciwo yake yi Sai na ce mata bari in dauko goggoronta in sa mata mu je mu yi rawa. Ta ce, "Wa ma ya kira masu kidan." Maganar masu kidan ta sanya aka manta da waccan maganar da ta yi niyyar gaya mani.
Ya aka yi kika samu labarin abin da ya faru?
SAFIYA: Ni da wasu kawayena su biyu muna gareji za mu tafi Kanon, har mun biya kudi, sai na ce ni na fasa. Mai lodin ya ce shi ba zai maido mani da kudina ba tunda na biya kuma ya gama lodi. Wani mutum ya goyi bayana kan cewa tunda ban gamsu da tafiyar ba in hakura. Su kawayen nawa suka matsa sai mun tafi tunda ni ce babbar kawa. Da muka tafi, har mun ga motar a inda suka yi hadarin, amma ba mu gane cewa ta su Balaraba ba ce, har muka isa Kano. Mun zuwa sai 'Young Producer' (Mudansiru Haladu, furodusan Badali) ya zo ya ce mani, "Safiya ya aka yi haka? Ba kya cikin motar ne?" Na ce mashi ni ban gane abin da yake nufi da ba na ciki motar ba. Ya ce, "Ai yanzu yanzu aka yo waya cewa Balaraba ta yi hadari har ana kyautata zaton ta mutu!" Nan take na ji numfashina ya dauke, na tsuguna a wurin. Daga nan muka je gidan yata muka kwana. Da safe muka dawo.
Da kuka dawo kin je gidansu?
SAFIYA: Na je gidansu na tarar da mutane, ina kuka, ana mani gaisuwa har na je ga iyayenta na gaida su.
Yanzu wace addu'a za ki yi wa Balaraba?
SAFIYA: Ni kam, addu'a a kan Balaraba, muna sa mata ran rahamar Allah. Don duk wanda ya san ta, ya san halayenta masu kyau ne. Ina ma iyayenta da shi Shu'aibu addu'ar Allah ya ba su dangana. Ni din nan ba na iya kwatanta halin juyayin da na samu kaina dangane da rasuwar Balaraba. Abu daya yake kwantar mani da hankali kan mutuwar tata, shi ne yadda a kowane lokacin take ce mani ita burinta ta auri Shu'aibu. Kuma Allah ya cika mata wannan burin nata kafin mutuwarta. Allah ya gafarta mata.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin