Kokarin kare mutuncin kanwarta ya sa ta sha tafi
Daga ABDULLAHI NASIR (ABILITY) a Zariya
A KODA yaushe, idan aka ce mutane sun taru don gudanar da wadansu ayyuka, ya-Allah ko na suna ko na aure ko kuma makamancin wannan, za ka ga mutane da halaye daban-daban, wasu masu hakuri wasu kuwa ba su da hakuri. Dalilin haka ne za ka ga sababbin maganganu nama juna shigan giragizai, musamman a wannan lokaci na shirin finafinan hausa.
A ranar Alhamis, 14 ga Maris, 2002 (kwana hudu bayan dawowarta daga bikin Musa Liman a Jalingo, kuma kwana biyu kafin rasuwar Balaraba), wani abin mamaki ya faru a Zariya cikin Jihar Kaduna a wurin daukar wani fim mai suna Manufa, wanda wani sabon furodusa ya shirya. Rukayya Umar Santa ('Dawayya') da Hadiza Kabara suna daga cikin 'yan wasan fim din.
Ita dai Rukayya, ta zo shirin Dawayya 2 na 'Iyan-Tama Multimedia' ne. Shi Dawayya na 1 yawancinsa an dauke shi ne a Zariya. Sabili da daya daga cikin 'yan wasan fim din, marigayiya Balaraba Mohammed, za ta yi aure, kuma ga shi ba a yi kashi na 2 ba, shi ya sa su furodusan fim din, Ahmed M. Sarari, suka zo don karashe fim din.
To a lokacin da suke gab da gama daukar Dawayya 2 sai faduwa ta zo daidai da zama, su ma masu shirin Manufa za su fara nasu fim din, kuma masaukinsu (location) ya kasance daya da na 'yan Dawayya 2, watau 'Congo Conference Hotel'.
Sai furodusan Manufa ya shirya da Rukayya Dawayya ta yi masa wasa a fim din nasa. Suka daidaita da ita. Da ma ta zo da wata yarinya mai kimanin shekaru 14 wadda ta ce kanwarta ce, mai suna A'ishatu, kuma ba 'yar wasa ba ce.
To a yayin da ake daukar Manufa, bayan 'yan Dawayya 2 sun gama nasu, a ranar Alhamis din, sai daya daga cikin 'yan wasan Zariya mai suna Maimuna Hussaini wadda tana daya daga cikin masu wasa a shirin, ta kulla kawance da A'ishatu, wadda kusan tsayinsu daya ne, koda yake Maimuna za ta ba ta kimanin shekaru biyu a duniya.
A cewar Maimuna, A'ishatu ta bukace ta ta zagaya da ita don ta ga gari, daga nan kuma su wuce gidansu, domin a cewarta ba ta taba zuwa Zariya ba.
To sai ya kasance Rukayya ba ta nan a lokacin da wadannan 'yanmatan suka fita, tana wurin daukar wannan fim din a daji da misalin karfe 4 na yamma.
Jim kadan sai su Rukayya suka dawo. Ta waiwaya ba ta ga kanwarta ba, ta tambayi mutanen da ke wurin, watau ma'aikatan 'Jari Video & Film Production' (a lokacin an taso daga otal din 'Congo Conference'). Sai mutanen da ke wurin, ciki har da wakilinmu, suka ce ba su gan ta ba.
Can, da misalin karfe 7 na dare sai ga Maimuna da A'ishatu sun iso. Sai Rukayya ta fada A'ishatu da zagi, tana tambayarta ina ta tafi, ita kuma ta kada baki ta ce ai ta bi Maimuna gidansu ne. Da fadin haka ba tare da Rukayya ta tambayi Maimuna dalilin da ya sa ta dauke ta zuwa gidan ba, sai kawai ta kama Maimuna da zagi, tana cewa wai za ta koya wa kanwarta gantali.
Nan da nan jama'a suka shiga ba Rukayya hakuri, amma ta ci gaba da fadin munanan kalamai. Jin yadda Rukayya ke ci mata tuwo a kwarya, sai Maimuna ta fusata, ta cakumi wuyan rigar Rukayya. Nan da nan Rukayya ta tattakura ta share ta da mari. Ita ma Maimuna, kafin a yi wata-wata ta tsunke Rukayya da mari. Kafin ka ce kwabo wuri ya yamutse, jama'a suka shiga faman raba fadan. Sai da aka sami akalla minti 15 ana kiki-kaka. Can sai ga shugaban wurin, Alhaji Nata'ala Aliyu, tare da dan wasa kuma mawaki Galin Money sun shigo. Su suka tsawata sannan wutar ta mutu.
A nan ne Gali ya bukaci ya san musabbabin rikicin. Sai Hadiza Kabara, wadda tana daya daga cikin 'yan rabo, kuma mai goyon bayan Rukayya kamar yadda wadansu suka fahimta a wajen rabon, ta yi masa bayani daga farko har karshe. Da jin yadda abin ya faru sai Gali ya nuna wa Rukayya kuskurenta, ya nuna mata cewa bai kamata kamarta ta kama fada da sa'ar kanwarta ba. Daga nan ne fa Rukayya ta fusata ta koma waje tana ta kuka, ita ko Hadiza Kabara tana ba ta hakuri.
A nan ne sai wakilinmu ya tuntubi Hadiza dalilin da ya sa Rukayya kuka, sai ta kada da baki ta ce tana kuka ne saboda Galin Money ya goyi bayan Maimuna wai don tana 'yar garinsu. Ana cikin haka ne sai ga Gali zai wuce ta wurin. Sai wakilinmu ya kira shi da ita Hadiza da Rukayya, ya nuna wa Gali ga abin da ke faruwa. A nan sai Gali ya ce ai shi ba yana goyon bayan wani ne ba, shi ya ba Rukayya shawara ne, amma idan ta ga cewa ya yi kuskure ne, to sai ta yi hakuri.
Wannan abu da ya faru a Zariya ya sa mutane sun kara raina 'yan fim. Da yawa wadanda suka kallon 'yan fim din sun yi kallon rikicin Rukayya da Maimuna, har wasu suna zunde, suna cewa ashe haka 'yan wasan Hausa suke, ba su da hadin kai, kuma ga su suna fadin muggan kalamai a kan junansu!
Wani wanda aka yi abin a kan idonsa ya ce, "Wannan abin kunya ne. Ya kamata 'yan fim masu hali irin wannan su rika rike girmansu domin jama'a ma su rika girmama su, don kowa ya san cewa fim din Hausa kamar wa'azi ne."
Na yi miji, cewar Rukayya Dawayya
Daga ABDULKARIM AL-BASHIR
a Jalingo
ALAL hakika, Hajiya Rukayya Umar Santa ba ta dade ba matuka da shigarta harkar fim, amma kuma dai ba boyayyiya ba ce ga masu kallon fim, musamman ma a cikin 'yan watannin nan. Kai, ko da wani zai ce bai san ta ba, to tambayar shi wacece yarinyar fim din Dawayya? Wannan fim din ne ya fito da ita a duniyar finafinan Hausa, kuma a yanzu kadai ne ya san iya inda ta taka a harkar fim.
Ga kuma wanda bai taba ganinta ido da ido ba, 'Dawayya,' kamar yadda ake yi mata lakabi ko aka fi saninta a yau, kyakkyawa ce, siririya, mai matsaikacin tsawo, fara.
Saukarta Jalingo, Jihar Taraba, ke da wuya a farkon watan maris na bana sai yara suka rika bin ta suna ihu da kararin "Dawayya! Dawayya!!" Tana sanye da bakin tabarau, tana murmushi da kuma dariya, kamar yadda ta saba. Rukayya dai na cikin wadanda suka yi takakka daga Kano zuwa Jalingo domin halartar auren furoduisan Izaya, Musa Liman Jalingo, wanda aka yi a ran 8 ga Maris. Wannan abin a yaba da ta yi ya sa ta kara samun farin jini da daukaka a idon 'yan Taraba, watau ta kau da zargin da ake yi wa wasu 'yan wasa na cewa "suna da daga kai".
Wani abin mamaki kuma shi ne ita jarumar ta Dawayya tana nan daram a kan burinta na ganin cewa ta yi aure, kamar yadda ta bayyana a mujallar Fim ta 23 (cewa "Nan gaba burina na yi aure, ko ba gaskiya ba?").
E, gaskiya kika fadi, domin burin kowace 'ya mace (ta kwarai) ne ta ga cewa ta yi aure, kuma tana dakin mijinta. Amma kuma Rukayya tana da wani ra'ayi na daban, cewa, "Ni kuma a gaskiya ba na son na auri dan wasa, don ban son a ce sana'ata guda da mijina".
Kuma a cikin hirar da ta yi da wakilinmu na jihohin Taraba daAdamawa, Hajiyar ta koda gwanarta ta fuskar aure, Fati Mohammed, inda ta ce, "Superstar (Fati Mohammed) gaskiya aurenta ya karantar da darussa da kuma daga mana aji, musamman ma kamar yadda ake zaginmu da cewa mu 'yan fim karuwai ne, ko kuma mutanen banza, alhali ba haka muke ba."
Har ila yau, ta tabo matsalar "auren-shiga-ki-fito" da wasu 'yan wasa mata kan yi, da matsayin soyayyarsu da jarumin da suka fito tare a Dawayya, watau Musbahu M. Ahmad, da kuma dangantakarta da wasu 'yan wasa mata, musamman Saima Mohammed. Kada dai in kai ku da nisa, a wannan zantawar ta cikin farin ciki da fara'a, Rukayya ta bayyana cewa ta kusa yin aure nan da wasu watanni masu zuwa, kuma tauraron nata kamar yadda ta ce "ba dan wasa ba ne", kuma a cikin birnin Kano yake. Amma ta ki ta bayyana mana sunansa ko kuma unguwar da yake. Amma ga dalilinta na kin bayyana sunansa: "Ka san mu mata kishi ne da mu, kuma da kin yi wasa sai wasu 'yan yada tsegumi su kai tsuguminsu su raba ki da tauraron naki."
Hajiya Rukayya ba ta ji dadin rashin zuwan wasu shahararrun 'yan fim daurin auren Musa ba. Ta danaganta abin ga "rashin hadin kai na furodusashi da kuma sauran 'yan Industry." Ta ce, "Ni ma na yi mamaki domin ya gayyaci akasarin 'yan industry, amma abin takaici sai mu 'yan kalilan kawai muka sami damar halarta. Ka ga kenan babu hadin kan da a kullum ake ta batu a kai. Domin mutum yakan so masoyinsa na kwarai ne a wasu lokuta biyu, watau lokacin da abin farin ciki ya sami mutum shi ne ka taya shi farin ciki, haka kuma kadan wani abu na bakin ciki ko damuwa ya same shi, to nan ma ka yi masa jaje."
Ta ce tana fatan 'yan fim za su gyara halayyarsu su zama tsintsiya-madaurinki-daya.
A kan batun da ake yi cewa akwai soyayya a tsakaninta da Musbahu, Dawayya ta karyata rade-radin, ta ce, "Ni kam ban san wata soyayya a tsakanina da Musbahu ba, sai dai mutunci, kuma ma ban taba saninsa ba sai a ranar da za mu fito waka tare. Don haka, mutunci ne kawai ke tsakanina da shi, kamar yadda mutunci ke tsakanina da sauran 'yan Industry."
Ta ki ta yi dogon bayani a kan halin dangantakarta da Saima a yanzu, kawai sai ta ce, "Kamar dai yadda na riga na fadi ne, cewa ni mutunci ne ke tsakanina da kowa, kuma fatana shi ne Allah ya sa mu gama lafiya."
Da aka tabo mata batun da ake yi cewar ta kusa aure kuwa sai ta yi murmushi.
"Alhamdu lillahi, wannan maganar gaskiya ne, kuma nan ba da jimawa ba za a yi," inji ta.
Shin waye tauraron nata, kuma a ina yake?
"Nan gaba za ku ji kuma ba zan iya fada maku sunansa ba, amma a nan cikin Kanon Dabo yake tauraron nawa," inji Rukayya. Ta ce ba za ta iya fadar sunansa ba don tana kunyar sunan tasa. "Kuma ban son 'yan tsegumi su sami kafar shiga tsakaninmu. Ka san mu mata kishi ke da mu!"
Rukayya tana da ra'ayi a kan korafin da ake yi na cewa ko da 'yan fim sun yi auren ma ba su son zama, har ana yi musu kirari da shiga-ki-fito.
"Ba haka al'amarin yake ba," cewar Dawayya. "Shi dai aure nufin ne na Allah, kuma komai Allah ke yi. Zan yi kira ga 'yan'uwana mata da su yi koyi da Fati Mohammed wajen zaman aure; domin ta samu daukaka da farin jini a idon duniya, amma duk wannan bai sa ta ki zaman gidan miji ba don kwadayin wani abin duniya. Kuma lokacin da ta yi tashe ita kadai ce, mu kuma yanzu muna da yawa. To 'yanmata matasa sai mu yi hankali, mu tuna fa cewa burin kowace 'ya mace shi ne ta wayi gari tana dakin mijinta."
Da aka tambaye ta me kuma za ta iya cewa dangane da zargin da ake yi na cewa wasu matan fim sukan shiga harkar fin ne domin neman kudi ko suna ko kuma duka biyun, sai ta amsa: "A gaskiya duk sana'ar da ka ga mutum na yi, to don riba yake yi. Amma hakan ya danganta ga ta fuskar da mutum ya raja'a. Fata dai shi ne Allah ya tsare mu kuma ya yi mana jagora." To amin, Rukayya.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin