Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Ra'ayi Ba Gaba Bane
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Laila Dogonyaro

Dalilin shigarta harkar fim

Daga ALIYU ABDULLAHI GORA II, a Kaduna

Hajiya Laila
Garkuwar Garki, Hajiya Laila Dogonyaro

SUNAN Hajiya Laila Dogonyaro ba bako ba ne ga jama'ar kasar nan. Ta yi fice a siyasar Nijeriya tun zamanin Jamhuriya ta Farko, musamman a kan gwagwarmayar nema wa mata hakkinsu a kasar da maza ne suka mamaye komai. Hajiya Laila tana a sahun gaba a kan wannan aiki, ya-Allah karkashin mulkin soja ne ko na farar hula. Bugu da kari, kusan in ban da 'ya'yan sarkin Daura, babu macen da aka nada sarauta a kasar Hausa a wannan zamani, sai fa ita. Ita ce Garkuwar Garki.

Kwanan nan Hajiya Laila ta kunno kai cikin harkar shirya fim na Hausa. Domin kuwa ita ce jagorar shirya wani fim mai suna Hannun Dama, wanda aka shirya a karkashin 'Mandawari Enterprises,' Kano. Fitaccen dan wasan nan Ibrahim Mohammed Mandawari ne daraktan fim din.

Shi wannan fim wani mataki ne a cikin doguwar tafiyar nema wa mata matsuguni wanda Garkuwar Garki ke yi. Fim din ya ta'allaka ne kan nuna tasirin mata a siyasar kasa. An dauki fim din a Kano da Abuja, sa'annan an sa kusan kowace fitacciyar 'yar wasa da kE kano cikinsa. Wata majiya ta gaya mana cewa wai an ba Mandawari milyoyin naira domin ya shirya fim din. A cewar Hajiya Laila, Gwamnan Jihar Jigawa, Alh. Ibrahim Saminu Turaki, shi ne ya biya kudin shirya fim din tare da wani na Turanci wanda Inyamirai da Yarabawa suke shiryawa a Legas.

Shin me sa Hajiya Laila ta shigo harkar shirya fim? Wane buri take son ta cimmawa? Kuma menene ra'ayinta a kan ita kanta harkar fim da kuma su kansu masu shirya finafinan? Na ziyarci Garkuwar Garki a gidanta da ke 'Dikko Road', Kaduna, inda suka tattauna kamar haka:

FIM: Shi wannan fim, naki ne, ko wata kungiya ce ta dauki nauyin shirya shi?

LAILA: Wannan fim ba nawa ba ne, na kungiya ne; na wani kwamiti ne wanda ake kira kwamitin kasa na agaza wa mata wadanda za su tsaya a harkar siyasa. Su kuma wadanda aka kafa kwamitin su su ne kungiyoyin 'yan kasuwa da kuma 'yan siyasa mata. Kuma kwamitin aikinsa shi ne ya duba irin hanyoyin da zai bi a taimaka wa matan da suke son su tsaya zabe domin su ma matan kasar nan su ba da tasu gudunmuwar wajen tafiyar da harkokin mulki a kasar nan.

Su wanene jagororin shirin fim din?

LAILA: Jagororin su ne akmai Hajiya A'ishatu, mai girma Ministar Harkokin Mata, wanda kuma ya daukin nauyin shirin shi ne Alhaji Ibrahim Saminu Turaki, Gwamnan Jihar Jigawa, sai kuma ni Hajiya Laila Dogonyaro a matsayin Co-ordinator, sai Ibrahim Mandawari wanda shi ne daraktan fim din.

Za ku saki fim din ne a kasuwa bayan kamkamala shi kamar sauran finafinai ko kaddamar da shi za ku yi?

LAILA: E, to shi wannan fim idan aka gama shi, abin da za mu fara yi na farko shi ne za mu nuna shi a gidajen sinima na kowace jiha da ke fadin kasar nan. Bayan nan, za mu kaddamr da shi a Abuja, za mu kaddamar da sai a shiyyoyi, sannan kum mu yi kaddamarwa a jihohi.

Zuwa yaushe kike sa ran fim din zai fito?

LAILA: Wajen 24 ga watan Satumba fim din zai shiga hannunmu. To sai bayan ya shiga hannunmu kwamiti zai kuma fara shirya-shiryen yadda za a kaddamar da shi.

Da yawa ana ganin rashin kashe wa fim kudi masu yawa don a samu abin da ake bukata yana jawo wa fim rashin kasuwa. Kamar nawa kike ganin fim din naku zai ci kafin a kammala shi?

LAILA: To wannan wani abu ne wanda yake sirri ne namu. Ba za mu iya cewa ga shi mun kashe kaza ba. Kuma abin da muka sani shi ne wannan fim, labarin da ke cikin an rubuta shi ne a kan ainihin abin da ya faru da kuma wanda ke faruwa na irin gwagwarmayar da mata ke yi a siyasa.

Wane mataki za ku dauka don ganin cewa an san da shi a kowane lungu na kasar nan?

LAILA: A gaskiya abin da muke tunanin yi ko kuma muke shirin yi shi ne, na farko dai za mu yi tallarsa a cikin finafinan Hausa da ake yi. Kuma a lokacin da za mu kaddamar da shi a kowace jiha, za mu yi amfani da gidan talbijin da rediyo na wannan jiha mu yi tallarsa. Kuma misali ka ga hirar nan ma da muke yi da kai, ita ma talla ce. Saboda haka muna nan muna daukar matakai na yadda za mu tallata fim din.

Kun ba da kwangilar yin fim din ne ga wani kamfani ko mutum, ko ku kuke yin abinku da kanku?

LAILA: Kamfani ne. Kuma a shirin da muka yi na yarjejeniya duk matakin da ake ciki game da daukar shirin, muna sane, wato da saninmu, da kuma yardarmu.

Ku kuka zabi 'yan wasan da kuke so su fito a fim din ko Mandawari ne ya zabe su da kansa?

LAILA: E to, mun zauna tare mun tattauna. Kuma kamar mu a fahimtarmu na 'yan kallo, da kuma yawanci kun san dai mata ne da yara masu kallon finafinai, da irin maganganun da muke ji, da kuma irin fahimtar da mata da kuma yaran suka yi wa wadannan 'yan wasa, wannan ya taimaka mana har muka zauna muka zabi 'yan wasan da muke so.

Ban da wannan fim din, akwai wani kuma da za ku shirya nan gaba?

LAILA: E to, ya danganta da irin yadda kwamiti ya ga ya kamata a ci gaba da irin wadanan ayyuka. Kamar yanzu ka ga ka san idan aka ce "matan Nijeriya," ba matan Arewa ne kurum ba. To amma sai muka ga cewa Arewa kusan rabin Nijeriya ne, saboda haka masu kallo da masu fahimtar Hausa da suke wurin, sun fi yawa. To amma kamar Yarabawa da Inyamurai sai muka ce to za a yi na Turanci. Na Turancin nan ka ga ya shafi Arewa da Yarabawa da Inyamurai din gaba daya. Shi ma wannan mun riga mun yi tunanin wadanda za su yi shi.

Me ya sa ba dauki wani sashe na fim din a Kaduna ba, sai dai Kano da Abuja?

LAILA: Idan ka lura, ga tamu fahimtar, idan ka je garin Arewa daya, ka gama zuwa ko'ina, yanayin ba bambaci. Saboda haka mu kuma muna ganin kai a matsayinka na dan jaridar finafinai ka san yadda yake da tsada a dauki 'yan wasa daga wannan wuri a kai su wannan wuri. Kuma abin da ya sa har Abuja ta shigo ciki, saboda Majalisar Tarayya, saboda kamar yadda ka sani kwamiti din nan ya roki arziki ne. Kuma ina alfaharin in ce Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Ibrahim Saminu Turaki, shi ne wanda ya taimaka ma wannan kwamiti da na Turancin. Wannan ya nuna mana irin sha'awar da yake da ita, da kuma kishin da yake da shi na taimaka wa matan Nijeriya domin su ma su ba da tasu gudummuwa a bangaren siyasa da kuma gwamnati. Kuma zan yi amfani da wannan dama in gode mashi kwarai da gaske. Ina gode mashi a madadin matan Nijeriya. Kuma muna fata Ubangiji Allah ya saka mashi da alheri.

Me ya sa kuka yanke hukuncin wayar wa jama'a da kawunansu ta hanyar shirya fim, maimakon amfani da gidajen talbijin ko rediyo kamar yadda kuka saba yi a da?

LAILA: Idan ka lura, idan kana kallon talbijin na kasa a wajen makonni shida da suka wuce da gidan Rediyon Tarayya, a kowace jiha kake, za ka ji ana maganar "mata su tashi tsaye" su yi rijista da jam'iyyun da suke so, wanda hakan zai ba su dama idan jam'iyya ta tsaida dan takara, musamman su samu ta-cewa. Haka nan kuma muna ce masu su je su tabbatar da cewa sun yi rijistar kuri'a, domin ranar zabe ya zamana sun fito sun zabi mata wadanda suka tabbatar za su iya kare masu mutuncinsu da hakkinsu.

Shi wannan fim, kun shirya shi ne don kungiya ta samu kudin shiga idan an sayar da shi ko kuwa dai akwai wata manufa?

LAILA: Abu biyu muka yi niyyar mu yi da shi. Na farko dai mu wayar wa jama'a da kawunansu. Na biyu kuma kudin da za a tara, za a taimaka wa matan da suka tsaya takarar mukaman kasar nan. Amma ba kudin za mu dauka mu ba su ba, a'a bukatansu da suke da su na yakin neman zabe, kamar su fostas, stickers, da baje, da sauransu. Za mu kuma biya masu kudi a tallata su a gidajen rediyo da talbijin. Kuma shi wannan fim, duk kudin da aka samu idan aka nuna shi a sinama ta wata jiha, to wannan jihar ita za a kashe ma wadannan kudin.

Shi labarin fim din, ku kuka rubuta shi da kanku, ko wani ne ya rubuto kuka ga ya yi daidai da ra'ayinku kuka saya?

LAILA: Mata ne suka taru kowacce ta kawo fahimtarta, "Ni na ga kaza da kaza," aka shirya labari. Shi kuma furodusan ya zo ya kawo nashi aka hada. Labarin dan taron dangi ne. Ganin irinku masu hannu da shuni kun shigo cikin harkar shirya fim, wane kira za ki yi ga takwarorinki manyan mutane don jawo hankalinsu da su rika tallafa wa masu karamin karfi a harkar shirin fim?

LAILA: Ina ganin shirya fim wata hanya ce da za a iya taimakawa a yi maganin matsaloli da yawa da ake fama da su. Sai dai mu irin finafinan da ake yi wurin wadanda ake yawan fada ko a nuna yadda yaro zai koyi sata, ba irin su muke so ba. Muna son fim wanda zai wayar ma jama'a kai ta hanyar siyasa ko zamantakewa. To a irin wannan masu hali za su iya taimakawa.

Amma abin takaicin shi ne, yawanci sai ka kalli fim amma ka rasa kansa ka rasa ginginsa, ka rasa ma inda fim din ya dosa. Saboda haka ina kira ga furodusoshi da kuma masu rubuta labari cewa don Allah su rika shirya fim a kan labari mai ma'ana, wanda jama'a za su amfana da shi.

Za ku iya taimaka wa furodusa ko da rancen kudi ne in ya nema?

LAILA: E, to, ka san yanzu ina yi maka magana ne a matsayina na 'yar kwamitin taimaka wa mata a kan harkar siyasa. Wannan kwamiti kuma ba kudi gare shi ba. Wannan kwamiti shi kanshi zuwa yake yi da kokon bara… kamar yadda na gaya maka a baya cewa finafinan ma da za mu yi guda biyu, wani ne ya taimaka mana. To saboda haka ga masu sha'awa idan sun ga cewa za su iya, ai ba laifi a taimaka wa mutane. Idan mutum ya san yana da hali kuma ya ga abin da aka rubuta zai taimaki jama'a ai ina ganin in ya taimaka ma kansa ya taimaka. Domin ladar da zai samu ba ta da iyaka.

Me za ki ce game da shirin fim na Hausa da ya zama gama-gari a arewacin kasar nan? Wace shawara kuma za ki ba su masu shirya finafinan?

LAILA: A nan ina ganin wani abu ne mai kyau da ya same mu. Ya taimaka mana ta hanyoyi da dama. Na farko dai, da mukan zauna ne mu kalli na wasu jinsi wadanda ba mu ma fahimtar abin da suke cewa, sai dai kawai mu mu kaga a cikin kwakwalwarmu mu ce ai wannan ake nufi, ai kaza aka yi, kuma muke ta kashe kudinmu a kanshi ana fita da su waje. Saboda haka ka ga wannan bai taimake mu ba ko kadan. Amma yanzu, wannan namu da ake yi a nan, mutannenmu sun samu aikin yi, kuma ko nawa za ka kashe wajen sayen fim, a nan kudin za su zauna, ba fita za a yi da su ba. Ka ga wannan abu ne mai alheri. Sannan kuma shawarata ga su masu shirya fim din ita ce: kamar yadda na fada a baya, cewa su taimaka su rika shirya finafinai masu ma'ana, wadanda za su amfane mu da 'ya'yanmu. Kuma ina fata cewa dukkanmu gaba daya idan muka samu dan lokacin shakatawa, da masu ilimin da masu sarauta ya kamata a ce muna kallon irin wadannan finafinai don su taimaka maka ka san wasu abubuwa da ke faruwa, mu ga kuma yadda yaranmu suke ba da gudummuwa ta wannan hanyar. A karshe zan yi kira ga 'yan wasan, musamman mata, da cewa su rike mutuncisu. Wallahi kar ka ji irin farin cikin da nake yi na ganin wadannan yara da suke wasan fim suna samun mazajen aure. Abin farin ciki ne kwarai da gaske. Kuma ina fatan wadanda suke fili yanzu, za su ci gaba da rike mutuncinsu har Allah ya kawo masu mazan da za su aura su ma. Kuma duk abin da zai kawo batanci ga sana'arsu, su guje shi. Sannan kuma su rage kishi da hassada a tsakaninsu.

To ranki ya dade mun gode, Allah ya ba da sa'a.

LAILA: Amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin