|
Ba kowa zan yi wa fim ba
Inji Sadiya Rano
SADIYA Abdu Rano bakuwa ce ga masu kallon fim, to amma ba bakuwa ba ce a wurin 'yan fim. A matsayinta na jami'ar kasuwancin mujallar Fim, a Kano za a iya cewa kusan dukkan 'yan fim da dillalan kaset na bidiyo sun san ta, ita ma ta san su. Kuma ba sani shanu ba. Shi ya sa tun da aka ji dan kyas cewa ta fito a cikin fim din da mujallar ta shirya a Kaduna mai suna Gagarabadau, sai furodusoshi manya da kanana suka fara yi mata dirar mikiya suna bukatar ta fito cikin finafinansu.
A ranar 20 ga watan jiya ne Gagarabadau ya fito kasuwa, kuma rahotanni sun nuna cewa ya samu karbuwa. Akwai wadanda suka kalli fim din domin yayata shi da aka yi musamman a mujallu, wasu kuma suna so su ga "abin da 'yan taratsin nan 'yan mujallar Fim suka yi," sa'annan wasu don kurum su sha dariyar da aka ce akwai a cikin fim din. Kamar yadda Sadiya ke cewa a wata waka cikin fim din, "Ga shi mun fito da sabo na yayi," haka din ne, domin kuwa ba a taba shirya fim a cikin mota, kuma labarinsa tun daga farko har karshe ya faru a cikin rana daya ba, sai Gagarabadau.
Wannan fim din dai shi ne na farko da Sadiya ta taba fitowa a fim. Bayansa kuma ta sake fitowa a wani shirin na mujallar Fim mai suna Daren Farko, tare da Ahmed S. Nuhu, Aisha B. Umar da kuma Hamisu Iyan-Tama.
Ita dai Sadiya, haifaffiyar garin Rano ce cikin Jihar Kano. Ta zo duniya a ran 7 ga Oktoba, 1978. Ta yi karatu a 'Findi Islamiyya Primary School'. Daga 1990 zuwa 1996 ta yi karatu a makarantar sakandaren 'yanmata ta Danzabuwa, sa'annan ta yi karatu a 'Aminu Kano School of Islamic Studies' inda ta samu difloma a fannin nazarin harshe. Yanzu kuma tana karatu a Jami'ar Bayero, Kano.
Can a watannin baya, bayan an gama daukar Gagarabadau, Sadiya ta tattauna da wakilinmu a kan tunaninta game da shirin fim. To amma mun aje hirar har sai mutane sun kalli fim din sun ga abin da ta yi. Kuma bayan an gama daukar Daren Farko, wakilinmu ya kara tattaunawa da ita. Saboda haka dai sai biyu ana tattaunawa da ita kenan.
A tattaunawarsu ta farko Sadiya ta yi magana kan Gagarabadau, dadi, wahala da kuma dalilan da suka sa ta fito a fim. Shin daga yanzu za ta tsunduma ruwa ko kuwa wankan-wuta ta yi wanda 'yan magana ke cewa "sau daya kan yafa?" Ku biyo mu:
Sadiya Abdu Rano
|
FIM: Me ya ba ki sha'awa kika shiga fim? SADIYA: To abin da ya ba ni sha'awa shi ne don na ga ina ra'ayin yin wasan ne, wasu idan suna yi suna burge ni. Shi ya sa na ce bari in fito a dan goga da ni.
Kamar su wa ke burge ki?
SADIYA: Ka ga dai kamar Ibrahim Mandawari, Hajara Dumbaru, Hamisu Iyan-Tama, Ahmed S. Nuhu, Saratu Gidado, Hindatu Bashir da Hajara Usman.
To ga shi an fara gogawa da ke daga Gagarabadau. Me za ki ce kan abin da kika yi a ciki?
SADIYA: Ni abin da ya ba ni sha'awa shi ne inda ake dora min macijin nan. Na kuma sha wahala inda muka rika hawa wani falalen dutse muna gangarowa. Sai da muka hau muka gangaro har sau it.
Kin yi da-na-sani tunda ba ki saba da irin wannan wahala da 'yan fim ke sha ba?
SADIYA: A'a, ban yi da-na-sani ba.
Ya kika ji da aka yarba maki sharbeben maciji na gaske a jiki?
SADIYA: Nauyi na ji a jikina, kuma na ji jikina na dan yin rawa. Kuma sai na dake na ce wai menene? Acting ne fa. Ba wani abin tsoro. Sai na natsu na nuna bajintata.
Kafin a dora maki macijin an cire masa dafi ne ko kuma an ba ki wani ruwan magani kin sha kin yi wanka?
SADIYA: Ba abin da aka ba ni kuma ban ga an cire masa wani abu ba.
To amma gumi ya karyo maki, ko?
SADIYA: A' a wallahi.
Shikenan ke yanzu kasuwa ta bude kenan sai finafinai ko?
SADIYA: Ni ba kowa zan yi wa fim ba. Alkawarin da na yi sai na kamfanin mujallar Fim kadai zan yi, saboda wasu 'yan dalilai.
Wadanne dalilai?
SADIYA: Ka ga dai makaranta nake yi (Diploma in Information Management, a B.U.K), ba na son abin da zai takura wa karatuna. Kuma ba hana ni iyayena suka yi ba. Sai dai kawai ba za su so su ga ina dinga fitowa a kowane fim ba. Ban da wadannan kuma ina da wanda zan aura, to ba zai so ya ga ina yawan fita a finafinai ba. Kuma gaskiya akwai halayen wasu 'yan matan fim wadanda ke ja wa saura zagi, a rika zargin sauran gaba daya. Ni gudun irin wannan zargi yana daya daga cikin dalilan da suka sa ba zan fada cikin shirin fim sosai ba.
Kina jin Gagarabadau zai karbu?
SADIYA: Na tabbatar zai karbu sosai, don har yanzu duk inda na je raba mujallar wurin dillalan kaset, sai sun tambayi Gagarabadau.
An fara neman ki fito cikin wadansu finafinai?
SADIYA: Kwarai kuwa, sai dai kawai in yi dariya. Akwai wasu ma tun kafin su gan ni har sun yi casting dina. To ni kuma lokacin ina jarabawa sai kawai na ce masu ba zan iya samun dama ba.
Amma ba ki saki jiki a wurin shirin fim din ba.
SADIYA: E, na zama ta-ware-ga-dangi don ba saba ba. Ranar da za mu fara har cewa nake zan iya kuwa?
Shi wanda zai aure ki da ya ji za ki yi fim ya dan nuna maki damuwarsa?
SADIYA: Da na fada masa da ya dauka wasa ne, sai da ana gobe zan tafi. Daga nan ya gane da gaske ne, na yi masa bayani ya gamsu, ya yi min addu'ar Allah ya bada sa'a.
A wurin daukar Gagarabadau su wanene suka debe maki kewar rashin sabo?
SADIYA: Suna da yawa. Kamar su Saratu Gidado, na ji dadi da ya kasance tare da ita muke. Ta ba ni wasu shawarwari. Sai na ji duk na saba da kowa a wurin . Ga Aliyu Gora II, Mary wadda ita ce jami'ar kasuwancin mujallar Fim a Kaduna, Lamte da sauran basawan da suka kama ni suka kai wa Gagarabadau aka tilasta min in yi masa waka.
HIRA TA BIYU (Yuli 2002)
Fim: Yanzu ga shi bayan Gabarabadau kin kara yi wa mujallar Fim Daren Farko. To wane bambanci kika fuskanta tsakanin Gagarabadau da shi Daren Farko?
SADIYA: A gaskiya sabanin da na samu dangane da wadannan finafinan guda biyu ba wani bambanci ne mai yawa ba, illa wajen acting ne kawai. Abin da ya sa kuwa shi dai Gagarabadau gaskiya akwai 'yar wahala tunda kwana da kwanaki aka yi ana ta tafiya a mota kuma a jeji, sannan ga gudu ga faduwa, kuma basawa za su shko mu ni da Baban Mulika.
Gaskiyar Gagarrabadau akwai wahala don su kansu na cikin mota sai da suka yi korafi cewa wahalar wasa ta koma ta gaske. Amma ka ga Daren Farko shi ba a sha wahala ba ta yawace-yawace kamar yadda aka yi kwana da kwanaki ana yawo a wancan fim din na na farko. Shi Daren Farko a cikin gari aka yi shi. Ka ga wannan ai ya fi dan sauki.
A takaice dai kin fi shan wahala a Gagarabadau.
SADIYA: Lallai ni dai na fi shan wahala a Gagarabadau.
Yanzu kin goge kenan ko har yanzu da sauranki?
SADIYA: Haba, fim biyu kadai na yi fa kenan! Ka ga kuwa ai da saurana.
Amma ai daga farawarki ba za ki rasa koyon wasu darussa ba.
SADIYA: Darussan da na koya kawai shi ne na yadda zan san yadda zan zauna da kowane dan wasa saboda wasu 'yan dalilai.
Yanzu akwai wani fim a gabanki?
SADIYA: A yanzu dai gaskiya ba ni da wani fim a gabana. Ba wai ko don babu ba, a'a sai dai don kawai da ma na riga na gaya maka cewa ina makaranta ba na son in yi committing kaina (cusa kai) saboda kar ya shafi karatuna.
Ka san ita wannan harka (ta fim) tana so a tsaya a maida hankali in dai da gaske mutum fim din zai yi. Sai dai kuma muna da wani fim a kasa na wata yayata saboda tana sha'awar harkar fim. Ba mamaki ni da ita za mu taka role din 'yanmatan cikin fim din. Kuma insha Allahu ni ma ina da sha'awar yin nawa na kaina.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|