A BISA dukkan alamu masu kallo za su daina ganin finafinan da kamfanin 'Home Alone Production' ke shiryawa. Dalili kuwa shi ne tun lokacin da furodusa kuma shugaban kamfanin, Hamza Mohammed Danzaki, ya auri jaruma Abida Mohammed, sai ya dauke kafarsa daf daga harkar fim. A yanzu haka ofishin a rufe yake kuma ya shafe watanni a garkame da kwado.
Ganin cewa an daina gani da jin duriyar Hamza, mutane a fagen shirin fim na Kano (Kallywood), suna ta fadar albarkacin bakinsu. Wasu na cewa Hamza ya karye daf da-da kuma bayan-aurensa da Jarumar Jarumai Mata, wato Abida; wai karyewar kasuwar finafinai ce ta shafe shi. Wani kuma ya ce, "Babban burin Hamza shi ne ya auri wata fitacciyar 'yar wasa. To, da ya samu Abida ya like mata ya ga bayan sauran manemanta ya aure ta, shikenan muradinsa ya biya. Wato ya gama yagar rabonsa a industiri kenan."
Mujallar Fim ta nemi jin ta bakin wasu na jingine da kamfanin, musamman bayan ta yi farautar Hamza amma ya ki ganuwa. Wani wanda da shi ne aka yi hidimar bikin Hamza da Abida ya tabbatar mana da cewa ko shakka babu Hamza ya daina harkar fim. "Domin ni kaina rabon da in sa shi a ido an kai wata uku," inji shi. Ya kara da cewa tun da aka gama shagalin biki, sau uku kacal ya sa furodusan a ido.
Da aka tambaye shi inda yake jin Hamza yake, sai abokin nasa ya ce, "An ce min ana ganinsa a 'NNPC Depot' (wurin manyan 'yan cuwa-cuwar man fetur), amma ni dai ban gan shi a can din ba". A karshe majiyar tamu cewa ta yi masu a garinsu Danzaki cikin Jihar Kano.
Wannan mujallar ta ji daga bakin wasu frodusoshin cewa lallai an rufe 'Home Alone'. "Fadi da kari. Wannan shekara ba su biya kudin haya ba, ka ga kuwa tashi za su yi kenan," inji wani.
Akwai alamun da suka bayyana haka. A duk lokacin da wakilinmu ya bi ta gefen ofishin, wanda ke kan Sabon Titi, Tal'udu, dare da rana duk a rufe yake; a da kuwa ofishin ya kan kai karfe 11 na dare a bude, ana hada-hadar sayar da kaset. Yanzu kuwa wata mace ce take dafa abinci tana sayarwa a bakin kofar ofishin.
Amma wakilinmu ya tsinci wata jita-jita da ake yadawa cewa wai furodusa darakta Rabi'u Ibrahim mai 'HRB Production' ya sayi ginin ofishin. Da Fim ta tuntubi Rabiu, sai ya rantse ya ce shi bai ma san maganar ba.
Ko ma dai ya abin yake, babban abin da zai kara sanya wa jama'a su yi tunanin 'Home Alone' ya tashi daga aiki shi ne barin Adamu Sani daga wurin. Adamu, wanda amini ne kuma abokin harkar Hamza, yanzu an fi yawan ganinsa tare da wani furodusa mai suna Sharu wanda ya fitar da fim din Qauli kwanan nan. Da ma can baya akwai masu cewa wai wasu finafinan da kamfanin 'Home Alone' ya shirya, na Adamu ne ba Hamza ba a ciki.
Adamu Sani matashi ne dan fim amma bai taba fitowa a cikin kowane fim ba. Furodusa ne. Duk wanda ya ya san shi, a kamfanin 'Home Alone' ya san shi tare da Hamza. Haka kuma Adamu ne mataimakin jami'in hulda da jama'a na Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano.
Cikin wata 'yar tattaunawa da wakilinmu ya yi da shi, Adamu ya bayyana cewa gaskiya ne ba Hamza ne kadai wuka da nama a 'Home Alone ba', shi ma yana da gado a ciki. Ya kuma fadi dalilan da suka sa 'Home Alone' ya tashi daga aiki da kuma inda abokinsa ya makale har 'yan fim ba su ganinsa. Ga hirar:
Fim : Me 'Home Alone Production' ke ciki?An daina ganin Hamza tun daga lokacin da ya auri Abida.
ADAMU: Har yanzu kamfanin 'Home Alone' yana nan, kuma yana yin fim, don yanzu muna da fim wanda muke yi da darakta Isahq, sunansa Siyasa, amma ba mu karasa shi ba.
To kai wanene a cikin 'Home Alone'?
ADAMU: Ni furodusa ne, Hamza abokin business dina ne. Hadin gwiwa muka yi ni da shi muka kafa 'Home Alone' a cikin 1999.
Wadanne finafinai ka yi a matsayinka na furodusa?
ADAMU: Na yi Nadama, Ajizi, Zahiri sai kuma yanzu da na ke yin Siyasa.
Amma kuma kowa ya dauka cewa Hamza ne furodusan Nadama, Ajizi da Zahiri.
ADAMU: Shi Hamza babban frodusa ne, wato 'executive producer'.
Daga cikin wadannnan finafinai uku, akwai wanda Hamza ya yi shi kadai da kudinsa?
ADAMU: Duk babu wanda babu kudina a cikinsa, duk cikinsu na zuba kudina a ciki.
To ana ganin kofafin 'Home Alone' a rufe, shi ya sa ake cewa an rufe kamfanin.
ADAMU: E, kamfanin 'Home Alone' zan ce ba ya daina shirya finafinai ba ne tunda ko yanzu ya yi sabo cikin azumi. Don an rufe ofishin ba za a ce an daina ba.
Kai ka tsaya kai da fata cewa 'Home Alone' yana nan, amma kuma kullum a rufe yake kuma an daina ganin Hamza.
ADAMU: Ai 'Home Alone' ya dawo nan kan titin gidan zoo tunda furodusanta (Adamu Sani) ya dawo nan kan titin na 'Zoo Road'. Ina so ka fahimta cewa kamfanin ya daina yin harkoki ne a Sabon Titi ne saboda irin halin da muke tafiyar da ofishin. Kaset ne ake sayarwa a ciki don a ci riba, amma sai aka wayi gari sai mutum ya rika zuwa yana dauka don yana ganin shi na kusa da kai ne, ya fi karfin abin, ba ya biyan kudi. To sai muka hakura da saida kaset da kuma wurin baki daya.
Yaya sunan wannan wurin da ka dawo?
ADAMU: A cikin sati da ya wuce muka bude shi. Sunan wurin 'Hazzi Business Centre', tare da Jamilu Dakan-Daka.
Akwai hannun Hamza a cikin Hazzi?
ADAMU: A'a, babu shi a cikin wannan sabon wurin.
Amma dai ana cewa ya daina fim ko?
Adamu: Karya ne. Duk wani wanda zi ba da labarin Hamza, to bayan ni ne. Tare muka shigo harkar fim. Ita sana'ar mai da Hamza ke yi ai da ma yana ciki. Ita iyayenmu ke yi. Da abin da muke samu ne wajen mai muke yin fim.
Ganin an daina ganin Hamza kuma kamfanin 'Home Alone' na rufe, sai wasu ke cewa yanzu ka hada gwiwa da Baba Sharu. Haka ne?
ADAMU: Wannan wautar mutane ce; tuni muke tare da Baba, idan an gan ni tare da Baba Sharu ba za a ce na bar Hamza ya bar fim to idan an daina ganin mutum sai a tuntubi wanda ke kusa da shi a ji dalili. Hamza ba guduwa ya yi ba, bai ci kudin kowa ba kuma bai yi fada da kowa ba. Sai dai kawai duk wanda ya yi aure zai so ya samu karin wurin bubbuga harkokinsa-saboda ka san harkar iyali.
Shi wannan sabon wuri da kuka bude wanda babu hannun Hamza a ciki, menene banbancinsa da 'Home Alone'?
ADAMU: 'Hazzi Business Centre' ba wurin yin fim ba ne, harkar komfuta na zane-zane (graphics) da buga ayyuka (typesetting) da sauransu, ita muke yi; shi ne bambancinsa da 'Home Alone'
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin