Rukayya Dawayya ta halarci bikin Misbahu, tare da yi musu addu'ar fatan alheri
LOKACIN da labarin bikin Misbahu ya bullo, mutane da dama sun zuba ido, kuma sun kasa kunne, su ji me fitacciyar jaruma RUKAYYA UMAR SANTA (DAWAYYA), wadda Misbahu ta taba nema da aure amma Allah bai yi ba, za ta yi ko za ta ce. Wasu suna zaton za ta dora kai a gwiwa ne ta yi ta rusa kuka kawai; wasu kuma na ganin ai tunda yarinya ce mai karfin hali, da wuya ne abin ya dame ta. To, wata majiya ta shaida wa Fim cewa labarin ya dan dami Rukayya din, kamar yadda zai iya damun kowace budurwa da saurayinta ya yi aure ya bar ta, to amma sai ta yi tawakkali, ta bar wa Allah komai. Da wata kawarta ta yi mata zancen ma, cewa Rukayya ta yi, "To me zan ce? Ai an ce matar mutum kabarinsa. Don haka ni ba na yin bakin ciki. Ita (Zainab) ce Allah ya kadarto zai aura. Wallahi ba na jin haushi."
Wannan matsayin da Rukayya ta dauka ya burge mutane da dama. To amma kuma ya ba wasu haushi. Wasu suna ganin bai kamata Rukayya ta ki jin haushi ba, domin ganin yadda ba kunya ba tsoro ya bata ta a mujalla, ya yi mata kazafin da bai da hujja a kanta a Musulunce. Lokacin da wata kawar Rukayya ta sami labarin cewa wai jarumar ta shirin Dawayya za ta halarci shagali auren, ce mata ta yi kada ta je. Da Rukayya ta je din, sai kawar tata ta nuna mata ba ta ji dadi ba, har ta yi barazanar za ta yanke huldar da ke tsakaninsu. Tana cewa Rukayya ta fa lura, hatta rigi-rigin bikin da Misbahu da abokansa suka shirya, sun yi shi ne don su ba Rukayya haushi, su nuna mata cewa ba fa karamin rashi ta yi ba da ba ta auri Misbahu ba. Da kyar Rukayya da kawar tata suka sasanta.
Ita kuwa Rukayya, tana da hujjarta ta halartar auren Misbahu. A wurin shagalin bikin ne suka kebe da wakilinmu SANI MOHAMMED MAIKATANGA, suka tattauna kan abin da suke ganin mutane za su so su ji daga Rukayya game da wannan aure na Misbahu. Ga yadda hirar ta kasance:
FIM: Malama Rukayya, kwana biyu, ko ina kika shiga?
RUKAYYA (tnaa murmushi) Wallahi ina nan. Na bar masu kaunata su huta ne su ma da jin bakaken magangamu a kaina, saboda ka san yanayin rayuwar, wani lokacin a zauna ne a ji dadi, wani lokacin a sha wahala.
FIM: Ga shi kin halarci bikin Misbahu da Zainab. Ko yaya suka karbe ki?
RUKAYYA: Alhamdu lillahi. Sun karbe ni hannu biyu-biyu kamar yadda ake karbar kowa da kowa. Na je biki saboda ina daya daga cikin wadanda aka gayyata domin ni ma na taya su murna, kuma kowa ya sani
FIM: Ko me ya hana ki zuwa wajen luncheon din, wanda shi ne aka fara a cikin shagulgulan?
RUKAYYA: Wallahi lokacin da aka yi ban sani ba, kuma da ma ba a buga katin gayyata ba. Kuma ma ba na garin; ina can (wani wuri). Da na ji gaskiya ban ji dadi ba, amma kuma sai na dawo na halarci wajen picnic da kuma pati.
FIM: Mutane sun lura cewa lokacin da kike yi wa Misbahu liki ya sunkunyar da kansa kasa, har kika gama bai kalle ki ba. Ba kya ganin wannan wata alama ce ta nuna har yanzu yana sonki? Kina ganin in ya dawo za ki amince ku koma kamar da?
RUKAYYA: Ni duk ban fuskanci wai ko yana kallona ko ba ya kallona ba, domin ni harkar gabana nake yi. Kuma maganar wani magana, kawai ka yi keeping dinshi aside. Allah ya ba ni miji nagari kamar yadda Allah ya ba shi mata, kuma Allah ya ba su zaman lafiya.
FIM: Kina ganin in ya nuna a koma kama da ba za ki koma ba kenan?
RUKAYYA: Ni ba na so ka rika dawo da hannun agogo baya, ka yi keeping din wannan maganr aside, ni na manta da na taba soyayya da shi tunda ya yi aure. Allah ya ba shi zaman lafiya da Zainab.
FIM: Mecece shawararki ga ango da amarya?
RUKAYYA (cikin dariya da fara'a): Ubangiji Allah ya ba su zaman lafiya. Zainab da Misbahu, Allah ya ba ku zaman lafiya, mu kuma 'yan baya Allah ya ba mu mazaje nagari cikin gaggawa, kowa ya zo ya sha shagahin bikinmu, muna gayyatar kowa. Kuma yanzu ni da Zainab mun zama aminai; in har wani abu ya faru na farin ciki ko na wani abu zan je in yi musu murna; amma (fa) ni ba na zuwa gidan wadanda sukai aure ba da wani dalili ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin