Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Yanzu dai ta tabbata:

Misbahu ne zai auri Rukayya Dawayya

Daga IRO MAMMAN a Kano

Rukayya da Misbahu
Rukayya da Misbahu suna wasa a shirin DAWAYYA 1 inda ake jin soyayyarsu ta fara kulluwa

GARBA Supa ne yake cewa abu kamar wasa, karamar magana ta zama babba. Batun soyayyar shahararrun jarumai Misbahu M. Ahmad da Hajiya Rukayya Umar Santa ya soma ne kamar wasa, ko ma a ce wasan, to amma yanzu ya zama babbar magana, domin kuwa bayan Sallah ne za a daura masu aure!

Rukayya, yarinyar bangon mujallar Fim ta watan Nuwamba 2001, ta yi matukar mamaki da ta ji Misbahu ya gaya mata cewa shi fa sonta yake yi da aure. Ba ta taba tunanin cewa farat-farat din da yake yi mata za ta rikide ta zama soyayya ba. To amma da yake a maganar aure babu wasa, nan da nan ta gane cewa shi fa lallai da gaske yake yi, saboda haka ba ta wani bata lokaci ba ta saduda, ta bada kai bori ya h au. A takaice, ta amince da bukatarsa har ta garzaya ta sanar da iyayenta abin da ake ciki.

Ba Rukayya ce kadai ta yi mamakin jin wannan magana ba. A fagen shirin fim, 'yan wasa sun rika tambayar junansu, "Wai ashe Misbahu ne zai auri Rukayya Dawayya?" Amsar ita ce, "Ni ma haka na ji." Wannan maganar ta karfafa bayan sabuwar mujallar Tauraruwa ta buga wani shagube a kan al'amarin a tsakiyar watan jiya.

To, yanzu dai ta tabbata cewa lallai 'yan wasan biyu, wadanda su ne jaruman shirin Dawayya inda Rukayya ta samo lakabinta, suna nan suna shirin bikinsu da za a yin nan da wata daya ko biyu.

Wani abin juyayi a kan wannan al'amari shi ne rawar da wasu finafinai biyu da wakokin da ke cikinsu suka taka a kan maganar auren da ta taso. Na farko shi ne fim din Dawayya. A fim din, Misbahu da Rukayya suke jaruman shirin, inda suka fara fitowa a matsayin masoyan juna. Wata waka da Misbahu ya rubuta a fim din mai suna "Ahayye Dawo Dawayya" ta taimaka wa Rukayya wajen yin fice a fagen shirin fim. Idan ka sake sauraron wakar a yanzu, za ka tsinci kalamai wadanda ke nuni da abin da ya faru a zahiri bayan fitowar fim din da kuma wanda yake faruwa a zahiri a yau. A shirin Dawayya, Misbahu ya yi soyayya da Balaraba Mohammed ne, amma a karshe Rukayya ce ta zama matarsa. To a zahiri ma Misbahu ya yi soyayya da Balaraba kafin ta fara yin soyayya da Shu'aibu Lawan, wanda ta aura daga bisani kuma Allah ya yi mata rasuwa a hadarin mota a bana.

Fim na biyu shi ne Kansakali, wanda shi Misbahu ya dauki nauyin shiryawa, wanda kuma zai fito kwanan nan. A fim din, ne aka yi wakar "Sangandali" inda Misbahu ya rera waka da kalamai wadanda idan ka yi nazarinsu za ka ga sun jibinci gaskiyar abin da ke faruwa a tsakaninsa da Rukayya a zahiri a yau.

Shin Misbahu ne ya tsara dukwannan abu da niyyar wata rana ya bullo ba zato ba tsammani ya nemi auren Rukayya? Ko kadan! Domin a lokacin da duk aka yi Dawayya da Kansali, zuciyar jarumin tana can wurin 'yan mata daban-daban wadanda ya nema da nufin ya aure su. Daya na Kano, daya a Gusau, daya a Kaduna… Sam, Rukayya ba ta cikinsu. Gaba daya yanzu kimanin wata hudu tun lokacin da ya gaya mata cewa yana son ta ita kuma ta amsa. Don haka dai Allah ne ya tsara wannan abu, kuma abin farin ciki ne wanda ya dace kowa ya goyi bayansa.

Mujallar Fim ta waiwayi wadannan masoyan biyu daya bayan daya domin jin yadda soyayyar tasu ta fara da kuma inda ta dosa. Sun yi bayanin farkon soyayyar tasu, da ra'ayin iyayensu kan batun, musamman kuma da yadda 'yan tsurkun industiri wadanda ba sa ganin zarau sai sun tsunka suka shigo cikin al'amarin suna son su bata ruwa ba don su sha ba. Ra'ayi dai ya daidaita tsakanin Misbahu da Rukayyarsa cewa soke-soke da gulmace-gulmacen da ake yi kan batun aurensu ba za su hana su yin auren ba. Wato dai bakin alkalami ya bushe. Ga abubuwan da suka gaya mani kwanan nan a Kano: Soke-soke ba za su hana mu yin auren nan ba -Misbahu

FIM: Akwai wata ji-ta-ji-ta da aka baza kwanan nan cewa wai kana neman auren Rukayya Umar Santa (Dawayya). Shin da gaske ne?

MISBAHU: Salamu alaikum, wannan magana da ake fada, gaskiya haka ne, akwai maganar aure tsakanina da ita. A halin yanzu a kan maganar muke. Sai dai kawai mun bar wa Allah zabi, ya zaba mana abin da ya fi alheri. Amma mu kanmu mun fahimci juna.

FIM: Kun dade kuna soyayya ne kafin maganar ta karfafa ta zama ta aure ko kawai kwanan nan ne maganar auren ta shigo?

MISBAHU: Ita maganar auren kwanan na ta shigo, amma magana ta soyayya haka ta dan dade tsakaninmu, wadda ta zama kamar ma ta 'yan'uwantaka ko abokantaka. Duk wani abu da za ka tambaya nata za ta ce ka same ni ko wani abu da za ka neme ni ko kana son adires za ka ga na kawo ta. Amma maganar auren, dududu ba ta fi wata biyu ba.

FIM: Fim dinku na Dawayya shi aka fi saurin tunawa a matsayin shirin da kuka fito tare a matsayin masoya. Shin za a iya cewa fim din ne ginshikin soyayyar da ta kullu a tsakaninku ko kuwa akwai soyayyar tun ma kafin a yi fim din?

MISBAHU: Wannan fim din ba shi ne ya sa na fara ganinta ba. Na san ta dai haka muna gaisawa, amma wannan fim din da shi muka san juna haka tunda mun je lokeshin tare, kowa ya san kowa. Kuma bayan wannan sai muka zama ana samun wasu 'yan finafinai mukai ta yi, kamar irin su Amalala; in zan yi fim in gayyace ta. Sai muka zama mun shaku. Amma Dawayya dai shi ne makasudin da ya sa muka shaku da ita sosai.

FIM: An ce a da can akwai wata 'yar wasa da ka so ka aura amma sai Allah bai yi ba, kuma kawar Rukayya ce. An yi haka?

MISBAHU: To ai ban san wadda kake nufi ba.

FIM: Marigayiya Balaraba.

MISBAHU: Gaskiya mun zauna da Balaraba, amma a lokacin ba mu yi magana ta aure irin wannan ba yanda ake nufi. Kawai dai akwai 'yar soyayya haka tsakanina da ita. Amma farko ta zauna a karkashina haka. Bayan kuma Allah ya sa abin namu bai dade ba sai ta bar wajen ta koma suna tare da Shu'aibu. To a daidai wannan lokacin ne kuma muka yi sabo da Rukayya.

FIM: Ita wannan maganar aure da ake ciki, yaya zurfinta yake? Shin ta kai ga iyaye ko kuma ba ta kai ba tukuna?

MISBAHU: Iyayenta sun sani, ni ma kuma iyayena sun sani. Amma a halin yanzu iyayenmu ba su zauna sun yanke sun ce ga ranar da za a daura auren ba. Amma ni da ita mun so mu je kowa ya huro wutarsa a zo a yi abin kafin azumi. To, da muka yi shawara, saboda wasu 'yan dalilai, da ayyuka da suka yi yawa, shi ne sai muka ce to mu daga mu maida shi bayan Sallah. To a yanzu mun kai shi bayan Sallah. Amma ka san komai na Allah ne; ba mamaki ko da mun sa ranar ko ba wannan ne lokacin ba-in ma Allah ya kaddara abin za a yi shi.

FIM: Menene ra'ayin iyayenku a kan wannan maganar?

MISBAHU: Ai ita ta gaya wa iyayenta kowa ya goyi bayanta; ni ma na gaya wa iyayena sun amince. Ni ka san namiji ne, ita ce da ma in za a sami matsala za a samu daga wajenta. Ni ka ga ba zan samu matsala ba domin harkarmu daya da ita: ni dan fim ne, ita 'yar fim ce. Da kamar a ce ba ta fim ne ko ni ne ba na fim shi ne za a ce za a samu matsala. Kamar yadda wasu iyayen da ba su fahimce mu ba, sai ka ga idan ka je neman 'yarsu wasu sai ka shafe watanni ko shekaru ma kana neman auren, an san fa kai dan fim ne, amma sai daga baya ka ji wasu kananan maganganu, ana hure mata kunne "dan fim ne, kaza kaza…" In ma mai raunin zuciya ce sai ka ga an raba ta da kai. Karshe sai ka ga abin ya watse. To amma ni tunda harkarmu daya da ita (fim), ka ga babu wata matsala. Idan iyayenta ko nawa suka ce ba za mu auri juna ba, ka ga ba su nuna fahimta ba, domin da me muke ci da me muke sha in ba ta hanyar fim ba?

FIM: Ko kun samu soke-soke daga wajen jama'a a kan wannan niyya taku?

MISBAHU: E, kwarai. Ka san dole za a samu. Duk abin da ake ganin akwai alkhairi a ciki in Allah ya sa abu ne mai kyau za ka yi shi, musamman duk abin da ka ce za ka yi shi kamar jihadi, za ka yi abin don Allah, ka sa abin nan a ranka, to sai ka dinga ganin Allah yana kawo maka jaraba iri-iri. Wannan ya zo ya ce kaza, wannan ya yi suka, wannan ya ce kada ka yi, wani ya kawo sukarta ya ce ta yi kaza ko ta ce kaza, ni ma a kai mata sukata na yi kaza ko na ce kaza… haka za ai ta yi. To in Allah ya taimake mu muna ta tsallakewa, addu'a dai muna ta yi, sai a zo ayi auren komai ya wuce. Shi ya sa ake cewa ko me za ka yi, ka bar wa Allah zabi, Allah ya zabar maka mafi alheri. Amma dai muna samun wadannan 'yan soke-soken. Ko da ma ba 'yan fim ba ne mu sai ka ga (irin) wadannan soke-soken.

FIM: A matsayinka na daya daga cikin 'yan wasa masu farin jini, mun san akwai 'ynmata da dama da suke son a ce su ka aura. To idan suka ji wannan maganar, zuciyarsu za ta karye. To me kake son ka gaya masu a yanzu?

MISBAHU: To, hakuri zan ba su. Ka ga ni a industiri ba ni da budurwa wacce za ta ce na yi magana da ita na ce zan aure ta. To amma yawancinsu ba harkar fim nake yi da su ba, yara ne haka wadanda suke gidansu. To irin wadannan ba wadda na ce ga-da-ga zan aure ta. Idan akwai ta, ba za wuce mace daya ba, to ita ma ban yanke huldata da ita ba, ban ce mata ba zan aure ta ba har yanzu, sai dai na kawo mata wasu dalilai. Da kanta ta bude bakinta ta ce lallai abin da na yi ya yi daidai kuma ta goyi baya.

FIM: To su sauran maza masoyan Rukayya fa? Yanzu ka kasa su kenan daga fitowarka, ba ko wahala?

MISBAHU: E, to, idan Allah ya kaddara abin ya yiwu, sai a ce an kasa su kenan. Amma ka san matar mutum kabarinsa. Kamar ni ne, ni ma wadanda na bari din kowace na ba ta dalili. Ka san yawancin abokaina sun yi aure. Ni ma kuma ina son in yi auren nan. Kuma duk 'yanmatan da nake tare da su, daga wacce za tai shekara biyu sai wacce za ta yi shekara uku tana makaranta (nan gaba). Wasu na bincike su na ji babu yadda za a yi iyayensu su fitar da su daga makarantar, ni kuma iyayena sun nuna min kawai sun fi son in yi aure. Ka ga yanzu na zauna shekara uku ina jiran mace, wacce ba ni da garanti a kanta? Rashin garanti shi ne abin da na gaya maka din nan; ka yi ta wahala kana jira, amma a karshe sai a zo a ce maka kai dan fim ne ba za a ba ka ba. Sai ka ga ko da an zo an yi auren ma, babu wata kyakkyawar alaka tsakaninka da su (iyayenta), sai ka ga ana yi wa juna kallon-kallo. Ni an matsa mani in yi aure nan da wata shidako shekara daya. To da yake an ce namiji mijin mace hudu ne, idan Allah ya sa zan auri daya daga cikinsu (wadanda zan bari in auri Rukayya) sai ka ga na aure ta a can gaba.

FIM: A yanzu dai lokaci ya karato sosai sosai a kan wannan aure. To yanzu ka fara sayen kaya ko kuwa har ka gama cika akwatunanka?

MISBAHU (dariya): To ai wannan kuma sirri ne. Amma duk (makaho) wanda ka ji ya ce a yi wasan jifa, ai ya taka dutse ne. Amma shi aure ai duk wadannan abubuwan wasu suna cewa ba a cika yi ba. To amma dai komai yana tafiya yadda ake so.

FIM: Wane irin shagali ne za mu sa ran mu gani a bikinka da Rukayya, musamman tunda ku fitattun jarumai ne?

MISBAHU: To, yanzu haka abin da ya shafi biki, ba mu san… Muna dai yi daidai gwargwado, muna tsattsara wasu abubuwan wadanda in an zo wajen bikin za a iya amfani da su.

FIM: Amma dai ai za ku girgiza kasar nan da bikin, ko?

MISBAHU (dariya): Haba, wane girgiza kasa? Kai dai Allah ya taimake mu. An yi na manya-manyan ma, duk ga shi nan…, to balle mu kanana!

FIM: Malam Misabahu, Allah ya sa alheri cikin wannan abu kuma ya nuna mana lokacin.

MISBAHU: To amin.

Shawarar da babata ta ba ni a kan aurena da Misbahu -Rukayya

RUKAYYA DAWAYYA ta yi mana bayani kan yadda ta ji a daidai lokacin da Misbahu ya fitar da 'maitarsa' a fili, da yadda mahaifiyarta, wadda ta dade tana zaune a Jidda cikin kasar Saudi Arebiya, ta karbi labarin zuwan auren, da kuma ra'ayinta kan mutane 'yan tsurku:

Fim: Yanzu dai Rukayya ta tabbata cewa akwai maganar aure tsakaninki da Misbahu. Ko za ki fada mana daidai lokacin da kika fahimci cewa yana son ki da aure?

RUKAYYA: Assalamu alaikum! Ni dai ban fahimci cewa Misbahu yana sona da aure ba, kwata-kwata bai fi wata uku zuwa hudu na fahimta ba. Kuma ni ban ma fahimta ba duk da irin abubuwan da yake min da sauransu, sai da ya furta min cewa yana so ya aure ni. Amma ni ban taba kawowa a zuciyata ba.

Fim: Amma da ma can ya yi wasu halaye da ke nuna cewa yana son ki?

RUKAYYA: A gaskiya da can ina friending (abota) da Misbahu amma ba ta soyayya ba. Saboda wani lokaci ina tare da shi zan ce, "Zan tafi gida saboda saurayina zai zo…," ko wani abu. To ka gani da na dauke shi saurayi ai da ba zan fada masa haka ba. Na dauke shi kamar dan'uwana saboda idan wasu matsalolina suka tashi zan je in kai masa shawara ya gaya min abin da ya dace.

Fim: To lokacin da ya furta maganar cewa yana son ki da aure, ya kika ji abin? Ya ba ki mamaki?

RUKAYYA: Gaskiya ya ba ni mamaki (kuma) bai ba ni mamaki ba. Abin da kuma ya sa bai ba ni mamaki ba, saboda ni mace ce. Yarinya ce budurwa, kowa zai iya cewa zai aure ni ba tare da na yi mamaki ba. Abin da kuma ya ba ni mamaki, saboda yadda nake da shi, ban taba tunanin irin… don yadda nake da ke da shi ban taba fuskantar wani abu wanda ya shafi soyayya mai karfi ba tsakanina da shi, sai direct (kai tsaye) na ji ya kawo min maganar aure. To shi ne sai abin ya ba ni mamaki. Ashe da ma can abubuwan da yake min sona yake sai yanzu ne da ta kai bango ya fito ya furta!?

Fim: Ko shigowarsa ya dagula maki lissafi domin na san ba za ki rasa wasu maneman ba?

RUKAYYA: A gaskiya ni kafin Misbahu akwai wadanda suka zo min da maganar aure, wanda har maganar ta je ga iyaye. To sai suka fahimci kamar ban dauki abin da gaske ba, kamar harkar fim ce a gabana, sai suka fara ja da baya. Ina nan da su sai na ji maganar Misbahu ta aure. Sai kawai na ji ya canza min ra'ayi, domin a gaskiya ni a tsarina wallahi ban da niyyar yin aure nan da shekara daya ma. Sai nan da shekara biyu ko uku! (dariya) Saboda ni a tsarina, zan ta fi Saudiyya. To idan na tafi zan je in zauna wurin mamata, sai na huta na yi kamar two years (shekara biyu) tukuna sannan ina dawowa sai in yi aure.

Fim: To yanzu duk wannan tsarin ya canza kenan?

RUKAYYA: E to, kawai ni da na yi wa Hajiya (mahaifiyata) waya na gaya mata, farko abin da ta ce min shi ne in ajiye komai gefe daya na sa maganar aure a gabana, in rike ta ita ce mafi muhimmanci tare da ni, tunda kuma ga shi dan fim ne. (Ta ce) shin ya ga hankalina ne ko menene (ya sa) ya ce har zai aure ni? To ni me ya sa ba zan aure shi ba? Ba wani suka da za a kawo mani game da ni wanda bai san ta ba, (tunda) dan fim ne dan'uwana.

Fim: Yanzu dai za a iya cewa hankalinki ya kwanta a kan Misbahu kenan, kowa ya ja baya?

RUKAYYA: (dariya) Ni yanzu alhamdu lillahi Misbahu shi ne saurayina da ya fito, iyayena sun san da maganarsa. Kuma duniya tana neman ta san wannan maganar aure tsakanina da Misbahu. Tunda dai ban daura aure da Misbahu ba, ba zan ce samarina su daina zuwa ba, amma dai kowa ya fuskanta ga inda na sa gaba, kuma ya ji cewar dan fim ne ya fito zai aure ni, to in shi ba dan fim ba ne sai ya janye jikinsa ya ce masu da ma 'yan fim ya mu-ya-mu muke aure. Ba ma sai an ce su tafi ba, su da kansu yanayina da suke gani suka kuma ji cewa magana ta yi karfi, sai su janye jikinsu (dariya).

Fim: Ya batun 'yan tsurku? An ce duk wata maganar aure idan ta taso sai an rika jin gulmace-gulmace da soke-soke.

RUKAYYA: Tun lokacin da maganata da Misbahu ta fara fitowa, ta wuce ni da shi ta koma ga abokai, sai na ji abu daban. Saboda ka san magana idan za ta yi albarka, kuma magana irin ta aure, dole ne sai ka samu 'yan tsurku. Ko mata ko maza, suna kawo min tsegumi game da Misbahu - (suna cewa) to na fa natsu da Misbahu saboda bai da kirki, menene? Mayaudari ne, da sauransu. To ni wanda ya fada min haka nan take nakan ba shi amsa cewa ni ban tabbatar da mayaudari ba ne tunda bai yi min ba, a bari sai ya yi min sai in yarda. Amma ni tunda bai yi min ba, ba zan taba cewa mayaudari ba ne. Haka nake maida masu bakaken maganganu. Amma suka dai, kawai toshe kunnuwana nake yi a kan abin da ake fada min, in mayar ba komai ba ne, don ni dai na san abin da ke tsakani a da shi, kowa ya je ya yi ta fadar abin da zai fada.

Fim: Shi ya gaya maki cewa ana kai sukarki ke ma a wurinsa?

RUKAYYA: Ni ba sai ma ya gaya min ba ballantana ma na sani, yana kuma gaya min. Duk wanda ya je ya kai mai zuga, to insha Allahu mutumin yana tafiya zai bugo min waya ya gaya min cewa wane ya ce masa kaza da kaza a kaina; ko ya yi min waya ya ce in zo ko ya je gidanmu ya fada min, "Amma ban ce ki nuna masu wani abu ba, kawai ke dai ki san irin yadda za ki zauna da su."

Fim: Wane kira za ki yi ga kawaye ko abokai wadanda ke irin wannan halayya ta idan suka ga za a yi aure sai su yi ruwa su yi tsaki su ce kada a yi - wai ba a dace da juna ba?

RUKAYYA: A gaskiya kiran da zan yi masu shi ne su natsu su san cewa ita fa magana ta aure ba magana ce ta banza ba. Magana ce ta gaskiya kuma sunna ce ta Annabi (s.a.w.). Ko da mutum yana wani abu, idan ka ga zai yi aure, to kada ka sake ka kai sukarsa wurin wannan wanda zai aure shi. Saboda idan mutum bai kai zuciyarsa nesa ba aka fada masa wani abin, zai iya cewa ya fasa wannan aure. To ka gani sun bata sunna, suna da alhaki, kuma su ma Allah zai iya saka wa mutum. To, ko me mutum zai fada ya fadi alhairi. Idan suka raya aure Allah zai ba su lada.

Fim: Yanzu wadanne shirye-shirye kike yi a kan batun auren? Kin fara hada kayan daki?

RUKAYYA: Ai na fada maka: a da ni ba ni da shirin yin aure nan da shekara ko biyu ma, sai da Misbahu ya kunno kai. Kuma ko da maganar ta taso, da na aika wa mahaifiyata sai ta ce shikenan addu'ar da take yi min ce, ta fada. Kuma in kara ci gaba da addu'a Allah ya zaba mani mafi alheri. Sai da wannan abu fa ya fara shiga raina (sannan) na fara shirin aure. Amma kuma ni har gobe ina nan ina ci gaba (dariya).

Fim: Kina ganin akwai isasshen lokaci ko kuwa za ki nemi a dan kara maki lokaci?

RUKAYYA: Insha Allahu nan da wata biyu na gama shiri.

Fim: Kina da kudi kenan?

RUKAYYA: (dariya) Shekarata nawa ina fim? Alhamdu lillahi mun nema mun samu. Da taimakon iyayenmu za mu je gidan mazajenmu, mu zauna mu yi zamanmu.

To Rukayya muna yi maki fatam alheri, kuma Allah ya nuna mana wannan lokaci.

RUKAYYA: To amin. Na gode, Allah ya saka da alheri.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin