A yi adalci kafin a zarge mu - Maikano
Daga Aliyu A. Gora a Kaduna
Ba wannan ba ne karo na farko da mujallar Fim ta tattauna da Babban Sakataren Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Malam Abdullah Maikano Usman. A baya, ya sha yi mana bayani kan alkiblar kungiyar da kuma nasarorinta.
An dan jima ba a ji duriyar Maikano ba. Kwanan nan Wakilinmu ya waiwaye shi don su tattauna dangane da wasu gunaguni da 'ya'yan kungiyar suke yi cewa tunda suka zabi shugabannin har yanzu ba a ga aikin da kungiyar ta yi na a-zo-a-gani ba in ban da yawan kiran tarurruka. Wannan zargin ya sa a watannin baya kadan sai da mujallar Fim ta fito ta yi wani sharhi mai taken 'Farkar da kungiyar Arewa daga gyangyadi', inda ta bukaci shugabannin kungiyar da su tashi tsaye don yi wa membobinsu aiki tukuru. A wannan hira da suka yi da Fim, Malam Makano ya yi kokarin kare shugabannin daga wancan zargi da ake yi musu ga yadda hirar ta kasance:
Abdullahi Maikano Usman, Babban Sakataren kungiyar Furodusoshi ta Arewa
| FIM: Alhaji Abdullahi, a matsayinka na babban Sakataren wannan kungiya, me za ka ce dangane da zargin da wasu ke yi maku cewa har yanzu ba su ga aikin da kungiyar ta yi na a-zo-a-gani ba tunda aka zabe ku?
MAIKANO: To, ita harka ta kungiya, kuma musamman ta kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Arewa, wato kungiya ce, amma kuma tana cike da siyasa. Bayan wannan, kungiya ce da take ta hada jihohi wadanda suna shirya finafinan Hausa. To wani abu da mutane ba su sani ba shi ne, yawancin jihohi su ne suke aiwatar da shirye-shiryen da akan gabatar a kungiyar Arewa. Ina so kuma mutane su sani cewa kungiyar Arewa tana tunkaho ne da jihohi, su kuma jihohi su ne suka kafa Arewar. Saboda haka duk wani aiki da za mu yi, za mu yi ne domin ci-gaban harkar fim a jihohin Arewa baki daya. Maganar cewa kuma ba mu yin komai, da ma shugabanci yana tare da haka. Ba mamaki wani ba a yi mashi yadda yake so ba, ba mamaki wani an yi mashi yadda yake so. Kuma da ma babu yadda za a yi ka ce ka gamsar da kowa da kowa a harkar shugabanci na kunyiya, kai ko da ma na gidanka ne. To amma ni a matsayina na sakatare, kamar yanda nake fadi a kullu yaumin, cewa wajibi ne 'yan kungiyar ne su kansu idan suka ga wani abu ana yin shi wanda bai dace ba, ko kuma suka ga wani abu wanda ya kamata a yi amma ba a yi ba, duk wajibinsu ne su fito su yi hanya mafi dacewa, a rubuto, ana taro (Delegates' Comference) a zo a fada (ceewa) ba a yi ba. Jama'a su tattauna, a yarda a kan za a yi abin nan, mu namu aiwataarwa ne. To idan mutane suna cewa mu ba mu yi aiki ba, ni kuma sai in rika ganin su ne ba su yi aiki ba. Saboda mu ya kamata a kalubalance mu (a ce) 'Ga abin da ya kamata ku yi ba ku yi ba.'
Amma ba zan yi maka musun cewa ana samun 'yan matsaloli wani lokaci ba. Ba mamaki, domin rayuwar duniya ce. Ni ba zan taba ce maka ba mu da matsala ba. Duk dan'adam yana da matsala. Saboda haka idan mu muna da matsala, ai ba wani abu ne sabo ba. Kai din nan da kake magana kana da matsala. Ba mamaki mai karanta labarinku yana da matsala. Saboda haka, matsala wani bangare ne ma na rayuwa. Saboda haka ni yadda nake ganin shugabanci kenan. Kuma 'yan kwanakin nan mun yunkuro gaskiya fisabilillahi, mun yanke wasu hukunce-hukunce wadanda za su yi ma masu shirya finafinan amfani, da aikin harkar fim din da masu kallo da masu saidawa da ma kowa da kowa. Kuma na san kwanan nan za a ji wannan tsari da muka shirya.
FIM: Rashin bude wa kungiyar ofis ya taimaka wayen daukar da masu farodushoshi suka yi cewa kungiyar ba da gaske take yi ba. Me za ka ce?
MAIKANO: To, zan sake komawa dai kan 'yan kungiyar. Ba ina so in maida hannun agogo baya ba ne. Amma a taron da muka yi a Katsina na farko, an yi magana cewa a tara naira dubu dai daya, kowane furoduso ya ba da gudunmumar N1,000. To, ina son wanda duk yake wannan maganar ka tambaye shi shi ya ba da dubu dayar? Idan ya ba da kuma, kowa da kowa ya ba a? Kamar yadda na gaya maka, mu shugabanni dole ne mu za a zarga. Na yarda da wannan. Amma kafin a zarge mu, shi mai zargin ya dubi kanshi tukunna, shi kanshi ya yi wa kanshi gyara. Sannan sai ya zo ya zarge mu, mu a shirye muke mu karbi laifinmu. As far as Abdullahi Maikano Usman is concerned, ni a shirye nake in karbi kurakurai, kuma na sha fadar wannan magana. Na sha fadi, ni ina da makiyi daya ne a duniya, ina da kuma masoyi daya a duniya: makiyina wanda zai ga na yi kuskure ya ki gaya mani, masoyina kuma shi ne wanda idan na yi kuskure zai same ni gaba da gaba ya yi mani gyara, ko ya ba ni shawara in gyara. To har duniya ta nade zan kaunaci wannan mutum, zan kuma so shi har abada.
FIM: Mutane suna kokawa game da kunnen-uwar-shegu da kuke yi game da matsalolin da ke tasowa tsakanin masu shirin fim a wasu jihohi. Ko ba ku da hakkin sa baki? Kungiyarku ba ruwanta da matsalar jihohi?
MAIKANO: Da ruwanta. Gaskiya da ruwanta. Amma, na daya idan ana son ita kungiya a yi mata adalci, tsakani da Allah nake magana, duk abin da ya faru, sai a runkako a zo a sanar da kungiya. To ka ga ka mutunta kungiyar kenan kuma ka nuna cewa kai dan kungiyar ne. To, amma sai na fahimci cewa wasunmu suna abubuwa gaba-gadi, ko kuma sukan yi gajen hakurin zuwa wurin kungiyar ne ? Gaskiya ban sani ba. Amma abin da nake ba da shawara a yi, idan har ana son kungiya ta rika tsoma hannayenta sosai a cikin irin wadannan rigingimu, Allah ya sauwake ba fatan samuwarsu ake yi ba, shi ne duk abin da ya taso, a nufo kungiyar. To idan ka zo wurin kungiya ka ga ba abin da aka yi maka, to ka ga nan ka samu hujja. Duk abin da ka fada ya yi daidai saboda ka zo ba a yi maka komai ba, ba a ba ka hujja ba, ba a yi magana mai dadi ba. To amma sai wani abu ya faru, sai ka yi gaba-gadi, to kana so ne a zo a rika ba ka hakuri a ce dawo kungiya a zo a yi maganar?
FIM: Me ya sa har yanzu kungiyar Arewa ta ki sa baki a rikicin dokar layin fitar da finafinai da 'yan Kano suka sa?
MAIKANO: Ta sa baki a taronta na Zamfara da aka yi a Gusau watan da ya gabata. Sa bakinta da kuma ta yi shine, wato an yarda a kan cewa wannan al'amari a gaskiya kungiyar Arewa ita ya kamata ta dauki nauyin irin wannan tsari kuma sannan har ma mun yi magana a cikin wannan taro cewa idan lokacin ya yi, to har 'yan kwamitin ma za mu rika biyansu alawus duk wata, ba wai su rika zaman banza ba. Wannan kenan.
Sannan kuma na biyu, an yarda a kan cewa shi fa wannan layi da ake magana a kan shi, ba wai ana yin shi ba ne domin a musguna ma wani, ko a cuci wasu, a'a layi ana yin shi ne domin gyara. Kuma wajibi ne idan muka zauna muka ga cewa an yi wasu 'yan watanni ko dai wani lokaci ya gabata, gyaran da ake so a yi din nan bai gyaru ba, to menene amfanin layin? Kuma dai a wannan taro da aka yi duk mun yarda cewa duk wani gyara da za a kawo a harkar shirin fim, ba ma layi kadai ba, kamata ya yi ya zama na gwaji ne kurum.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|