Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Nura Imam: Dashen da Allah ke so..

Nura Imam
Nura Imam
Daga MUHAMMED NASIR

NURA Imam yaro ne matashi dan shekara 21. Fari ne, kyakkyawa, wanda wasu mutane idan sun gan shi sukan yi tunain ko dan wani mai hannu da shuni ne ya kyamaci dukiyar mahaifinsa ya shiga harkar fim. To, baban Nura dai ba wani hamshakin attajiri ba ne, amma kuma hamshaki ne a matsayin da aka san shi a Kano kafin ya rasu a cikin 1984. Jin sunan baban Nura zai tabbatar wa mutum da cewa hakar fim ta tara jinsin mutane daban-daban.

Ka ga akwai jinsin rikakkun 'yan boko irin su Abdulkareem Mohammed, da A.A. Kurawa. Idan aka koma bangaren masu hannu da shuni ko kuma 'ya'yansu, akwai irin su Ibrahim Maishinku da Mansir A. Shariff. Akwai kuma 'yan tun fil azal din harkar fim kamar su Kasimu Yero da Ibrahim Mandawari.

Duk wadannan ba za su dauki hankalin mai karatu ba kamar yadda asalin Nura Imam zai daukar masa. Nura da ne a wurin limanin birnin Kano kaf, marigayi Liman Dan'amu. Daga cikin 'ya'yan da ya mutu ya bari guda 26 masu rai a yanzu, Nura ne na 24. A unguwar Soron Dinki, cikin birnin Kano, aka haife shi. Bayan rasuwar mahaifinsa sai ya zauna a Marmara. Ya yi karatun firamare da na sakandare. A halin yanzu kuma ya sami nasarar shiga Jami'ar Bayero don yin kwas ta difiloma. "Ina kammalawa kuma in Allah ya yarda digiri zan zarce," inji shi.

Nura ba "dan Malam" ba ne wanda akan ce wai "ya ki halin Malam." Ya yi karatun Alkur'ani mai tsarki da na littatafai da yawa. Tun yana karami ana yi masa kallon masani duk da karancin shekarunsa.

Ga shi dan Liman kuma dan fim. Cewa ya yi don ya ga harkar fim fadakarwa ce shi ya sa shi ma yake yi. "Kuma ba za ta tauye min karatun da na sa himma zan yi ba," inji shi. Kan batun shigarsa shirin finafinai kuwa, ya ce shi 'yan'uwansa wayayyu ne, sun fahimci al'amurran duniya, shi ya sa ba su hana shi ba. "Kawai na san dai lokacin da suka fara ganin fim dina a shekarar 2000, sai suka zaunar da ni suka tambaye ni idan akwai wasu illoli. Bayan na yi masu bayani gamsasshe, sai suka yi min addu'a."

Kamar yadda aka san yawancin 'yan wasa a karkashin wani kamfani, shi ma Nura hakan ya yi a farkon shigarsa harkar fim. Ya zauna a kamfanin shirya finafinai na Sarauniya, amma daga bisani sai ya kwatar wa kansa 'yanci, ya zabi ya ci gashin kansa. Sai ya hada kai da wani wanda ya kira a matsayin amininsa, Aminu M. Ahmad, suka bude wani ofishi na kashin kansu mai suna 'Amnur Moving Image,' inda tuni har sun shirya wani fim mai suna Maqasudi.

Da aka tambaye shi dalilin kafa kamfani nasu na kansu, sai fitaccen jarumin ya ce, "Muna da buri don mu ga cewa mun ci gaba, ba don jayayya da kowa ba. Kuma ai ko don mu ga cewa wasu sun karu da mu kamar yadda mukan karu da wasu." To yanzu ba shi karkashin kowa kenan? Nura amsawa ya yi da cewa, "Ba fada muka yi da kowa ba ko wani cacar-baki, sai don ci gaba kawai. Duk wanda ke karkashin wani ba zai yi tunanin ci gaba ba."

Dan wasan ya ce bai taba yin da-na-sani ba kuma ba a taba wulakanta shi ba don yana fim. "Ka san ni ba na son takura kuma ba na so a takura min." Shi ya sa, inji shi ya ce, "Ina da wata kima wadda na samar wa kaina."

Duk da cewa samari matasa sai kara cika suke suna tumbatsa a cikin rijiyar finafinai, Nura cewa ya yi shi bai yin nukura da kowa. "Ko da matasa dari za su kara shigowa yau, ba zan tada hankalina ba. Duk abin da Allah ya sa ni ne zan yi, to babu wanda ya isa ya hana."

Ya samu abubuwan alheri a dalilin fim, kuma ta dalilin fim ya je garuruwa masu nisa ciki har da Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar. Amma cewa ya yi babban alherin da ya yi takama da shi shi ne yabon da yake samu daga mutane. "Kusan don mutane nake yi; kuma ni ba a taba samun wani ya zo ya ce min tafi mu ba ka burge mu ba."

Kafin mu rufe hira da shi Nura ya bai wa 'yan fim 'yan'uwansa shawara: "Ina ba da shawara ga kowane dan fim: Bai kamata wata harka ta bakin ciki ta shiga tsakani ba. Duk wanda ya ja da wata baiwa da Allah ya yi wa wani mutum, to kamar ya ja da Allah ne. Saboda haka a fahimta, sa ido a lamarin Allah shi ya fi sauki. Idan mutum ya ga zai iya, to bismilla." To Nura, Allah ya sa wadanda aka yi shawarar dominsu su ji kuma su yi aiki da ita.

Wasu daga cikin finafinan da Nura ya fito cikinsu su ne: Zarge, Garwashi, Sirace, Mushaqqa, Ta'asa, Maqasudi, Illa, Mujadala, Da Walakin, da sauransu.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin