Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 46   Junairu 2004
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Ali Nuhu ya janyo sabuwar muhawara?

Daga ALIYU A. GORA II a Kaduna

Ali Nuhu da A'isha
Ali Nuhu da A'sha suna cashewa a wurin piknik

Duk yarinyar da ta rasa miji, to ta zo industiri mu tallata ta ta samu, inji shi

HAKIKA, kowa ya san irin cece-ku-cen da ake yi a kan 'yan fim, musamman mata. Kusan gani ake yi duk yarinyar da ta shiga harkar fim, to sallamammiya ce daga gidansu. Da yawa 'yan fim suna ganin tsangwamar da ake yi musu kusan nema ake a dake su, tamkar su suka kirkiro duk wani iskanci da ake yi. To sai dai wani abin mamaki shi ne, duk da irin kyamar da ake yi musu, wadda har ta hada da ko aure kake nema, sai a ce ba za a ba ka ba, wai don kawai kana fim. Amma da wuya ka ga an yi bikin da yake yin armashi kamar na 'yan fim din.

To da yake kun san an ce komai da lokacinsa, da yawa na ganin yanzu yarinya idan ba fim din take yi ba, kusan babu wata hanya mafi sauki da za ta iya tallata kanta har ta samu mijin aure. Ga alama, fitaccen jarumi kuma darakta Ali Nuhu yana daya daga cikin masu irin wannan tunanin, kuma bai bar maganar a cikinsa ba, sai da ya amayar da ita a gaban dubban mutane a wajen bikin Zulai da Lilisco, wato lancin da aka yi a Kaduna a ranar Lahadi, 12 ga Disamba 2003, a 'Space 2000' da ke unguwar Barnawa.

Daga cikin bayanan da daraktan na shirin Khusufi ya yi a lokacin da aka nemi ya tofa albarkacin bakinsa, a matsayinsa na babban abokin ango, Ali ya yi alfahari da yadda 'yan fim suke aure kuma su zauna, musamman manyan 'yan wasa, wadanda wasu ke zaton ba za su dade a gidan miji ba saboda ganin irin sabon da suka yi wa kudi, ga kuma 'yancin walwala, kamar su Fati Mohammed, Maijidda Abdulkadir, Abida Mohammed, marigayiya Balaraba Mohammed, Hindatu Bashir, Rabi Mustapha, Wasila Isma'il, A'iusha Musa, A'isha Ibrahim, da dai sauransu.

Lokacin da yake tsokaci a kan al'amarin 'yan fim, musamman mata, akwai inda jarumin yake cewa, "Jama'a zan ce wani abu. Bara kamar yanzu an yi bikina, wasu sun halarta, wasu kuma kila sun yi aure. To a takaice, ina son duk wadda ba ta samu mijin aure ba, to ta shigo film industiry mu tallata ta, ta samu miji. Sannan kuma a gaskiya ba abin da za mu ce wa 'yan matan industiri, sai Allah-sambarka. Domin a da can baya, gaskiya 'yan matan da ke cikin wannan sana'a akwai wani irin kallo na kaskanci da ake yi musu cikin al'aumma. Amma alhamdu lillahi, yau Allah ya kawo rana da kuma lokaci da suka zamo abin sha'awa, wanda da zarar ance yarinya tana yin fim, to za ka ga maza suna rubibin dauke ta su kai ta gidansu."

Wannan jawabi ya yi wa wasu dadi, suna ganin lallai Ali ya wanke abokan sana'arsa, kuma a wurin da ya dace. To, sai dai kuma wasu (musamman 'yanmata da ba su shiga fim ba) suna ganin kamar ya tozarta su ne Tun daga wurin, wakilinmu ya ji mata da yawa sun fara zaginsa, suna cewa, "An gaya masa mun rasa mazan aure ne da za a ce wai sai mun shiga fim sannan a aure mu?"

Kai wasu ma ofishin mujallar Fim da ke Kaduna suka yo takakkiya suna kumfar baki.

"Ai abin duk rashin kunya ne, domin yawancin masu zagin 'yan fim din, kullum tare da su ake, idan mutum yana ganin mu 'yan iska ne, to ya kaurace mana," inji wani furodusa da ya ce a sakaya sunansa.

Ga alama, 'yan fim da dama za su yi na'am da kalamin da Ali ya yi, sabanin dariyar da suka rika yi masa lokacin da jama'ar gari suka yi masa caa a kan kalaminsa kan malaman Mass Comm. Don haka lallai za mu iya cewa yanzu 'yan fim a shirye suke su fara maida martani ga masu yin batanci a kansu. Ali Nuhu ya bude musu kofar yin hakan.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin