Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 45   Disamba 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Mu Guji Abubuwan Zubar Da Mutunci

Inji RAHAMA ISA

Rahama
Rahma Isa

Daga AISHA ABBA AHMED a Kano

RAHAMA Isa tana daga cikin 'yan wasa da shigo harkar fim ba da dadewa ba, wadanda suke kokarin yin suna su ma a san su sosai. A industiri, an fi saninta da sunan Rahma Sirace, saboda rawar da ta taka a fim din "Sirace" na kamfanin Sarauniya Films. Makasudin hirarmu da ita shi ne don mu zanta game da halayyar 'yan matan fim da suka yi fice kuma suke amfani da wannan dama suke wulakanta wadanda ba su yi suna ba. Tana bai wa 'yan'uwanta shawara da su yi koyi da 'yan fim kamar su Fati Mohammed, Abida da marigayiya Balaraba wadda har ta koma ga Ubangiji ana yabonta. Ta ce, "Mu yi koyi da irin wadannnan halayen domin kowa ya karbe mu hannu biyu-biyu, shi ne mutuncinmu, shi ne darajarmu. Wasu matan idan sun karbu sai su rika tinkaho wanda babu kyau".

Rahma ta ambato kawarta ta farko a industiri, wato Rukayya Umar Santa, bisa burge ta da ta yi lokacin auren tsohon saurayinta Misbahu M. Ahmed da har ta boye kishinta na 'ya mace ta halarci bikin kuma har ta yi rawa a ranar dina. Ta yi addu'ar Allah ya bai wa Rukayya miji nagari mai kaunarta. Da Fim ta tambaye ta dangantakarta da Rukayya din, musamman farkon haduwarsu, sai ta ce, "Mun hadu ne lokacin da muka je daukar shirin "Mu Shakata 2" na Mandawari inda aka raba mana wakokin da za mu yi. To a nan muka shaku da ita har ta ba ni labarin farkon zuwanta kuma ta ce min Saima Mohammed ce uwardakinta wacce ta kawo ta gurin Mandawari. Aminu Hassan Yakasai ma Allah ya jikansa ya taimaka wajen dada dangantakarmu da ita domin muna haduwa a ofishinsa. Na san 'yan'uwanta da dama don har idan mun je mitin ba mu dawo da wuri ba muna kwana a gidan yayarta a nan 'Brigade'. Saboda haka ba don ta zama 'star' nake bin ta ba, a'a mun shaku ne tun kafin ta zama wani abu. Kuma duk 'yan fim babu wacce za ta nuna min sanin Rukayya, domin ko Hawwa Ali Dodo tare da Rukayya din muka je gidanta a Tukuntawa domin mu gan ta, har muke cewa 'yan fim suna da farin jini mu ma Allah ya nuna mana namu."

Game da shirin fim, Rahma ta ce sai dai hamdala duk da dai ba ta zama wani abu ba. Ta tabo finafinan da ta fito a cikinsu wadanda wasunsu ma ba su fito ba takuna. Fim din da ya fito da ita har ake mata inkiya da shi shi ne "Sirace", wanda ta ce dalilinsa ta je har garin Mambila gurin da ba ta taba tunanin zuwa ba. Wasu finafinan nata kuma da suka fito su ne "Harsashi" da "Jan Kunne" na kamfanin 'Two Effects Empire'. A cewarta, duk da dai "Jan Kunne" bai karbu sosai ba, amma dai ta taka rawar gani, kuma tana alfahari da "Harsashi," "Duhun Damina," "Dangantaka" da kuma "Dangana."

Ita dai Rahma mahaifinta mutumin Makarfi ne a cikin Jihar Kaduna, amma ya tashi ne a Gaya, cikin Jihar Kano, inda a nan ne ma ya yi karatunsa na firamare kuma har Allah ya hada aurensu da mahaifiyarta. Daga baya kuma aiki ya kai shi Maiduguri cikin Jihar Borno, inda aka haife ta. Ta ce an yi mata aure tana da shekara 17 kuma ta samu danta mai suna Adamu kafin Allah ya kawo rabuwarta da maigidan nata. Bayan rabuwarsu sai ta dawo Kano gurin yayarta da ke aure a Unguwa Uku inda a nan ne take ganin 'yan wasa kamar su Yautai, Hankaka, Ciroki, da sauransu. A lokacin ta shaida wa yayarta cewa tana sha'awar yin fim amma yayar ta ki yarda sam. A haka dai Rahma ta je 'Social Welfare', wato inda 'yan fim kan taru a Fagge, inda ta gan 'yan wasa da yawa kuma ta shiga kungiyar wasan kwaikwayo ta '5 Star'. Rahma ta ce finafinai kamar su "Linzami Da Wuta", "Ukuba" da "Wasila" ne suka janyo hankalinta zuwa ga harkar fim.

Ta kara yin bayani a kan rikicin da suka yi da yayarta domin a lokacin akwai wanda ya sa niyyar aurenta amma ta ce ba ta sonsa. Daga baya ta ce har sai da ta je wurin dan'uwan mahaifinta a garin Gaya ta shaida masa abin da ta ke ciki da yayarta, shi kuma ya zo ya yi wa yayar fada a kan ta kyale ta ta shiga fim. Ta fada wa Fim cewa daga baya ta je ta shaida wa iyayensu, su kuma suka ba ta kwarin gwiwar ta yi, ta kuma ce har yanzu ta kan kai musu ziyara kuma su rabu ta dadin rai. Jarumar ta gaya mana cewa sun daidaita da yayar tata bayan shirin "Sirace" ya fito inda ta kai wa yayar domin ta kalla.

Rahma ta fara fim ne a cikin 2001 da fim din "Kantafi" wanda a shi ne aka fara dora mata kyamara. Ta tuno da lokacin kamar haka: "Jikina yana ta rawa. Da har na ce ba zan iya ba sai su Hajara Dumbaru ne suka rika ba ni baki har na yi" Ta kuma fito a fim din "Shehu Jaha" a Wudil inda ta fito a matar Ibro

Game da kawarta ta farko ta ce ita ce Amina Sangaya a lokacin suna kungiya sannan kuma sai Rukayya.

Daga karshe Rahma ta kara yin kira ga 'yan'uwanta 'yan fim da su rika iyawa bakinsu idan sun tashi aure, ta ce su daina yadawa. Ta ce, "Duk abin da za mu yi mu rika yin na sirri, kar mu rika yin rashin hankali; ciki ba a yi shi don tuwo ba sai don sirrinta maganganu. Mu rage yin abubuwan da za su zubar mana da mutunci." Ta yi addu'ar Allah ya ba mu sa'a kuma ya kara daukaka su, ya kuma ba su mazajen aure.

To Rahama, mun ce amin summa amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin