Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 32   Agusta 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
MU LEKA HOLLYWOOD
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Finafinan Hausa suna dagula al'adunmu

Inji Malaman Jami'a

Dr. Haruna
Dr. Haruna Abdullahi Birniwa, Shugaban Sashen Harsunan Nijeriya na Jami'ar Danfodiyo, yana nasa bayanin a taron

Daga BASHIR ABUSABE a Sokoto

WANI kasaitaccen taro da aka yi a Jami'ar Usmanu Danfodiyo a Sakkwato ya yanke shawara, bayan kwana biyu ana tattaunawa, cewa an samu karin gurbacewar al'adun Hausa sakamakon finafinai da litattafan soyayya na Hausa da ake yayinsu a yanzu. Kuma mahalarta taron sun cimma kudirin cewa akwai wasa da addinin Musulunci wajen gabatar da wasu finafinai da litattafan zamani, sa'annan akwai yawaitar tasirin bakin al'adu, musamman na Indiyawa da Turawa, sakamakon finafinan da litattattafan.

Wadannan manyan soke-soke kadan ne daga cikin ragargarzar da malaman jami'ar da malaman addini da sauran jama'ar gari suka yi wa harkar fim da rubuce-rubuce a taron wanda Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Danfodiyo din ta shirya.

A ranakun Litinin da Talata, 8 da 9 na Yuli, 2002 aka gudanar da taron na kara wa juna sani. Taken taron dai shi ne: "Nazarin Finafinan Hausa da Littattafan Zamani Daga 1980-2002: Ci-gaba ko Ci-Baya?"

Shi dai wannan taro ana ganin shi ne na farko da wata cibiyar bincike ta shirya domin tara masana a kan harshen Hausa don tattaunawa a kan finafinan Hausa da littattafan zamani. Ya samu halartar masana da manazarta a kan al'amuran yau da kullum, da 'yan fim. Daga cikin 'yan fim sanannu, Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alh. Ibrahim Mohammed Mandawari, kadai ne ya samu halarta daga Kano, shi ma gab da kammala taron, amma daga Kaduna an samu halartar mutane hudu, su ne Sani Idris Kauru (Moda), Yusuf Barau, Yahuza A. Ilu, da Lawal Amadu (Ka-ci-mari). Ta bangaren masana kuwa, taron ya tara masana harshen Hausa da dama, musamman daga jami'ar ta Sakkwato, da kuma jama'a daga sassa daban-daban. Sun hada da Mataimakin Shugaban Jami'r Danfodiyo, Furofesa Aminu Salisu Mika'ilu, da Dr. Ibrahim Malumfashi, Dr. A.M. Bunza, Dr. Salisu Yakasai, Dr. D. Argungu, Furofesa Ibrahim Mukoshy, Furofesa J.M. Kaura, Lauya Matazu, Dr. Haruna Birniwa, A.A. Dunfawa, Malam S.S. Ibrahim, Malam Isah Talatar Mafara, Malama Balbasatu Ibrahim, Dr. Ahmed Bako … kai, bari dai mu yi maku ta babban mahaukaci, duk wani malami, masani, mai son fayyace ra'ayinsa game da fim ko littattafan zamani daga wasu manyan makarantu da ke zagayen nan, ya bayyana a wurin; haka su ma uwayen kasa ba a bar su a baya ba, domin Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Dr. Muhammadu Maccido Abubakar III shi ne uban taro kuma Alhaji Abubakar Tunan Mafara, Kayayen Sardauna, ya zo a matsayin babban bako. Shi kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, shi ne babban bako na musamman.

Da yake jawabi a wurin bude taron, Gwamna Bafarawa, wanda ya samu wakilcin kwamishinan yada labarai na jihar, ya jaddada cewa, "Babu shakka finafinan Hausa da littattafan zamani hanyoyi ne na ilimintarwa da kuma nishadantarwa, kuma suna matukar taimakawa wajen inganta harshen Hausa da kuma bunkasa al'adun Hausawa." Saboda haka ne ma ya nuna farin cikinsa da godiya ga Cibiyar Nazarin Harshen Hausa ta Jami'ar Danfodiyo da ta shirya wannan taro. Ya ce, "Don haka ne ma wannan taro na kara wa juna ilimi ya dace daidai wannan lokaci da matanmu da 'ya'yanmu suka karkata ga wannan fanni na adabi. Ta haka ne za a yi nazari da kuma tantance abubuwan da ke gurbata addini da al'ada." Garkuwan na Sakkwato ya yi kira ga marubuta da masu shirya finafinai su lura da irin babban kalubalen da yake fuskantarsu domin su gyara kurakuran da aka samu a baya.

Shi ma da yake jawabi, Furofesa Aminu Salihu Mika'ilu ya nuna farin ciki da wannan taro kuma ya sha alwashin cewa da yardar Allah kafin karshen wannan zangon karatun za a maida cibiyar a mazaunin jami'ar na dindindin ( permanent site) domin ta samu kusanci da intanet don samun saukin yin bincike-bincike. Sannan kuma ya ce jami'ar za ta buga dukkan kasidun da aka gabatar a wurin taron.

Da take nata bayanin, mukaddashiyar daraktar cibiyar, Hajiya Sa'adiya Omar, ta yi dogon jawabi a game da finafinan Hausa da littattafan zamani. Ta ce, "Me zan kira finafinan Hausa da littattafan zamani a yanzu? Gama-gari ko hantsi-leka-gidan-kowa? Lallai rubutun littattafa da wasannin Hausa yana daya daga fannin adabin Hausa amma dangane da rubutu da gabatar da finafinan Hausa da littattafan zamani mun ga wani sabon tafiya da akwai habakar wannan rubutu kamar ruwan marka wanda bai tsagaitawa, kuma ko da ya tsagaita wanda ya fi shi ne zai biyo baya. Marubucin littafi ko waka ko shirya wasa shi ne idon al'umma, ya watso tunaninsa, ya ilimantar da al'ummarsa, ya fadakar da jama'arsa amma ta tsarin da ya dace da al'ummar tasa da kuma karbabben tsarin rubutu." Hajiya Sa'adiya ta ci gaba da cewa, "A matsayinmu na masu nazarin adabi, aikinmu ne mu nakalci kayan cikin wadannan aikace-aikace na finafinai da littattafai, mu fito da jigo, wato sakon marubuci, mu tantance salon sarrafa harshe, mu kula da zubi da tsarin marubuci, mu dubi 'yan wasa, mu fitar da al'adun da ke kunshe a aikinsu. Idan ka bai wa mai nazarin adabi littafi, ko wasa ko waka, to kamar ka bai wa mahauci dabba ne ka ce ya yanke ya fede ya fitar da komai dalla-dalla." Daraktar ta ce da yardar Allah haka taron zai fitar da komai dalla-dalla dangane da finafinan Hausa da littattafan zamani.

Hajiya Sa'adiya ta zayyana irin kasidun da za a gabatar a wurin taron domin tattaunawa, kamar haka:

1. "Adabi da Bidiyon Kasuwar Kano a Bisa Faifai: Takaitaccen Nazari", daga Dr. Ibrahim Malumfashi.

2. "Gamin-Gambiza: Nazari a kan Al'adun da ke Kunshe a Cikin Finafinan Hausa da Littatatafan Zamani", daga Dr. A.M. Bunza.

3. "Rubutu da Gabatar da Finafinan Hausa a Matsayin Sana'a: Amfani da Matsaloli", daga Tahir Fagge.

4. "Jigo a Cikin Finafinan Hausa da Littatafan Zamani: Ina Aka Dosa?" daga A.A. Dunfawa.

5. "Tasirin Finafainan Hausa da Littatattafan Zamani Ga Raguwar Mata da Matasa da Magidanta", daga Malama Balbasatu Ibrahim.

6. "Salon Sarrafa Harshe a Cikin Finafinan Hausa da Littattafan Zamani", daga Dr. D.M. Argungu.

7. "Wakokin da ke Cikin Finafinan Hausa da Littattafan Zamani: Gyara ko Barna?" daga Dr. S.A. Yakasai.

8. "Yawaitar Finafinan Hausa da Littattafan Zamani: Kalubale Ga Al'ummar Musulumi", daga Malam Isa Talatar Mafara."

Bayan nan, Hajiya Sa'adiya Omar, a matsayinta na masaniya kan harshen Hausa, ta yi kira ga ma'aikatan kafofin watsa labarai, musamman na gida, da su kyautata amfani da harshen Hausa wajen gudanar da shirye -shiryensu. "Babu sha'awa a ce kafofin watsa labarai na waje irin su BBC da Muryar Amurka da Muryar Jamus da sauransu sun fi kafofin gida kwarewa da yi wa harshen Hausa kwalliya. Misali, wajen fassara labarai akwai wanda ya fassara Bar Association 'Kungiyar Mashaya' maimakon 'Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya da kuma Ethical Revolution aka fassara zuwa 'Juyin Da'a' maimakon 'kyautata tarbiyya,'" inji ta.

Tun da tarko, sai da Hajiya Sa'adiya ta fara gutsuro aikin Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo inda ta ce, "An bude cibiyar a 1983 a matsayin cibiyar bincike a kan duk fannoni da suka shafi harshen Hausa da yanayin kasar Hausa da al'ummar Hausawa da tarihinsu da kimiyyarsu da kere-kerensu da tsarin iliminsu da maganganunsu da sauransu. Cibiyar nazarin Hausa tana bincike a kan al'adu da adabin Hausa na baka da rubutacce. Ayyukan da Cibiyar Nazarin Hausa ta yi tun kafa ta zuwa yanzu sun hada da shirya taron duniya, wato tsakanin kasa da kasa, guda biyar a kan fassara kalmomin fasaha da kimiyya daga Turanci da Farasanci zuwa Hausa wanda aka yi a nan Jami'ar Usmanu Danfodiyo a 1988, da kuma 1998."

Bayan jawabin ne aka ba da fage ga masu gabatar da kasidu a kan su zo su gabatar da kasidunsu kafin a fara tattaunawa a kan kasidun. An ko fara ne da kasidar Dr. Ibrahim A.M. Malumfashi na Sashen Harsunan Nijeriya na jami'ar zai gabatar wadda ita ce ke kan taken taron. An san Malumfashi, wanda shi ne mawallafin mujallar Garkuwa, a matsayin rikakken dan adawa da littattafan soyayya da kuma finafinan Hausa. Don haka wadanda suka san shi sun gyara zama domin jin abin da zai amaryar a ranar. Malamin ya fara da kawo tarihin lokacin da adabin Hausa na zamani ya fara yin tasiri ga yara da matasa da kuma yadda aka yi "Adabin Kasuwar Kano" ya samu asali da kuma yadda marubuta suka fara yin rubuce-rubucensu inda har yake cewa, "Wasu daga cikin marubutan abin da ya faru gare su ne suke ayyanawa a rubuce. Mu dauki misalin Ado Gidan Dabino. Littafin In Da So Da Kauna, wanda ya rubuta a 1990, bakin cikin abin da ya same shi game da Sumayya ya sa ya amayar da duk abin da ya faru tsakaninsu."

A ci gaba da gabatar da kasidarsa malamin ya ci gaba da nuna yadda aka yi ta yin rubuce- rubuce ya juye, da yadda ya koma na bidiyo, inda ya fara da lokacin da aka fara bude gidajen rediyo a Nijeriya da kuma daga bisani gidan talabijin ya kunno kai har zuwa lokacin da aka fara yin wasannin dirama don wayar da kan jama'a, zuwa lokacin da aka yi ta kafa kungiyoyin wasannin kwaikwayo mafi yawanci daga Kano. Dokta Malumfashi ya yi nuni da cewa mafi yawancin masu sukar fianfinan Hausa ko littattafan "Adabin Kasuwar Kano" sun fito ne daga jami'o'i, ya ce wasu 'yan jarida ne, wasu malaman addini, wasu iyaye da masu fada a ji a cikin al'umma. Kuma ya yi nuni da cewa mafi yawancin labaran da ke cikin littattafan aro su aka yi kai tsaye daga Indiyanci, Ingilishi da Larabci. "Dubi littafin Sara Da Sassaka na Bala Anas Babinlata, fim din Indiya ne na Dostana, haka In So Ya Yi So na Badamasi Burji, Iglik De Khaliya ne daga Indiya; shi kuwa littafin Farar Tumfafiya na Zuwaira Machika, Kabhie Khabie ne, da wasu da dama," inji shi. Ya ci gaba da cewa, "Sai dai da alama soke-soken da bace-bacen da aka yi ta yi game da littattafan sun sa an dan canza salo, su kuwa finafinan yanzu suke cin kasuwarsu, don haka ba su san ana yi ba, kuma da alama za su dade suna jan zarensu zuwa wani lokaci su kuma su ba da fili ga wani abu sabo. Ba komi ya sa aka fadi haka ba sai ganin cewa adabin kasuwa abu ne da ke zuwa ya wuce, ba tabbatacce ba ne, saboda da ma can ba orijina ba ne, gwanjo ne. Tuni kasuwar littattafan ta yi sanyi, tana sonsamin mutuwa. Ita ma ta finafinan, lokaci ne kurum ake jira. Shi ya sa idan na ga ana ta hakilo wajen suka ba tare da an yi wani abu ba, daga gwamnati na dabaibaye harkar ko tsugunar da ita, sai na ce ana dai shirin kashe maciji ne, amma ba a sare kansa ba, sai dai kuma ai ba kullum ake kwana gado ba. Nan gaba kadan sai labari, za a ga kamar ba a yi finafinan ba. To sai dai kamar yanda muka sha nunawa, abin nan ne da Hausawa ke cewa kan ka ga biri, ya riga ya yi barna."

A karshen makalar, malamin ya yi nuni da cewa, suka da baci basu hana "adabin kasuwar Kano" ci-gaba da wanzuwa. Sai dai ya yi kira ga gwaimnati da ta kara sa ido ga hukumar da ta kafa ta tace finanfinan domin, a cewarsa, ba abin da hukumar take tacewa sai kudi. Ya ce, "Yadda gwamnati ta tashi tsaye ta kafa hukumar NAFDAC don duba ingantuwar magunguma da makamantansu, an yi hakan ne don magance aukuwar annoba," saboda haka gwamnati ta tashi tsaye ta lura da harkar finafinan yadda ya kamata.

Bayan Dr. Malumfashi ya gama gabatar da kasidarsa ne, kuma an sallami manyan baki, sai aka kasu rukuni-rukuniomin tattaunawa a kan kasidun da daktocin da malaman addini suka gabatar. Kafin nan sai da aka fara zafafa tumbi da ruwan shayi da kayan ciye-ciye da tande-tande, kai ka ce gidan biki ake. Shi ya sa da wuya ka ga wani ya bata rai yayin da ake yin wannan tattaunawar. An tattauna na tsawon awa biyu sannan aka tashi aka yi hutu da salla. An dawo wajen karfe 4 aka ci gaba da tattaunawa har zuwa karfe 6, sa'annan aka rufe taron na wannan rana da burin in Allah ya kai mu washegari za a ci gaba da tattaunawa kuma a tashi.

Washegarin an ci gaba da tattaunawa a rukuni-rukuni din kamar yadda aka tsara. Bisa ga lurar da jama'a suka yi, sun fahimci cewa rukuni guda biyu su suka fi tada jijiyar wuya, wato daga rukunin Dr. Malumfashi sai rukunin su Tahir Fagge wanda an lura cewa sun fi tara masana a cikin rukunin nasu. An ci gaba da tattaunawa har zuwa karfe 12 na rana sannan aka bude fili ga masu tambayoyi ko wani karin bayani dangane da finafinan Hausa har zuwa karfe 2:00. Kafin nan sai da aka ba kowane rukuni fili da ya zo ya gabatar da abin da suka binciko a cikin tattaunawar da suka yi sannan aka tafi hutu da yin salla, kuma 'yan kwamitin da aka dora wa alhakin duba sakamakon bayan taron su je su duba kuma a san abin da za a yi.

Shi ma din dai an dawo da karfe 4 na yamma. Aka ci gaba da yin tambayoyi da neman karin bayani kafin kwamiti ya kawo rahotonsa. An cikin wadanda suka fito suka ba da gundunmawa har da tsohon dan wasan nan Danwanzam wanda ya yi kira ga masu yin finafinan Hausa da su gyara irin batancin da ke faruwa a cikin finafinansu, kuma ya yi kira da a kiyayi yin amfani da sunan gaskiya a cikin fim, don ya ce a wani lokaci can baya cikin wani wasa da suka gudanar inda aka nuna shi bakon haure ba dan kasa ba, da aka yi amfani da sunansa na asali abin ya shafe shi tsakaninsa da iyalinsa. Shi ma da yake jawabi 'Boka' Muhammad Khalil na cikin wasan su Danwanzam ya ce, "Gwamnati ita ta kashe dirama a nan Sakkwato. Ana cewa za a gyara amma har yau ba wani gyara da aka yi."

Sani Idris Kauru (Moda ) ya ce, "Ana ce wa'yan fim 'yan iska ne, suna bata tarbiyyar yara, an mance da mata na cikin gida wadanda ke zagin 'ya'yansu, ka ji sun ce 'shege ya yi kaza' ko kuma 'dan banza'. A nan in akwai mala'ika, da ya ce 'amin' shikenan yaro ya zama dan banza. Ka ga ba masu fim suka bata shi ba."

Haka dai aka yi ta ce-ce ku-ce; masana, daktoci, malaman Musulunci, dalibai, mata da sauran mutane 'yan kallo suna ta tofa albarkacin baki har zuwa lokacin da kwaniti ya kawo rahotonsa. Bayan an fadi jawabin bayan taro ne aka kuma rarraba takardun shaida ga wadanda suka gabatar da kasidu da wadanda suka tattauna su. Sannan daga karshe aka rufe taro da addu'a aka watse.

Jawabin bayan taro

1. Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, ta shirya taron kara wa juna ilimi na kwana biyu daga ran 8 zuwa ran 9 ga Yuli, 2002, a kan "Sabon Salon Tafiyar Adabin Hausa - Nazari a kan Finafainan Hausa da Littattafan Zamani (1980-2002)" a dakin taro, mazaunin cikin gari na Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

2. A wannan muhimmin taro an samu halartar masana ilimin harshen Hausa da masu rubuta littattafai da gabatar da finafini da malaman addinin Musulunci wadanda suka zo daga jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Kaduna da Kano da Katsina. A wannan taron an gabatar da takardu guda takwas, kuma an tattauna a kansu.

Bayan tattaunawar taron ya lura da abubuwa kamar haka:

(i) An samu gurbacewar al'ada sakamakon wadannan finafinai da littattafai.

(ii) Akwai wasa da addinin Musulunci wajen gabatar da wasu finafinai da littattafan zamani.

(iii) Akwai yawaitar tasirin bakin al'adu, musamman na Indiyawa da Turawa.

(iv) Akwai rashin kulawa ta hukuma da iyaye game da tabarbarewar tarbiyya, wanda finafinai da littattafai suka haifar.

(v) Akwai yawaitar tasirin finafinai da littatafan wajen daukar hankali, musamman ga mata da matasa.

(vi) Akwai rashin kula da maida hankalin dalibai wajen karatu.

(vii) An yaba wa Cibiyar Nazari Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, kasancewarta farko da ta shirya irin wannan taro na kara wa juna ilimi.

DANGANE DA WADANNAN MATSALOLI WADANDA AKA LURA DA SU TARO YA YARDA DA WADANNAN SHAWARWARI, YA YI KIRA KAMAR HAKA:

1. Inganta samar da finafinai da littatafai wadanda suka dace da addinin Musulunci da al'adunmu.

2. A yi kokarin tace da tsabtace harshe da al'adun da ke cikin finafinai da littatafai.

3. Marubuta da masu gabatar da finafinai su yi la'akari da bukatun al'umma ta hanyar gabatar da abubuwan da suka shafi rayuwa daban-daban maimakon karkata ga jigon soyayya kadai.

4. A kashe raye-raye da wake-wake da ba su dace da addini da al'adu ba.

5. Masu shirya finafinai su yi la'akari da ka'idojin da Musulunci ya amince da su a matsayin jagora gare su.

6. Wadanda suka dauki rubutu da shirya finafinai a matsayin sana'a kada su fifita son kudi da abin duniya fiye da addini da al'ada. Su san cewa Allah zai tambaye su game da wanan sana'a tasu.

7. Taro ya yi kira ga mata da matasa wadanda kallon finafinai da karatun littattafan ya zama lalura a gare su da su kiyaye abubuwan da suka fi zama muhimmi da alheri a gare su.

8. Taro ya yi kira ga hukuma da iyaye da malaman addini Musulunci da su yi aikinsu na kyautata da inganta tarbiyyar al'umma.

9. Taro ya yi kira ga Cibiyar Nazarin Hausa da ta ci gaba da shirya wannan muhimmin taro lokaci lokaci.

10. Taro ya gode ma Allah (SWT) da ya ba da ikon da aka yi wannan taro cikin nasara aka kuma gama shi lafiya.

Mun cimma kudirinmu a wannan taron
Cewar Malama Sa'adiyya Omar

HAJIYA Sa'adiya Omar ita ce Mukaddashiyar Darakta ta Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto. Ita ce ta jagoranci shirya wannan babban taron kara wa juna sani da aka yi. Jim kadan bayan an kammala taron, mujallar Fim tuntube ta don jin dalilin shirya taron da kuma wasu tambayoyi a kan wannan namijin kokari da ta yi. Ga yadda hirar, wadda suka yi da wakilinmu BASHIR ABUSABE, ta kasance:

Hajiya Sa'adiyya
Hajiya Sa'adiyya Omar, MUkaddashiyar Darakta ta Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usman Danfodiyo, Sakkwato

FIM: Hajiya, muna taya ki farin ciki kan kammala wannan taron lafiya.

SA'ADIYA: Alhamdu lillahi, na gode kwarai da gaske.

FIM: Za mu so mu ji dalilin shirya wannan taron.

SA'ADIYA: Da farko dai, da ma manufar wannan taro da yake Cibiyar Nazarin Hausa tana nazarce-nazarce a kan adabi da sauran bangarorin da suka shafi Hausawa, irin su tarihinsu da kimiyarsu da kere-kerensu da tsarin iliminsu da magungunansu da sauransu, sai muka ga akwai wani abu sabo da adabi ya samu daga 1980-2002, kuma muka ga ya dan bambanta da adabin da aka sani da, shi ne harkar finafinan Hausa da littattafan zamani, sai muka ga aikinmu ne da mu tsaya mu bincike shi mu gani. Kuma abin da muka kara lura da shi, shi ne irin yadda masana, iyayen yara da sauransu suka yi caa a kan wannan harka suna suka ba tare da wani sashi ya nemi ya duba wannan fage don samar da mafita. Sai mu muka fara, muka tara masana Hausa, 'yan wasa, malaman addini, domin hada kai baki daya domin a ga ci-gaban da aka samu da ci-baya, a kuma yi mashi aunin sikeli, mu ga kuma me aka samu.

Kamar yadda na ce a jawabina, shi mai nazarin adabi kamar mahauci yake: ya yanka, ya fede, ya gyara 'yan ciki da sauransu, har zuwa sayarwa, to kusan haka mai nazarin adabin Hausa yake. Hakkinmu ne mu ga mun tace wannan sabon yanayi na adabi mu cire gurbataccen da ke cikinshi kuma mu yaba inda ya wajaba da kuma yin gyare-gyare a kan abin da ya shafi shi wannan adabin.

FIM: Wace nasara za ki ce an samu daga wannan taron?

A gaskiya ni da na shirya taron ba ni ya kamata in fadi nasarsa ba. Amma tunda an tambayan bari in fadi. Akwai nasarori da dama da aka cimmawa, daga cikinsu akwai: malaman da muka gayyato domin gabatar da kasida duk sun gabatar kuma na ilimi, abubuwan da suke faruwa da kuma kallon finafinan kafin a rubuta a kan maudu'i. Kai kanka ka halarci taron ka ga irin maudu'an da aka gabatar; an dubi jigo, al'adu har muka kira su gamin-gambiza, an kawo nazarin harshen da ke cikin finafinan Hausa da littattafan zamani domin akwai abubuwan gyara a ciki misali harshen batsa, shakiyanci, harshen da ba namu ba. Saboda haka dukkan maudu'an an yi bincike a kai, kuma wadanda suka gabatar malamai ne masana harshen Hausa da kuma masu gabatar da finafinan. Bayan nan, duk wadanda muka gayyata a matsayin masu tattauna makalolin kusan duk sun halarta, da masu rubuta wasannin da littattafai, kai, har da masu mujallu irinku.

Kuma wannan wani fage ne na samun fahimtar juna tsakanin 'yan wasa, masana, matasa da sauran jama'a. An kuma samu yarjeniya na yadda za a yi nan gaba. Su kansu masu gabatar da finafinan sun amince kuma sun gane kurakuransu kuma za su gyara. Irin fahimtar da aka samu ya jawo kiraye-kiraye da a ci gaba da yin irin wannan taron a kai a kai ko a fadada shi.

FIM: To, Hajiya, bayan wannan taro, wace matsaya aka cimmawa?

SA'ADIYA: Matsayar da aka cimmawa an yaba ma wannan taro, kusan kowa ya same shi, an yi matsayar cewa kowa zai yi nashi aikin, kowane bangare an ce ya yi gyara, ko dabbakar da abin da aka zartas, kuma Cibiya ta ci gaba da himma ta rinka shirya irin wannan taron. An yi kira ga gwamnati na cewa ta kula da abubuwan da ke faruwa, ta ba 'yan wasa kwarin gwiwar da suke bukata, kuma su tabbata hukumar da suka kafa (censors) na cikinta yadda ya kamata, in kuma an saba duk dai gwamnati ta dauki mataki. An yi kira ga malamai da iyaye da su ci gaba da aikinsu na wayar wa jama'a har da masu yin finafinai da littattafan zamani kai.

FIM: Mun san ba za ku rasa 'yan matsalolin da kuka fuskanta ba, ko dai kafin wannan taro ko bayansa. Me za ki ce game da wannan?

SA'ADIYA: To, matsalolin da muka samu kusan na yau da kullum ne, sai dai ta kudi ita ce kan gaba. Cibiya na bukatar kudi da yawa domin samun damar ci gaba da bincike-bincike, kuma bincike ba haka nan ake yin shi a zaune ba, sai an yi tafiye-tafiye, tattara ayyuka da ajiye su. Tana kuma shirya taruka na kara wa juna sani irin wannan da aka yi da sauran abubuwa da dama wadanda dole sai da kudi za a samu saukin aiwatar da wadannan ayyukan. A kasafin da ake ware ma jami'o'i na bincike a gaskiya ba a ba su abin da ya kamata. Ba wai ina nufin jami'ar Danfodiyo kadai ba, a'a, duk sashen bincike na jami'o'i ba a cika ba su kula wadda ta dace ba.

FIM:Daga karshe, wane irin mataki ko hanyoyi za ku bi don ganin cewa sakamakon taron nan ya kai ma wadanda aka yi dominsu?

SA'ADIYA: Da ma ai za mu yada shi ga jama'a don su san irin aikin da sakamakon da muka samu. Ba mu son yin aiki kai tsaye, za mu yi zama na musamman a kan sakamakon da irin kiraye-kirayen da ake mana na mu ci gaba da shirya irin wannan taron. Za mu yi nazarin shawarwarin mu gani. Kuma Cibiyar Nazarin Hausa tana karkashin Jami'ar Usmanu Danfodiyo ne, tilas sai ta kai sakamakon ga jami'a domin ta yarje mata ta ci gaba da wasu ayyukan irin wannan domin harshen Hausa ya ci gaba, kuma jama'a su amfana da aikinmu. Kamar shawarwarin da aka ba mu za mu yi kokari mu rika bibiyar gwamnati da takardun da aka gabatar da shawarwarin da aka gabatar domin ta aiwatar da su. Su kuma malaman Musulunci za mu isar masu da nasu da iyayen yara da aka ja hankalinsu da su kula da tarbiyyar 'ya'yansu a kan finafinan da suke kallo, duka ta hanyoyin yada labarai za su ji wannan sako. Kamar yadda aka yi shawara an bukaci Cibiya ta ci gaba da irin wannan taro, in Allah ya taimake mu za mu ci gaba da irin wannan kokari.

An yi magana a ilimintar da masu yin littattafai don su san ka'idojin rubutu don sanin cewa abin da suke rubutawa bai saba ma al'ummarsu da al'adarsu ba. An kuma yi kira gare mu da mu shirya gasa ta rubutu tsabtatacce, karbabbe. Game da wannan kwasa-kwasai ba zan iya cewa komai ba sai na tuntubi V.C. Sannan mu san abin yi, amma Cibiya na da alhinin yin haka.

'Yan fim sun yi na'am da taron

'YAN fim da suka halarci taron na Jami'ar Usmanu Danfodiyo sun bayyana wa mujallar Fim cewa su kam taron ya yi masu daidai kuma Allah-maimaita-mana. Ga bayanansu:

YUSUF BARAU:

FIM: Me za ka ce wa mujallar Fim game da wannan taron?

YUSUF: Kalubale gare ta na irin wannan kwasa-kwasai da aka yi. Ya kamata ta buga shi da murya mai karfi ga 'yan fim. Kamar yadda 'yan Nigerian films (wato 'yan Kudu) kan dauki wata uku ba su yi fim ba, ya kamata mu ma a Arewa a rinka yin haka don samun damar tsabtace abin. Kuma muna godiya ga Cibiyar Nazarin Hausa da ta shirya wannan gagarumin taro na daya irinsa a arewacin Nijeriya. Mujalar Fim ta yi kokari ta kyautata abubuwan da aka tattauna a wannan taro ta hanyar fadakar da jama'a.

FIM: Kana ganin taron nan ya cimma nasara kuwa?

YUSUF: An yi nasara kwarai da gaske. Idan har ana ci gaba da shirya irin wannan taron, duk wani dan fim zai gane irin kurakuran da yake yi, kuma zai gyara. Za mu yi takama da wannan taron domin 'yan Kudu tuni suke shirya irin wannan taron a wurinsu. Daga karshe abin da aka manta da shi shi ne mafi yawancin masu rubuta littattafai matan aure ne, na cikin gida. Su da ba su samu damar zuwa ba, hakkin mujallar Fim ne ta yayata har su ji. Kuma ta hanyar mujallar Fim ne mai daraja su matan za su san irin shawara da aka zartar. Ina ma mujallar Fim fatan alheri, Allah kara ma masu ba ta rahotanni kuzari, ya kuma ba ta ikon ci gaba.

FIM: Wane kira za ka yi ma wadanda suka shirya wannan taro?

YUSUF: Allah ya saka masu da alheri. Yadda suka shirya wannan taro,Allah ya ba su ikon shirya wanda yai wannan. Ina kira ga gwamnatin Sakkwato da ta ba wannan Cibiya dukkan goyon bayan da take bukata. Na yi bakin ciki ganin 'yan kasuwar finafinai ba su samu zuwa ba.

SANI IDRIS MODA:

FIM: Shin taron nan ya burge ka?

MODA: Muna godiya ga Allah da ya ba mu damar zuwa taron da Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta shirya. Hakika Cibiyar ta taka rawar gani wadda duk cibiyoyin da ke jami'o'i daga lokacin Jahiliyya zuwa yanzu ba su taka ba. Babu shakka taron ya burge ni, abin a yaba ne. An kira mu don mu warware zargin da ake mana na 'yan iska da ake kiranmu. Alhamdu lillahi muna godiya da wannan abu da Cibiya ta yi.

Fim: Yaya ka ga tasirin taron?

MODA: Tasirin wannan taron ya nuna mana matsalolinmu 'yan wasa, furodusoshi, daraktoci, 'yan kallo, gwamnati, kai da duk wani wanda yake kallo ko rashin kallon fim. An gano matsalolin an kalle su da idon basira kuma mutane sun amince. Kuma ba 'yan wasan kwaikwayo ne kadai ke da matsaloli ba. Duk dan wasan da ya yi abu mai kyau shi zai ga mai kyau. Saboda haka a kiyaye. Mu 'yan wasa ba mu kadai ne matsalar al'umma ba, amma mu ne mu ke da damar mu isar da sako ga al'umma. Wallahi wannan taro ya dace.

Fim: Kana ganin kuna iya yin amfani da shawarwarin da aka zartas?

MODA: Insha Allah za mu yi kokari. In fa muka yi mai kyau mu za mu ga mai kyau, kuma wadanda ba mutanenmu ba (ba 'yan Arewa ba) idan suka ga marar kyau daga gare mu shikenan sai su kara sukarmu yadda suka ga dama. Kuma mu ake ganin fuskarmu a fim, ba a ganin furodusa ko darakta. Saboda haka in ba mu yi marar kyau ba mu za a zaga. Saboda haka ya kamata mu tsare. Idan aka kawo maka wasa ka tsaya ka dubi jigonshi har karshe, idan ka gamsu da shi sai ka yi. Gyara a gare mu yake. Na tabbata idan furodusa ya kawo maka wasa ka ga bai cancanta ya zama wasa ba ka ki yi, gobe ba zai kawo maka ba. Ina kira ga masu kallon finafinai da su kara fahimtar abin da mutum ya yi a cikin fim ba halinshi ba ne. Yawancimmu muna da dan iliminmu; akwai masu satifiket, difloma,digiri da sauransu. Kuma dan wasa bai son a zage shi, yana da son tsare martabarsa.

YAHUZA ILU

Yahuza A. Ilu shi ne shugaban Kungiyan 'Yan Wasan Kwaikwayo ta jihar Kaduna.

FIM: Yaya ka ga taro ya gudana?

YAHUZA: Sai godiya ga Allah Ta'ala. Cibiyar Nazarin Hausa ta gama wa kowane dan fim abin alheri, domin sai mutum ya damu da kai zai yi ma abin alheri. Hakika mun ji dadi da wannan taro domin shi ne na farko da aka taba yi domin duba irin matsalolin da ke addabar finafinan Hausa da littattafai. Abin da aka yi yanayi ne na gyara. Kuma sabon salo na yadda za a gyara harkar fim. Hajiya Sa'adiya Omar, daraktar Cibiyar, gaskiya ta yi abin da ba wanda ya taba yin irinshi, muna yi mata fatanalheri. Ina kira ga 'yan fim da duk wanda bai samu damar halarta ba to ya nemi wanda ya je domin ya ba shi labarin abin da ya faru, saboda an tattauna abubuwa da dama da suka shafi finafinan Hausa. Ina kira ga mujallar Fim ta yi kokari ta yayata abin da aka tattauna a wurin domin isarwa ga jama'a. Abin bakin ciki, ban ji dadin yadda ba a samu wadanda suka zo wurin taron da yawa ba. Daga Kaduna mu hudu ne muka zo. Ban ji dadi ba da Mandawari bai tsinci abin da aka yi a wurin taron ba sai daga karshe ya zo. Ina kira ga 'yan wasa da su rinka kintsa kansu domin kunya da kawaici shi aka sani ga dan Arewa. Idan muka yi haka za mu ci nasara in Allah ya yarda. Kuma 'yan fim su rinka neman shawara ga masana da ilimi a kan abin da suke yi. Hukumar Tace Finafinai ta bar barin ana sakin fim kara-zube, a dinga kiyayewa. Idan ana barin irin wannan shi zai kara ta'azzara abubuwa. Ta yi hobbasa game da wannan. Ka ga kamar wani fim da 'yan Kudu suka yi mai suna Stubborn Grasshopper, ba komai cikinsa sai batanci da aka yi mana mu 'yan Arewa, domin fim din Abacha ne aka yi ma kaca-kaca a ciki. Mu din nan mu muka yi tsaye don ganin an dauki mataki a kai.

FIM: Wane irin kira za ka yi?

YAHUZA: A madadin 'yan wasan Kaduna muna godiya ga wannan Cibiya, musammman a kan abin da ta yi mana. Godiya ta musamman ga Daraktan Hukumar Fasaha da Al'adu ta Jihar Kaduna, Dr. Halliru Ahmed Amfani, domin shi ne wanda ya yi tsaye ya ga mun halarci wannan taron saboda zuwanmu din nan ya taimaka kwarai da gaske.

FIM: A matsayinka na shugaban 'yan wasa na Kaduna, wane mataki za ka dauka don ganin kowane dan wasa na Kaduna ya san abin da aka zartas a Sakkwato?

YAHUZA: Zan yi kokari mu yi amfani da abin da aka zartas. In na koma zan tara 'yan wasanmu gaba daya in fayyace masu abin da ya faru kaf. Wannan kalubalena ne, zan yi kokari in bi duk hanyar da ta dace in sanar masu in dai sun ba ni hadin kai.

Baje kolin finafinan Hausa zai fitar da zarata

LALLAI birnin Kano yana shirin kwasar dimbin jama'a a cikin watan Disamba lokacin bikin Karamar Salla. Shagalin biki ne wanda wata kungiyar finafinan Hausa mai suna 'Hausa Film Academy' ta shirya. 'Hausa Film Academy' tana shirya wannan biki ne tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyin finafinai daban-daban, dilalan kaset da masu gidajen sinima da masu mujallu.Ana sa ran bikin, mai suna 'Hausa Film Festival,' zai dauki hankalin jama'a musamman ganin cewa za a yi laccoci, bikin baje kolin finafinan Hausa, da kuma bayar da kyaututtuka ga zaratan finafinai da 'yan wasa da suka yi fice.

Wajen neman shiga gasar kuwa, akwai fom wanda za a fara sayarwa a cikin watan Agusta 2002 har zuwa karshensa. An kebe wurare daban-daban a garuruwa inda furodusa zai iya zuwa ya sayi fom ya cika don neman cin gasa. Ga wuraren da za a iya zuwa a sayi foam.

KANO

1. Ofishin Hukumar Tace Finafinai.

2. Kamfanin hada hotunan bidiyo na 'Kwality Audio-visual'.

3. Kamfanin 'Fasaha Films'

4. Kamfanin hada hotunan bidiyo na CBC da ke Dandago Sabon Titi.

5. Ofishin mujallar Fim.

6. Wuraren sayar da kaset da suka hada da Bata da Malam Kato Square.

ZARI A

Wurin Balarabe Sauri-sauri .

KADUNA

Koli Trading Company.

JOS

Lenscope Media

KATSINA

Ofishin Hukumar Yada Al'adu da Tarihi ta jiha.

SOKOTO

I.U.I.

Akwai kuma fom wanda masu sha'awar baje kolin hajarsu za su iya saye domin samun damar damawa da su.

BANGARORIN DA ZA A NEMI CIN GASA A KAI SUN HADA DA:

1. Best film

2. Best director

3. Best screem play

4. Best soundstrack

5. Best cameraman

6. Best editor

7. Best special effect

8. Best supporting actress

9. Best suporting actor

10. Best actress

11. Best actor

12. Best comedian

13. Best lighting

14. Best story

15. Best moral and cultural upright/sharia film

16. Best child actor

17. Best father role

18. Best mother role

19. Best new actor

20. Best new actress

21. Best lyrics

22. Best music

23. Best playback singers (male and female)

* Finafinan da aka shirya cikin 2002 ake bukata.

* _5,000 kacal ne kudin fom. Za a rufe sayarwa a kashen watan Agusta.

Sa hannun

Kwamitin Gudanarwa

Al'adunmu za mu tallata wa duniya da kalankuwar finafinan Hausa

Dr. Umar Faruk Jibril

Dokta Umar Faruk Jibril kwararre ne a harkar shirya fim. Malami ne a sashen koyon aikin jarida, rediyo da talbijin na Jami'ar Bayero, Kano (Mass Communications), kuma yana daga cikin daraktroci na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano. Shi ne kuma babban sakatare na sabuwar kungiya mai suna 'Hausa Film Academy'. Ya tattauna da Editan Fim, Ashafa Murnai Barkiya, a kan manufar shirya bikin baje kolin da ba da kyaututtuka da ake cikin shiryawa yanzu:

FIM: 'Yallabai, me ake ciki dangane da wannan gagarumin biki da kuke kokarin shiryawa?

DR. UMAR FARUK JIBRIL: Assalamu alaikum. Wannan gagarumin taro da muke kokarin shiryawa a yanzu, taro ne wanda ba a taba yin irinsa ba kan harkar finafinan Hausa. Taro ne wanda ya hada kowane irin mutum wanda harkokinsa sun ta'allaka a kan harkar fim. Kuma ya hada dukkanin kasashen Hausa, saboda bai tsaya a Nijeriya kawai ba; musamman arewacin Nijeriaya, arewacin Ghana, yammacin Kamaru, kudancin Chadi da wurare kamar su Burkina Faso da irin su Mali da Nijar. Wadannan wurare duk akwai Hausawa kuma wannan harka ta finafinai na Hausa ta kai wadannan wurare, ya Allah ta hanyar kallo ko shiryarwa.

FIM: Me za a yi a wurin bikin yadda jama'a za su fara shiri tun yanzu don su san irin zanen da za su daura su je bikin?

DR. JIBRIL: Wato wannan wani taro ne da muke kokarin yinsa wanda abubuwan da ya kunsa suna da dama. Na farko akwai laccoci, taro na kara wa juna ilimi tsakanin masu yin finafinai da harkar shiryawa don 'yan wasa, masu shirya kaset daga manya manyan malamai masu so su tofa albarkacin bakinsu game da yadda harkar nan ta shigo mana da kuma yadda ya kamata a yi ta, mutanen da suna da sha'awar kawo gyara a wannan harka ko kuma masu sha'awar su zo su tsunduma a yi da su. Akwai kuma bangare na biyu wanda shi ne bangare na cinikayya wanda za mu bude kasuwar baje koli na finafinai wadanda aka yi su da can a baya da kuma wadanda ake kan ganiyar yin su a yanzu.

Za mu yi kokarin mu ga cewa an samar da wadannan finafinai wuri guda, a dandali guda, inda kowa zai iya zuwa ya gan su an baje su a farashi mai rahusa. Sa'annan akwai tsari na bayar da kyaututtuka ga wadanda suka yi fice a wannan harka ta finafinan Hausa.

Akwai kuma tsari na kyaututtuka da za a bai wa wasu manya-manyan mutane iyayenmu da kakanninmu wadanda suka taimaka ta bangaren bunkasa wannan harka. Sa'annan akwai tsari da za a yi wanda shi kuma yana da alaka da kyautata wannan sana'a ta finafinan Hausa ta hanyar masu yin finafinan Hausa da masu zuba kudinsu a fim inda za a ba su wani horo na koyarwa kan finafinai.

FIM: Ga alama wannan abu da ji ba karamin kudi za a kashe ba. Ko gwamnatin Jihar Kano ta tallafa maku da wani dan ihisani?

DR. JIBRIL: E to, da dai ban so in yi maganar a nan ba saboda wasu abubuwa. Amma zan so in tabbatar maka da cewa mu babu irin abin da za mu ce wa gwamnatin Dokta Rabi'u Musa Kwankwaso a yanzu saboda goyon baya na farko da aka ba mu shi ne da gwamanti ta ce a dawo a tsara harkar fim a bisa wani tafarki wanda a da ba a taba yin irin wannan tsari ba.

Gwamnatin Dokta Rabi'u Musa Kwankwaso ita ce ta fito da wata ma'aikata ta kula da kyautata wannan harka ta finafinai wanda alhamdu lillahi wannan hukuma ta taimaka kwarai, kuma da hadin gwiwarta ne za a yi wannan taro. Kuma mun aika masa sako na musamman cewa za mu yi wannan taro muna neman tubarrakinsa. Kuma da ikon Allah ya yarda, ya albarkaci abin kuma ya ba mu goyon baya har daga cikin aljihunsa. Wannan tallafi na kudi da ta ba mu, daga baya za mu shaida wa jama'a shi.

Amma mu ba tallafin ba ne ya fi burge mu, a'a sha'awa ta gwamnati; don mun yi taro da kwamishinan yada labarai da daraktocinsa. Mun dade muna shirya wannan abu, kusan shekara guda kenan. Muna so ne bikin ya daukaka sunan Jihar Kano da arewacin Nijeriya da ma kasar baki daya, domin duniya ce za ta hadu a lokacin bikin.

Babu abin da za mu ce sai Allah ya kara jan ragamar wannan mulki. Allah kuma ya kara ja mana gaba a kan wannan harka.

FIM: Jama'a za su so sanin shin a ina ne za a yi kuma wane lokaci ne za a yi bikin?

DR. JIBRIL: A yanzu a tsarin da muka yi muna hangen cewa tunda taro ne na biki, muna so ya zo a lokacin da Hausawa Musulmai suke bukukuwa nasu na karshen shekara. Mun dauka cewa lokacin da za a yi bikin Karamar Sallah ne za mu yi wannan babban biki saboda ya dace da al'adunmu.

Kuma a nan ne za mu san cewa mutane masu so su kawo gyara a wannan harka za su sami dama su zo hutun Sallah. A satin da ake shagulgulan Sallah ne za a yi shi. Biki ne da zai dauki kwanaki biyar. Mun tanadi wurare daban-daban. Akwai wuraren da muka kebe don taron ba da kyaututtuka, da inda za a yi baje koli na finafinai, sa'annan akwai wurare da muka tanada na musamman don karrama hamshakan iyayen wannan sabga wadanda suka taimaka sosai saboda duniya za ta san irin gudunmuwar da suka bayar.

FIM: Wane tanaji aka yi don tsaron lafiya?

DR. JIBRIL: Harkar finafinai a kasar Hausa abu ne sabo da muka shige shi. Abin takaici shi ne wasu na yi wa harkar wani kallo na kazanta.

To tanajinmu dai shi ne da bakin da za mu gayyato, da 'yan fim da 'yan kasuwa da kuma har masu zuwa don kallo, za a kare lafiyarsu. Tsari za mu bi irin na shari'a irin ta addinin Musulunci yadda mata da maza ba za su gwamutsa ba.

Na biyu akwai tsari na tsaro da aka shirya da jami'an tsaro da masu tsaro na sa kai. Akwai kuma tsari na neman bayanai na yadda za a kyautata tsaron wurin. Abu ne wanda duniya za a tara. Abin da muke so mu fada wa jama'a da dan kallo da wanda zai zo a yi kalle shi, rayukansu da dukiyoyinsu duk za a yi kokarin kare su. Insha Allahu babu abin da zai salwanta.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin